← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 183

Sashe 61

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can Rugar Bani kuwa.
A hankali Shatu ta ɗago kanta ta kalli Ba'ana jin tunda suka tsaya baice mata komaiba, ganin yadda ya zuba mata idone yasata, saurin yin ƙasa da kanta,
cikin sanyi muryar tace.
"Ya Ba'ana zamu tafi rana tanayi fa!".
Wani dogon numfashi ya ja ya sauƙe da ƙarfi, kana a hankali ya ƙara matsowa kusa da ita da sauri tayi baya cikin tsoro, hannunshi ya ɗaga mata alamun karta gudu, kai ta jujjuya tare da ƙara matsawa cikin rawan murya tace.
"Ba kyau ina tsoro".
Kanshi ya jingina da jikin bishiyar gamjin da suke ƙasanta, ido a rufe yace.
"Da dai inada niyar cutar dake, da bamu kawo zuwa yau ban cutar dakeba Shatu, kadafa ki mance tun kina Æ´ar tatsitsiyarki nake sonki kuma nake tare dake, dare da rana, kada ki mance kullum sai kinje gidanmu da dare da asuban fari kin amsowa Ummey mgninta, da har ina son cutar dake da tun wancan lokacin zan cutar dake.
To amman bani da niyar cutarki, ina sonki ne sabida Allah, da kuma gsky da zuciya ɗaya, Shatu koda zaki ƙi yarda dani a kan komai dan Allah ki yarda dani cewa ina sonki, na kuma soki a baya zan soki har gaban abadan, wlh babu ƙarya a cikin soyayyarki a zuciyata, Shatu sonki shine babban raunina a duniya.
Har yau babu wani abu dake firgitani da bani tsoro sai rasaki.
Babu wani abu na duniya daya taɓa sani zubda hawaye sai soyayyarki, dan Allah ki dena zaton dan na matso kusa dake zan cutar dake, ki amince dani in baki abinda idonki zai buɗu da gane sihiri duk ƙanƙantarshi".
A hankali take juya mishi kai cikin sanyi tace.
"Na sani Ya Ba'ana wlh na yarda da kai akan soyayyata, na sani bazaka cutar daniba, tunda baka cutar dani a bayaba, nasan kana sona, na kuma yarda da son gsky kakemin, to amman ni bana son wadannan abubuwa asirce-asircen sabida haramun ne.
A hankali ya zame jikinshi ya zauna kan jijiyan bishiyar.
Ganin haka itama tayi sauri ta zauna bisa guiwowinta ta durƙushe a ƙasa.
Cikin mamaki tace.
"Dan Allah ya Ba'ana meyasa kwanan nan duka sai kayi ta zubda hawaye a gabana, hankalina yana tashi."
Kanshi ya É—an É—aga ya kalli sama, a hankali yace.
"Shatu ina sonki zan kuma soki har iya numfashin na, bazan bari wani abu ya rabani da keba, in kuma akasamu wani ya zama ƙaddarar rabani dake, to shi kuwa tabbas zan rabashi da rayuwarshi, kiyi haƙuri in dai a kanki ne zan iya yin komai, na kuwa san duk duniya babu wanda yasan hanyar da za'abi a kamani ko aci galaba a kaina, sai ke ranki ke ɗaya tak ce kikasan duk wani sirrina ban saniba ko zaki iya min halacci ki sirranta min rayuwata".
Da sauri tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
"Ya Ba'ana ai rayuwa a hannun Allah take, wata ƙilma in rigaka mutuwa, kuma in dai nice in sha Allah bazan baiyana sirrinka dan a cutar da kaiba, ko ba komai kana soma kuma kace dan zaka nemo su ya Gaini ne kayi wannan tsarin gudun kada mugaye su cutar da kai, Ni na sani Ya Ba'ana waɗannan layun bazasu kareka ba, sabida ba hanyar Allah ka biba amman ni zanyi ta maka addu'a".
Ido ya zuba mata a zahiri da baɗininta gsky ta faɗi dan yaga hakan cikin ƙwayar idanunta.
A hankali ya jawo tandun duma dake rataye a kafaÉ—unshi, cikin sanyi yace.
"Ga ruwa kisha".
Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa.
"Bana jin ƙishi".
Tura mata tandun yayi gabanta tare da cewa.
"Eh ba mgnin ƙishi bane, kishi dan kiji sanyi a zuciyarki naga kina kuka".
Cikin share hawayenta tace.
"Ba kai bane ka sani kukan kana ta barmin amanar sirrikanka bayan kuma shi amana rikeshi nada girma da nauyi da wuya".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Zaiyi wuya ki riƙe kenan?".
Da sauri tace.
"In sha Allah zan riƙe".
Kanshi ya gyaÉ—a tare da cewa.
"Bazaki sha bako?".
Kanta ta gyaÉ—a mishi alamar eh.
Kana ta miƙa tsaye, gaba ta ɗan yi kusa da Rafi'a, tace.
"Rafi'a mu tafi".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Rafi'a ku tsaya".
Cikin tsoronshi Rafi'a tace.
"To Ya Ba'ana".
Da sauri ya ƙara so gabansu, tare da cewa.
"Mata É—ago hannunki mu gani kinada zobene?".
Kai ta girgiza alamar a a babu.
kana ta É—aga hannunta na dama,
Yatsarshi ya karkaÉ—a mata tare da cewa.
"Lalala É—ago hannun hagu mu gani".
Cikin gajiya ta É—ago hannunta, fararen tausasan zara-zaran yatsunta suka zubawa ido gaba É—ayansu.

Babu zobe ko É—aya a yatsunta,
Murmushi yayi kana yace.
"To bari in baki zoben ziyara, koda bakya tare dani, duk lokacin da na nake kusa dake kawai zakiga zoben a yatsunki".
Da sauri ta buÉ—e baki da nufin cewa a a.
Kawai sai tayi shiru ganin wani irin zoben azurfa mai masifar ƙyalli da sheƙi sai ɗauke ido yakeyi.
Ta juyo zata ce mishi a a Ya cire sai kuma tayi shiru ganin ya ɓace daga gabansu.
Yatsunta tasa da nufin cire zoben da sauri ta barshi jin tamkar yatsunta zasu tsinke.
Rafi'a kam tuni tayi gaba, haka yasa itama tabi bayanta.

Suna zuwa bakin titin suka samu motar zuwa cikin Ɓadamaya.

A can cikin masarautar JoÉ—a kuwa,
Bayan an idar da salla, kamar kullum LamiÉ—o ya gaggaisa da mutane, talakawan garinshi.
Shi kuwa Jabeer dashi da tawagarsa duk sun nufi cikin gida.
Sabida Galadima nata ce mishi su tafi cikin gida su fara shirin tafiya.

Haka yasa duk suka nufi cikin gidan masarauta.
A nan babban farfajiyar suka É—an tsaya.
Ido Jabeer ya ɗan zubawa jerin motocin da a ƙalla sun kai ashirin da biyar zuwa talatin an bisa alamu anyi manyan baƙi ne ko kuma za'ayi fita mai mahimmanci.

Cikin suka wuce a falo suka samu Umaymah, Hajia Mama, Aunty Juwairiyya, da Ummi, duk suna zaune suna É—an hira.
Hibba kuwa tana kitchen.

Suna isowa ta fito da sauri jin muryarsu.
A hankali ta isa gefen Jalal cikin yin ƙasa da murya tace.
"Ya Jalal kazo kaci abinci karku tafi bakaci komaiba".
Kanshi ya É—an gyaÉ—a mata,
Jamil ne ya hararesu tare da cewa.
"Allah shi ƙara, ai in dai Jalal ne kaɗan kika gani da gwatsalel, mutumin da ba'a iya masa bare a masa gwaninta".
Haroon ne ya É—anyi dariya tare da cewa.
"Haka suke shida Jabeer yadda suke kamanninsu iri É—aya hakama halinsu".
Da sauri Jamil ya zare ido tare da É—an ja da baya yace.
"Tab a a Ni dai wlh bance hakaba".
Jabeer kanshi Jamil ya bashi dariyar da dole ya É—an murmusa, tuni sukuma sauran dariya sukeyi.
Ya Jafar kuwa shi ganin murmushin Jabeer shine ke sashi murmusawa.

Ita kuwa Hibba tura baki tayi ta koma gefe ta zauna alamun tayi fushi, baibi ta kantaba, sai Jamil É—in ne ya É—an lallasheta, haka dai sukayi ta yar raha, saida LamiÉ—o ya aiko su fito kafin.
Suka miƙa duk suka fita, shi kuwa Sheykh Jabeer gefensu Hajia Mama da Umaymah ya ɗan rusuna kusa da Umaymah a hankali yace.
"To Umaymah bari inje bisa umarnku ba don raina yaso ba".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Allah ya bada Sa'a ya kaiku lfy ya kuma dawo daku lfy, Allah ya tabbatar mana da al'khairan dake cikin wannan tafiyar, al'farma Annabi da Alqur'ani".
Amin Amin suka amsa baki É—ayansu, Hajia Mama dasu Ummi ma duk sukayi mishi addu'a, kafin ya fito.

Yauma kamar ranar mota É—aya suka shiga da Haroon da LamiÉ—o da Ya Hashim da Laminu.

Kana sauran tawagar sarki.
Daga nan suka nufi hanyar fita gari su nufi garin Shikan.
A cikin motocinsu kamar na ranan.

A tsakiyar garin Ɓadamaya ne suke tafiya sun zo dai-dai bakin Genaral Hospital Ɓadawaya.
LamiÉ—o ya bada umarnin cewa su shiga cikin asibitin zai kai ziyarar dubiya wa marasa lfya.

Nan take kuwa suka jujjuya akalan motocin.
Suka fara kutsa kai cikin asibitin.
Da ƙarfi Jabeer ya rumtse idanunshi tare da furta.
"Lahaulawalaqutailla billah".
A hankali sabida wani irin masifeffen bugu da zuciyarshi tayi da ƙarfin masifa.
Wani irin taraddadi ya diro masa.
Ya ilahi shine abinda ya ambata a saman lips É—in shi.
Dip dab dip dab dip dab dip dab haka zuciyarshi ke harbawa da bugawa a tare a tare,
addu'o'in ya fara karantowa a zuciyarshi da harshenshi, yadda suke ƙara kutsawa cikin asibitin haka bugun zuciyarshin ke ƙaruwa.

Anan cikin asibitin kuwa, A maraba da baƙi Shatu take tun zuwanta sabida, anan aka juye duk fulanin da suka samu rauni sanadin wannan faɗan,
an zubesu a wurin gwamnatin jiha kuma tayi burus da batunsu sam bata bawa likitoci damar dubasuba,
Sai ma cewa sukayi sai fulanin sun nemo polices kafin a karɓesu.
Su kuma dama Æ´an agaji ne ma suka taimaka suka kawosu nan É—in ma.

Zuwan Shatu ne da Rafi'a da ta samesu a yashe hankalinta ya tashi.
Ranta yayi matuƙar ɓaci nan ta haura gidan sama inda can jerin jadawalin officer's ɗin DOCTOR'S suke.
Rafi'a na biye da ita tana rabka mata kira.
"Garkuwa! Garkuwa!! Ke GARKUWA!!! Ina zakije ne wai?".
Sam bata kula Rafi'a ba sabida abin da akayiwa Æ´an uwanta yayi masifar ci mata rai.

Ganin yadda take gudu-gudu da sassarfa ne yasa itama Rafi'a ta fara Binta da gudu-gudu da sassarfa.

Yayinda kuma dai-dai lokacin LamiÉ—o da tawagarsa ma ke tafe suna shiga cikin gidan saman.
LamiÉ—o ne a gaba sai Jabeer da Galadima dake gefenshi da Sarkin ShaÉ—i.
Kana su Waziri da Wambai Matawalle da Makawa Ɗurɓi Turaki Tafida da dai sauransu, kana Dogari na rike da laima wa Lamiɗo,
ÆŠanzagi kuwa ya kware murya yanata.
"Gyara kimtsi sarki ya gaisheku".
Kana sauran fadawa masu red and blue ɗin Uniform kuwa da tabka-tabkan rawuna babu kunne ko ɗaya suna biye dasu a baya da gefe gefe, suna tafe babu takalma, ga dogin bulali masu masifar tsawo da kauri suna jansu a ƙasa.

LamiÉ—o, Galadima, duk shigar manyan kaya na sarakuna, masu al'farma sukayi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer shigarsa ta al'farma na limamai yayi, wannan yasa kwarjinshi ya fi nasu.
Daga nesa zakace yafi shekarunshi in ka hangoshi sabida kamala da haibarsa da suka baiyana a fili.
Chapter 61 · 0% Book details