Sashe 139
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai tun dazu ma tayi baccin, bari in tasheta".
Safiyyah ta faÉ—a tana nufar gadon.
Da sauri Mamma tace.
"A a kada ki tasheta da ƙarfi ba'a son tada mai ciki daga bacci ta sigar da zata firgita".
Aunty Rahma dake shigowane tayi saurin ƙarasowa tare da cewa.
"Kai Aunty Hafsat haba dama ni na lura kamar ciki take dashi naga tana yawan bacci".
Juyowa sukayi suna kallon Safiyyah daketa dariya ƙasa-ƙasa cikin dariyar tace.
"Au ku dama kallon mai ciki kukeyi mata ashe.
To wannan kam yanzuma bata salla, kuma dama wasu in suna al'ada suna yawan bacci inaga ita hakane".
"Kai Safiyyah wannan tsarabe-tsaraben naku na Nurses baya gaya muku gaskiya wasu lokutan".
Mamma ta faÉ—a da iya kar gskyar ta.
Ita dai Safiyyah dariya tayi kana ta fara kiran Aysha.
Ita kuwa Aysha tun mgnar Mamma na forko ta farka daga baccin ta dai ci gaba da rufe idonta ne kawai sabida karta katse musu hirarsu.
A hankali ta buɗe idonta tare da yin salati kana ta miƙe zaune.
Cikin kula Mamma tace.
"Sannu ko tashi kiyi salla ki shirya dan har an fara kai mutane wurin walimar".
Cikin sanyin bacci tace.
"To Mamma".
Daga nan ta miƙa ta nufi Bathroom.
Ita kuwa Mamma miƙawa Safiyyah ledar kayan Jannart tayi kana ta ajiyewa Aysha nata a bakin gado tare da cewa.
"In kin fito ga kayan da zakisa a cikin jakar nan a bakin gado".
"To ngd Mamma".
Tace tana rufe ƙofar Aunty Rahma kuwa hannu tasa ta ɗauki Ishma dan zataje ta kimtsata.
Safiyyah kuwa da sauri ta kaiwa Jannart nata kayan ta dawo.
Tuni ƙawayen Umaymah manyan mata da matan abokan Abbansu Haroon matan sarakuna Da ƴaƴan sarakuna duk anata kaisu wurin da aka tanada dan yin walimar.
Manyan mutane dattawa maza masu karamci da mutunci yan kasuwa da yan siyasa da sarakuna duk sun cika maƙil a babban hall ɗin.
Katon hall ne wanda a ƙalla zai iya ɗaukar mutune dari takwas zuwa ɗari dubu ɗaya.
An gyara wurin an ƙawatashi.
Ansa wani labule mai zaman kanshi an raba wurin biyu, kasan cewar dama ƙofofin shigowan biyune, haka yasa aka tsara wurin yadda mata zasu zauna a gefe ɗaya maza a gefe ɗaya bazama su ga junaba.
Sai can sama akayi wani É—an dandamali wanda sai ka taka steps huÉ—u ana biyar zaka hau.
Shine wuri na musamman wurin zaman malami.
Ƙasa kaɗan dashi kuma wani ƙawataccen table ne mai kujeru shida, inda nanne wurin zaman angwaye da amare.
Can gefen inda malamin zai zaunama akwai ƙofar da ta nan zai shigo.
Tako ina ka cilla idonta haskene ras tamkar rana, wurin yayi kyau gwanin ban sha'awa.
Gaba ɗaya wurin mata da mazan ya cika maƙil duk manya-manyan baƙin sun samu isowa.
Hatta Sarki Ahmadu da tawagarsa da Abbansu Haroon da tawagar abokanshi duk sun iso.
Hakama Umaymah da da mutanenta hakama Mamma ta iso da Hajia Mama da Ummi da Aunty Juwairiyya da Hibba da Azeema.
Isowar Sheykh Jabeer da Ango da amaren kawai ake dako.
Madadin zama shurun sai akasa, sautin karatun al'ƙur'ani mai girma.
A can gida kuwa, Ibrahim, Haroon Sheykh da ne tsaye a harabar farfajiyar Side Umaymah, suna cikin wata iriyar fitinenneyar shiga mai masifar kyau da ban sha'awa.
Shigar fararen jallabiyar ƙirar Pakistan irin mai riga da wonɗonan ne kalar Sky blue mai azabar kyau da taushi da sheƙi.
Sai wasu tattausan al'kyabbar farare ƙal tamkar madara, al'kyabbar sun irin mai shara-sharan nanne haka ya bawa kolliyar tasu damar zama kamar adon sararin samaniya.
Sai hiramin dake kansu ne ya banbanta na kan Haroon da Ibrahim farine tas.
Sheykh kuwa nashi farine sai É—igo-É—igon Sky blue, hakama takalminshi hafl cover suma fararene sai É—igon Sky blue.
Sai kekyawan zoben Daimond mai É—igon Royal blue mai masifar kyau sai wal-wal yakeyi.
Sai ƙamshi sukeyi da sheƙi.
Ibrahim ne ya kira Safiyyah a waya tare da cewa suyi maza su fito mana.
To tace kana ta kalli Aysha dake cikin shigar doguwar riga mai masifar kyau da tsada, rigar iri É—aya ce da Tata data Jannart.
sai dai tafi kama jikin Aysha sabida ta fisu faɗin ƙasa da sama.
Sunyi kyau sosai sunyi rolling kawunansu da gyalullukan suka fito tamkar yammatan larabawa.
Cikin sauri ta fesa turare kana ta kalli Safiyyah tare da cewa.
"To na gama mu tafi ko".
Murmushi Safiyyah tayi tare da cewa.
"Masha Allah kinyi kyau. Mu tafi".
Da haka suka fito.
A falo suka samu hadiman Umaymah nata gyara gidan.
Suna fitowa Aunty Rahma da Jannart suma suka iso.
Da sauri Ibrahim ya buÉ—e motarsa ya shiga, Safiyyah ta shiga gefenshi.
Aunty Rahma da Ishma suka shiga baya.
Haroon kuwa kama hannun Jannart yayi suka shiga bayan motarsa direbanshi na gaba.
Sheykh kuwa a hankali ya buÉ—e motarshi dasu Sulaiman da Ya Hashim suka zo da ita, kuma su tuni an kaisu can wurin walimar.
Kasan cewar babu mai janshi ne yasa ya shiga ya zauna a mazaunin gireban.
A hankali tabi bayanshi ganin tuni Ibrahim yaja motarshi hakama motar Haroon.
Cikin takun nitsuwa ta iso gab da motar, hannu tasa zata buÉ—e baya ta shiga.
Jin marfin a rufe yake yasa ta É—an matso kusa da inda yake tare da cewa.
"A rufe yake".
Ƙwayar idanunshi ya juya mata tare da mata alamun ta zagaya ta shigo can gefenshi.
Kasan cewar yana latsa wayarshi haskenta ya haska fuskarshi yasa ta gane manufarshi.
Zagayawa tayi ta buÉ—e ta shiga kana ta maida marfin.
A hankali ta juyo ta É—an kalleshi jin yace.
"Bismillah". Kana ya tada motar yaja suka bar harabar wurin.
Kasan cewar wurin babu nisa sosai da masarautar.
Tuni su Haroon sun isa har sun shiga sun zauna yanzu isowar Sheykh kawai ake jira.
Suna isa harabar wurin. Bayan yayi parking, suka fito.
Suna isa suka samu tarin fadawa a bakin ƙofar.
gaba yayi ya nufi ƙofar da zai shiga ta wurin.
Ita ma binshi a baya tayi.
Suna shiga, tayi maza ta kange fuskantar da bayanshi sabida. Tarin mutanen da ta gani sun firgitata, sam batayi zaton yawan mutanen ya kai haka ba.
Fahimtar hakane, yasashi yin gaba ita kuma tana biye dashi.
Har inda su Haroon suke. Kujerar dake gefen Jannart ya nuna mata.
Ai da sauri ta zauna.
Shi kuwa sunkuyowa ya É—anyi kan Haroon kana yace.
"Ka nitsu da kyau ka saurari abinda Allah da Manzonsa suka ce a tsakanin ma'aurata".
Cikin murmushin dake bayyana zallar jin daÉ—i da zumuÉ—in amarci Haroon yace.
"To Sheykh".
Daga nan ya juya ya koma inda aka tanada domin shi.
Yana zama wani É—an agaji ya dawo bayanshi ya tsaya.
kana ya miƙo mishi abin mgn.
Amsa yayi kana ya saƙalashi a bakin al'kyabbar jikinshi.
Gyara zamanshi yayi da kyau kana ya fuskanci taron al'ummar baki É—aya.
ÆŠaya daga cikin Æ´an agajin ne yasa hannunshi ya katse sautin karatun Alqur'ani dake tashin.
Cikin nitsuwa kamala haiba da ilimi ya É—anyi gyaran murya tare da fara bude taro da bimilla da addu'a da sallama.
"Bismillah rahmanirrahim. Assalamu alaikum warahmatullahi wa barka tuhu.
Innal hamdalillah nahmaduhu wanasta inuhu wanastagfiru wana uzubillahi min shururi am fusina wa sai'yi ati amalina. Manyahadillahu fala mudillalah, famanyuddul fala hadiyala wa asshahu'alla'ila'ha'illalahu wahdahu lasheri kallah, wa asshahadu annamuhammadan abduhuwarasulu.
Ya ayu allazina amanuttaƙullaha haƙƙa tuƙatil wala ta mutunna illah wa antum muslimun ya ayu hannasu taƙu rabbakum.
Kalakum min nafsin wahida, wa kalaƙa minha zaujaha wa bassa minhuma rijalan khasiran wa nisa'ah wattaƙullah lazitasa'aluna bihi, wal'arhama innallaha kana alaikum raƙiba, ya aiyu allazina amanutaƙullah wa ƙulu ƙaulan sadidah yuslahlakum amalakum wayagfirlakum zunuba kum, waman yuɗillah wara sulahu, faƙadfaza fauzan azeema ambaduhu fa inna'asdaƙal hadisi kitabullah wa'ahsanal hadi hadiyu Muhammadin (S.A.W) wa sharal umuri muhdasatuha fa innakulla mudasatin bidi'a wa kulla bidi'atin balala wa kulla balaltun finnar."
Dogon nufamshi ya sauƙe mai ɗan nauyi sabida jan dogon numfashin da yayi, kana ya kalli Side ɗin dasu Abbansu Haroon suke yace.
"Alhamdulillah kamar yadda muka sani, walimace ta farin cikin auren Æ´an uwanmu, kana kamar yadda kowa ya sani walima shine aci asha kana a watse.
To a madadin muyi zaman da ci da sha kawai ya dace mu haɗa da ambaton sunan Allah, dayiwa ango da amrya taƙaitacciyar nasiha akan tsarin aure a musulunce da haƙƙoƙin ma'aurata ga junansu da addu'an zaman lafiya."
A hankali yayi gyaran murya.
Kana ya muskuta ya gyara zamanshi da kyau ya fuskanci taro al'ummar Annabi dake gabashin.
Manya da yara maza da mata.
Especially matasa, yatsarshi manuniya yasa gyara zaman siririn farin gilashin dake manne a fuskarshi.
ÆŠan sunkuyar da kanshi yayi.
Dai-dai inda abin sautin mgnar ke saƙale a wuyan al'kyabbar jikinshi.
Gaba É—aya hall É—in yayi tsit bakajin motsin kowa sai sautin numfashin mutane dana A/C.
Cikin tattausan lafazi muryarshi ta ratsa kunnuwan duk wanda yake wurin inda yace.
*AURE*
Ma'anar aure a musulunce shine. Sunnan Allah a wojen halittar Allah daya halitta ya haliccemu ne a jinsi guda biyu macce da namiji.
Kamar yadda Allah (S.W.A) ya ce, a Suratul Zariyya aya ta 49:-
(WA MIN KULLI SHA'I'IN KHALAƘNA ZAUJAINI LA ALLAKUM TAZAKKARUM)
"Kan ko wa wane abu Allah ya halice shi namiji da mace don ku yi tunani a kansa.
Sannan Allah maÉ—aukakin sarki a wata ayar ya sake cewa a Suratul yashin aya ta 36:-
(SUBHANALLAZII KHALAƘAL AZWAJA KULLAHA MIMMA TUMBITUL ARDU WA MIN AMFUSIHIM WA MIMMA LA YA ALAMUN)
"Tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya halicci ma'aurata namiji da mace, dukkansu daga abinda ƙasa ke sirarwa, kuma daga ko wannensu kuma da ma abin da basu sani ba!."
Kanshi ya É—an É—ago ya kalli gefen maza, idonshi ya É—an lumshe sabida gamsuwa da nitsuwarsu data tabbatar mishi, zantukanshi na ratsasu.
Idonshi ya É—an tsaida kan fuskar Haroon ango mai jiran gado.
Sai kuma ya janye idonshi yaci gaba da cewa.
"Tabbas da wannan tsarin na auratayya ne. Allah ya zaɓa mana ya zama hanyar da zamuyi ta haife-haife muyi ta karuwa a bayan ƙasa.