Sashe 110
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daga nan suka shiga kitchen.
Jamil kuwa tuni yaje yayiwa wani mai musu aikin gidansu.
Yasa ya nemi irin wannan tayis É—in. Yace gobe da safe misalin sha É—aya zaizo ya É—auke shi.
Washe gari da safe.
Misalin karfe tara, Sheykh ya fito cikin shiga ta al'farma, yau ba al'kyabba a jikinshi riga da wondone sai malum-malum gariya mai kyau.
Getzner ce mai masifar kyau Brownish red color mai ɗan karen kyau da sheƙi, gariyar tasha aiki mai ɗan karen kyau da zaren surfani mai sheƙin piash color.
Hular kanshi da red and piash color, takalmin shi kuwa fatar ta kifa kalar red É—in.
Yayi kyau sosai ya kafa hular nan cas a kanshi. Kekyawan suman kanshi ya konto gefe da gefe da ƙeyarshi sai sheƙi da ƙelli yakeyi.
Sajenshi ya kwanta lib, gashin girarsa dana gemunshi ɗan cas dashi misalin kamu ɗaya, sai sheƙi suke zubawa.
Ɗan madai-daicin bakinshi mai jajayen laɓɓa sai sheƙi sukeyi.
Yar ƙaramar jakar na'urar System ya riƙe a hannunshi, sai wani ƙamshi mai daɗin ji yake fiddawa, ɗan farin siririn Glass irin na manyan Doctors ya manna a fuskarshi kana ya fito.
A falonshi ya sameta, tana jera mishi breakfast.
Ganin zai wucene ta É—an biyoshi a hankali ya zama suna tafe a jere.
Cikin kallon suman ƙeyarshi tace.
"You are breakfast is ready".
Bai kulata ba yaci gaba da tafiya.
Ita kuma ƙeyanshi ta mannawa harara.
A haka suka fito.
Ya sallami Ummi da Jamil da tunda suka karya bai tafiba.
Da sauri Jamil yabi bayanshi yana cewa.
"Uhum Dakta sai yaushe zaka dawo ne?".
Juyowa yayi ya kalli Jamil sai kuma yace.
"Kanada matsala ne?".
Da sauri ya jujjuya kanshi tare da cewa.
"No. I'm very fine".
yayi mgnar yana jijjiga jikinsa.
Kai ya kaÉ—a ya juya zai fita,
Da sauri Jamil ya kuma tambayarsa.
"Dakta yaushe zai dawone".
Cikin tsuke fuskarsa yace.
"Ban sani ba".
Daga nan ya fita, shi kuwa Jamil tsalle yayi tare da cewa.
"Yesss, Dakta Allah ya kiyaye hanya, a wuni lfy a asibiti".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Yi maza to ka É—auki shi".
To yace kana ya miƙe ya fita.
Sanin cewa yanzu Sheykh yana sashin Hajia Mama ne.
Haka yasa ya rigashi fita.
Ummi kuwa miƙewa tayi taje ta rufe ƙofar sabida bata son wani yazo ya shigo.
Kiran Jamil tayi a waya tace in sun isoma ya kirata a wayane zata buÉ—e mishi.
Tana katse kiran ta juyo ta kalli Shatu dake zaune gefenta tana ce mata.
"Yauwa to Ummi muje mu fara aikin kafin ya iso mun kusa cimma aikin."
Cikin mamaki tace.
"A a keda kikace sai an matsar da gadonshi sannan aikin tono ai bazamu iyaba. Dole sai mazan".
Cikin muryar da har yau Ummi ta kasa banbance shi da asalin muryarta tace.
"A a ba matsala Ummi muje zamu iya".
Ta ƙarishe mgnar tana yin gaba, ganin hakane yasa Ummi Binta a baya.
A hankali suka shiga falon.
Tana mai cewa Ummi.
"A nan ma an mishi wani aikin amman shi bai shiga jikinsa ba, sabida yanada Garkuwar addu'o'in da yakeyi yau da kullum.
Shiyasa duk sabbin sihirurruka basa shigarsa.
Sai dai waÉ—anda akayi mishi tun bai gama girma ba."
To kawai Ummi ke ce mata sabida jin kamar muryarta na canza mata.
A haka ta kuma nuna mata wani wurin.
Tare da cewa.
"Uhumm Ya Jafar suke nema, su maida majanunin kan bola sai kuma sharrinsu ya zame mishi al'khairi,
Tsawon shekaru baya mgn sai ambaton Allah. Bashi ba zunibi sai tarin lada da yake samu na karatun al'ƙur'ani da ya zame mishi abokin hira.
To ita kuma me take nema a duniya da zata cutar da baiwar Allah da ahlinta duka haka.
In banda lalaci da son duniya na miji ya lalace da bin matsafa yana sawa ana sabauta É—an uwanshi da yayanshi."
Ita dai Ummi binta takeyi da ido da ƙafa har suka isa bedroom ɗin shi.
ÆŠan lungun da É—aya Bedside drower'n take ta shiga.
Kana ta kalli Ummi fuska a juye tace.
"NaÉ—e min carpet É—in nan.
To Ummi tace da sauri ta fara naÉ—e carpet É—in.
Bayan ta janyeshi da kyar ne, ita kuma Shatu.
A hankali tasa hannun damanta bisa jikin gadon ba tare da ta ɓallashi ba ko, ta cire wani abu a jikinshi ba, ta yunƙura ta tura gadon tare da cewa.
"Bismillahirahamanirahim".
Da sauri Ummi taja da baya cike da mamaki da tsoron ganin yadda take tura tamfatsetsen gadon mai É—irkekiyar katifa da ko tura katifar kawai aikine.
Guuuuuuh haka sautin tura gadon yake badawa.
Saida ta turashi har jikin Waldurob.
Kana ta tsaya a tsakiyar inda gadon yake kafin ta turashi.
Dai-dai lokacin kiran Jamil ya shigo wayarta.
Da sauri taje ta buÉ—e mushi.
Kana suka shigo,. A falon suka bar ÆŠalha mai tayis,
kana Jamil ya amshi kayan aikin yabi bayan Ummi yana cewa.
"Yauwa É—alha É—an jirani bari inzo mu isa kaga wurin".
To É—alha yace kana ya fara cin abincin da Ummi ta saka mishi.
Suna shiga suka maida ƙofar falon suka rufe.
A inda Ummi ta barta a han suka sameta.
Da sauri ta miƙawa Jamil hannun tare da cewa.
"Bani gudumar da ma'ɓamɓarin."
Cikin sauri ya iso tare da ajiye ɗan buhun ya fito da gudumar da Maɓamɓarin yana mai mamakin yadda aka tura gadon yace.
"Bari Aunty Shatu nuna min ina zan fasa".
Da sauri tace a a, ku É—an matsa gefe, musamman ma kai koma can".
Ta nuna mishi gefe.
Sake mata gudumar yayi jin ta fizgeshi.
A hankali ya tashi sabida cewa da tayi ya tashi.
Ido suka zuba mata, ita kuwa, gudumar tasa ta rinƙa buga tayis ɗin dake wurin saida ta fasa uku lafiyeyyu.
Kana ta ture fasassun tasa maɓamɓari tana ɓalle sauran, saida ta ciresu kab.
Sannan ta fara fasa fulon simintin dake ƙasan.
Da mamaki Ummi ke kallon wurin sabida tasan babu wani fulo da akayi kafin asa tayis É—in.
Fasashi tayi kana ta fara caccaka ƙasan wurin da matonin, tanayi yana fito da ƙasa.
Shiru sukayi ganin ramin yayi zurfi kuma ba komai.
A haka taci gaba da tono tana kuma faɗaɗa ramin ta ƙasa.
Wani irin zabura Jamil da Ummi sukayi lokacin da suka ga wani baƙin hayaƙi yana fitowa cikin ramin.
Ita kuwa Shatu da sauri tasa hannun damanta taci gaba da tonon.
Tare da yin mgna da sauri tace.
"Jamilu buɗe windows da sauri hayaƙin nan ya fita".
Cikin rawan jiki yace to.
Kana ya fara buɗe wa da sauri sabida, hayaƙin ya fara cika ɗakin.
Yana buɗe windows ɗin kuwa hayaƙin ya fara fita.
Tonon taci gaba dayi tare da cewa.
"Inama da akwai wani yardajjen mu a kusa, bayan ku biyun nan da yabi hayaƙin nan zaigane mana ina zai shiga cikin sashukan mutanen gidannan shaidar aiki ya koma kan wanda ya yishi."
Da sauri Jamil yace.
"To ko in fitane inbi hayaƙin".
Cikin sauri tace.
"A a kada ka fita ku tsaya kaida Ummi."
Numfashi suka fara sauƙewa, a hankali lokacin da sukaga duk hayaƙin ya gama fita.
Sai kuma suka fara takowa suna zuwa inda take ganin yadda hannunta dake cikin ramin yake karkarwa.
Ga wata zufa dake keto mata kamar da bakin kwarya.
Wani marfin tukunyar ƙasa ta ɗago.
Kana a hankali ta É—ago tukunyar.
Ta ajiyeta gefe kana ta koma ta jingina tana mai jan numfashin.
Cikin sauri Ummi taje ta kunna sauran wutan É—akin duka, ya zama kamar farin wata.
Jamil ne ya fara leƙa cikin tukunyar.
Da sauri yace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ummi zo ki gani".
Ya ƙarishe mgnar yana sunkuyowa da kai hannunshi zai kama tukunyar ƙasan cikin sauri da ƙarfi Shatu ta buge hannunshi da hannunta na hagu tare da cewa.
"Jininka ɗaya da Yah Sheykh in ka taɓa duk abun zai iya dawowa jikinka."
Ta ƙarishe mgnar da ɗago hannun ta na dama tasa a ciki.
Tukunyar da sauri ta rumtse idanunta sabida wani irin masifeffen tsikara da taji an mata a hannunta.
A can ƙasar Cameroon kuwa cikin Rugar Duno dake, kusa da Rugar Malam Babayo.
Ba'ana ne zaune bisa buzun aikinshi.
Da kasko a gabanshi yana kallon cikin kaskon gaba É—aya jikinshi rawa yakeyi cikin tashin hankali da fargaba yace.
"A'a A a Mata kada ki taɓa, baki amince na baki mgnin kariyar tonar sihiriba, iya ganin idan a zuba sihiri a abinci yake na shayar dake shi nanma a bisa dole baki saniba.
Kada ki taɓa zai cutar dake".
Ya ƙarishe mgnar hawaye na zubo mishi, Allah ya sani baya son abinda zai cutar da Shatu ko kaɗan.
Ita kuwa Shatu a hankali ta fara fito da wasu irin tabka-tabkan layu wanda aka liƙesu da yadin al'kyabba daga gani kasan na Sheykh ne sabida shi ɗaya kesa irinsu a masarautar Joɗa tun yana ɗan yaro matashinsa.
Wani dogon ajiyan zuciya taja tare da fizgo wani dogon maciji a cikin tukunyar ƙasar.
Da sauri Ummi taja da baya, shi kuwa Jamil sai leƙowa yakeyi.