← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 183

Sashe 71

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Umaymah kuwa cikin daƙile fuska tace.
"Zauna kaci abinci".
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta, cikin tonƙoshe kai bisa kafaɗunshi ya ɗan taɓe baki kana a hankali yace.
"Sai na dawo".
Shiru tayi sabida ta lura sauri yakeyi.
Kanshi ya É—an juyo ya kalli Jakadiya cikin sanyi yace.
"Ummi lfy kuwa na ganki haka ba walwala".
Nisawa tayi tare da cewa.
"Ina fa zanyi wal-wala bayan Sheykh na cikin yanayin fushi, da rashin jin daɗi alamun na gaza riƙe amanar da uwar ɗakina ta danƙamin kenan".
Wani É—an guntun tsaki yaja tare da kallonta da kyau cikin sanyi yace.
"Ba komai Ummi kin riƙe duk amanar da aka baki, ba matsalar komai fa".
Cikin É—an sakin fuska tace.
"To Alhamdulillah, yanzu ina zuwa?".
Bayan Jalal ya É—an matso tare da cewa.
"Vallai zan je inada zama na musamman da sauran likitocin, domin jaddada musu kula da marasa lfyan da aka kai jiya".
Kusan a tare sukace to Allah ya taimaka".
Amin yace a taƙaice kana ya tsare Jalal da ido cikin tuhuma yace.
"Jamil jiya ina ka kwana?."
Cikin mamakin ya akayi Hammanshi ya gane bai kwana a gidaba ya É—an sunkuyar da kanshi cikin sanyi yace.
"Club naje to bamu taso da wuriba ne, sai na biya gidansu a bokina Hayatuddeen na kwana a can".
A hankali yasa hannunshin ya kamo kunnenshi tare da matseshi da yatsu sa biyu.
Da ƙarfi Jamil ya saki ƙara tare da cewa.
"Wayyo Hamma Jabeer bazan sakeba, na tuba".
Bai sakeba sai ma kauda kanshi da yayi yana kallon Umaymah cikin rauni yace.
"Kinji ba, shi kullum yana Club music sai kace ɗan ma kaɗa ko maroƙa, yaje ya kwana cikin yan iska azo ayi ta musu video ana yaɗawa duniya, ana liƙa sunana a ƙarshen sunayensu a social media kamar nine uban daya haifesu.
Haka kenan zanyi ta fuskar ƙalubale ina rasa yadda zan karesu ko in zagesu."
Ya ƙarishe mgnar rai a ɓace.
Ita kuwa Umaymah faÉ—a ta fara yiwa Jamil.
Shi kuwa gaban Jalal ya tsaya tare da kafeshi da ido.
Cikin tura baki Jalal ya fara bayani ba tare da an tambayeshi ba yace.
"Shiya shiga sabgata Ni kuma na dakeshi".
Cikin nuna ɓacin rai yace.
"Da yake kaine sarkin duka, ko kunyan Baba Kamal bakaji ba, ka kama Salis da duka kawai dan ka wuce da MP kana danna waƙe-waƙe da suɓale wonɗo shine tsokanar?".
Cikin yin ƙasa da kai yace.
"To ai zaginka yayi wai ilimi ka na banza tunda gamu a lalace bakayi mana wa'azi mun shiryuba, shiyasa Ni kuma na mishi aikin wanda ba shiryayyu ba".
Kwaffa yayi tare da cewa.
"Zagi kuma na nawa? Ba kune ke jazamin zaginba, kada ka yarda in sake jin ka taɓa shi Uhummm!".
Ya ƙarishe mgnar da kwaffa.
A hankali Jalal yace.
"Kayi haƙuri in sha Allah bazan sakeba".
Nan duk suka nufo cikin falon.
Suna isowa Hajia Mama na shigowa Batool na biye da ita a gefe.
Jafar kuwa da sauri ya koma bayan Sheykh tare da riƙe hannunshi ya fara ja alamun su tafi.

Shi kuwa Sheykh ƙara tsuke fuskarsa yayi ganin Batool cikin sauri ya gaida Mama, ta amsa fuska a sake tare da sanya masa al'barka.

Kana ya nufi hanyar fita, da sauri Jafar yabi bayanshi.

Umaymah kuwa da Ummi da Juwairiyya da Batool nan suka zauna suna É—an hirarsu.

Jalal kuwa da Jamil a tare suka fita, shi kuwa Haroon falon Jabeer ya koma.

Yana shiga ya kira Jannart bayan sun gaisa take tambayarshi yaushe zai je masarautarsu nan yake ce mata.
Yana nan tafe a satin nan.

Shi kuwa Sheykh Jabeer yana fita kai tsaye Valli Hospital ya nufa.

Asibitinshi mai zaman kanshi.
Asibitin da duk nahiyar Ɓadamaya babu kamarshi.
Asibitin da in kana cikinsa zakayi zaton a ƙasashen turawa kake.

Haka lamarin yaci gaba da tafiya.
Babu mai yiwa Sheykh Jabeer batun Aysha.
Itama Aysha gani take kamar ziyara tazo ba aureba.
Tunda ita dai da idonta bata taɓa ganin mijinba, sai dai taji sunanshi.

Sosai ta shaƙu da Hibba da Umaymah, hakama Gimbiya Aminatu da Ummi.

Lokuta da dama takan shiga Bathroom tai ta kuka sabida begen Æ´an uwanta.

Yau kwananta uku cur a gidan.
Idonta ma baiga ranaba.

Umaymah kuwa a sashin Jabeer yana fita.
Wata tirela ta iso har bakin Side É—in shi.
Nan aka fara sauƙo da kayayyakin ɗaki na amare.
Ana shigarwa ciki. Kana masu aiki na É—aure komai suna kimtsashi.

Sai kusan la'asar suka gama komai kafin.
Suka tafi kana su Umaymah suka taho.

Suna shiga asalin babban falon, Aunty Juwairiyya da Hibba suka haÉ—a baki wurin cewa.
"Wow masha Allah, Kai Umaymah ƙara so da sauri kiga falon nan yadda ya zama fadar masarauta".
Da sauri Umaymah da Ummi suka ƙara so.
Masha Allah! Masha Allah!! Masha Allah!!! Shine abinda kawai Umaymah keta mai-mai tawa, sabida kyau da tsaruwan falon yayi masifar kyau.

Kasan cewar falon irin ƙaton nanne mai faɗi da tsawo.
Wasu irin kujeru ne Daimond set masu masifar kyau da tsada, a shirya a cikin tamfatsen falon.masu Golding color mai ɗan karen sheƙi sai surkin Brown color mai sheƙin gaske da ratsin ruwan madara..
Kana haka ma kalan labuyen falon masu tsawo da faÉ—i da taushin gaske.sai wani table na glass mai Golding color da aka ajiye a tsakiyar falon bisa wani tattausan carpet mai azabar kyau.
Sai wani babban Tv dake liƙe a jikin bongon, kana gefen dama kuwa wani babban majigine manne wanda yake baiyana rubutun Kur'ani reras daki daki.

Can gefen kuwa steps É—in hawa Dinning area ne,
wanda aka canza Dinning table and chairs É—in,
Aka zuba wasu masu masifar kyau da tsadan gaske.

Ba'a wani cika falon da tarkace ba, amman yayi matuƙar kyau.

Tafiya kaÉ—an zakayi ta gefen hakun zaka ratsa cikin wani madaidaicin falo.
Yayinda na Jabeer yake hannun dama.
falon ɗakin da Umaymah ke tsauƙa in tazo kenan.
2 bedroom ne wannan falon yake dashi ko wanne da bathroom a ciki.
Kana sai Dinning area matsakaici daga nan gefen Dinning area kuma akwai ɗan ƙaramin corridor wanda zai sadaka da kitchen da store.
wasu irin datsa-datsan kujeru masu masifar kyau da É—aukar hankali aka kimtsa a falon wanda komai na ciki.
Peach and white coffee ne mai É—an karen kyau.
Hakama Dinning table and chairs É—in.
Still labulayen ma hakane.

Sai kuma cikin bedroom ɗin wanda duk girmansu ɗaya, haka yasa aka shirya wasu tagwayen gadaje masu masifar kyau suma Golding color ne mai sheƙi da ɗaukar ido.

Saɓanin side ɗin Jabeer komai Sky blue and white ne, wanda hakan yasa kana shiga sashinsa sai kayi zaton a sararin samaniya kake rayuwa.

Komai yayi kyau.
Especially kitchen É—in dake matsakaicin falon.

Domin wancan kitchen ɗin dake babban falon ba'a taɓa shi ba, hakama Side ɗin Sheykh.

Sai kuma sama wanda shi a rufe yakema, sam babu kowa a ciki.

Sosai fa su Umaymah suka yaba da kyan shirin da akayiwa wurin.

Nan suka zauna a falon.
Umaymah ce ta kalli Jakadiya cikin sauƙe numfashin tace.
"Alhamdulillah, gobe kuma zakiyi musu jagora shida matarshi su zaga ta gaida ahlin masarautar JoÉ—a, ta gansu su ganta su san juna, gudun kada a haÉ—u a wani wurin ba'a san junaba".
Wani gwauron numfashin Ummi ta sauke tare da cewa.
"A nan gizo ke tsakar ko ta ya zamu samu, Sheykh yayi wannan al'adar yadda ya dace ake kuma yinta, kinsanshi mutunne mai kunya, koda yana son abunma bare ba wani son abun yakeyi ba".
Cikin yarda da kai Umaymah tace.
"Kada ki damu yana É—aya daga cikin dalilin da yasani, na zauna sai naga kamun ludeyin zaman nasu."

Haka dai suketa tattaunawa,
Suna nan zaune Gimbiya Saudatu ta shigo tare da hadimanta, kana da Laminu da Baba Basiru da Baba Nasiru.
Cikin isa da ƙasaita ta nufi kujerar da duk canjin da akayiwa falon ba'a canzashi ba sabida kujerace ta masarautar Jalaluddin, cikin isa take taku yayinda ta bawa ƙofar shiga baya.
Cikin gatsali ta kalli Umaymah data tsareta da ido. Kallon uku saura tayi mata kana tace.
"Duk mutun muna fuki abin tsorone. Amman munafurcin balaraben Mutun yafi na kowa muni da bada tsoro.
In banda salon munafurci ayi aure yau kwana uku a gaza fito da amarya a nunata ga mutanen masarauta, bare a fanshi idonta."
Ta ƙarishe mgnar tana kai mazaunanta bisa, Kujerar.
Sai kuma tayi maza ta miƙa, jin muryar Jabeer da yanzu ya shigo, ko mgnar ta, ta ƙarshe baijiba.
Cikin isa da ƙasaita da rashin tsoronta, da kuma tsare fuska alamun Ni bani da lokacin ki, kuma ni ba sa'an yinki bane ya nuna mata hanyar fita da yatsarshi tare da yamutsa fuska cike da ƙarfin zuciya ya kalleta ita da ƙannen Mahaifin nashi yace.
"Fice min daga gida, bacci na dawo zanyi so banda lokacin jin ihunku na kar...!
Chapter 71 · 0% Book details