Sashe 98
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummi kuwa ci gaba da kiran sunanta tayi.
Cikin tsoro Hibba tace.
"Ummi kinga idonta ya koma dai-dai."
A tare sukace Alhamdulillah.
Sai kuma Ummi ta kuma kiranta.
"Shatu!".
A hankali tace.
"Na'am Ummi".
Sai kuma ta kalli inda take, kana ta juya ta kallesu baki ɗayansu, cikin mutuwar jiki ta yunƙura ta tashi.
Murya a sanyaye tace.
"Jamil sharan kenan ka tsaya kanata kallona.
Gaya min ya za'ayi sharar".
Cikin sauƙe tagwayen numfarfashi suka kalli juna,
Cikin mamaki Jamil yace.
"No ki huta kawai my Aunty zan share".
Bata da ƙarfi a jikinta ko ta dage tace sai tayi sharar.
Bazata iyaba jikinta duk a mace.
Hakane yasa tace to.
Hannu ta miƙa Ummi tare da cewa.
"Ummi É—an jamin hannuna mana".
To tace tare da kamo hannun.
Ta tsaida ita, cikin tafiyar sanÉ—a ta juya ta nufi hanyar fita.
Binta sukayi a baya gaba É—ayansu.
Jamil kuwa dube-dube yayi a cikin É—akin kana.
Ya fara tattarewa da kimtsawa da sherawa, ya canza mishi beshit and blanket, da rigunan pillows.
Kana ya goge ko ina fes
Sannan ya shiga bathroom ya wonke ya goge mishi.
Su kuwa suna biye da ita har falonta.
Ganin ta wuce bedroom É—inta ne yasa Hibba da Juwairiyya suka tsaya.
Ita kuma Ummi tabi bayanta.
Ganin tana shiga ta hau gado ta kwanta ne a take sai bacci yasa Ummi ta juyo ta fito.
Can babban falon suka koma suka zauna.
"Ikon Allah sai kallo wannan abu da ban tsoro da ban mamaki".
Ummi ta faÉ—a cikin al'hini.
Jiki a mace Aunty Juwairiyya tace.
"Sosai kam wannan al'amari ya firgitani".
Hibba dai sai zuru-zuru tayi da ido.
Nan sukayi ta mamakin wannan abin.
Jamil na fito shida Jalal suka tafi.
Shi kuwa Ya Jafar bayan matarsa yabi suka tafi.
Hibba kuwa da Ummi nan suka zauna.
Ummi ce ta kalli Hibba tare da cewa.
"Sai anjima zan kira Umaymah na sanar mata abinda ya faru".
Kai kawai Hibba ta kaÉ—an mata.
Ita kuwa Shatu baccin tayi mai nauyi sai kiran sallan azahar ne ya tasheta.
Su Sheykh Jabeer kuwa suna can sunata keta hazo.
Tafiya awa huɗu ne zai kawosu ƙasar mun.
A hankali ta buɗe idonta, miƙa tayi tare da yin salati.
Kana ta tashi zaune.
Bathroom ta shiga, wonka tayi da ruwan É—umi.
Kana tayi al'wa tana fitowa.
Ta zura Hijabi tayi salla.
Bayan ta idarne, ta zauna gaban dreesing mirror.
Simple makeup tayiwa fuskarta.
Sannan ta sauya shiga, wani tattausan lace mai É—an karen kyau da tsada tasaka duguwar rigace tayi cib-cib da jikinta. Kasan cewarta kalar pink guava da É—igo-É—igin mint green ne yasa tayi masifar dacewa da kalar jikinta.
Gyara gashin kanta tayi ta tubƙeshi tare da kitsen jelar.
Ta saketa bisa kafaÉ—unta.
ÆŠaurin asseta tayi ya zauna É—as a kanta, tattausan gyale minti green color ta yafa a kafaÉ—unta.
Kana ta fesa turarukan ta masu daddaɗan ƙamshi.
Sosai jan lallen gargajiya dake kan Æ´an fararen yatsun hannunta yayi masifar kyau.
Ga kuma zanen da akayi a saman hannun hakama ƙafafun ta, suma sun sha zanen jan lalle tayi kyau sosai,
Ta fito ras da ita.
Baki É—auke da sallama ta foto falon.
Cikin murmushi Ummi ta amsa sallamar tana mai kallonta,
Hakama Hibba da Ummi ta kokkontar mata da hankali taji tsoron ya ragu.
Gefen Ummi ta zauna, tana kallon Hibba na É—aukarta hoto tana cewa.
"My Happiness Aunty kinyi kyau".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Na kaiki ne?".
Da sauri Hibba tace.
"Kin fini ma".
Murmushi ta kumayi tare da cewa.
"Ngd matuƙa".
Sai kuma ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi me zamuyi abincin dare".
Cikin jin tausayinta Ummi tace.
"A a akwai abinci harda na gobe da safe ma, yanzu kam ki huta, sai dai in akwai abinda kikeso ki gaya min in yi miki".
Kai ta jujjuya alamar a a kana tace.
"To Ummi a kaiwa Hadimai wani abincin kada ya lalace a banza ko".
Cikin gamsuwa Ummi tace to.
A can Airport kuwa ƙarfe uku dai-dai jirgin Ahlin masarautar Joɗa ta sauƙa.
Nan motoci suka kwatsosu.
Suna isa masarautar ana kiran sallan la'asar hakane yasa matan cikine kawai suka shiga cikin gida su mazan.
Masallaci suka wuce.
Ana idar da salla kuwa fada suka wuce baki É—ayansu.
A sashin Gimbiya Saudatu kuwa wani irin dariya mai cike da masifar jin daÉ—i tayi tare da cewa.
"Dai-dai kenan yaro zai dawo ya taradda da mummunan lbrin matarsa ta zama zautacciyar mata...!
By
*GARKUWAR FULANI*
"Mummunam labarin amarya ta haukace.
Ai kaÉ—an ma kenan, kowa yaci tuwo dani miya yasha. Hegen yaro mai jajayen kunnuwan da shegen baki mutun nace masa cuta zai ce ajali, kana ce mishi cas zaice maka kulle, wannan bakin nashi mai zaro zance da inada hali dana rufeshi kirib".
Hadimarta dake zaune gabanta wacce taji cikekken bayanin abinda ya faru da Shatu a sashin Hajia Mama da itama yar rahotontace ta kamo mata.
Shiyasa itama ta kawo mata rahoto.
Cikin jin daÉ—i ta kalli Laminu dake gefe yanata murmushin jin daÉ—i tace.
"Shiga É—aki zaka samu kuÉ—i a kan gadona, kazo ka bata tukuicin wannan daddaÉ—an labari mai armashi".
To yace kana ya miƙa ya ɗauki kuɗin yazo ya bata, tayi godiya kana ta miƙe ta fita.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu Baba Basiru da Baba Nasiru ta kira ta shaida musu abinda ya faru.
Nan sukayi ta murnar abun, da shirya yadda abin zai É—unguzuma yaci gaba.
A can su Sheykh kuwa saida aka idar da sallan isha'i kana kowa ya nufi Side É—insa kamar yadda sukeyi duk shekara in sunje umrah sun dawo.
A Babban falon sashin Jabeer kuwa.
Ummi ce zaune bisa kujera Hibba na gefenta.
suna mgn da Umaymah a wayar Hibbab nan Ummi ke sanarwa Umaymah abinda ya faru É—azu da hantsi na firgitarwa.
Cikin tarin mamaki da al'ajabi da tsoro tace.
"Ummin Jabeer to yanzu ina take? Kuma ya jikin nata? Meya jawo hakan ne?".
Juyawa Ummi tayi ta kalli bayanta a hankali tace.
"Tana É—akinta tunda tayi sallan isha'i ta konta, yau ko abinci babu abinda taci, tunda gari ya waye, dan koda muka dawo idi munci dukanmu amman ita ko ruwa bata shaba, kuma har yanzu babu abinda taci".
Cikin fargaba Umaymah tace.
"Jazlaan É—in ya shigo wurinku ne? Ya sanine ko bai saniba?".
"A a bai shigoba, eh gsky babu wanda yasan da wannan zancen duk Masarautar JoÉ—a, saini, da Jamil, Jalal, Hibba, Juwairiyya, Jafar.
Mune kaÉ—ai muka san da zancen".
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Umaymah ta sauƙe cikin sanyi tace.
"Kada ku damu zanyi mgna da Jazlaan, kada ku gaya mishi, in lokacin saninshi yayi zai iya sani".
Ta tace tare cewa.
"Masha Allah gashi ma sai yanzu ya shigo".
Tana faÉ—in haka ta katse kiran.
Ta miƙe da sauri hakama Hibba cikin jin daɗi suke cewa.
"Oyoyo mutanen saudia garin Manzon Allah, Barka da zuwa lfy da dawowa lfy".
Ɗan gajeren. Murmushi yayi tare da ƙarasowa cikin falon.
Jalal, Jamil, Ya Jafar na biye dashi a baya.
Bisa kujera ya zauna tare da kallon Ummi fuska ƙunshe da annuri yace.
"Barka dai Ummi na sameku lfy!?".
"Lfy lau Alhamdulillah Sheykh ya kuka baro Sheykh Abdulkareem da ahlinshin.
Ina mai sunanka Sheykh Jabir Ali".
Cikin jin daÉ—in kulawarta ga yan uwan mahaifiyarshi yace.
"Alhamdulillah suna lfy, Sheykh Jabir Ali yace in gaidaku gaba É—aya".
Cikin jin daÉ—i tace.
"Ina amsawa kuwa ngd matuƙa".
Jamil dake riƙe da jakukkunan da Sheykh yace ya ɗauko a motarsa ne ya wuce dasu.
Yaje ya ajiyesu a bedroom É—in shi kana ya dawo falon.
Hibba kuwa ruwa ta kawo mishi.
Murmushi yayi tare da amsar goran zam-zam É—in yace.
"Baku shanye tsohon ba Ummi ni gashi na samo sabo".
Hibba ce ta É—an kalleshi tare da cewa.
"Hamma Jabeer, su Sitti ma sun dawo ne?".
Kai ya gyaÉ—a mata alamar eh.
Kana ya miƙe tare da cewa.
"Ummi bari inje in É—an huta".
Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.
"Ai dole kam saida hutu dan gajiya da rashin bacci kam ka kwasosu dole kayi ramuwar bacci".
Ta ƙarishe mgnar tana kollonshi tuni ya shiga corridor'n shiga cikin falonshi.
Dama kuma tuni ita da kanta ta kai mishi abinci a Dinning table É—inshi.
Nan sukaci gaba da hira.
Hibba na cewa.
"Umaymah na ta dawo na kusa komawa".
Cikin taɓe fuska Jalal ya kalleta a fakaice.
Jamil kuwa dariya yayi tare da cewa.
"Za dai ki gudu yarinya faÉ—i gskyarki".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ba wani tsoro ai na gaya mata ta kontar da hankalinta."
Jafar kuwa karatunshi yakeyi.
A hankali saɓanin baya da in zai karatun da ɗan ƙarfi yakeyi.
Sosai suka É—an yi hira kana suka watse kowa ya tafi makoncinsa.
Shi kuwa Sheykh yana shiga.
Ya rinƙa sauƙe numfashin gajiya tare da rage kayan jikinshi.
Wonka ya shiga yayi kana yasa wasu riga da wondo masu taushi yazo ya konta.
Ba tare da yasha ko ruwaba, sabida tarin gajiya da bacci.
Gaba É—aya wunin yau a zaune yayi yishi ko a É—an tsaye.
Gashi rabonsa da bacci tun jiya da safe da ya É—anyi kaÉ—an kafin ya tafi harami sallan walaha.
Yana konciya kuwa yayi addu'o'in ya shafa jikinsa.
Kana ya fuskanci allon majigi dake liƙe a bongon ɗakin wanda yake ɗauke da full ƙura'an. Karatu ya farayi daga ƙasa zuwa sama wato nasi.
ÆŠaga nan bacci yayi awon gaba dashi ko inna'alzzan bai jeba.
Ummi da Hibba kuwa suna isa falon Shatu cikin kula Ummi tace.
"Kije ku kwana kinji ko Hibba babu abinda zai sameki,
Bazata miki komaiba, bata da lfy bai dace mu barta ita É—aya ba".
Cikin sanyi Hibba tace.
"Gsky Ummi bazan iyaba wlh ina tsoro".
Cikin hikima Ummi tace.
"To muje ki hau gado ku kwanta ni kuma sai in kwanta a ƙasa kam carpet ɗin.
Gyada tayi cikin gamsuwa da hakan.
Haka sukayi Ummi ta kwanta a ƙasa ita kuma Hibba ta konta gefenta a ɗan tsorace.
Ita kam Shatu batama san sunayi ba, domin bacci mai nauyi takeyi.
Haka dai Ummi tai shiru saida ta tabbatar Hibba tayi bacci kana ta koma É—akinta.