Sashe 86
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Motarshi na gama tsayuwa yan agaji suka rufa mishi baya, babban cikinsu ne ya buÉ—e mishi marfin motar tare da É—an rusunawa yace.
"Barka da safiya Malam".
Cikin tsananin kulawa Sheykh Jabeer ya kalli dottijon da ya kai ya haifeshi.
Hannu ya miƙa mishi tare da cewa.
"Barka dai Baba Sule Ya ibada".
Cikin jin dadi yace.
"Alhamdulillah".
Sai kuma ya kalli sauran wanda yawanci bazasu wuce sa'annim ƙaninshi mai binshiba Affan kenan,
Murmushi yayi tare da basu hannun yana mai tuna cewa tabbas da Affan yana Æ™asar nan To bana a Æadamaya zaiyi azumi, kuma ya sani da yanzu suna tare anan, dan shi ba irinsu Jalal bane.
Zagayeshi sukayi suna buÉ—a mishi hanya yana wuce.
Ta kofar da liman ke shiga ya shiga.
sit kakeji da yake duk mazane, gashi kuma ansan ƙa'idarshi shi baya son surutu in yana tabsir.
Zama yayi tare da kallon ɗan agajin dake saƙala mishi abin ɗaga sauti mgn a jikin al'kyabbar jikinshi.
Yayinda wasu kuma suka koma bayanshi wasu suka tsaya gefenshi, yan É—aukan awazin kuma na gidajen Radio da TV duk sun kafa na'ura su a gaban table É—in da yake zaune.
Bayan an gama kimtsa mishi komaine, ya gyara zamanshi tare da kallon alaramma Abdulƙadir wanda shine zai jamishi baƙi.
System ɗinshi ya buɗe tare da gyara mata zama, haka shima Alaramma Abdulƙadir yayi da Qura'an ɗin gabanshi.
Gyara murya Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero yayi tare da fuskantarta taron al'ummar dake gabanshi cikin É—an É—aga sauti yace.
"Bismillah rahmanirrahim. Assalamu alaikum warahmatullahi wa barka tuhu.
Innal hamdalillah nahmaduhu wanasta inuhu wanastagfiru wana uzubillahi min shururi am fusina wa sai'yi ati amalina. Manyahadillahu fala mudillah, famanyuddul fala hadiyala wa asshahu'alla'ila'ha'illalahu wahdahu lasheri kallah, wa asshahadu annamuhammadan abduhu warasulu.
Ya ayu allazina amanuttaƙullaha haƙƙa tuƙatil wala ta mutunna illah wa antum muslimun ya ayu hannasu taƙu rabbakum.
Kalakum min nafsin wahida, wa kalaƙa minha zaujaha wa bassa minhuma rijalan khasiran wa nisa'ah wattaƙullah lazitasa'aluna bihi, wal'arhama innallaha kana alaikum raƙiba, ya haiyu allazina amanutaƙullah wa ƙulu ƙaulan sadidah yuslahlakum amalakum wayagfirlakum zunuba kum, waman yuɗillah wara sulahu, faƙadfaza fauzan azeema ambaduhu fa inna'asdaƙal hadisi kitabullah wa'ahsanal hadi hadiyu Muhammadin (S.A.W) wa sharal umuri muhdasatuha fa innakulla mudasatin bidi'a wa kulla bidi'atin balala wa kulla balaltun finnar."
Nufamshi ya sauƙe mai ɗan nauyi sabida jan dogon numfashin da yayi, kana ya kalli taron al'ummar musulmi dake zaune gabanshi manya da yara, masallacin yayi maƙil har woje.
Kusan gaba É—aya taron jamar suka haÉ—a baki wurin cewa.
"Wa alaikassalam warahmatullahi wa barka tuhu".
Kanshi ya É—an rusunar tare da ci gaba.
Gyara masaƙalin abin sautin mgnar dake wuyan al'kyabbar jikinshi yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah. Kamar yadda aka saba haɗuwa a wannan masalaci mai Al'barka bana kuma Allah ya ƙaddara dani za'ayi.
Kamar yadda aka fara a wancan shekarar, zan ɗaura a kan darasin da Malam Abubakar ya fara, duba da kasantuwar mafiya yawa yan kasuwa ne, to zamuyi maudu'in bisa haƙƙin tauye mudu, da kuma barin salla ta wuce dan gudun cinikayya ya wuce ka."
Daga nan ya shiga cikin shirin gadan-gadan.
Yayinda gaba ɗaya mutane sukayi tsit suna jin nasiharsa da hujjoji da yake jawowa daga al'ƙur'ani zuwa ahadisai, yana shigarsu yana ratsa musu jiki, jini, da zuciya.
Musamman dama mutane nason wa'azinshi.
Haka yasa koda lokacin tashi yayi sai suka ga kamar miti biyar sukayi ba awa É—aya ba.
Yana tashi a wurin yan agaji sukayi mishi rakiya, har bakin motarshi.
Daga nan Masallacin Masarautar JoÉ—a ya nufa.
Sha biyu dai-dai tayi mishi yana cikin masallacin
tuni an shirya an kimtsa komai yadda abu zai tafi, shiyasa yana isa shida Alaramma Abdulƙadir suka fara.
A can cikin masarautar JoÉ—a kuwa.
Dai-dai lokacin Shatu ta fito cikin É—akinta ta nufi falo.
Shiru babu kowa, haka yasa ta wuce kitchen da nufin yin wonke-wonken da sauran gyara-gyare ganin komai tsab-tsab ne yasa ta dawo falonta.
A hankali ta nufi É—akin Ummi.
daga bakin ƙofa ta tsaya tare da yin sallama.
Cikin kula Ummi ta amsa mata tare da cewa.
"Ki shigo mana".
To tace kana ta shiga, cikin sanyi tace.
"Ina kwana Ummi".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Lfya lau Alhamdulillah, amman yanzu dai ina wuni ne ko".
Cikin murmushi tace.
"Eh hakane fa, yanzu har sha biyu da rabi tayi".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ai tunda naji Sheykh ya fara tabsir nace to rana ta tsala".
Shiru suka É—an yi tare da kasa kunne, ras muryarshi ke tashi sabida ansa amsa kuwa ta cikin masarautar.
shiru Shatu tayi tare da yin ƙasa da kanta tana mai lumshe ido, Allah yasani tana masifar son tabsir ɗin shi, in taji yana jan baƙi sai take jinta kamar a harami take.
Ummi ce ta ɗan kishin ƙiɗa tare da cewa.
"Gyara zamanki muji wa'azin."
Kai ta É—an É—ago tare da cewa.
"Ummi naje kitchen zan mana wonke-wonken na samu an gyara komai ba dai ke kikayi aikinba?".
Cikin maida hankalinta ga sauraron tabsir É—in tace.
"Nice nayi, amman daga yau Saratu zata na zuwa tanayi wanke-wanke da share-shere da yan gobe-goben da dai sauran ƴan wasu aiyuka, kamar fere dankali ko doya da tsinkan ganyen ko wanke wake ko jiƙa shinkarfa masa da kai markaɗe, duk itace zatayi mana, mu kuwa in munyi azahar mu shiga kitchen,
zatake É—an taimaka mana da wasu aiyu kan. Amman banda girki, hadimar Gimbiya Aminatu ce, amman duk azumi nan ake bamu ita".
Cikin gamsuwa da hakan tace.
"To ba damuwa Ummi, amman dan Allah in ɓata zoba, kada kice zakiyi aikin ki barshi ni zanyi".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Zama tazo, kullum da asuba ana idar da salla zata zo.
In ta gama aiyu kanta kafin ƙarfe goma dai zata tafi, sai anyi sallan azahar kuma zata zo.
Daga nan kuma sai mun gama aikin buÉ—e baki, ta tafi dana Gimbiya Aminatu da nata, sannan sai ansha ruwa anyi sallan isha'i da asham sai ta dawo tayi yan wonke-wonken da taimaka mana aikin sahur, to in ta tafi kuma sai washe gari in anyi sallan asuba ta dawo."
Cikin É—an fito da idonta tace.
"Wannan zirga-zirga haka Ummi to ta zauna anan kawai mana ta huta".
Juyowa tayi ta É—an kalleta kana tace.
"Mijinki ba irin waÉ—annan mutanen bane, baya son a turo mishi yara suzo suyi ta zirga-zirga a kanshi, kinga duk lokutan da take zuwa basa haÉ—uwa."
Baki ta ɗan taɓe tare da yin mgna a zuci.
"Kai mutun komai tsari, wannan babu shakka baida gskya ne wannan ɓoye-ɓoyen waya sanima ko cin zan-zanane a jikinshi da saɗaure wata ƙil shiyasa yake kima tabka-tabkan Al'kyabbar ajikinshi dan ya boye abubuwan".
Murmushi Ummi tayi dan ta lura Shatu bata san mgnar ta fito fili ba.
Shiru Shatu tayi ganin alamun Ummi na jin wa'azin,
Hakane yasa tayi shiru sabida kada ta takura mata.
Ƙarfe ɗaya dai-dai na rana, akayi addu'a aka rufe taron sai kuma Goben in Allah ya kai rai.
Da yawa mutane basu fitaba,
mafi akasari Kur'anai suka É—auka suna karatu.
Kamar yadda Sheykh yakeyi.
Ƙarfe ɗaya da rabi aka kira sallan azahar.
Miƙewa Shatu tayi tare da cewa.
"Ummi bari inje inyi salla zan zo muyi wata mgna".
Cikin binta da ido Ummin tace.
"To".
Bayan anyi sallan azahar an idar ne, ta fito ta nufi É—akin Ummi, ganin bata nan ne, yasa ta nufi falo, nan kuwa ta sameta zaune bisa kujera.
gefenta taje ta zauna.
Tana zama wata Æ´ar matashiyar budurwa ta shigo,
cikin nitsuwa tazo ta rusuna gabansu tare da gaidasu, Cikin kula Ummi tace.
"Yauwa Saratu kin zo ko?".
Cikin nitsuwa tace.
"Eh Ummi nazo É—azu bakwa nan sai na koma sai yanzu na kuma zuwa".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Yayi kyau,". Inda Shatu take ta É—an kalla tare da cewa.
"ÆŠiyata ga Saratu. Saratu ga Saiyada Shatu matar Sheykh Jabeer".
Cikin mamaki da dariya sunan da Ummi ta liƙa mata wai Sayyada, ta kalli Saratu tare dake gaisheta cikin ladabi da biyayya,
fuska a sake ta amsa.
Cikin sanyi Saratu tace.
"Ummi me za'ayi ne?".
Gyara zama Ummi tayi tare da cewa.
"Ki wonke shinkafar masa dama na jiƙata, kana ki gyara mana ganyen alaiyahu, sannan ki fere Arish.
Sai kuma ki jajjaga kayan miya, ki yanka al'basa mai É—an yawa."
Cikin nitsuwa da bin umarni tace.
"To Ummi".
Ta ƙarishe mgnar tare da miƙewa ta nufi kitchen, tana shiga ta fara aiyukan da aka sata.