Sashe 140
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Domin shi aure wata muhimmiyar igiyace wadda idan aka ƙullashi zai bawa ma'aurata daman saduwa tsakaninsu ba tare da wata ƙyama ba, kuma ta hakane ma'aurata zasu zama sutura ga junansu kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a Suratul Baƙara aya ta 187:-
"Su mata suturane gareku maza, sannan kuma maza sutura ne garesu-su matan.
Saboda haka zamu tabbatar lallai akwai al'ƙawari da amana mai ƙarfi a tsakanin ma'aurata, kuma Allah ya al'barkaci aure kuma yana son tabbatarsa , yana kuma ƙin ɓacinsa ba tare kwakkwaran larura ba.
Shi aure sunnace daga cikin sunnonin da ɗan Adam ya sami kansa a ciki, sannan kuma larurace daga cikin larurorin rayuwar ɗan Adam domin da aurene mutun zai kiyaye dangantakarsa, kuma ya ƙididdige ƴaƴansa wanda ya haifa kuma da shine zai kiyaye mutuncinsa, martabarsa dama dukkan dangantakarsa ga sauran ƴan uwansa da jama'a baki ɗaya kamar yadda Allah (S.W.A) ya faɗa a Suratul Furƙan aya ta 54:-
( WA HUWALLAZII KHALAƘA MINAL MAA'I BASHARAN FAJA ALUHU NASABAN WA SIRRAN WA KANA RABBUKA ƘADIIRA)
"Kusani Allah shine wanda ya halicci mutun daga ruwa kuma mai dangantaka surukuta kuma ka sani Allah mai iko ne akan haka".
Sassanyan numfashi ya fesar a hankali, kana yaci gaba da cewa.
"Shi Aure sunna ne mai samar da nitsuwa tsakanin ma'aurata. ÆŠan Adam bazai samu cikekkiyar nitsuwa ba a gidansa ba, sai in har yanada mata wacce ya aura.
Domin zata É—ebe masa kewa ta sashi ya samu nitsuwar hankalinsa.
Saboda zamansu tare a inuwar aure zatayi masa maganin kaÉ—aici kamar yadda Allah (S.W.A) ya faÉ—i a Suratul Rum aya ta 21:-
(WA MIN AYATIHI AN KHALAKA LAKUM MIN AMFUSIKUM AZWAJAN LITASKUNUW ILAIHA WA JA'ALA BAINAKUM MA'WADDATAN WA RAHMA INNA FII ZALIKA LA AAYAATIN LIKAUMIN YATAFAKKARUN)
ma'ana.
Yana daga cikin ayoyin Allah mai girma da ya halitta mana mataye daga kawunan mu, mataye da muke aure da su.
Domin su samu nitsuwa da junansu, sannan kuma ya sama musu soyayya a tsakanin su, tare rahama da tausayawa juna lallai a cikin wannan al'amari akwai ayoyi abin lura ga jama'an da suke masu tunani.
Saboda haka idan muka dubi wannan ayar ga ma'aurata zamu gane girman kudirar Allah da hikimarsa mai girma da ya halicci maza da mata kuma ya sanya ko wanne sashi mai karkata ga junansu kuma ya sanya igiya ya ɗaure tsakaninsu, wannan igiyar kuwa itace soyayya da tausayin juna da jinƙai.
Kuma Annabi (S.A.W) ya ce, cikin hadisin da Ibnu Majah ya ruwaito cewa.
(Babu wata fa'ida da mutun zai samu bayan ya. Takawar da Allah (tsoron Allah) wanda yafi masa al'khairi fiye da ya samu salihar mata ta kwarai wanda idan ya umarceta da tayi masa abu zata yi masa biyayya idan ya dubeta ta faranta masa ransa idan yayi rantsuwa game ita akan zatayi abu kaza ko bazata aikata abu kaza ba, zata kuɓutar dashi akan wannan rantsuwar da yayi, idan baya gida baya tare da ita, zata kiyaye mutuncinsa (Bazata yi fasiƙanci ba) kuma zata kula da dukiyarsa.
Ku duba cikin Fikihul Wadi littafin Dr Muhammad B Isma'il shafi na 9 zaku sami wannan hadisin.
A hankali Haroon ya ɗan juyo ya kalli fuskar amaryarshi Jannart, hannunshi yasa ta ƙasa table ɗin dake gabansu, tafin hannunta ya haɗe da nashi, tare da ɗan ronƙofowa kaɗan kana yace.
"Kina ji da kyau dai ko?".
Cikin lumshe ido tace.
"Sosai ma kuwa".
Aysha dake gefensu Haroon ya kalla tare da cewa.
"Al Sheƙiya matar Sheykh, ko zakije ki ja mishi baƙine?".
Ido ta É—an sunkuyar tare da fidda nannauyan numfashi kana a hankali tace.
"Ba dan gefen can da tarin maza manya iyaye da kakanni da sarakuna ba, tabbas da naje na zauna gefenshi na ja mishi baƙi".
Safiyyah da Ibrahim dake bisa kujerun dake gefensu ne suka kalli juna tare da yin murmushi.
Abokan Haroon kuwa gaba É—aya sun nitsu.
Abbansu Haroon da tawagarsa kuwa sai jinjina kai suke alamun gamsu É—ari bisa É—ari.
Ita kuwa Aysha a hankali ta É—ago kanta ta kalli inda yake, aikuwa karab idonsu ya haÉ—e cikin na juna,
taɓe laɓɓansa yayi tare dasa hannunshi ya shafi tattausan sajenshi kana a nitse yaci gaba da cewa.
"Aure kariya ce, kuma GARKUWA ce ga Musulmi saboda duk wanda yakeda mata, to ba zaka ganshi ya bar gida yana yawace-yawace ba ko ka ganshi yana leƙe-leƙe a woje ba, don yana da irinsa a gidansa, saboda haka mata ta zama GARKUWA a rayuwar ɗan Adam. Saboda haka ne ma Annabi (S.A.W). Ya kwaɗaitar da matasa samari da yin aure a cikin wani hadisin da muka samu a cikin Fiƙhul waɗi littafi na 2 na Dr Muhammad B Isma'il shafi na tara, Annabi (S.A.W) ya ce:-
Yaku samari wanda ya samu iko daga cikin ku to yayi aure.
Domin shi aure yana kare mutuncin farji da aukuwa cikin haram, (Yin zina) wanda bai sami iko ba to lallai ne ya juri yin azumi.
Domin assaumu junnatu, shi azumi GARKUWA ne.
Kuma shi aure cikon addini ne, saboda idan muka dubi aure sosai. Zamu fahimci aure yana taimakawa musulmi wajen tsare-tsaren addininsa kuma da wannan ne addininsa yake cika kamar yadda.
Dabarani da Hakim suka ruwaito daga Buhari da Muslim inda Manzon Allah (S.A.W) yake bamu labari a kan cewa aure tsari ne wanda yake taimakawa ga mutum ya cika addininsa a in da yake cewa:
Yana daga cikin arzikin Allah.
Allah ya azurtaka da mace salihan ko salihan mata, haƙiƙa zata taimaka ko wannan auren zai taimaka akan wani yanki na addini ka sai kuma kaji tsoron Allah akan sauran yankin.
Aure sunnace ta Annabawa da manzanni, saboda haka idan kayi aure ko yi ne da Annabawa da manzannin Allah. Allah maÉ—aukakin sarki ya faÉ—i:-
(WA LAKAD ARSALNA RUSULAN MIN ƘABLIKA WAJA'ALNA LAHUM AZWAJAN WA ZURRIYYAH)
Haƙiƙa mun aiko manzanni kafin kai, (Muhammad, S.A.W) kuma mun sanya matayen aure da zuriya a garesu.
Idan muka duba zamuga cewa yin aure koyi ne da aikin Annabinmu Muhammad (S.A.W) ne in da yace:-
(Kuyi aure ku yawaita domin ni zanyi alfahari da yawanku ranar lahira".
Juyowa yayi ya fuskanci gefen taron maza, kana yaci gaba da cewa.
"Kamar yadda muka sani cewa.
Mace abokiyar zama ce kuma shimfiÉ—a ce ga mijinta kuma mai rainon gidansa ce kuma abokiyar rayuwarsa ce, sannan kuma uwar Æ´aÆ´ansa ce sannan mai kula da dukiyarsa ce da mutuncinsa cikin amana saboda haka idan mata-ta zamo salihan ta gari to sai ta zamo kyakkyawan abu na duniya kuma ni'ima daga cikin manya-manyan ni'imomin da Allah ya azurtaka da ita".
Gyaran murya yayi tare da gyara zamanshi, kana ya fuskanci Haroon da Jannart da kyau, sannan ya É—an kalli Aysha da wutsiyar idonshi.
Tura bakinta ta ɗanyi fahimtar ita yake kallo, kanshi ya jinjina kana ya buɗe muryarshi da ɗan ƙarfi dai-dai misali yadda amon mgnarsa zata ratsa kunnen kowa yace.
HAƘƘOƘIN MA'AURATA GA JUNANSU.
bari mu fara da haƙƙin macce akan mijinta.
HAƘƘIN MATA A KAN MIJINTA.
Haƙƙoƙin mata a kan mijinta suna da tarin yawa.
Kuma ya zamo wajibi a kan mai gida ya tsareshi dai-dai gwargwadon hali, kuma wannan haƙƙoƙin Allah da Manzonsa sun tabbatar dashi, ga faɗin Allah madaukakin sarki akan haka inda yayi mgna cikin Suratul Baƙara aya ta 228:-
(WALAHUNNA MISLULAZII ALAIHINNA BIL MA'ARUF WA LIRRIJALI ALAIHINNA DARAJAT)
Mata sunada haƙki a kan mazansu kamar yadda aka sani. Sannan maza suna da wata daraja akan mata.
Haƙƙokin mace a kan mijin ta, suna da yawa amman ga wasu daga cikinsu.
(1) Wurin zama ga matar aure wajibi ne a kan mijinta. Miji zai tanadi wurin zaman matarsa gwargwadon ikonsa da samunsa kamar yadda Allah maÉ—aukakin sarki ya faÉ—a a cikin Suratul ÆŠalak aya ta 6:-
(ASKINU HUNNA MIN HAISU SAKANTUM MIN WUJIDIKIM WALA. TUDAARUHUNNA LITUDHAYYIKUM ALAIHIN)
Ku zaunar da matanku inda kuke zaune wato gidajenku.
Ba mummunan wurin zamaba kada ku cutar dasu don ƙuntata musu.