← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 183

Sashe 5

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wani mai keke Napep ne ya gangara gefen titi har kusa da wani mai saida su Oranges Banana da dai sauransu.
Dogon tsaki mai Napep É—in yaja tare da cewa.
"Wannan ai mulkin mallaka ne da izza duk an tsaidamu sabida wani can zai wuce ai duk nan muma saurin mukeyi munada babban uzuri, saurin da duk mutanen wurin nan keyi duk an katse mana hamzarinmu na son isa masallaci kan lokaci muji huÉ—ubar jumman wannan rana".
Mazan dake cike a bayan napep É—in ne suka haÉ—a baki wurin cewa.
"Wallahi kuwa, gashi motocin nasu nada yawa.
zasu sa mu rasa jin hudubar wannan fasihin Malamin".
Wani mai motane dayake gefensu ya amshi zancen da cewa.
"Kuma gaba ɗaya mutanen nan wurin masalacin zasu tafi, sabida duk mai son jin huɗuba mai ratsa jiki da zuciya baya ƙaunar ko furuci ɗaya na wannan malamin ya wuce shi domin Allah ya rigada ya mishi baiwar lafazi mai shiga zuciya".

Wanda ke gefensu ne ya amshi zancen da cewa.
"Gaskiya ne wannan sabida shi Allah yayi mushi baiwar lafazi da iya tabsiri mai nusar da gafalelle".
Mai saida kayan yayan itatuwan dake gefen sunne yayi ɗan murmushi kana ya miƙawa ƴan matan daketa kallon motocin da ido, lemun da suka saya ya miƙa musu.
Kana ya kalli dan-dan zo matasa daketa wuce da kafa,
mutanen daketa maganar Malamin ya kalla tare da cewa.
"Eh kam gsky duk malaman ƙasar nan babu yashi a lafazi, cikin second ɗaya zai yi maka lafazin da zai gamsar da kai tsawon shekaru Talatin,
koda yake hakan baya rasa nasaba da tsatson mahaifiyarshi, da ta kasance balarabiya kuma alarabawanma a cikin ƙabilar da tafi dukkan ƙabilun duniya a baiwar lafazi da iya sarrafa harshe".
Cikin mamaki suka kalleshi,
Alhajin dake cikin zazzafar motar shin nanne yace.
"Haba sai haka mana ashe Balarabe ne wani yanki na tsatsonshi Allah yayi mishi rahamomi masu tarin yawa.
Gashi wannan zai hanamu muje muji KuÉ—ubar".
Murmushi mai Appul É—in yayi tare da kallon gefen baya yadda ya hango dandazon motoci da keke Napep dama masu tafiya da sawu ma.
Wasu na meda motocinsu gefe sukayi suna fitowa da sallayoyinsu a hannu suna takowa da ƙafa,
kanshi ya É—an rausayar ya kalli mutanen dake gaban nashi tare da cewa.
"Kasan su wayene a cikin motocin nan da kuketa zagin kuwa?".
Da sauri suka jujjuya kai tare da cewa.
"A a waye ne?".
Tsala-tsalan motocin ya zubawa idanu zazzafar farar mota kirar Rolls Royce É—ince ya zubawa ido a hankali ya maida kallonshi garesu tare da cewa.
"Shine Sheykh J....!

Uhummmm wasa farin girgi.

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 3

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*FREE PAGE*

*LITTAFINA NA KUƊI NE. TURO 300 DOMIN samun damar KARANTASHI. Ko ki turo 1k domin shiga SP Group, inda zaku samu posting fiye da na 300. Ayyah Ƴan SPG bana son katin, turo dubu ɗayan ta asusuna na, 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta layina na 09097853276. Kuma masu 300 in dai kinada damar turawa ta ac tura,in kuma baki da dama to turo katin mtn na ɗari ukun ta layina na 09097853276, ba hoton katin zaki turoba, numbers ɗin zaki kofa ki turon*

```ALHAMDULILLAH MASU NEMAN TSOFFIN LITTATAFAINA, NA SAMESU GABA ƊAYA, SAI RIGAR KOWA NE BAN SAMUBA. IN KINASO KIZO DA KATIN MTN NA ƊARI UKU kacal IN BAKI DUK LITTAFIN ƊAYA DA KIKESO, A CINSU.ƳAR FULANI, MU'WASMITI, NAMIJI BAYA KAƊAN, A TAUSAYAWA JUNA, BANDIRAWO, RUBUTACCEN AL'AMARI, HUKUNCIN ALLAH, NAKASA BA KASAWA BACE, DA KUMA GARKUWA.```

"Sheykh Jabir Habibullah Nuruddeen Bubayero JoÉ—a ne.
Doctor Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero kenan. Ina nufin GARKUWAN FULANI".
Da mamaki a fuskokin su sukace.
"Astagafirullaha. Bawan Allah ashe sauri yake ya rigamu kada muje muyi ta jira".
Kai mutumin ya jinjina musu tare da nuna motoci biyu wanda Jalal da abokanshi ke ciki, wanda kiÉ—an dake tashi cikin motocin ya cika ko ina, a hankali yace.
"Wannan kuma Jalaluddin kenan ƙanin Sheykh Jabir Habibullah Nuruddeen Bubayero".
Dai-dai lokacin kuma motocin su Jalal keta gilmawa suna bin bayan nasu Sheykh da azaban gudu har kamar zasubi ta kan motocin gaban nasu, cikin mamaki mutanen sukace
"Ikon Allah to wannan saurin duka na menene? shi kuma".
Kai ya jinjina musu lokacin da yake rurrufe kayayyakin shi dan shima shirin tafiya masallacin yakeyi cikin yin ƙasa da murya yace.
"Kuyi a hankali kada ya jimu domin takadirinin yarone, saurin da yakeyi kuma, yasan muddin Sheykh bai gansu a masallaci ba ranshi zai ɓaci".
Cikin nisawa mai Napep É—in yace.
"Kai masu saida kaya a titi iyayen gulma, dasa ido to kai ina kasan su haka?".
Da
Murmushi mai lemun ya É—anyi tare da cewa.
"Wallahi sam ba gulma bace, akwai ƙaninshi Jamil abokin tagwaicin Jalal ɗin mutumi nane yakan tsaya a nan in zai shiga gari, kuma yanada ɗan karen surutu da fara'a shiyasa na sansu, akwai randa yana tsaye a nan yaga Jalal ɗin ya wuce a guje shine yayi dariya yace.
"Hege mai komaÉ—eÉ—É—iyar fuska bosawa Sheykh ne ke nemanshi shine yake gudu kamar zai tashi sama".
to nan ya É—an bani labarinshi. Kuma Sheykh É—in da kanshi akwai shekarar da yayi azumi a garin nan yakan sayi kaya wurina, wani lokacin
Shiru sukayi tare da zubawa motocin idanu.
ganin sunata gilmawa, saida suka wuce gaba É—ayansu.
Sannan sauran al'ummar gari suka fara biyo bayansu.
Mafi akasari ababen hawan dama mutanen dake tafiya a ƙafa kab masallacin Masarautar Joɗa ba fadan jihar suka nufa wanda tuni Sheykh ya isa har yanata gabatar da Hudubar jummar sa mai taken, mu tsaida salla a lokacin ta.

A can cikin masallacin Masarautar Joɗa kuwa tuni al'ummar Annabi sun cika sunyi maƙil tako wacce kusurwa jama'a ne saffan-saffan suke shigowa,
yayinda cikin masallaci yayi maƙil har harabar masallacin ma ya cika tab da muminai salihan bayin Allah.

Kusan a guje wasu ke shigowa sabida lokaci na gab da ƙure musu domin bisa dukkan alamu an kusa ƙare Huɗubar.

Duk da tarin mutane manya da yara, amman sabida ladabi irin na addinin musulunci addinin mafi karamci da tsari, shiyasa baka jin motsi ko sautin kowa.
Sai wata iriyar zazzaƙar murya mai tsanani daɗin ji da sauraro da iya sarrafa harshe, cikin nitsuwa da iya laffazi muryar Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ke tashi yayinda yake ratsa zuciya da jiki da Kunnuwan dukkan muminin dake sashin da sautin muryarsa ke kaiwa.

A can cikin masallacin yake a fili na musamman wurin da aka ware domin Limami,
Yana tsayene bisa sawunshi ya fuskanci tarin bani Adam dake cike maƙil a wurin.

Kekyawan matashine mai tarin kwarjinin da haiba mai firgita magautanshi,
Sanye yake cikin shiga ta al'farma shigar dake nuna nasabarsa ta wanne sashi,
Wani datsetstsen yadin Getzner ne fari ƙal-ƙal wanda yasa riga da wondo,
Kana sai wata hamshaƙiyar al'kebba dake nuni da nasabarsa mai tarin ilimin addini da kuma alaƙantuwa da jinin sarauta,
Wani irin rawani ne ke murze a kanshi wanda jelanshi ke kwance a gadon bayanshi.

Farar fuskarsa dake zagaye da tattausan saje baƙi ƙirin mai fitinenne sheƙi da ɗaukar ido,
Ne yayi matuƙar kara mishi ƙwarjini sai tsabtataccen gemunshi da bazai gaza kamu ɗaya ba.

Cikin rahama da nimar da ubangiji yayiwa laraba ta baiwar iya sarrafa harshe da tausasan laffuza, yake gabatar da Hudubar jummar da yakeyi.
Wanda yana bayayi ne da jan hankali kan girma da darajar salla da tsaida ita a kan lokacin ta.

Shiru mutane nen ya ƙara tsananta ne a lokacin daya fara tsorotarwa a kan illloli da masifun dake bibiyar mai wasa da salla.

Shiru masallacin da farfajiyar sukayi baki ɗayanshi sai sautin A/C da kuma sauƙar numfarfashi mutane da shessheƙan kukan da wasu salihan bayin Allah sukeyi sabida yadda wa'azin ke ratsa jiki da zuciyar mai imani.
Chapter 5 · 0% Book details