← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 183

Sashe 94

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kana akayi taiya akayi sallama duk kowa ya nufi gidanshi.
Daga nan kuma aka kama aikin sahur.

Suna dawowa Hibba ta kuma kunna TV nan ta samu su tuni su sun idar. Wasu nata É—awafi ne sai addu'o'in ake jerawa.
wanda sai kaji tsikar jikinka na tashi sabida yadda yake ratsa zuciya da jini.

Washe gari da bayan sallan isha'i da asham, yanzu Jalal da Jamil ne kaÉ—ai ke zuwa dan Imran da Sulaiman ma dasu aka tafi.

Haka yasa yanzu duk suna zama a Dinning table suyi buÉ—a baki a tare.
Jalal ne ya É—an kalli Ummi cikin cin Beans salad da Shatu tayi musu.

Hibba ce keta santi tana cewa.
"Alhamdulillah yanzu dai saura mana azumi tara ko takwas".
Murmushi sukayi, ita kuwa da sauri tace.
"Kai takwas nema in sha Allah".
Jamil kam tuni yake dariya tare da cewa.
"Tara ne".
da sauri ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi wai haka ne?".
Cikin dariya tace.
"A a ban saniba Hibbat."
Plate É—in data zuba ferfesun jan nama ta jawo tare da fara ci tana lumshe ido tace.
"Takwas É—in nema in Allah ya yarda".
Allah yasa haka Shatu tace.
Sai yanzu Jalal ya É—an kallesu tare da cewa.
"Ashe dai duk kanwar jace".
Murmushi Ummi tayi kana sukaci gaba da cin abinci.

Yau dai ana zaton salla saura kwana biyar ko shida.

Da hantsi suna zaune dan yau sun tashi da wuri.
Aunty Juwairiyya ce tayi sallama tare da shigowa, Bayan Ummi ta amsa mata.
Gefen Hibba ta zauna tare da cewa.
"Alhamdulillah Ummi É—inkunan mu sun dawo, yanzu KB ya kawosu ya shigo ko?".

"Eh ya shigo mana".

Juyawa tayi ta kalli Hibba tare da cewa.
"Je kice ya shigo Hibba yana nan zaki kanshi cikin baƙar mota".
To tace tare da miƙewa da sauri.

Jim kaɗan suka shigo tana gaba da jaka a hannunta yana biye da ita a baya da ƙattin jakunkuna guda biyu da wani yaro shi shima da manyan jakukkunan biyu.

A tsakiyar falon bisa carpet suka aniye jakunkunan kana, É—aya yaron ya juya ya fita.
Shi kuwa Kabir ya zauna a ƙasa bisa carpet ɗin tare da cewa.
"Barka da hantsi Ummi".

"Barka dai Kabiru, munyi Sa'a an cika mana al'ƙawarin ko".

Murmushi yayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa Ummi aini telane mai amana".
Hibba ce ta É—anyi murmushi tace.
"To ka bari a yebeka mana".
Cikin dariya É—an matashin yace.
"A a ai duniyar yanzu kawai ka yabi kanka, dan ba lallai bane wani ya yaba maka".
Dariya sukayi duka.
Kana ya fara firfito da kayayyakin.
Ko wanne da sunan maishi a jikinshi.

In ya fito dana Ummi sai ya miƙa mata, in ya fito dana Aunty Juwairiyya da yaranta sai ya miƙa mata.

Hakama na Hibba yana fitarwa yana miƙa mata.

Shatu da yanzu ta fitone, ya kalla tare da cewa.
"Barka da safiya Sayyada Shatu".
Murmushi tayi Allah ya sani in sun ce mata Sayyada dariya suke bata wato irin ita matar Al Sheykh ko.
Cikin nitsuwa da danne dariyarta tace.
"Barka dai".
Sai kuma ta ƙara so ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi waye ne shi?".

"Telan mune". Ta bata amsa a taƙaicd.
Cike da mamaki tace.
"To ina ya sanni?".
Hibba ce ta amshi zancen da cewa.
"A hoto ya sanki, da mukaje kai É—inkunanki hotonki kawai aka nuna mishi, ya É—inka kuma kinga komai yayi dai-dai ko".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Lallai kam yayi ƙoƙari".

Cikin dariya yace.
"Uhum ai na iya aikina sosai Sayyada".
Yanzu kam dariya sukayi duka.
Kana ya zaro kayanta a ƙalla kala takwas ya miƙa mata.
Amsa tayi tare da cewa.
"Sannu".
Hibba kuwa irga kayan tayi tare da cewa.
"Kb saura kala bibbiyu a namu nan gani basu".
Kanshi ya É—an sosa tare da cewa.
"Wannan yarinya akwai son kalato laifin mutum to sai jibi zan kawosu ko kuma in bawa Su Jamil in sunje amsar kayansu".
Cikin murmushin Aunty Juwairiyya tace.
"Yauwa ka bawa su Jalal É—in ma kawai".

To yace, kana ya miƙowa Ummi ƙatuwar jakukkuna guda uku tare da cewa.
"To Ummi ga na yaranki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ka kyauta min Kabiru ngd matuƙa, Allah yayi al'barka".
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita.

Ita kuwa Ummi Saratu ta kwaÉ—awa kira tana zuwa.
Ta tace.
Jeki kira duk sauran hadimai suzo duk wadannan Kabiru yazo ya gansu ranar."
Da sauri tace.
"To kana ta juya ta fita.
Ita kuwa Ummi. Inda take zaune ta nunawa Shatu.
Tare da cewa.
"Zo nan ki zauna, zasuzo, ko wacce zata gaya miki sunanta, sai ki duba sunan jikin kayan sai kibata, su duk kala ur'uku akayi musu.

Zaki basu da kuÉ—i dubu biyar-biyar.
Kai ta gyaÉ—a kana da sauri ta koma É—alinta.
Sabida. Sai yanzu ta gano me zatayi da wannan kuÉ—in da ya bata kenan.
KuÉ—in ta kwaso kana tazo ta zauna.

Nan suka rinƙa zuwa suna gaidata da gaya mata sunansu. Kana Hibba ta irga dubu biyar, ta ɗaura kan kala bibbiyu sun ta basu.
Ummi kuwa jakan gabanta ta buÉ—e tana basu takalma.
Aunty Juwairiyya kuwa jakar hijabai ta buÉ—e tana basu.
Suna godiya suna tafiya.
Haka sukayi tayi har kusan awa biyu kafin suka gama, duk kayan sun ƙare sai kuɗin ne ya rage.

Ganin lokacin salla yayi ne, suka tafi.

Bayan sun idar da salla ne, suka fito.
Nan a falon Shatu suka zauna.
Suna É—an hira sabida yau aikinsu baida yawa, kuma Saratu nacan na rage musu.

A hankali wayar Ummi ta fara suwa, alamun ana kiranta.
Da sauri ta kalli Hibba tare da cewa.
"Hibba É—auko min wayata a É—aki".

Miƙewa tayi tare da cewa to.
Jim kaɗan ta fito da wayar da sauri ta miƙa wa Ummi wayar a kunne tare da cewa.
"Amshi Ummi kiyi mgna na amsa kiran Hamma Jabeer ne, kin sanshi baya kira biyu."
Cikin sauri da tarin jin daÉ—i Ummi tace.
"Assalamu alaikum".
Shi kuwa Sheykh Jabeer a can saudia yana tsaye ne a gaban dreesing mirror yana gyara igiyoyin al'kyabbar jikinshi.
Tare da saƙala wayar a kunnenshi ya matseta da kafaɗarshi.
Alamun sauri yake yana shirin tafiya haramine.

Cikin sanyi yace.
"Wa alaikissalam. Barka da gida Ummi".
Fuska a sake tace.
"Barka dai Sheykh, ya ibada?".

"Alhamdulillah Ummi, yasu Jalal".

"Suna lfy, kuma basa wasa da ibada, yanzu Jamil ya dena zuwa hirama wata ƙil kuma ya ɓata da Khadijah naji yanzu wata Maryam yake kira, Jalal ne dai yake ɗan fita shima ba sosai ba".
Gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa.
"To Alhamdulillah, eh shi Jalal ba matsala fitanshi, nasan dashi.
Ya Hibba kuma tana azumi ko batayi?".
Cikin murmushin da kallon inda Hibba take tace.
"A a Hibba ai an girma yanzu ta rage rakinma".

ÆŠan karamin mataji ya É—auka yana kontar da sajenshi yace.
"To Ummi na gaisheku, na kira Aunty Juwairiyya kam nani jikin ya Jafar da sauƙi sosai mun gaisa da Hajia Mama, har take cemin Affan ɗina zai dawo a salla".
Da sauri tace.
"Uhum Sheykh".
Ajiye kum É—in yayi tare da cewa.
"Na'am Ummi".
Cikin sanyi tace.
"Ga Shatu".
Shiru yayi baiyi magana ba, kuma bai katse kiranba,
jin haka yasa ta kuma cewa.
"Sheykh".

"Na'am Ummi".
Ya kuma cewa.
A hankali tace.
"Ga Shatu".
Still baiyi mgn ba, hakanne yasa a hankali ta mannawa Shatu wayar a kunne ta.
Kana ta sa hannunta ta kamo hannun Hibba suka fita babban falon.

Shi kuwa Sheykh Jabeer shiru yayi tsaye gaban dreesing mirror, yana kallon gemunshi.
A hankali yake jiyo sautin sauƙar numfashin can ƙasa-ƙasa, ɗis ɗas haka yaji ƙasan zuciyarshi na harbawa.

Ita kuwa shiru tayi tanajin sautin tasbihi da yakeyi can ƙasan-ƙasan maƙoshinsa,
Lips ɗin shi na motsawa a hankali suna fidda sautin can ƙasa.
Jin shirun yayi yawane yasa a hankali ta buÉ—e bakinta tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
Sai kuma tayi shiru ta kasa kunnen dan jiran amsarshi.
Gyara zamanta tayi tare da ƙara riƙe wayar, numfashi ta sauƙe a hankali.
Hakan yasa yaji sautin iskar.
Har ta cire tsammanin zai amsa sai kuma taji muryarshi can ƙasa yana cewa.
"Wa alaikissalam. Ashe kin iya sallama?".
Ya jefo mata tambayar a gajarce.
Cikin juya ido tace.
"Ba'a koya min da wuri bane!."
Shine mgnar da tayi niyar gaya mishi, sai kuma tayi mgnar a zuci, ta danne abun.
Sabida tana son ta nemi al'farman addu'o'in a kaba, aka yayunta da suka bace, shiyasa cikin sanyi tace.
"Eh, Ummi ta koya min".
Shiru yayi kamar bai jitaba,
ita kuwa a hankali tace.
"Ina kwana".
Kanshi ya É—an kalla a madubi tare da cewa.
"To Kifin rijiya su nan yanzu wunine".
Cikin sanyi da sassauta Muryar son isar da buƙatar ta tace.
"To ina wuni".

"Alhamdulillah".
Ya bata amsa.

Miƙewa tsaye tayi ta nufi bedroom ɗinta.
Tare da cewa.

"Ya ibada?".

"Alhamdulillah". ya kuma cewa.
"Har ya kai hannunshi zai janye wayar sai kuma ya tsaya jin tana cewa.
"Uhmm, Ayyah Yah Sheykh..".
Sai kuma tayi shiru. Cikin saurin jin an kira salla murya a nitse yace.
"Uhumm Ayyah, me É—in?".

Da sauri tace.
"Dama.. dama!!...".
Gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Sauri nakeyi zan tafi masallaci, kada kisa na rasa damata".
Cikin rauni da muryar dake nuna cewa tana zubda ƙwalla tace.
"Ayyah dan Allah da Manzonsa.
In kaje kayi min addu'a a harami mana".
Juyowa yayi yana kallon Haroon da Ya Hashim da suka shigo yanzu alamun kiranshi zasuyi.
Cikin wata iriyar murya a hankali yace.
"Addu'ar me zan miki?".
Murya na rawa tace.
"Allah ya dawo min dasu Yayana lfy, ya kare minsu a duk inda suke, ya baiyana sucikin gaggawa".
Cikin rashin fahimtar zancen nata yace.
"To zan miki saboda Allah da Manzonsa da kikace".
Cikin jin daÉ—i tace.
"Ngd matuƙa Allah ya biya maka buƙatunka."
Wani irin sassanyan numfashi ya sauƙe tare da lumshe ido a hankali yace.
"Amin ya rabbil izzati, kema kuma kiyita addu'a ki dage da ambaton Allah zai cika mana dukkan burinmu".
Yana faÉ—in haka ya katse kiran.

Ita kuma murmushi tayi tare da share hawayenta.
Cikin sanyi tace.
"Ya Allah ka dubemu da idon rahama".
Hibba dake shigowane tace.
"Amin Amin."

Daga nan suka fito falo suka kama sabgoginsu.
Chapter 94 · 0% Book details