Sashe 156
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana shiga ta sameshi yadda barshi haka ta sameshi.
Zaune,
ta jiye tray'n a hankali, shi kuwa tuni ya miƙe tsaye.
bakin ƙofar ya nufa, tsayawa tayi ta jira ya fita kafin ta fita.
Can babban falon ya nufa, tana biye dashi a baya.
Ƙofar falon ya rufe, tare da addu'a kamar kullum.
Ya juyo kenan sai ya ganta tana ƙoƙarin shiga falonta,
Yafitota yayi da hannunsa tare da cewa.
"Zo". Yayi mgnar a hankali.
juyowa tayi ta nufi inda yake a zatonta ko wani abun zai sa tayi mishi.
Tana isa wurin yasa hannunsa a hankali ya kamo nata.
Kana ya juya ya nufi Side É—insa bayan ya kashe wutan ko ina.
Ita dai tana biye dashi kamar raƙumi da akala sai tsoronshi dake ƙara tsananta a zuciyarta.
Suna shiga falonshi ma ya meda ƙofar ya rufe, nanne ta kalleshi a hankali tace.
"Zanje in kwanta ne bacci nakeji".
Kanshi ya gyaÉ—a mata alamar to.
Wutan ya kashe da komi na wuta kana ya nufi bedroom É—insa da ita.
suna shiga ya meda ƙofar ya rufe da key a hankali tace.
"Zan tafi É—akina".
jawo hannunta yayi suka iso gaban tray'n kana a ya zaunar da ita shima ya zauna suka sa tray'n a tsakiya cikin hikima da É—an sakin fuska yace.
"Nawa kika sayi É—akin ya zama naki?".
Cikin kwaɓe fuska tace.
"Ban saya ba".
Kanshi ya É—an sunkuyar kana yace.
"Shine kuma kike cewa É—akinki.
Rau-rau tayi da ida nunta. Tuni sun ciko da ruwa.
Ganin haka ne yasashi É—an matsowa ta inda take kana a hankali yasa hannunshin ya jaw...!
Littafin GARKUWA na kuÉ—ine Special Group 1k Normal group 300 babbancinsu a yawan posting ne. In special Group kikeso kiyi min TRANSFER É—in 1k É—in a asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, in kin tura sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276. Kuma yan 300 ta nan accutan É—in zaku turo, ku turo shaidar biyanku ta whatsapp. In baki da halin turawa ta Account ki sayi katin Mtn na É—ari uku ki copy numbers É—in ki turo min ta whatsApp 09097853276 bana son VTU ko transfer'n kati, in kinyi ba ruwana.
Yan special Group Please bandaku a kati mtn É—in ma. Ku ku bada a POS a tura.
By
*GARKUWAR FULANI*
Ya jawo hannunta na hagu ya haÉ—e da nashi hannun.
Kana a hankali yace.
"Kici abinci sai muje in rakaki, tunda bakya tsoron kwana ke É—aya ko?".
Da sauri tace.
"Eh bana tsoro".
Foodflaks É—in ya buÉ—e tare da cewa.
"To kici abinci tukun, ba kyau kwanci da yunwa".
A hankali tace.
"Na ƙoshi ɗazu da muka gama girki naci abinci".
Plate ya É—auka.
Kana ya buÉ—e kular,
yasa Fork ya soko zabuwar ya É—aura kan plate É—in kana yace.
"Me kuka dafa?".
"Tuwo ne". Ta bashi amsa a gajarce da kuma yanayin tsoronshi.
"Miyar me". Yace mata yana mai kallon ƙwayar idanunta.
"Miyar kase ne".
Kanshi ya É—an juyo ya kalleta kana yace.
"Uhumm shine ko ki kawo min".
Shiru tayi, shi kuwa ƙaramar kular ya buɗe.
romon ya É—an sa a gefen plate É—in.
Kana yace.
"Uhumm duk wanda yaci shi É—aya shi É—aya zai mutu ai".
Ya ƙare mgnar yana murmushin gefen baki".
Still shiru tayi.
shi kuwa, cikin son sama mata nitsuwa dan ya lura ta firgita da shi.
A nitse yace.
"Rowa ba kyau".
Cikin sanyi tace.
"Ai nasa maka, yanzuma na sameshi a can, in kawo maka in kana so?".
Kanshi ya jujjuya kana yace.
"A a, saida na roƙa meyasa tun ɗazu baki kawo min ba".
ÆŠan kallonshi tayi a fakaice kana tace.
"To ai naji kace Ummi ta gasama zabuwa".
Kai ya jinjina alamun gamsuwa kana yaci gaba dasa Fork yana saɓule kasusuwan zabuwar yana turesu gefe sai tururi da ƙamshi naman yakeyi.
Ruwa kuma har yanzu tsugashi akeyi.
Saida ya gama saɓule sokokin ya zare ƙasusuwan ya medasu gefe, kana ya tura mata plate ɗin gabanta, sannan yace.
"To muci, sai ki tafi tunda bakya tsoron Jahan yazo ya sameki a É—akinki ke É—aya."
Cikin sanyi tace na ƙoshi".
Kanshi ya ɗan kauda kana, ya fara cin naman da sauri-sauri kuma yana taunan da ɗan ƙarfi kamar dai yadda ko yaushe inda fushi a zuciyarsa haka yake komai.
Ta fuskar ibadace kawai fushinsa baya tasiri bare ya sashi yin abu da gaggawa ko da karfi.
Duk fushin da yake ciki, in dai ya fuskanci abu na ibada ne to a take nitsuwarsa ke dawowa.
KaÉ—an yaci kana ya tsiyayi sassanyan madara da zumar nan, cikin kofi, ya kafa kai bai ajiye ba saida ya shanye.
Kana ya sake tura mata plate ɗin gabanta, sannan ya cika mata kofin da madarar zuma, kana ya miƙe tsaye tare da cewa.
"Zan shiga wonka in kin cinye kafin in fito to na miki al'ƙawarin zan buɗe miki ƙofar ki koma ɗakin naki, in kuma kinƙi cinyewa to dole a nan zaki kwana".
Yana faÉ—in haka ya shiga bathroom.
Shiru tayi tana nazartan kalamansa, da kuma abubuwan da suka wakana.
Wannan nafila raka'a biyu da addu'arga da yayi ya É—ura mata ruwa a cikinta, ya kuma kaÉ—a mata hanjin cikinta tsoronshi ya rufeta.
Ta lura gaba É—aya ya sauya komanshi na yau wani sabon al'amari ne.
Jawo plate ɗin tayi sabida tasan ya fita sanin girman al'ƙawari da mahimmanci cikashi.
Fork É—in tasa tana sokan naman tana sawa a baki tana tauna tana haÉ—iyewa, sabida É—anÉ—anonsa yayi mata daÉ—i.
Ci takeyi tana kallon ƙofar Bathroom ɗin.
A hankali ta ajiye fork É—in kana tasa hannunta ta É—auku cup É—in madarar, tasa a baki.
Ido ta lumshe sabida wannan shine haÉ—in da tafi so.
Sabida dashi Ummey ta raineta.
Zuƙeshi tayi har kusan rabi.
Kana ta janyeshi daga bakinta, tare da buɗe idonta data lumshe cikin sanyi tayi wata gyatsa mai tabbatar da ƙoshi.
Dai-dai lokacin kuma ya fito daga bathroom,
daga ƙafarshi ta fara kallo har zuwa sama.
wasu tattausan riga da wondo masu masifar kyau Sky blue ne mai É—igo-É—igon fari.
Wondon dogone har ƙasa rigar kuma irin mai hular manne ya kwantar da hulan a bayanshi bisa kafaɗunsa.
Hannun rigar yan dadai.
Wani irin ƙamshi yakeyi mai masifar daɗin shaƙa.
Sejenshi yayi lib sai sheƙi yakeyi.
Kanshi ya É—an jujjuya kana yace.
"Kada ma kiyi ta turawa a dole, barshi kawai kin faÉ—i sharaÉ—in.
Janye plate É—in yayi kana ya juye naman cikin kular.
Cikata mata cup É—in yayi da madarar zuman kana ya ture tray'n can gefe, sannan yace.
"Shanye madarar kizo ki hau gado ki kwanta".
Tura baki tayi alamun zatayi mgna, sai kuma tayi shiru ganin ya shimfiɗa sallayarsa can gefe, ya kuma ɗauki al'ƙur'ani,
alamun karatu zaiyi.
Hakane yasa tayi shirun.
Shi kuwa karatu ya fara kamar yadda ta zata.
A hankali tasa kofin a baki taci gaba da shan madarar, tanayi tana lumshe idonta, sabida haÉ—in yayi iri É—aya sam dana Ummeynta kamar itace ma ta haÉ—ashi.
A hankali ta shanyeshi tas, kana ta ajiye cup É—in kan stoll dake gaban gadon.
Zama tayi tana jin ƙira'arsa mai daɗin sauraro.
Ƴar ƙaramar wayarshi dake gefenta ta kalla, ƙarfe goma harda rabi.
Zuwa yanzu kuma ruwan saman ya tsaya cak sai walƙiya da rugugin da akeyi tako ina wanda haka ke nunin da hadarin bai gama hucewa na zubda ruwanba, ko ma wani hadarin ne ke tasowa daga ƙasa.
Wani sassanyan hamma tayi mai cike da bacci.
Inda yake ta kalla, sam hankalinsa baya kanta.
Hakane yasa ta miƙe a hankali, sabida hankalinta ya ɗan kwanta dashi ganin bai kulata ba.
A hankali ta zagaya can gefe, ta zauna bakin gadon.
Tana mai lullumshe idanunta.
Minti talatin tsakani ta É—an gyara zamanta ta mirgina ta kwanta, kana ta bashi baya.
sannan ta gyara ƙaton hijabinta ta duƙunƙune a ciki.
A hankali take jiyo muryarsa yana karatun.
Shi kuwa Sheykh duk abinda takeyi yana sane bai kulata bane, dan yana son ta nitsu.
Sha biyu dai-dai agogon wayarsa ya nuna masa.
A hankali yayi addu'an samun zuriya ta gari da Addu'o'in kariya da kuma cikar burinshi ya shafa sannan ya miƙe ya ninke sallayar,
ya ajiye al'ƙur'ani.
Kana ya tako ya iso jikin gini, gudun A/C ya dai-dai-ta kana ya kashe wutan É—akin.
Sannan ya kunna hasken wayarsa ya nufo kan gadon.
A hankali ya zauna a bakin gadon bakinsa É—auke da tasbihai.
A hankali ya É—aga hannunshi ya haÉ—esu kana ya buÉ—e tafin hannunshi yayi addu'o'in bacci ya tofa, ya shafawa jikinsa.
Kana ya hawo saman gadon da kyau.
Cikin sanyi da nitsuwa ya isa inda take.
A hankali yasa hannunshin ya fara jan ƙaton hijabin dake jikinta.
Da sauri tasa hannun ta ta kamo nashi,
sabida dama baccin nata ba wani nauyi yayiba.
Jin yadda ta riƙe hannunshi ne yasa ya sunkuyo ya kawo bakinshi kusa da kunneta kana yace.
"Addu'a zan shafa miki, kuma bazan shafawa hijabiba".
Cikin muryar bacci tace.
"Sanyi nakeji ai".
Ci gaba da janye hibajin yayi tare da cewa.
"In na shafa miki sai ki meda".
Sake mishi hannun tayi kana, tayi shiru tana jinsa yana karanto addu'o'in yana tofawa a tafin hannunsa.
Saida ya gama kana ya sunkuyo ya kife tafin hannunshi kan fuskarta. Ya fara shafawa daga saman kanta har zuwa ƙasa kana har bayanta.
A hankali tace.
"To bani hijabin".
Konciya yayi tare da cewa.
"Yayi nisa".
Shiru tayi tana jin wani irin fitinenne ƙamshin jikinsa da sanyin ɗakin suna ratsata.
A hankali ta fara fidda numfashi.
walƙiya kuma in ya haska har cikin ɗaki.
Har yana É—auke ido.