← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 183

Sashe 80

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka fita, sannan Umaymah ta shigo, gefenta ta zauna cikin nitsuwa tace.
"ÆŠiyata ga kayan sawarki naso ace sun iso tun kafin yau.
To sha'anin nesa, shiyasa kikaga bai iso da wuriba, duk kayan nakine kisa wanda kikeso a sanda kikeso.
Sabida ke akayi komai."
Cikin tarin jin daÉ—i da ganin darajar ta tace.
"Ngd Umaymah Ngd matuƙa, Allah ya saka da al'khairi".
Amin Amin tace kana ta miƙa tare da cewa.
"Naga kina son dogayen riguna ranar da zan aika kince su kikafi so, gasu an kawo miki su da yawa".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Nagode sosai Umaymah Allah ya ƙara girma".
Amin Amin tace kana fita.

Ita kanta Shatu tasan babu ƙaranta a duk kayan da aka jinbga mata.
Komai mai kyau ne.

Yau talata da hantsi suna zaune a falon.
Hadimai sukayi sallama da Jakadiyarsu, bayan ta basu izinin shigowane.
Suka fara shigowa suna wucewa kitchen da kayayyakin abinci kamarsu shinkafa ta tuwo buhu biyu ta wara buhu biyu, sai gero ƙaton buhu, wanda a surfe yake, taliyar manya data yara katon biyar-biyar, kiret-kiret na ƙoyaye biyar, jarakunan mai dana manja bibbiyu katon ɗin maggi ɗaya dasu doya da dankalin turawa mai yawa.
Haka suka rinƙa jida suna kaiwa store.
Bayan sun gamane, Umaymah ta kalli Aysha cikin yin ƙasa da hannu ta miƙa mata dubu biyar.
Kana tace.
"Engo basu tukuici, wannan daga store É—in masarautar JoÉ—a ne, duk ko wani sashi haka ake kai musu in Ramadan ya kawo kai."
Cikin jin kunya tasa hannu ta amshi kuɗin kana ta miƙa Hibba tare da cewa.
"Hibba basu".
Da sauri Umaymah ta girgiza mata kai, sai kuma ta kalli hadiman suna shirin fita tace.
"Kuzo matar Sheykh na kiranku".
ÆŠaya daga cikin sune, ya dawo.
a hankali ya iso ya rusuna gaban Shatu tare dayin ƙasa da kanshi.
Cikin nitsuwa yace.
"Gashi mun gode Allah ya kaimu baÉ—i lfy".
Amin Amin suka amsa baki É—ayansu.
Kana ya amsa ya miƙe ya fita.

Su kuwa sukaje sukaci gaba da hirarnsu.

Washe gari kuma ranar Laraba.
Wanda ana zaton kwana huÉ—une ya rage Ramadan, koma biyar.

Umaymah ce zaune ita da Sheykh,
ido ya zuba mata har ta gama mgnar da yakeyi na batun ran jumma'a fa zasu koma.
ta jaddada mishi kadafa ya mance yanzu yanada mata.
Kanshi ya jingina jikin kujerar tare da son kauda wannan zancen yace.
"Jadawalin jerin malam da zasuyi tabsirin Ramadan a jahohi mabanbanta ya fito".
Cikin alfahari da hakan tace.
"Wacce jahar kuma aka turaka bana?".
ÆŠan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Tun da da nake ta son a barni a jihata, kullum sai a turani wata jihar, sai bana kuma da nake son in tafi wata jihar suka barni a nan".
murmushin jin daÉ—in hakan tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah kaga darajar aure ko".
Bai tanka mataba,
itama bata jira ya tanka matanba tace.
"Ya batun tafiya umarah kuma".
Kanshi ya É—an É—ago ya kalleta hannunshi yasa ya shafa sajenshi cikin nitsuwa yace.
"Sha biyar ga watan zan tafi".
Da sauri tace.
"Zaka tafi ko zaku tafi?".
Kanshi ya É—an dafe tare da nazarin ya zai yanke mgnar cikin nitsuwa yace.
"Eh zamu tafi".
Yalwataccen murmushi tayi sabida bata gano manufarsa ba.
Cikin kula yace.
"Kefa yaushe zakuje".
Tana ƙoƙarin miƙewa tace.
"Shatara ga watan Ramadan zamuje".
Da sauri yace.
"Umaymah". Komawa tayi ta zauna tare da cewa.
"Na'am".
Cikin kwaɓe fuska yace.
"Muna mgna kuma zaki tafi, me zakije kiyi ne a can ".
Cikin murmushin tace.
"Zanje wurin Aysha akwai mgnar da zamuyi".
Ba tare da ya san waye kuma wacce mai suna Shatu'n ba yace.
"Uhumm shike nan".
Cikin kula tace.
"Ko akwai wani abu ne?".
Kai ya girgiza mata, ganin haka yasa ta miƙa ta fita.

Shi kuwa ya miƙa ya shiga bedroom ɗin shi dan yana son yin baccin tsakanin azahar da la'asar, sabida wannan baccin yanada al'fanu.
Dan zai taimakawa mutun wurin tashi da dare.

Ita kuwa Umaymah a falo ta samu.
Shatu da Ummi. Dan Hibba tana can sashin Aunty Juwairiyya.

Gyara zamanta, tayi tare da kallon Ummi cikin nitsuwa da shaƙuwarsu tace.
"To Ummin Jabeer, Ni dai tafiya ta ƙara to in Allah ya kaimu, jibi jumma'a zamu tafi, zan barki da sauran aikin".
Cikin sauri Ayshs ta É—ago kanta ta kalli Umaymah cike da fargaba tace.
"Umaymah tafiya?". Ta ƙarishe mgnar cikin sanyi.
Ido Umaymah ta É—an zuba mata cikin karantar yanayin da take ciki tace.
"Eh Aysha zamu tafi jibi da yamma jirginmu zai tashi zamu tafi Hibbab ya dawo yace yana kewar Hibba".
Da sauri tace.
"Ayyah Umaymah dan Allah kada ki tafi da Hibba, ayyah Umaymah a bar mana Hibba".
Ta ƙarishe zance fuska cike da rauni".

Shiru Umaymah tayi sabida ganin hawaye suna shirin zubo mata,
sai kuma ta miƙa da sauri ta nufi ɗakinta, sabida jin bazata iya danne hawayen nataba, Allah ya sani ta saba da Hibba sosai, itake ɗebe mata kewar Junainah, Umaymah ke meye mata gurbin Ummeynta, sannan wai duk zasu tafi.
Tabbas ta saba da Ummi amman ba kamar Umaymah.
Sam tama kasa yarda da Juwairiyya kam ma.

Koda ta tafi, Umaymah da Ummi murmushi sukayi.
Cikin sanyi Umaymah ta fara mgn da Ummi bisa dukkan alamu mgnace ta sirri domin nima banjisuba.

Na dai ga daga ƙarshe duk suna zubda hawaye.

Bayan sallan isha'i ne Hibba ta nufi Side É—in Gimbiya Aminatu.
Dan amsowa Hamma Jabeer É—insu aiken da ya mata.

Bayan ta dawone ta ajiye Foodflaks a gaban Umaymah tare da cewa.
"Umaymah gashi, a kai mishi".

"Jeki gayawa matarshi tazo ta kai mishi."
To tace tare da juyawa ta nufi falon Shatu.

Ganin bata falone yasa ta wuce bedroom.
A kwance ta sameta bakin gado.
Ta konta rubda ciki, tanayin kuka mai sanyin sauti.
da sauri ta zauna gefenta tare da cewa.
"Aunty Shatu meya faru?".
da sauri tasa tafin hannunta ta shere hawayen, kana ta miƙe zaune hannun Hibba ta kama ta riƙe tare da zuba mata ido cikin sanyin murya tace.
"Please Hibba mu zauna kada ki koma, ki cewa Umaymah zamuyi azumi a nan."
Shiru Hibba ta É—anyi kana ta É—an yi murmushi tare da cewa.
"To zan gaya mata, kuma kema ki gayawa Hamma Jabeer in shine yace mata ta barni bazata hanani ba."
Cikin sanyi tayi shiru, alamun nazari, ta ina? kuma ta yaya? yaushe zata mishi mgna? Mutumin da ko kallon inda take bayayi! Anya kuwa yama sanni ne?!.
Tayi mgnar zuci.
Ita kuwa Hibba cikin murmushi tace.
"Allah muwa in kin gaya mishi za'a barni".
kai ta jinjina tare da komawa zata jingina da kan gado, da sauri Hibba ta kamo hannunta tare da cewa.
"A' a taso Umaymah tace kizo".
To tace tare da miƙewa, a tare suka fito falon.
Cikin kulawa Umaymah ta nuna mata Foodflaks É—in.
"ÆŠauki ki kai mishi falonshi".
da sauri ta zaro ido cike da mamaki, gane hakane yasa Umaymah kauda kanta,
ita kuwa Shatu shiru tayi tare da zubawa kulolin idanu.
Muryar Ummi ce ta kuma ratsa kunnuwanta.
"ÆŠauki ki kai mishi in dare ya É—an yi nisa bazai cibafa".
Bazata iya musu musu da gardama ba.
haka yasa cikin sanyin jiki ta sunkuyo ta É—auki Foodflaks É—in, kana ta juya a hankali ta nufi corridor da zai kaita Side É—insa,
tafiya takeyi cikin nitsuwa kanta a sunkuye.

A bakin ƙofar falon ta ɗan tsaya cikin sanyi murya can ƙasa tayi sallama , yadda ita kanta batayi dan wani ko zaton wani yajiba.

Yana can Dinning area, yana zaune bisa É—aya daga cikin chairs É—in Dinning table É—in.
Yasa System nashi a gaba.
hankalinshi duk yana kai, ga woyoyi a ƙalla uhu suna gefenshi.
sai cup mai cike da madarar shanu mai É—umi.

Murya can ƙasa bisa saman tattausan jajayen laɓɓansa ya amsa sallamar da ya jita raɗau cikin kunneshi sai dai bai fahimci mai muryar kai tsayeba,
asalima ji yayi kamar muryar Umaymah ce.

A hankali ta turo kanta ta yaye labulen kana ta sako ƙafanta cikin, falon da bata son koda kallon ta inda yake, ba don bai mata kyauba sai dan wasu manyan dalililai da abubuwan da take gani tako ina a falon,

A hankali take taku, i zuwa inda ta hangoshi zaune ya bawa ƙofar shigowa baya.
cikin nitsuwa ta take step É—in forko,
tare da ɗago kai ta kalli ƙeyanshi.
baki ta murguɗa tare da taɓe bakin kana ta manna mishi harara bisa tattausan suman ƙeyan nashi.
A haka ta ƙara motsowa, shi kuwa Sheykh Jabeer tabbas yasan da mutun a bayanshi.
Ya kuma gano wancan abun ne, shiyasa ko ta kanta baiba.

Aikin da yasha mishi kai yakeyi ba kama hannun yaro.
Da sauri ta ajiye Foodflaks É—in bisa glass É—in Dinning table É—in, wanda hakan ya bada wani sautin.
Idonshi ya É—an rumtse tare da buÉ—esu, kana yaci gaba da aikinshi ko gefen da take bai kalla ba.
Ita kuwa sai ruwan harara taketa manna mishi tako ina.
kana kuma dai tana tsaye bata juya ba.
a ƙalla 55 second bata tafiba, bata kuma ce mishi komaiba, sai hararan da takeyi mishi har ta fara jin idonta na ciwo,
sabida harara ba É—ani'arta ta yau da kullum bane, sai in tana masifar jin haushin mutun da tsanarsa take mishi wannan abun.

Bai kulataba, ganin ba kulata zaibane yasa ta ɗan ja wani gajeren tsaki can cikin maƙoshinta, a zatonta baijiba.
shi kuwa Sheykh Jabeer kanshi ya ƙara rusunarwa sabida sam ya lura wannan abun ba kunya ne dashiba.
Cikin murhuÉ—a baki da harara tace.
"Dan Allah ka cewa Umaymah ta bar min Hibba muyi azumi a nan".
Ta ƙarishe mgnar da ɗan ƙarfi.
Shiru yayi tamkar bai jitaba ko baisan da ita a wurinba,
Sabgogin gabanshi yakeyi tamkar babu wani halittan dake wurin.
cikin kufula ta kuma cewa.
"Dan Allah kace a barta muyi azumi anan".
Ko gezau baiba. Sai dogayen fararen yatsunshi da yake sarrafawa bisa ma dannin System ɗinsa tamkar shiya ƙirƙirota.
Shi sauƙinshi ɗaya tunda yanzu zuciyarsa ta dena bugawa da tsinkewa in mayyar tana kusa.
A karo na uku ta kuma yin mgna tare da juyawa ta fita.
Chapter 80 · 0% Book details