← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 183

Sashe 169

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali tayi sallama tare da kutsa kanta cikin falon.
Shiru babu motsin komai sai na A/C, bisa Dinning table ta ajiye tray'n kana a hankali ta juyo ta É—an tsaya tsakiyar falon.
Ido ta ɗan zubawa ƙofar ɗakinshi.
har kamar zata shiga sai kuma ta juya da nufin fita.
da sauri ta ɗan ja da baya ganinshi tsaye a gabanta ya tankwara kanshi bisa kafaɗarsa, a hankali ya ƙara matsota.
Batayi yunƙurin matsawa ba, saima idonta data ɗan lumshe.
a hankali ta buɗe idonta jin ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa a hankali yace.
"Tafiya zakiyi bazaki duba lfyata bako?".
Cikin kula tace.
"A a nayi tunanin ko kana baccine kada in shiga in tada kai".
Murmushin gefen baki yayi kana yace.
"Zo in baki saƙonki to".
"Toh". Tace mishi kana tabi bayanshi.
Har ya nufi Bedroom ɗinsa, sai ya kuma juyo a hankali ya fuskanci ƙofar nan da zata sadashi da Garden ɗin Masarautar Joɗa.
Ita dai Shatu ido ta zuba mishi tare da bin bayanshi.
Hannunshi yasa ya tura ƙofar tare da juyowa ya ɗan kalleta a hankali yace.
"Muje kiga yadda tsuntsayema ke nunawa juna kula".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Yakai rabin kular da nake nuna maka ne".
Yatsarshi yasa ya É—an lakaci tsinin hancinta tare da cewa.
"Muje dai kiga yadda sukeyi, ke zaki yanke hukuncin irin kular da kike bani".
Wani irin sassanyan numfashi suka sauƙe a tare dai-dai lokacin da suka shigo cikin filin, sanyin iskar da ƙamshi ya'yan itatuwa da kukan tsuntsaye yasasu jin wani irin masifeffen shauƙi na musamman.
Ido ta fara jujjuya tana kallon tsarin wurin da kyanshi, sai kuma ta ɗan juyo ta kalli ƙofar da suka shigo ɗin wanda bata taɓa sanin da zamanshi ba, tsawon watanni kusan bakwai da take gidan.
Cikin lumshe ido ta juyo ta kalleshi.
kanta ta ɗan manna a ƙafaɗarsa, jin haka yasa hannunshi ya ɗan shafi haɓarta, ido ya zuba mata jin tana cewa.
"Uhummm Yah Sheykh kenan".
Cikin yin sassayan numfashi yace.
"Me nayi?".
A hankali tace.
"Uhumm naga ƙofofin dake sade ɗin kane kamar basu da adadi, ashe shiyasa wasu lokutan kake ɓacewa."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ɓacewa kuma kamar wani al'jani".
Cikin sanyi tace.
"Ɗan baiwa dai, dan tabbas dai kam kana ɓacewa tunda dai a Bedroom naka dai kam naga babu wata ƙofo to amman ina gani ka shiga a take in shiga in nemaka in rasa, to gashi kuma yau dai naga wata ƙofar da ban san da itaba."
Wani irin ɓoyeyyen murmushi gefen baki yayi tare da ɗan manna mata kiss a goshinta, kana a hankali yace.
"Wato bincike kike min a É—aki".
Dai dai lokacin kuma suka iso cikin fagen da tsuntsayen suke, gyaran murya yayi a hankali ai kuwa a take sai ga tsuntsayen wurin kab sun nufoshi.
Wani irin narkekken murmushi tayi tare da ƙara manna kanta a damtsen hannunshi a hankali tace.
"Ni É—akin mijina nake bincika".
Wani irin yalwataccen murmushi yayi dai-dai lokacin kuma.
ÆŠawisun nan na tarin masarautar JoÉ—a ta iso gabanshi.
Wani irin taku yakeyi cikin rigima, ya iso garesu a hankali ya fara zagayasu.
"Wow masha Allah".
Tace dai-dai lokacin daya gama zagayasu kana ya dawo gabansu ya É—aga binÉ—insa sama ya buÉ—a fikafikinsa, ya baza a gabansu.
Wanda ya iso har kan fuskarta shi kuwa Sheykh zuwa kan ƙirjinsa.
Wani irin murmushi Sheykh yayi tare da cewa.
"Kekkyawar tsuntsa a gaban kekkyawar sarauniya, kiyi haƙuri karon farko dai na kawo miki sarauniyar data fiki kyau, sabida na halittar bani Adam amman dai a cikin tsuntsaye har gobe babu ya kai".
Wani irin juyowa tsuntsuwar tayi, ƙuntunta mai cikar blue color ya manna bisa saman rumfar sawun Shatu.
Murmushi tayi kana ta sunkuyo ta shafata tare da cewa.
"Masha Allah da kekyawar halinta".
A hankali ta juya ta fara tafiya cikin rigima.
Da sauri Shatu ta ɗago kanta ta kalli sama ganin yadda suntsaye masu masifar kyau sukayi musu ƙawanya suna kukansu mai daɗin ji.
Murmushi tayi ta kalli Sheykh dake musu kirarin zaƙin muryarsu.

Ruggumeshi tayi ta bayanshi tare da lumshe idonta lalacin daya nuna mata tattabarun daketa yiwa juna ƙoto kana suna kusantar juna.
Cikin murmushi da shauƙi yace.
"Lallai ke ta musamman ce, kalli É—awisun nan batama jira na gabatar mata da keba, to ko-dai-ko dai".
Da sauri tace.
"Ko-dai-ko-dai mefa?".
Ido ya lumshe tare da kamo hannun ta ya manna a habarshi tare da cewa.
"Kodai jinin masarautar JoÉ—a ya gauraye da nakine, wanda ba sai an gabatar da keba".
Ya ƙarashe mgnar yana sa tafin hannunshi yana shafa lafeffen cikinta".
Cikin lumshe ido tace.
"Kamar ya".
Sunkuyowa ya É—an yi bisa kunnenta ya kai bakinshi a hankali yace.
"Kamar ko mun samu ƙaruwar akwai shigar cikin Muhammad jikin Shatu".
Da sauri ta manna kanta da ƙirjinshi dai-dai lokacin kuma suka iso bakin ruwan nan inda agwagin ruwa ke cike murya can ƙasa tace.
"A a kam ba wani ƙaruwa".
Ƙara jawota jikinshi yayi tare da matseta murya can ƙasa yace.
"To muje muyi fatauci Allah yasa muyi dace da katarin ƙaruwa, mu samowa Mamey jikoki masu kama dake in ta dawo ta samu masuyi mata surutu."
Da sauri ta É—an kalleshi dai-dai lokacin kuma ya juyo da ita suka nufi hanyar komawa falonshi murya a nitse tace.
"Wacece Mamey Ina take? Yaushe zata dawo".
Cikin sanyi ya É—an kalleta a hankali yace.
"Da gaske Aish ina son haihuwa matuƙa gaya, inason inga jinina ina son samawa Mamey na jikoki".
Ya kauda zancen tambayar da tayi mishi.
Da wannan batun yana kuma mai kai hannunshi kan cikinta.
Dai-dai lokacin kuma suka shigo falon.
Meda ƙofofin yayi ya rufe kana a hankali yace.
"To muje in baki saƙonki".
Cikin nazarta zantukanshi tace. "To". daga nan suka nufi bedroom É—insa.

A hankali suka shiga bedroom É—insa,
Komai kimtse sai ƙamshi turarukanshi da suka kama ɗakin.

A hankali ya iso da ita bisa, carpet zama yayi kana itama ya ajiyeta.
Suna fuskantar juna, kwaren da ke gefen gadonshin ya jawo ya ajiyesu tsakiyarsu.

Cikin nitsuwa ya janye fefeyin saman.
ya É—aura matashi bisa cinyarta, wasu dandatsa-dandatsan al'kyabba na matan sarakuna ya fidda masu masifar kyau guda uku ya É—aura mata kan fefeyin dake bisa cinyarta.
kanshi a sunkuye yace.
"Wannan kyautar tukuicin budurci ne daga tambarin Masarautar JoÉ—a."
Ya ƙarashe mgnar yana fito da wasu takalma da linzamin dawakai biyu, ya ɗora bisa rigunan.
kanshi ya É—an É—ago ya kalleta ido cikin ido.
Idonshi ya É—an lumshe mata ganin yadda take kallon sajenshi.
cikin tsokana yace.
"Ya dai kin ƙyatsa ne?".
cike da kunya tayi murmushi tare da cewa.
"Nida abuna."
Wani yalwataccen murmushi, sai kuma ya tsareta da ido jin tana cewa.
"Ngd matuƙa Allah ya saka da al'khairi".
"Amin Amin". yace kana ya jawo ƴar ƙaramar ƙwaryar dake gefen babbar, a hankali ya buɗe hannunshi yasa ya ɗauki wata iriyar fitinenneyar sarƙar ɗanyen gol mai ɗan karen kyau da masifar sheƙi na ɗaukar idanun mutun.
da sauri ta waro idanunta woje cikin tsananin mamaki da al'ajabi take kallon sarƙar.
Shi kuwa Sheykh miƙo mata sarƙar yayi tare da cewa.
"Ga kyautar da ko wacce matar masarautar JoÉ—a ke harin ya kasance a sashinta.
sai dai banda Mamey na, ita batayi harinshi ba, kuma Allah ya ƙaddara aka batashi, wanda kuma batashi bai zame mana al'khairi ba. Tsawon shekaru babu wanda ya sake ganin makamancinsa, sai kuma gashi a karo na biyu ya shigo cikin ahlinta a hannunki."
Ya ƙarashe mgnar yana jawota jikinshi.
Ba musu ta kwanta cikin ƙirjinsa sabida ƙamshin jikinsa da take son shaƙa.
Sarƙar daya saƙala mata a wuyan nata ta kalla, cikin al'ajabi da mamakin ganin irin sarƙar Ummeynta ce.
Dan komai nasu iri ɗaya harta tambarin jikin sarƙar to sai dai wannan tafi sabunta da sheƙi.

Wannan banbanci na saraƙunan da kuma jin abinda yake matane yasa tayi shiru.
Ta gaza cewa komai, ido ta lumshe jin ya manna bakinshi bisa wuyanta, harshensa yasa yana É—an lasar fatan wuyan nata a hankali.
Kana hannunshi na zuge zib É—in rigarta.
batayi yunƙurin hanashi ba, jin yadda yake jan wasu tagwayen numfarfashi masu nauyi.

Ido ta É—an lumshe ta faÉ—a jikinsa, lokacin daya gama zare mata rigar tata.
Jingina bayanshi yayi da jikin gado, kana a hankali yasa hannunshin ya jawo jallabiyar jikinshi daga ƙasa yayi sama da ita, ya cireta ya rage dagashi sai gajeren wondon iya guiwa wanda ƙasan shi kuma akwai boxes.

Ita kuwa Shatu manne jikinta tayi da nashi kana tasa hannun ta zagayo bayanshi tayi lib a jikinshi.

Ƙugunta ya zubawa ido cikin tsananin Feeling dake ɗawainiya dashi, yasa yatsunshi biyu ya kama bakin robar gajeren wondon dake jikinta wanda yayi cib da jikinta.
da sauri ta mirgino kanshi tare da tashi zaune bisa cinyarshi ya zama suna fuskantar juna,
hannayenta ta meda ta saƙale wuyanshi, tare da kai bakinta kusa da kunnenshi a hankali tace.
"Na gode Yah Sheykh, Allah ya cika maka burinka Allah ya kare min kai da kariyarsa yayi maka rahama da rahamominsa, ya albarkaci ahlinka da albarkarsa yasa ka gama da duniya lfy".
Hannunshi yasa ya mata wani irin masifeffen rugguma ya matse Caɓɓullenta da ƙirjinshi murya can ƙasa yace.
"Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati. Yah Aish Mar'atussaliha."
Sai kuma yasa hannunshi ya tallabo kanta ya haÉ—e goshinsu,
tsinin hancinsa ya goga kan nata,
a hankali kuma yasa harshensa ya fara lasar lips É—inta kamar mai lasar askirim.
ido ta lumshe jin wani irin masifeffen abu ɗaya taso mata daga ƙan babbar yatsar ƙafarta har zuwa maɗigan kanta.
sabida yadda ya cusa harshensa a bakinta ya kamo nata, yanayi mata sahihin kiss mai lankwasa tunanin.
Chapter 169 · 0% Book details