← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 183

Sashe 58

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zuwa har falonta suka wuce.
Wani kekyawan akoshi mai masifar kyau ta É—auko mishi.
Ta ajiye a gabanshi.
Inda yake zaune a ƙasa bisa carpet ya naɗe sawunshi.
fork É—in dake saman fefeyin ya É—auka.
Daddageggen gaseshen jan namane wanda yaji wuta ya gasu gashin tukunyar ƙasa yayi tiɓis.
Sai wani irin ƙamshi na musamman yakeyi,

A hankali yake sa Fork É—in yana yagan tattausan tsokokin yana sawa a baki.
Ita kuma tana zaune gefenshi.
Tafashesshen madaran shanu mai ɗan ɗumi ta miƙa mishi a wata ƴar ƙwarya mai kyau.
Taune naman yayi tare da haÉ—iyewa kana cikin zuba mata ido yace.
"Dole sai na karɓa da hannun nane? Ki ajiye mana.
Da wanne hannun zan amsa tunda inacin abinci dana daman".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Dole sai ka amsa, bazan baka shi a ƙasa".
Kanshi ya É—an rausayar tare da cewa.
"Allah ya nuna min ranar da za'a bar.
Wannan tsare-tsaren shamfi na masarautar Joɗa. Komai da ƙaida da yadda ake yinshi".
Ita dai miƙa mishi ƙwaryar takeyi dole ya ajiye spoon ɗin yasa hannunshi ya amsa.

Nan suma sukaci gaba da hira.
Sai kusan sha É—aya Umaymah da Jakadiyarsu suna fito.
A nan Gimbiya Aminatu ta ajiyesu suma saida sukaci gashin nata kafin suka tafi.

Kafin su isa Side É—insa dai sha biyun dare tayi.

Haka yasa suna isa suka samu ba kowa a falon.

Sai Haroon da suke jiyo muryar sa, a falon Jabeer.

Cikin nitsuwa ya matso kusa da Umaymah a hankali yace.
"Sai da safe Umaymah kiyi bacci ki huta."
To tace har ta juya zata tafi sukaji Muryar Haroon yana cewa.
"Abba yazo wurinki zaku gaisa bai samekiba, nace mishi kun tafi wurin Lamiɗo yace, to saida safe ya gaidaki da hanya Hajia Mama ma yanzu ta fita, tace Lamiɗo ya riƙe mata ƙanwa".
Murmushi tayi tare da cewa.
"To Allah ya bamu al'khairi saida safen".
Amin Amin suka ce.
Kana shida Haroon suka wuce Side É—insa.

It's kuma Umaymah da Jakadiyarsu suka wuce.
Side ɗin da kullum in dai Umaymah tazo nan take sauƙa.

Suna shiga suka samu, tuni Hibba tayi bacci, wannane ya basu damar tattauna wasu mahimman sirrukansu.

Nisawa Umaymah tayi bayan ta saurari jawaban Jakadiyarsu Jabeer cikin tsantsar tafasar zuciya da tarin baƙin ciki tace.
"Uhummm suyi dai Ni nan ina dai-dai- da ƙugun ko wanne shege da shegiya,
In sha Allahu zasusha mamaki.
Zasuga yadda Ubangiji ke ikonsa, ban cire raina Æ´ar uwarta zata sake rayuwar enci da salama, da izinin Ubangiji zataga sakayar waÉ—anda suka cutar da ita da yaranta a gaban idonta.

Cikin zubda hawaye Jakidaya tace.
"In sha Allah, sai farin ciki ya dawo, a sashinta, inata addu'a a kullum a cikin dukkan sallolina, Allah ya kare ahlinta, ya kuma baiya gsky tayi halinta kowa ya gani".

Amin Amin Umaymah tace tare da share hawayenta.

Washe gari ranar Alhamis. Ta kama yau kwana shida da faruwar gasar ShaÉ—i, kana gobene za'a koma dan ramuwa,
A goben kuma zai cika kwana goma da kisan gilla da kafurai ƙabulun Ɓachama sukawa Fulanin Rugar Bani.

Misalin ƙarfe sha biyu na safe.
Fadar Sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa, cike take maƙil da tawagarsa kama daga.
Galadima, Waziri, Wambai, Dan buram, Dan iya, Ɗan isa, Ɗan Kade, Sarkin fada, Sarkin yaƙi, Sarkin Dowaki, Sarkin Gabas, Sarkin Kudu, magayaƙi, Jarma uban doma, Makawa Ɗurɓi, Turaki, Da dai sauran members ɗin masarautar baki ɗayansu, an cika anyi maƙil.
Sallama na tsaye can bakin ƙofar shigowa.
Dogari kuma suna tsaye gefen hagu da daman LamiÉ—o.
Suna rike da mafici sunayi mushi fifita, É—anzagi kuma yana gefe,
Kana wasu fadawan duk suna gefen.
Gyaran murya LamiÉ—o yayi tare da gyara zaman shi cikin shugarsa ta sarakuna masu al'farma, a hankali yace.
"To da farko dai fatan duk kowa na lfy".
Da sauri ÆŠanzagi yace.
"Sarki ya gaisu yana yi muku fatan alkhaiy".
Sai ya kuma juyo ya kalli LamiÉ—o tare da cewa.
"Godiya suke."
Kanshi ya ɗan jingina da tattausar kujerarsa da masu son gadonta sunfi a ƙirga, cikin ƙasaita yace.
"Kamar dai yadda muka tattauna, kwanakin baya akan sarkin Garin Shikan,
to yanzu zan zantar da hukunci.
Sarkin aike na bada umarni kaje garin Shikan ka karɓo min sandar sarautar Shikan ka kawo min shi, yau ɗin nan.
Kaje da jagorancin Galadima, da Matawalle da Makawa, sai sarkin yaƙi".
Da sauri duk suka runsunar da kayu kansu tare da cewa.
"An gama".
Nan take kuwa suka miƙa suka tafi.

A cikin gida kuwa. Tunda asuba da Jabeer da tawagar ahlinshin suka dawo masallaci.
Kai tsaye É—akin Umaymah ya nufa, suna biye dashi a baya.
Bisa sallaya suka sameta riƙe da al'ƙurani mai girma tana karatu cikin tsananin nitsuwa.

Ganin hakane duk suka fito falo.
Nan Aunty Juwairiyya taja Ummi suka tafi side É—in ta da Hibba da Æ´ar aikinta suka shiga kitchen.

Jalal kuwa shine yaje wurin Ya Jafar, don bashi mgni kamar yadda Jabeer ya umarceshi.

Jamil kuwa waya yakeyi da sabuwar budurwarsa da ya samu.
Wacce yake masifar sonta,
Ko yaushe suna liƙe da juna a waya.

Haroon kuwa a falon Jabeer ya zauna yana kallon lbrin CNN.

Shi kuwa Sheykh Jabeer.
A hankali ya wuce ta gaban Haroon.

Gefen gabas ya fuskanta, inda labulaye sukayiwa wurin ƙawanya.
A hankali yasa hannunshin ya yaye labulen.
Wani ƙofa ya buɗe a .
Sai ga wani É—an siririn corridor.
Shiga yayi, kana ya saki ƙofar ta koma ta mannu da ƙofar sai dai bata rufuba.

A hankali yake taku cikin nitsuwa,
Lips É—in shi na É—an motsawa alamun tasbihi yakeyi.
Tafiya mai ɗan tsawo yayi sai gashi ya kuma riski wata ƙofar.
Hannunshi yasa ya murɗa key ɗin ya buɗe, ƙofar.
Sai ga kuma wata ƙofa irin ta ƙarafuna kana dai iya hango woje.
Buɗe wannan ƙofarma yayi.
A hankali ya kutsa kai.

Wani irin sassanyan ajiyan zuciya mai tsawo yaja ya sauƙe a hankali.
Idonshi ya lumshe sabida wani irin sanyi mai masifar daÉ—i daya ratsa mishi jiki da zuciya.

Wani irin É—an madaidaicin Garden Park ne mai masifar kyau.da sanyi da tsaruwa.

Daga nan bakin ƙofar daya fito ɗin.
Tayis ne fari tas a malale iya ganinka, sai gefen damanshi da bishiyoyin ayaba masu masifar duhu da sanyi dake jere reras.
Gefen hagunshi kuma bishiyoyi mangoro ne irin yan duƙus-duƙus ɗin nan ke jere,
Reras.
A hankali yake taku yana tafe yana tasbihi.
Yana jin kukan tsuntsaye mai daÉ—in ji yana ratsashi.

Tafiya kaÉ—an yayi sai gashi ya baiyana a wani irin wurin mai masifar kyau.
Wasu yan zagayen gini dakalin bulok bibbiyu akayi a ƙalla sunfi hamsin.
A ciki ko wanne zagayen akwai bishiyar dabino. Na gabanta inabi na gaban inabi tuppa, kana sai Yazawa, sai kuma na tsada, daga tsada sai na kanya, sai goruba da na giginya.
Cikin ko wanne zageyen kuma ƙasanshi koriyar ciyawa ce mai sanyi.

Can tsakiyar filin kuma wata iriyar ƙoramace mai masifar sanyi,
Ruwanshi na kwance fari ƙal-ƙal bakin wurin kuma jeren bishiyoyi goibane wanda sukayiwa kwaramar inuwa.

Gaban ƙoramar kuma wasu irin kujerun silver ne masu masifar kyau da sansi a jere a ƙalla sun kai goma zuwa ashirin.

Can gefenshi kaÉ—an kuma wani shingene aka zagaye da waya.
Shuke-shuken gargajiya akeyi a wurin.

Nan kusa da ƙoramar kuma shingen farar waya akayi a cikin ta wanda akayi ƴan ɗakuna-ɗakuna a cikin.

Tsuntsaye ne a ciki iya ganinka ko wanne da muhalli shin.

Kama daga Tattabaru farare ƙal-ƙal.
Sai kuma tsuntsu carki jajaye masu kyan launi ga kuma kanari da suke blue.

Sai kuma zabbi da suke yawo a ƙasa tako ina.
Can bakin ruwan kuma agwagin ruwa ne sunfi ɗari ƙwa-ƙwa.

Sai kuma zabbin daji.
dangin tsuntsaye dai babu irin wanda babu.

Ido ya zubawa tsuntsaye tamkar mai son yin magana dasu.

A hankali ya sunkuyar da kanshi jin tattausan gashin ÆŠawisun Masarautar JoÉ—a da ya kai shekaru masu tarin yawa.
A hankali ya rusuna tare dasa tafin hannunshi ya shafa dai-dai ƙunɗun Ɗawisun inda wurin yake mai kalar blue mai kyau sabida Sheykh blue ne kalar da yafi so.
A hankali ta fara taku, ta juya mishi baya kana ta ɗaga bindinta sama samɓal har yana iya taɓo geminshi.
Wani irin takun ƙasaita tayi kana ta buɗa fikafikinta ta bazasu, ta fara tafiya a hankali.
Wannan itace suntsuwar da muddin mutun ba jinin Masarautar JoÉ—a bace, in ka shigo mata gaba gaÉ—i ba tare da an gabatar mata kai ba, zatayi ta yagune mutun tana caccakarshi.
Amman muddin dai kai jinin Masarautar JoÉ—a ne, kana shiga zata zo gabanka.
Tayi maka hakan.

Sai dai kuma bayan yin hakan in mutun nada wata zazzafar nasaba a masarautar misali shine sarki maici to in tayi wannan baza fikafikinta takanyi ta zagaya sarki sau bakwai kafin ta tsaya a gabanshi sai sarkin ya umarceta data tafi kafin zata tafi.

To babban abinda ya ƙara jazawa Jabeer matsala a rayuwarsa shine,
Duk sanda yazo gaban tsuntsuwar ÆŠawisun nan sai tayi mishi wannan abin da zagaya sau bakwai abinda a tarihin masarautar sarki kawai yakeyiwa abin.

Matsalar abin a gaban Barrister Kamal da kuma Baba Bashiru da Abba sai LamiÉ—o ne ta fara yimishi wannan abun.
Tofa ta bakin Baba Basiru ne mgnar ta zaga kunnen mazauna masarautar JoÉ—a.

Babban tashin hankalin masu son gadar wannan kujerar, shine yadda side É—in Jabeer ke kusanci da Garden É—in da take ciki.
Tashin hankalinsu ya ƙara tsananta ne tun randa Suka ga Lamiɗo yasa an buɗawa Jabeer hanyar shiga wurin ta cikin falonshi ba sai ya zagaya yabi hanyar da kowa ke bi ba,
Ya zama shida LamiÉ—o sune masu hanya kowa daga falonshi zai shiga wurin.

A hankali Jabeer yayi murmushi tare da kallon yadda tsuntsuwar ta gama zagayashi kana tazo ta tsaya gabanshi tare da baza fikafikinta.
Cikin harcen Larabci yace mata.
"Fatana dai ba bauta min kikeyi ba! Domin babu wani abin bautawa da gsky sai Allah, wanda shine ya halicce ni ya halicceki.
Ni kuma ba kowa bane face halittarsa, sai dai na kasance cikin halittarsa mai girma da karrama fiye da komai, dan shi da kanshi yace.
Walaƙad karramna bani Adam."
Wani irin juya kai tsuntsuwar tayi kana ta meda fiffigefa ta rufe, kafin ta juya ta nufi wani kekyawan wurin da aka ware mata, inda take tare da yayanta da mijinta.
Chapter 58 · 0% Book details