← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 183

Sashe 150

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita kuwa Aysha tana shiga, ta ajiye jakarta gefe kana ta faɗa kan gado ta kwanta a kife, ta kifa kanta bisa pillow kuka mai ƙarfine ya kwabce mata, sabida suya da zafin da zuciyarta keyi na tuno ƴan uwanta da suka ɓace.
Duk da kuma kontar mata hankali da Bappa keyi na cewa anji lbrinsu har an gansu.

Kuka tayi tayi sosai wanda ita kanta bata san tsawon lokacin da tayi tana kukanba.

Sai ƙarfe uku dai-dai ta samu bacci ya saceta.

Shi kuwa Sheykh yana shiga,
yayi ajiyan numfashin sabida ya samu komai tsab-tsab a gyare a killace ko ina na ƙamshi.
Kasan cewar ana zabga zafin da rashin ruwan sama da akayi kwanaki ba'ayi bane yasa, garin É—inkewa da zafi.
Gudun A/C'n ya ƙara kana ya ajiye jakarshi cikin drower'nshi.
Rage kayan jikinshi yayi kana ya shiga bathroom wonka yayi tare da al'wala sannan ya kimsa cikin tattausan rigan bacci riga da dogon wondo ne.

Yana fitowa ya rage hasken É—akin kana yazo ya zauna bakin gadon.
Ya buÉ—e hannunshi ya É—agasu sama alamun zaiyi addu'o'in kwanciya baccine, kiran Haroon ya shiga wayarsa.
Yasan idan ba É—agawa yayiba Haroon ba barinshi zaiba, hakane yasa ya amsa kiran da sauri.
"Alhamdulillah mun iso lfy yanzuma bacci zan kwanta".
Ya faÉ—a da sauri. Dariya Haroon yayi tare da cewa.
"Ya haka dai malam kamar korata kakeyi, nima sabon ango banma hakaba sai kai tsohon ango, to a huta gajiyar hanya, ni yanzu zan kama hanyar fatauci ne".
Wani gajeren tsaki yaja tare da katse kiran.
Dariya Haroon yayi kana ya jawo hannun Jannart É—inshi suka nufi É—auki shi.

Shi kuwa Sheykh addu'a yayi ya tofa a tafin hannunsa ya shafe jikinsa duka kana ya kwanta bisa hannun damanshi.
Lumshe ido yayi tare da sauƙe numfashi kana ya fara tasbihi kamar yadda ya saba, lokaci ɗaya bacci ya samu nasarar ɗaukeshi.

Haka sukayi bacci a gajiye gaba É—ayansu.

Ƙarfe biyar saura kwata, ya fito cikin shirin tafiya masallacin Masarautar Joɗa domin limancin sallan asuba.
Da sauri ya buɗe ƙofar kana ya fita sannan yaja ƙofar ya rufe.

Dai-dai lokacin Ummi kuwa ta farka daga baccin da ya samu nasarar sata makara, da sauri ta miƙa bathroom ta faɗa al'wala tayi kana ta fito.

Aysha kuwa can cikin bacci take cin sautin karatun Alqur'ani da yakeyi na suratul Al-Burooj. Sosai sautin muryarsa ke ratsa ko ina na cikin masarautar JoÉ—a, a hankali take buÉ—e kwayar idanunta wadanda bacci da kukan da tayi ya kumburasu suka yi wani É—an ja haka mai gauraye da farin.
meda idon tayi ta lumshe jin yadda yaja tsakiyar aya ta 8.
Yadda yaja illahhhhhhhh ɗin cikin taƙib mai ja shida, kana ya maida numfashi.
Saida taji tsikar jikinta na tashi yar-yar, da sauri ta buɗe idonta kana miƙa zaune, cikin kasala da yanayin bacci bai isheta ba sam ta miƙe tsaye ta faɗa bathroom.
Wonka tayi da ruwan sanyi sabida wani irin zafin da ake zabgawa, kai baka ce tsakiyar damuna bace.
Al'wala tayi kana ta fito, wata tattausar doguwar riga ta zura a jikinta, kana tasa hijabi.
Sannan ta shimfiÉ—a sallayarta.

Bayan ta idar da sallan ta fara du'a'u Azkar tanayi tana lumshe idonta sabisa sam da baccin bai isheta ba.
Koda ta ida addu'o'in ta shafa, a hankali ta miƙa ta ninke sallayar da hijabin kana ta ƙara ƙarfin A/C'n sannan ta kashe wutan ɗakin ta koma ta konta,
Mustsuke idon tayi jin har wani yaji-yaji suke mata, gyara kwanciyar ta tayi take kuwa baccin yayi awon gaba da ita.

Bakwai dai-dai Ummi ta fito asalin babban falon.

Kitchen ta nufa jiyo motsi a ciki alamun Sara tazo kenan.

Tana shiga kuwa ta samu Sara na fere Arish ga kuwa ruwan tea ta ɗora ta zuba citta kanamfari sunata ƙamshi.
"Ina kwana Ummi".

"Lfy lau Alhamdulillah Sara mun sameku lfy".

"Alhamdulillah".

"Masha Allah". Tace tana haurawa saman steps É—in da zasu sadata da inda freezer yake.
BuÉ—ewa tayi, zabbi uku ta É—auko kana ta sasu a wata Æ´ar madai-daiciyar roba.
Kana ta dawo jikin sink wuƙa ta ɗauko sannan tazo ta fara gyarawa.

Sheykh kuwa karfe bakwai da kwata ya fito cikin wasu tattausan farin yaÉ—in boyel riga da wondo da malum-malum yadin irin mai gidan dara-daran nanne. An watsa gariyar aiki da surfani Royal blue mai masifar kyau, hular kansa itama farace mai rashin Royal blue.
Hakama takalmin shi half cover suma Royal blue ne masu azabar kyau, sajenshi ya kwanta lib gwanin burgewa.
Jakar System É—inshi ya rataya a kafaÉ—arshi ta dama, kana ya fito ya nufi Valli Hospital É—inshi.

Ƙarfe tara saura kwata Jalal, Jamil, Ya Jafar, Imran suka shigo falon.
Jamil ne ya lumshe idanunshi tare dacewa.
"Wow Ummi wannan ƙamshin na girki shine ƙungiyar yunwa, duk yawunmu ya tsinke."
Dariya Ummi dake Dinning area tana jera Foodflaks bisa table É—in tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah kuwa kun iso a Sa'a an gama kenan kun iso, maza ku ƙara so nan."
Jalal dake riƙe da hannun Ya Jafar dake karanta Suratul Al-monafiqoon a hankali yake motsa laɓɓansa saɓanin da da yakanyi da ƙarfi.

Zama sukayi baki É—ayansu, kana suka fara yin karin kumallon da kekkyawan girkin Ummi.

Ita kuwa Ummi kitchen ta koma, ta sawa Sara nasu, kana tace.
"Yauwa kije ki É—an huta sai shabiyu sai kizo mu É—aura na rana".
ÆŠaukan kularta tayi kana ta fita ta tafi.

Ita kuwa Ummi É—akin Aysha ta nufa jinta shiru-shiru bata fiton ba.
Sallama tayi a bakin ƙofar, shirun da tajine yasata ƙarawa, still ba amsa,
Sallama ta uku tayi kana ta tura ƙofar a hankali sannan ta kutsa kai ciki.
Can ta hango Aysha konce lib tana sharan bacci cikin salama, murmushi tayi kana ta juya ta koma falon ta É—ebi nata abincin taci kana ta koma É—akinta dan yin walaha.
Su Jalal kuwa sai goma da rabi suka bar falon, ya zama shiru.
Bayan fitansun ne Ummi ta fito ta kimtsa Dinning table tsab, sannan ta zauna a falon.

Sha É—aya dai-dai Aysha ta farka daga baccinta mai cike da mafarkai, bathroom ta kuma shiga, ruwa ta watsa sabida zafin da akeyi.
Tana fitowa ta zauna gaban dreesing mirror body lotion É—in ta mai É—an karen kanshi ta shafa, kana ta É—anyi light mackup akan Kekkyawar fuskarta tayi kyau sosai kuwa, wata atamfar Super Engla mai kyau, green, red, and white color, yanada zanen tsintsiya a jikinshi É—inkin doguwar rigace takoyi dabas a jikinta gwanin burgewa, É—an kwalin ta murza a kanta irin É—aurin mai stpes É—innan sosai fuskarta ta fito ras, ta kitse jelar gashinta ta konto bayanta, gyale ja ta yafa turare ta fesa, sannan ta fito ta nufi falon tana É—an hamma alamun yunwa.

Ummi na ganinta ta mike zaune tare da cewa.
"Sai yanzu".
Gefen Ummi ta zauna a ƙasa bisa carpet tare da cewa.
"Eh Ummi gajiya. Ina kwana".
Fuska a sake tace.
"Lfy lau Alhamdulillah gsky kam kinsha bacci".
Kai ta rausayar tare da yin wata hammar, miƙewa Ummi tayi ba tare da tayi mgna ba, ƴan kananun Foodflaks ɗin da ta zuba mata breakfast ɗin ta jera a tray da flaks ɗin tea da plate spoon and cup. Gabanta ta ajiye kana tace.
"Yauwa ga abinci maza kici ki shiga kitchen ki shiryawa Sheykh nasa karin dan inaga ya tafi asibitinshi".
Jawo tray'n tayi tare da cewa.
"Toh". Soyeyyen dankali da kwai ta zuba a plate kana ta haÉ—a tea sannan ta É—an sa ferfesun zabbin kaÉ—an kana ta faraci suna, hirar bikin haron.
A nan Safiyyah ma ta kira nan akayi yar hira da ita.

12:00 Sara ta shigo.
"Ina kwana Aunty". Tace tana kallon Aysha, cikin sakin fuska tace.
"Lfy lau Alhamdulillah Sara ya gida".
Alhamdulillah itama tace.
Tray'n ta tura mata gabanta tare da cewa.
"Yauwa muje kitchen ki É—an tayani aiki Arish zaki É—an fere min kaÉ—an. Sai ki gyara min kayan miya."
To tace tana muƙewa rabi bayanta.

Itama Ummi bayansu tabi, ita ta fara aikin Lunch su kuma suna aikin na Sheykh.
Jan nama mai kyau ta É—iba tayi musu yanka yan mitsi-mitsi ta wonkesu kana ta juyesu a tukunya, tasa al'basa da Curry Maggi kanamfari citta tafarnuwa kaÉ—an da dai sauran kayan É—an-É—ano ta rufe tukunyar bayan ta É—aura a wuta,
Bayan an fere mata dankalin ne, ta amsheshi tayi mishi ƙananun yanka, sannan ta amshi tattasai, attaruhu da al'basa, da Sara ta jajjaga mata.
Ta ajiye a gefe tuni naman nan yaketa sulala yana zuba ƙamshi yayi lugub.
juye naman da ruwan tayi a wani É—an kwano na tangaram kana tasa mai a tukunyar ta meda kan wuta.
yankekken al'basa ta watsa a man take ya baza ƙamshi a Side ɗin gaba ɗaya, kayan miyar tasa ta soya ya soyu da kay, sannan tasa ɗauki ruwan naman nan da naman ta juye ciki.
Kana ta rufe sannan ta ɗan ɗauko maggi da gishiri ɗan ƙanƙani ta watsa ciki.
Sannan ta rufe, wata ƴar ƙaramar tukunya ta ɗaura tasa ruwa kaɗan kana tasa kwai guda bakwai ciki kana ta rufe.
Sannan ta É—auko sufageti rabin ledar ta karya tasa a cikin haÉ—in tukunyar.
tare da watsa dankalin nan a ciki sannan ta maida ta rufe.
Chapter 150 · 0% Book details