← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 183

Sashe 138

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi mai cike da so da tsammani da zato Jadda yayi tare da cewa.
"Amaryar Sheykh jikar Sitti da Jadda".
Cikin murmushin tace.
"Allah rene Jadda Allah nɓeddu sabbugo".
Wani irin murmushi mai cike da masha hurin daÉ—i Jadda da Sitti sukayi tare da haÉ—a baki wurin cewa.
"Amin Amin, tare dake da mijinki".
Cikin tura baki Safiyyah tace.
"Ikon Allah wato banda mu".
Da sauri Sitti tace.
"Wa lakum".
murmushi sukayi dukansu, kana Jadda yasa tafin hannunshi bisa tsakiyar kan Sheykh da Ibrahim tare da cewa.
"Wannan kawuna biyu duk masu É—aukan rawanin girmane, hakama na ukunku Haroona shima akwai nauyin rawanin bisa kansa.
Ibrahim da Haroon bani da fargaba a kanku.
Amman shi Muhammad Jabeer akwai ruÉ—u a al'amarinsa akwai firgitarwa, yana tsakiyar Magauta.
Sun kuma rigayemu sanin rawani na bisa kanshi.
Shiyasa sukeyi mishi zagon ƙasa tun yana ƙaramin yaro."
Shiru sukayi dukansu suna jin zantu kanshi, shi kuwa ɗan tsagaitawa yayi kana ya kalli Aysha yafi tota yayi da hannu alamun ta ƙara matsoshi.
A hankali ta rarrafa ta matsoshi, kanta ya dafa kana yace.
"Wata rana kina iya zama a matsayin da Gimbiya Aminatu take a yau.
Ban saniba ko kafin lokacin ina raye, ko na amsa kiran Ubangiji na.
Ga Muhammad Jabeer mijinki ne, kuma uban Æ´aÆ´an kine, in sha Allah, sannan GARKUWArki. Dan Allah Aysha na baki amanarsa ki zame mishi GARKUWA ki kula da damuwarsa tun kan ta riskeshi.
Yanada nauyi a cikin zuciyarshi mafataucine a faɗin duniya yana neman wani abu nasa mafi, ƙololuwar daraja ga ɗan adam daya ɓace matsa tsowon shekaru masu yawa, a hasashen da akayi mana zaki iya haska mishi hanyar da zaibi ya ganoshi".
Kai kawai take gyaÉ—a Dattijan tanajin hawaye na cika mata ido.
Da kalmarshi ta ko yana raye ko ya amsa kiran Ubangiji.
Shi kuwa Sheykh lokaci É—aya yanayin fuskarshi ta sauya cikin muryar dake nuna dafin zafi da tiririn da ke cikin zuciyarsa yace.
"Uhummm Jadda taimakon Ubangiji na mahaliccina masanin zahiri da baÉ—ini kawai nake nema, shi zai haskamin hanya in riski haskena.
Zanyi ta roƙonshi kuma da fatan ya baku aron rai da lfy har sanda burinmu zai cika.
Ina addu'o'in Allah ya bawa magautanmu lfy da rai har zuwa lokacin da gsky zatayi halinta".
Tuni Safiyyah da Sitti sun fara sakin Shessheƙan kuka.
Wanda sam Aysha ta gaza gane dalilinsa kalaman Jadda da Sheykh kuwa sunyi mata ɗaurin talala a ƙoƙolwarta, ta gaza gane bakin zaren haka yasa ta tattare yawun bakinta cikin kukan da taji yana son kubce mata tace.
"In sha Allah Jadda zan kula da amanarka iyakar iyawata.
Zan kuma tayashi da addu'a koda bana yankin da yake.
Tabbas watan-wata-rana gsky zatayi halinta".
Sai ta kuma kalli Sitti da Safiyyah tare da cewa.
"Sitti kiyi haƙuri du ban san zafin me kikeji a zuciyarki ba, amman kukanki yamin kama da kukan uwar data rasa ɗanta, kiyi haƙuri".
Da sauri Sheykh ya miƙe ya fita, hakama Ibrahim.

Safiyyah kuwa hawayenta ta share kana ta kamo hannun Aysha tace.
"Jadda mu zamu tafi kada dare yayi mana".
A hankali Yace.
"Bazaku tsaya kuyi sallan la'asar ba".
Sitti ce tace.
"Sai dai suyi a hanya naga yadda Sheykh ya fita bazai dawo cikiba".
Kai ya jinjina kana yace.
"To Allah ya kaiku lfy ya tsare hanya.
Aysha Allah yayiwa aurenku al'barka".
Kusan a tare sukace Amin.
Kana suka miƙe suka fita.
Shi kuwa Jadda ya kira Sarkin dogarai ya bashi umarnin a haÉ—a motar dogarai hudu suyiwa jikokinsa rakiya.

Biyu a gaba biyu a baya tasu Sheykh a tsakiya.

Wacce Sheykh da Aysha suna baya.
Ibrahim da Safiyyah suna gaba, Ibrahim ke jan motar.

A haka suka bar masarautar Jalaluddin suka nufi jihar Tsinako.

Tafiyar mai yar tazara ce.

Shiru cikin motar Ba maiyin mgn, Sai sautin Radio da suka kunna.

Jingine yake da kujerar yayi shiru, idonshi a lumshe sai lips É—in shi da yake motsawa alamun yana tasbihi kamar ko yaushe.

Ita kuwa Aysha sosai ta faÉ—a duniyar nazari.

Ibrahim kuwa ya maida hankali kan tuƙin.

Safiyyah kuwa bacci nema ya saceta a motar.

A ƙalla tafiyar awa ɗaya sukayi, kana suka fita jiharsu Jadda suka fara tafiya cikin dajin jiharsu Haroon.

A hankali ya buÉ—e idonshi.
Jin Ibrahim na cewa.
"Tab lallai Abban Haroon da Sarki Ahmadu suna ji da wannan walimar da za'ayi.
Kajifa duk gidajen rediyon Tsinako, gaiyatar walimar akeyi ba ƙaƙƙautawa kaji ko zasu sakeyi."

Meda kunnuwansu sukayi kan abinda ake faÉ—in.
"A madadin iyalan mai girma sarki Ahmadu suna farin cikin gaiyatar walimar auren. jikokinkin mai Martaba Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen JoÉ—o da matarsa Aysha Aliyu Garkuwa.
Da kuma Haroon Abubakar Ahmadu. Da amaryarsa.
Jannart Umar Jalaluddin
Za'ayi walimar ne a wurin babban filin taron al'ummar musulmi na Tsinako, ana gaiyatar ɗaukacin al'ummar musulmai wurin walimar wanda za'ayi yau misalin ƙarfe takwas na dare zuwa goma da izinin ubangiji, in da sanan malamin nan Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa wanda shima angone kuma shi zaiyi nasiha ga mauratan.
Saƙon gayyata daga Mai martaba Sarkin Ahmadu. Allah ya bada ikon zuwa Amin...".

Gajeren tsaki Sheykh ya É—an ja tare da cewa.
"Kai tsoffin nan fa sunada matsala, ji wani dogon sharhi iya sunayemmu ya ishi a gunduri mai sauraro".

Murmushi Ibrahim yayi tare da cewa.
"Kuma wlh tallatar tayi armashi."
"Sosai ma kuwa". Safiyyah tace, cikin jin daÉ—i.
A gogon hannunshi ya kalla kana yace.
"Tsaya nan garin muyi salla la'asar tana gab da wucewa".
To Ibrahim yace, kana sukaci ga da tafiya.
Tafiya kaÉ—an sukayi suka isa.
Wani masallaci mai kyau wanda dama dan matafiya akayishi.
Gefen mata da ban gefen maza da ban.

Bayan duk sunyi parking ne fadawan, suka fara fitowa.
Da sauri sukazo suka buÉ—e musu mota.
Ibrahim ne ya fara fita kana Safiyyah.
Juyowa yayi ya É—an kalleta ganin ta gyara zamanta ta kishin giÉ—a tare da lumshe idanunta.
fuska ya É—an yamutsa kana yace.
"Fitowa zakiyi muje muyi salla. Ba gyara zama zakiyi ba."
Shiru batayi mgna ba, haka yasashi haÉ—e fuska ya kuma maimaita mgnar.
Fuska ta kwaɓe tare da cewa.
"Ni nayi".
Idonshi ya zubawa fuskarta na daƙiƙu biyar.
Uhummm yace kana ya sa ƙafarshi ya fita.

Bayan sunyi sallan ne kana suka dawo sukaci gaba da tafiya.

Ƙarfe biyar dai-dai suna cikin masarautarsu Haroon.

Suna shiga fadawan suka wuce masauƙinsu dan sai gobe zasu koma.
Su kuwa Sheykh da Ibrahim Side É—in Abban Haroon Suka nufa sabida kiransu da yayi a woya.

Aysha da Safiyyah kuwa Side É—in Umaymah suka wuce.
Suna Shiga Hibba tace.
"O oyoyo My Aunty's Umaymah gasu Aunty Aysha sun iso".
Da sauri Umaymah da Aunty Hafsat da Rahma suka fito.
Cikin kula Umaymah tace.
"Allah sarki ÆŠiyata sukayi muku wayo suka dawo a jirgi ku suka barku da gajiyar mota ko".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai tace.
"Ina wuni Umaymah Aunty Hafsat barka da yamma".
Murmushi sukayi suka amsa cike da kulawa.
Aunty Rahma ce tace.
"Yaseen kuwa Umaymah ba wayo mukayi musuba Ibrahim ne yace mu barsu zasu dawo tare tun randa mukaje hutasa bayi shirin dawowa dasu a jirgiba".
Ta ƙare mgnar tana kallon Aunty Juwairiyya da Jazrah da suka shigo yanzu.
"A Safiyyah sai yanzu kuka iso".
Jazrah ta faɗa tana ƙin kallon inda Aysha take.

"Eh ba kun musu wayo ba".
Aunty Hafsat ta faÉ—a.

Murmushi suka É—an yi.
Cikin kula Umaymah tace.
"To Safiyyah yanzu dai kuje ku É—an huta, kafin ku fara shirin zuwa walimar."
To tace kana suka nufi ɗakin Hibba dan yau Side ɗin Umaymah cike yake maƙil da taron al'ummar Annabi.

Suna shiga Aysha ta wuce Bathroom da hand bang nata a hannunta.
Meda ƙofar tayi ta rufe tare da sauƙe ajiyan zuciya.
Dan tana son kimtsa jikinta sabida larurarmu ta mata da take tare da ita.
Allah yasa ma ita in tana fashin salla bata yawan fitsari.
A wuni bazai fi sau biyu zata zagaba, dan fitsari sai dan ko kimtsa jikinta, shima kuma baya mata wawan zuba, a bisa tsari yake zubo mata sai dai tana yawan bacci in bata salla.

Wonka tayi kana ta kimtsa jikinta da kyau, kana ta fito ba kowa a É—akin sai É—an Safiyyah dake bacci.
Akwatinta ta buÉ—e ta zaro wata doguwar riga mara nauyi ta zura.

Tana rufe akwatin Hibba da Aunty Rahma Suka shigo da Foodflaks a hannunsu.
Ishma biye dasu da plate and spoons.

A tsakiyar É—akin suka ajiyesu bisa carpet.

"My surka ina Safiyyah".
juyawa sukayi jin muryar Safiyyah a bakin ƙofar shigowa tana cewa.
"Gani Aunty Rahma naje nayi wonka a wancan É—akin ne".

"Ok to ga abinci zo kuci".

Cewar Rahma to tace kana ta shigo.
Aunty Rahma da Hibba kuma suka juya zasu fita Ishma na biye dasu.
Cikin yanayin gajiya Aysha tace.
"Ishma na zo mu zauna mana".
Cikin sanyi tace.
"Mommy tace in barki ki huta".
Fuskar Rahma ta kalla tare da cewa.
"Aunty bar min ita".
Sake hannun Ishma tayi tare da cewa.
"Ai shike nan gata in ta buwayeku da surutu Safiyyah ta korata".

Da sauri ta dawo ta zauna bisa cinyar Aysha kana su kuma suka fita.

Safiyyah ce ta zuba musu abincin.
Bayan sunci sun shane.
Aysha ta koma kan gado sabida har yanzu tana É—an jin ciwon cikin kaÉ—an-kaÉ—an duk da tasha mgnin ta.
Kwanciya tayi tare dasa Ishma a gaba.
Ganin kamar bacci zatayi ne yasa Safiyyah fita, ta koma can cikin Æ´an uwa nan sukaci gaba da hirarsu.

Saida aka kira sallan magriba ne duk suka tashi duk sukayi al'wala sukayi sallan magriba da yawa basu tashi bisa abin sallaba saida sukayi sallan isha kafin suka tashi.
Nan suka fara shirin tafiya walimar.

Aunty Hafsat Maman Safiyyar kenan wacce suke kiranta da Mamma ce ta nufi É—akin Hibba tana cewa Safiyyah dake bayanta.
Yauwa zo ki kaiwa Jannart nata kayan da zatasa a walimar, gana Aysha kuma."
Ta ƙarishe mgnar tana tura ƙofar Bedroom ɗin Hibba.

A hankali ta ƙarasa cikin ɗakin.
Kana a hankali ta juyo ta kalli Safiyyah cikin yin ƙasa da murya tace.
"Har tayi bacci ne ma?."
Chapter 138 · 0% Book details