Sashe 144
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin wani irin yanayi ya rumtse idanunshi da ƙarfi kana ya buɗesu da sauri, yayinda tuni suke jazir kana shima jikin nashi tsuma yakeyi.
Hannunshi yasa ya ruggumeta gam-gam a jikinshi da kyau, al'kyabbar jikinshi ya ware da kyau ya buÉ—a ta kana ya rufeta dashi rib. Sabida yadda jikinta ke rawa abin ya zarta zaton mutun.
Cikin wata iriyar murya mai cike da diriricewa tausayi rauni murya a sarƙafewa yace.
"A'ich! A'ish!! Kiyi haƙuri I'm so sorry, in sha Allah bazan sakeba, ki yafe min kinji".
Ina babu amsa sai ƙara cusa kanta da takeyi jikinshi bata kuma haiyacinta har yanzu bare ta fahimci me yake faɗin.
Cikin taune lip ɗinsa na ƙasa yace.
"A'ich ki nitsu ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameki. Kinji ba gani ba.
Babu kowa da zai cutar dake da izinin Allah".
Ina ita dai sai ƙara ƙwaƙumarshi takeyi.
A hankali ya juyo ya kalli gefenshi jin ana ɗan ƙwanƙwas glass ɗin motar,
Ƙasa yayi da glass ɗin.
Ya Hashim ne da Affan da Jalal Imran da Sulaiman sai Kabir ƙanin su Haroon wanda suka haɗa uba, kuma a motarsa suke da kuma motar ɗaya Haroon dake hannun Jalal,
kasan cewar bai sauƙe gilashin sosaiba, basa iya ganin Aysha dake kwance a jikinsa.
Affan ne ya É—an motse kana yace.
"Ya Sheykh mufa gobe sammako zamuyi, shiyasa muke son key É—in motar ya kwana a hannunmu".
Kanshi ya jingina da jikin kujera kana ya kalli Ya Hashim da Sulaiman da Imran yace.
"Ku bari sai jibi ku tafi, mana kunzo jiya, gobe kuce zaku koma ku dai bari jibi".
Kai Sulaiman da Ya Hashim suka gyaÉ—a alamun yarda.
daga nan suka juya suka nufi motar Kabir tare da cewa.
"To sai da safe".
Allah ya bamu al'khairi yace kana ya É—aga glass É—in.
Su kuma suka shiga mota sukaja suka tafi.
A can gida kuwa bayan duk sun watsa ruwa kowa yayi shirin baccine, sai kuma duk suka firfito falo suka kafa hira irin ta Æ´an uwa in an haÉ—u a biki.
Umaymah ce ta kalli Aunty Rahma dake kwance gefenta tayi pillow da cinyarta tace.
"Wai ina Safiyyah da Aysha ne, su ban gansuba".
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"Safiyyah dai tabi mijinta, ita kuma surkar tawa inaga itama suna tare da É—an naki".
Ummi ce ta É—an kallesu tare da cewa.
"Ai kuwa ni tun É—azuma naketa kiranta bata É—aya wayar".
Mamma ce tace.
"Halan suna can tare".
Hajia Mama dake zaune gefen Umaymah ce ta ɗan kishiƙiɗa da tum-tum tace.
"Uhummm". Daga nan bata kuma cewa komaiba.
Ummi kuwa ci gaba da kiran Aysha tayi, wayar tana shiga amman ba'a É—agawa.
A can kuwa wurin Sheykh da Aysha.
Gyara zamanshi yayi da kyau bayan, abokan Abbanshi duk sun tafi.
Gyara mata zamanta a jikinshi yayi da kyau yadda bazata takurashi yin tuƙiba gaba ɗaya zuciyarshi a hautsine take, ya rasa gano wake tura mishi wasu pictures ɗin Shatu da mishi zantukan ita yar iskace.
Allah ya sani baya zarginta ko wannan abun ya fara faruwa ne dan ta ganshi da kamanninsa na sirri, da fari tsiya yake mata, sai kuma yake jin dadin yanayin yakanyi ta murmushi in ya tuno tsoron da yake gani a kwayar idanunta, yana mmkin yadda take gaza gane muryarsa, to batun hotunanta fa da ake tura mishi da wani yanzu ya gama gamsuwa aiki magautansa ne.
Ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi tare da tada motar, A/C'nta ya kunna, sabida wata iriyar fitinenneyar zufar dake tsastsafo musu su duka biyun.
Ƙafarshi ya murza ya kaita kan birki, lokacin da ya iso gab da bakin gate, ɗan tsayawa yayi aka buɗe musu gate ɗin, kana ya cilla hancin motarsa woje.
Da hannun É—aya yake murza siterin motar, hannun damanshi.
Kana hannun hagunshi kuma na ruggume da ita.
Zuwa yanzu yaji rawanda jikinta keyi ya fara tsagaitawa.
Ita kuwa Aysha cib tayi a jikinshi tana jin yadda bugun zuciyarshin ke harbawa da sauri-sauri kana kuma da ƙarfi-ƙarfi.
Tafiya mai tsawo sosai, har ya fara fitowa wojen gari.
A hankali ya ratsa wani titin ya shiga, tafiya kaÉ—an yayi ya ratsa cikin wani tamfatsetsen hotel mai masifar kyau wanda yake killace a bayan gari, sabida manyan mutane ba kasafai suke son hotel É—in dake sarari ba.
Bayan ya gyara parking ya kashe motar.
ÆŠan sunkuyar da kanshi yayi kanta
sannan a hankali yasa tafin hannunshi ya tallabo kanta, cikin sanyi ta buÉ—e idonta.
Ta É—an kalleshi kana ta medasu ta lumshe.
Manyan yatsunshi yasa yana É—an shafa kuma tunta dasu.
Kana a hankali yace.
"A'ish kiyi haƙuri kinji bazan sake yin nesa da keba".
Sai kuma ya É—anyi shiru kana ya kusanto da fuskarshi gareta sosai, a hankali ya hura mata iskar bakinshi kan idanunta tare da cewa.
"BuÉ—e idon Yah Sheykh É—inki ne, ba Jahan ba".
A hankali ta buÉ—esu, ta kalleshi.
Wani dogon nannauyan ajiyan zuciya ta sauƙe tare meda kanta saman ƙirjinshi".
A hankali yace.
"Wayyo Mamy zata karya min cinya, sauƙa muje ciki."
Bata kulashi ba, ganin hakane yasa ya buɗe ƙofar kana ya ɗan mirginata gefe, sannan ya sauƙo.
Gyara tsayuwarshi yayi tare da gyara hiraminshi ya rufe fuskarsa da kyau sannan yace.
"Aish fito ko BoÉ—É—i".
Da sauri ta zuro ƙafafuwanta woje sabida gani take yana matsawa Jahan zai zo.
Marfin baya ya buÉ—e. Wasu ledodi masu kyau ya É—auka kana ya rufe motar tako ina, sannan ya juya, ya nufi ciki da sauri ta bishi a baya.
Tafiya kaÉ—an sukayi suka haÉ—u da Jamil.
cikin sauri ya iso gabansu, key ya miƙa mishi tare da cewa.
"Room number 37 VIP Side".
Kai ya gyaÉ—a tare amsar key É—in.
"Sai da safe". Yace yana mai wucewa.
"Allah ya bamu al'khairi yace kana.
Suka wuce shima ya wuce.
Suna shiga, É—akin.
A hankali ya miƙa mata ledodin.
Sannan ya juyo ya rufe ƙofar, duk da yasa Jamil ya bincika masa ɗakin saida ya ƙara duba jikin ƙofar da makunnin fanka da A/C da kyau. Kana ya dawo tsakiyar ɗakin ya ɗaga kanshi sama ya kalli sanan sosai hakama ya shiga bathroom ya duba komai saida ya tabbatar ba komai daga cikin ababen da ya kamata duk musulmi in larurar zuwa hotel ya kamashi ya tabbatar da ya bincikesu da kyau Especially in ku mata da miji ne.
Ita kuwa Aysha da Ido take binshi, ta rasa me yake nema a duk ɗakunan hotel da suka taɓa zuwa.
Bathroom É—in ya koma, bai daÉ—e sosai ba, ya fito, bisa alamu ruwa ya watsa, kana dan al'kyabbar shi na hannunshi yanzu dagashi sai jallabiya.
ninke al'kyabbar yayi, kana, ya ajeshi gefe, inda ya ajiye hiraminshi da wayoyinshi.
Ledodin hannunta ya amsa tare da cewa.
"Je kiyi wonka kizo ki kwanta".
Cikin sanyi tace.
"Ni nayi wonka É—azu".
Kanshi ya gyaÉ—a dan ya lura har yanzu a tsorace take.
Zama yayi bisa sallayar da yasan Jamil ne ya shimfiÉ—a misa kana yace.
"To zauna kici abinci".
Da sauri tace na ƙoshi".
Ido ya É—an zuba mata, kana yace.
"Uhummm, to kwanta kinga gani nan kusa babu abinda zai sameki da izinin ubangiji".
Da sauru tace.
"Toh".
Ta ƙare mgnar tana nufar kan luntsumemen gadon.
Ledodin da Safiyyah ce ta ajiye musu cewa na abincin walimar ne kuma tace mishi Ummi da Umaymah da Mamma ce da kansy sukayi aikin ne yasa, ya gamsu da aikin kuma zaici.
Sosai yaci naman zabuwar da Arish É—in.
ÆŠan saura kaji akayi na zabbin na musamman ne shiyasa su Umaymah suka yishi da kansu.
Ruwa yasha, kana ya gyara zamanshi tare da tattare sauran bakin ledar ya ƙulle. Jingina bayanshi yayi da jikin gadon.
Kana ya fara rairai karatun al'ƙur'ani cikin zazzaƙar muryarsa haka yasa yaji sanyi zafin da zuciyarsa keyi na fahimtar sharrin magautanshi har baiwar Allahr da bataji bata ganiba, kawai dan ta kasance matarsa magautansa ke bita da sharri.
A hankali Aysha ta sauƙe ajiyan zuciya, tana mai jin daɗin sautin muryarsa da karatun da yakeyi a hankali.
Mirginowa tayi bakin gadon.
Kana ta kwanta tayi lib ta matso da kanta kusa da kafaÉ—unshi.
Lokacin É—aya taji bacci na fizgarta.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya juyo ya kalli wayarshi daketa haske alamun ana kiranshi.
kasan cewar yazo ƙarshen suratul Maeda sai yayi addu'a ya shafa.
Kana ya miƙa hannunshi ya ɗauki wayar, Ummi ya gani a saman screen ɗin ya kai yatsarsa kenan kiran ya katse.
Dama shima katse kiran zaiyi shi zai kuma kiranta.