← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 183

Sashe 171

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin wani irin yanayi ta faɗa jikinshi ta rungume gam a jikinta murya can ƙasa tace.
"Ciki kuma Yah Sheykh?".
Da sauri yace.
"Yes ciki mana Aish".
Da sauri tace.
"A a ni kam bani da wani ciki bayan na cin abinci".
Da sauri ya ɗagota har lau hawayen farin ciki na zubo mishi babu ƙaƙƙautawa cikin ruɗani yace.
"No kada kice min haka. Kada ki cemin baki da ciki ga nan alamomi duk sun baiyana.
Kina da cikina mana Aish, ya zaki cemin baki da ciki".
Cikin tura baki da son ɓoye mishi batun tana da cikin tace.
"Ni dai bani da ciki".
A kiɗime ya miƙe tsaye, tare da cewa.
"Ok tashi, tashi mu tafi Valli muje in duba".
Da sauri ta maƙe kafaɗarta tare da cewa.
"Ni dai bani da ciki".
Ta ƙarashe mgnar tana sa hannunta cikin boxes ɗin sa.
da sauri yace.
"Ni kada ki cemin haka muje in gwada in ga Zahiri".
Da sauri ya dawo ya zauna jin yadda take mishi wani salo.
Murya a mace tace.
"Sai dai in yanzu zaka bani cikin".
Ta ƙarashe mgnar da sigar yaudara da mantar dashi batun cikin da tasan yanzu watanninsa biyu harda kwanaki, a jikinta.
Ruggume ta yayi da ƙarfi tare da cewa.
"Tun tuni ai na baki ciki Aish, wlh kina da ciki.
Ya za'ayi ina Dr ki musa min".
Bakinsu ta haÉ—e wuri É—aya tare da fara mishi wasu abubuwan da dole ya haÉ—iye regowar mgnarshi.
Yayinda zuciyarshi ke cike fal da farin ciki.

Kiran sallan la'asar ne yasa suka sahirtawa juna.
Ganin lokacin sallan yayine yasashi yin wanka a gaggauce ya tafi masallaci.

Ita kuwa Shatu.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da sa hannunta ta shafa ɗan lafeffen cikinta.
Lokacin da take wonka.
murmushi tayi tare da cewa.
"Abbanka yana cikin tarin farin cikin gano alamun kana jikina, duk da ɓoye mishi da nakeyi.
sabida ina gudun kada ya gaza ɓoye farin cikin sa har magautansa su gano da kai su rabani da kai."

Sai kuma ta lumshe idonta.
Tana ganin yadda jikin Sheykh yayita rawa yana fidda hawayen dake bayyana tsantsar jin daÉ—insa ziryan.
A hankali tace.
"Abbanka yana sonka so mai tarin yawa, wanda har ya kaishi da zubda hawaye.
Ina sonka so mai yawa wanda ya zame min dole in sirrantaka, dan É—anyen mamlngoro buya yake sai ya nuna ya baiyana. Ina soron magautan Abbanka su dawo gareka".
A haka tana surutai taje tayi salla.

Tana idarwa tajoshi a falo yana cewa Ummi.
"Ummi ina Aish?".

"Tana É—akinta, tana salla".
Ta bashi amsa,
Kai ya gyaÉ—a tare da cewa.
"In ta idar tazo".
Yana faÉ—in haka yayi cikin falonshi.
Ita kuma Ummi to tace kana ta shigo ta gayawa A'isha.

Ita kuwa to kawai tace tana fita.
Ta nufi sashin Aunty Juwairiyya sabida tasan in taje mgnar su tafi asibiti zai mata.

A falo ta samu Aunty Juwairiyya gefenta ta zauna.
Hannun tasa ta kamo hannun Mimi É—iyar Aunty Juwairiyya kana a hankali tace.
"Yah Jafar fa".
Cike da mamakin sauyawar da Aishan tayi mata a ya kwanakin nan tace.
"Bai dawo masallaci ba".
Kai ta jinjina kana a hankali ta juyo ta kalli Aunty Juwairiyya cikin sanyi tace.
"Dan Allah Aunty Juwairiyya kiyi haƙuri da wasu abubuwan dake faruwa a wasu ma banbanta lokuta.
Abune da dole ya faru tunda ban san gaibuba bare in banbane abunda ke ɓoye, sai iya abinda Allah yaso in sani ya sanar dani ya nuna min cikin hikimarsa".
Cikin sanyi da rauni Aunty Juwairiyya tace.
"Uhummm Shatu kenan ba komai.".
Tayi mgnar hawaye na zubo mata.
Da sauri Shatu tace.
"Dan Allah kiyi haƙuri".
Kai ta jinjina hawaye na zuba murya na rawa tace.
"Nayi kuka a lokuta da dama, na rasa wa zan gayawa damuwata ya fahimceni, kin nuna kina zargin zan cutar dake da kuma Æ´an uwana.
Mahayarfiyarsu Yah Jafar da mahaifina uwa É—aya uba daya suke.
Bani da kowa sama dasu a Masarautar Joɗa, sune ƴan uwana sune farin cikina rana ɗaya na fahimci kina zargin zan cutar dasu nayi kuka mai ƙuna a raina naji tsoron in gayawa Umaymah kada itama ta zargeni.
Ta yaya zanyi haka, Æ´an uwana na jinina.
Ta ya zan cutar dasu.
Bayan tarin son da nakewa Yah Jafar wanda yasa duk da halin da yake ciki a haka na dage akayi mana aure wanda a lokacin su Sitti sun so a fasa aurena dashi.
Ina son Sheykh a raina tamkar yadda nake son Ibrahim É—in mu".
Sosai take kuka alamun ƙuna a ranta.

Cikin sanyi da zubda hawaye Shatu ta riƙo hannunta a hankali tace.
"Aunty Juwairiyya, akwai dalilin nuna rashin yardarta.
Amman yanzu na gano ta ina matsalar take.
Ina neman al'farmar ki sallami Huwaila mai tayaki aiki.
tana cutar dake da yaranki da ingiza cutar Yah Jafar ita ke ƙara sa mishi abinda ke hanashi mgn, nanma Allah yayi yana yawan zama da al'wala da yawan karatu.
Ba dan hakaba da tuni sun kaudashi a masarautar JoÉ—a sun medashi kan juji.
Ki kuma kula kisa lura.
In babu halin ki sallameta kuma to ki cireta a masu tayaki aikin girki".
Cike da mamaki da tsoro Aunty Juwairiyya tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Cikin nitsuwa.
"Tace no kada ki tada anhlalinki ki lura zaki gane abinda nake nufi.
Kiyi kwana bakwai kacal ba tare da kin bawa Yah Jafar abinci da Huwaila ke dafawa ba, zakisha mamaki".
Cikin gamsuwa da shawarar Shatu tace.
"In sha Allah kuwa zan gwada da izinin ubangiji".
Daga nan sukaci gaba da hirarsu.
Yah Sheykh kuwa jin shiru-shiru bata zo bane.
Yasa ya fito.
Ya tambayi Ummi da ita kuma a zatonta suna can tare.
Ganin bata É—akinta ne Ummi ta kirata a waya.
Cikin murmushi tace.
"Ummi ina wurin Aunty Juwairiyya ne".
Jin hakane yasa Sheykh yace.
Ba matsala a barta.
Daga nan ya juya ya fita, kai tsaye gidan Malam Abubakar ya nufa.
Inda suka ƙara tattauna batun Sulaiman.

Ita kuwa Shatu tun jiyan gudunshi takeyi.

Wayewar garin yau kuma sun tashi da aiyukan tarban su Umaymah.

Shi kuwa Sheykh wunin yau duk yana tare da LamiÉ—o da Galadima suna tattauna wa.

A ɓangaren su
Aysha ƙarfe 3 suka shiga kitchen
girki na musamman suka fara ƙoƙarin shiryawa baƙin nasu,
Cikin kula Ummi ta kalli Sara da yanzu shigowar ta tace
"Yauwa Sara ƙaraso ki yankamin waɗan nan".
TafaÉ—i tana nuna Mata Karas da green beans da kabejin data rigada ta wankesu ta tsane cikin kwando
"To". Sara tace tare da karasowa tad'au wuka ta fara yankan kamar yadda aka umurceta.

Shatu kuwa gaban tukunyar data É—aura.
Kan gas taje tabuÉ—e tuni shin kafar da tazuba ciki yatafasu yadda take so irin tafsaa É—aya zuwa uku'nna,
sauƙewa tayi kana tatsaneshi cikin kwando,
Wata tukunyar ta É—aura tasulala Mai a ciki tare da wasa yankakken al'basa a ciki
Al'basar tana soyuwa Ummi tamiƙo mata jajjagegen kayan miyar da ta jajjaga bawani mai yawa bane tazuba cikin man,
shin kafar data tsane ta É—auko tarika zubawa cikin man tana mosawa sai da tajuyeshi Kaf, kana takalli Ummi tace
"Ummi karasa wanna". TafaÉ—a tare da Mika Mata ludayin dake hannunta wanda take motsa shinkafar dashi,
amsa Ummi tayi ita kuma tamatsa can gefe.

ÆŠan ma dai-dai-cin roba taÉ—auka ta nufi in da fridge yake tabuÉ—e taÉ—ebi hanta mai yawa sai jan nama É—an dai-dai.
Wanke hantar da naman da taÉ—ebo cikin roban tayi tazubashi cikin tukunya kana ta kunna wuta,
Citta da kanumfari da tafarnuwa tazuba a ciki sannan tazuba thym da curry da Maggi sai É—an gishiri É—an dai-dai, kana ta É—auki al'basa ta yankashi mai É—an yawa
ta wasa a ciki kana ta rufe tukunyar.

Attaruhu da al'basa ta É—iba tawanke ta jajjagasu.

Tuni Naman ya dahu har ruwan cikin sa ya kafe yayi dai-dai yadda takeso
Sai wani tashin daddaÉ—an kamshi na namusamman yake,
A nitse tasauke tukunyar taÉ—an barshi yahuce,
Sannan taraba hantar da Jan namar ko wanne tacire shi daban,
hantar tajuye cikin madaki ta dakeshi yaÉ—anyi laushi, kana tazuba cikin wani roba Mai d'an faÉ—i.

Attahuru da albasan da ta jajjaga tazuba cikin dakekkeyer hantarna, sannan tafasa kwai guda15 takaÉ—a tajuye ciki,
tazuba curry da Maggi da gishiri daÉ—an garin citta kad'an tayanka al'basa tazuba ta É—ibi Karas acikin wan da Sara ta yanka ta haÉ—a da É—an
Ƴaƴan green beans tazuba ciki,
kana ta É—an zuba mai me É—an yawa ba sosai ba
sokokim naman nan ta yayyanka shi kanana tatajuye ciki, motsashi tayi sosai, kana taɗaki laida tafara ƙullawa.

Matsowa kusa da ita Sara tayi kasan cewar tagama aikin da Ummi tasa ta,
idan Shatu tazuba haɗin cikin laida saita amsa ta ƙulla, a haka har suka gama ƙullashi kamar ƙullin alale,
A tukunya tajuye
Tazuba ruwa taÉ—aura kan wuta.

Ummi kuwa tuni tagama shirya lafiyayyen Friend Rice wan da yaji wadataccen nama da sauran kayan haÉ—i.

Wani haÉ—É—en foodflaks mai kyan gaske mai É—an girma Ummi ta É—auka tazuba a bincin, kana taÉ—au wata karamar kula tazuba ragowar abincin a ciki.

Shatu kuwa matsowa tayi jikin tukunyar ganin yanda yataso, har yana É—aga murfin tukunyar murmushi tayi lokacin data buÉ—e murfin ganin Yadda yahaÉ—a jikin sa yayi wani tip-tip dashi gwanin sha'awa,
Laida É—aya taciro taÉ—aki plate tasa a ciki kana ta yaga laidar da fork sabo da tirriin da yake bazata iya sa hannunta cikiba,
Wani hamshakin kamshine yabigi hancinta nan take kamshin yagauraye ilahirin cikin kitchen É—in, kamshin ta zuko tare da lumshe idanunta kana
tayan koshi takai baki Kai ta gyad'a alamar gamsuwa,

Murmushi Ummi tayi kana tamasota ganin yanda take gyaÉ—a kai har tana wani lumshe idanu,
Murmushi tayi tare da cewa.
"To zauna kici Mana Aysha da ma ai bakici wani abun kirkiba tun safiya".

Idanunta tabuÉ—e tare da faÉ—in
"Mugama tukun zamuci da su Umaymah nasan ma yanzu haka suna can suna shiri ".
Ta ƙarshe mgnar tana sauƙe tukunyar.

Wata haɗeɗɗiyar kula Ummi tamiko mata nan suka fara cire haɗin hanta da nama da kwan nan wanda yajuye yadawo alale suka rinƙa cireshi cikin laidar suna sakawa cikin kula,
Sara kuwa in da suka ɓata tafara tsaftacewa, suna gama cirewa Shatu tamaida kular gefe batare da ta rufe kular ba,sotake yaɗan huce kafin ta rufeshi dan kada zufa ya ɓatashi.
Chapter 171 · 0% Book details