← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 183

Sashe 29

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye har bakin masarautar suka tsaya dan an hanasu shiga,
sai da ɗaya daga cikin hadiman dake tsaron ƙofar, yaga duk manyan daddatawa ne yasa yaje ya samesu bayan sun gaisane sukayi mishi bayanin abinda ke tafe dasu.
Jin abin babbane yasa yaje yayiwa sarkin ƙofa bayanin.
Nan shima yaje suka gaisa suka ƙara jaddada mishi, zancen abinda ke tafe dasu, sannan
sukayi musu izini suka shigo cikin asalin farfajiyar mashigar masarautar.
Kan kujerun dake jere a wurin suka nuna musu su zauna.
Bayan sun zaunane sarkin kofa yaje, wurin sarkin fada ya sanar mishi, to nan sarkin fada ke cewa.
"To ai babu abinda zamu iya musu, tunda shi GARKUWAN FULANI, baya ƙasar waye zai saurari kukansu, suje sai ya dawo su sake zuwa".
Cikin rauni sarkin ƙofa yace.
"Ranka ya daÉ—e sarkin fada, da dai an nema musu izinin ganin mai martaba, domin bazaiji daÉ—i ba in yaji sunzo kuma an medasu".
Cikin isa da izaya sarkin fada yace.
"A kul sarkin ƙofa ka tsaya iya matsayinka, kaje kace suyi maza su bar nan domin GARKUWANSU baya nan".
Cikin sanyi da mutuwar jiki sarkin ƙofa ya juya ya fita, koda yaje ya sanar musu, abinda sarkin fada ya faɗa hankalinsu yayi masifar tashi.
Cikin tashin hankali ArÉ—o Yabani yace.
"Shikenan danmu fulanine makiyaya mazauna daji, sai ya zama matsalarmu ba abar dubawa bace, wa al'ummar birane, duk inda muka kai kukanmu sai a koramu".
Cikin sanyi sarkin ƙofa yace.
"Kuyi haƙuri ba korarku akayiba, in sha Allah za'abi kadunku, wlh shi kanshi mai martaba in zaiji abinda sarkin fada yayi to zai barranta dashi, kuma haka nan shima GARKUWAN FULANI in da zaiji abinda sarkin fada yayi wallahi zai haɗu da fushinsa mai tsauri, domin shi zuciyar Sheykh zuciyace mai cike da imani da tausayi".
Cikin rauni Alhaji Haron yace.
"Ana binmu ana kashemu, ana sace yaranmu ana kora dabbobinmu.
Munje Police station an koramu, da mukaƙi tafiya suka watsa mata tiyagas, muje masarautar Numan akaci mana zarafi, sannan yanzu mun gudo gareku da yaƙinin zakubi kadunmu sannan kuma zaku koramu, so kuke mu ɗauki makami domin ramuwa ne?".
Da sauri suka juyo gaba É—ayansu jin muryar Jamil da yanzu ya iso wurin da hadimanshi, cikin sanyi yace.
"A a Baba kada ku É—auki makami domin ramuwa zuwanku nan shine babban abinda ya dace".
Cikin jin daɗi suke kallonsa, murmushi sarkin ƙofa da sauran hadiman sukayi dan sun san yanzu dai sarkin fada bai isa ya hanasu ganin Maimartaba. Domin yanzu bai fito fada bama tukun so zasu ganshi a kebantaccen wuri na musamman.
Cikin kulawa da sakin fuska Jamil yace.
"Baba ku biyoni".
Cikin jin daÉ—i sukace mishi to, kana suka bishi a baya.
Ta gaban shashin Sarkin fada suka shiga, kai tsaye har cikin fada ya shiga dasu,
shida kanshi yasa hadimai suka kawo musu ruwa.
Sannan a nitse yace.
"Baba ku zauna a nan zanje in sanarwa mai martaba, duk sanda ya fito daku zai fara, tattaunawa
In da masu buƙatan zagawa gacan wancan kusurwar in kumbi cikinta zata sadaku da bayi".
Cikin jin daÉ—i sukace.
"Mun gode yaro Allah yayi maka al'barka".
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita.
su kuma sukaci gaba da zaman jiran fitowan sarki.

A can kasa mai tsarki kuma,
Sheykh ne zaune a gaban Sitti, kana Haroon da Jannart na gefenshi Sheykh Aliyu Abdulkareem, kuma da Sheykh Jabeer Aliyu da wasu manyan malamai na zuriyar tasu duk suna zaune a cikin falon.
Jazrah kuma na gabanshi da wani tray mai masifar kyau da tsada.
Madara da zuma take zuba mishi a cikin wasu Æ´an kananun kofuna masu masifar kyau da É—aukan hankali.

Wannan ya kasance al'adarsuce ta baiyana nuna yarda da soyayya ko akasinshi, indan ana son a haÉ—a yara aure, to za'a tattauna tsakanin manya, bayan sun gama dai-dai-ta magana tsakaninsu kamar yadda yanzu su Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen, da kuma su Sheykh Jabeer Aliyu da babban babansu Sheykh Aliyu Abdulkareem da kuma Sitti suka gama haÉ—a zancen auren Jazrah da Sheykh Jabeer, to yanzu ta zuba mishi madara da zuma a gaban kowa, ta ajiye mishi, idan ya É—auki kofin madara to yana nufin yana sonta ya kuma amince da ita da aurenta.
In kuma ya É—auki kofin zuma, to yana nufin ya tsaneta baya kuma sonta bazai kuma auretaba bare ya zauna da ita.
Za'ayi komai a gaban manya ne, don suga zahiri kuma a tsarin ko ɗan uwanka zai iya yi maka zaɓin da kuma in dai am zaɓa maka sai ka aura.

Shiru sukayi baki É—ayansu falon, kowa da tunanin da yakeyi.

Sheykh Jabeer dake zaune a tsakiyarsu cikin shiga ta al'farma sai sheƙi al'kyabbar sa keyi, ga tattausan hirami a kanshi, ido ya lumshe daya gane manufarsu.
"Domin shi basu gaya mishi cewa, zasuyi wannan abun bane daya sani wallahi da yasan duk yadda zaiyi ya gudu, ya tafi harami, har sai sun gaji sun watse.
A hankali ya kalli Sitti dake kallonshi cikin rauni da alamun.
"Dan Allah kada kace, a a yar É—an uwanane, kada ka bamu kunya nida kakanninka maza yar uwarkace kasan tarbiyarta".
Kauda idonshi yayi daga kallon Sitti, wani irin kallo yayiwa Haroon daketa yi mishi, murmushin muguntan yau dai an titseka baka da hanyar tsira.
Cikin ranshi yake mgnar zuciya.
"Ta yaya zan amince ince zan aureta? Dame zan zauna da ita?".
Sai kuma ya É—an fidda nannauyan numfashi.
"To idan ban amince da aurentaba me zamcewa, waÉ—anannan bayin Allah'n da sukayi min dukkan gatan duniya, na zauna a gidansu tsawon shekaru masu yawa nayi karatuna har na gama, sukemin komai na rayuwa, suna nuna min soyayyar da mahaifinama baya nuna min, da wanne idon zan kallesu inna É—auki zuma alamar na tsani yarsu?".
A hankali ya buÉ—e idonsa, jin muryar. Sheykh Aliyu Abdulkareem kakan Mamanshi kenan, baban kakarshi Sitti dottijon daya yake sonshi tamkar ranshi yana cewa.
"Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, kayi zaɓin da ranka keso, bamu da nufin yi maka dole, sai dai ina da burin aurar maka jikata Jazrah ɗiyar mai sunanka. Ina so da fatan ganin nasabarka ta cika, cikar nasabarka kuwa, shene aure."
Wani irin sassanyan numfashi ya shaƙa a hankali, wasu irin zafafan tunanuka ne ke zirya a zuciyarshi".
Cikin harshen hausar katsinawa, Haroon yayi mgna can ƙasa yadda ko Sitti bazata jisuba.
"Sheykh kafa, shanyamu, nifa zan É—aukar maka Madara".
Ido ya lumshe tare da É—an jingina da jikin kujerar da yake zaune, wanda yake kusa da Sheykh Abdulkareem.
Sitti ce ta ɗan kalli Haroon tare da mishi alamun ya taɓo Sheykh.
cikin harshen larabci Haroon ya kalli kakar tasu, tare da cewa.
"Sitti ai nasan zaɓinsa, bari ki gani in nuna miki".
Ya ƙarishe mgnar yana kai hannunshi kan kofunan.
da sauri Sheykh Jabeer ya buɗe kekkyawar ƙwayar idanunshi da wasu ke kiransu da zaiba, wato kamar idon mage, idon ya ɗan zaro ganin Haroon yasa hannunshi kan kofin M...!

😂😂😂😂😂

Masu cewa na kulle musu kai kada ku damu zan kuce kawunanne, lokaci ne😂🙏🏻🤝🏻

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 12

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘

Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku ta wannan number 09097853276. KO kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz domin samun shiga Special Group, wanda cikin kwanaki ƙalilan za'a gama littafin da izinin ubangiji. Ga asusun kamar haka 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, 1k ne SPG sai ki turo min shaidar biyan
ki ta wannan number 09097853276.

Gareku iyayen ƴan mata da za'a aurar, akwai sittin amare mai kyau na gyaran jiki, bisa farashi mai sauƙin, akwai na manyan robobi akwai na ƙananan robobi, akwai haɗin masu jego, da na maida tsohuwa yarinya, sayan na gari meda kuɗi gida, in kayan gyaran kikeso ki fara min text message ta inbox ta wannan number 09097853276 sai ki gaya min kaya kikeso, kana sai ki kirani to nan zan ɗaga kirankin sai muyi mgn zaki turo kuɗi ta ACCOUNT number ni kuma zan tura miki kaya ta mota, duk garin da kike a Nigeria ina aikawa, in dai ba lungu yayi sosaiba. Kana mutanenmu mazauna ƙasashen ƙetare kamarsu Saudia, India, Gabon, Ghana, Niger, Cameroon, da dai sauransu in kinada dalili kayana na zuwa can cikin salama. Ina saida kaɗan-kaɗan ina kuma bada sari.

A dai-dai kan kofin madarar ya sa hannunsa, alamum zai mishi zaɓi kenan, murmushi yayi dan ya samu damar, da zai tserewa tsarinsu. Cikin ihima da sanin makaman kariyar kai daga jin kunya ko yin abinda zai ɓata ran wani, ƙafarshi ta dama dake kusa da hannun Haroon yasa cikin hikima ya bugi hannun Haroon da ke gab da ɗaukar kofin.
ture hannun yayi da babbar yatsarsa, wanda, hakan yasa hannun Haroon ya bugi kofunan da É—an karfi, sai gashi duk sun tuntsure a tsakiyar tiren madarar da zumar kab suka malale cikin tray É—in.
A tare suka zubawa tray idanu gaba É—ayansu.
Sitti kuwa wani irin kallo tabi Madarar dashi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin iya taku da kamalarsa murya a mutunce ya kalli Haroon daya kafeshi da idon tuhuma, cikin harshen larabci da kamala yace.
"Harooon meyasa baka da nitsuwa?".
Cikin tarin mamaki Haroon ya gwalo ido tare da cewa.
"Haaahh".
sai kuma ya kalli Sitti da ta kwaɓe fuska tamkar zata kurma ihun takaici.
Shi kuwa Sheykh Jazrah ya zubawa ido, ganin yadda ta zuba mishi kekkyawan idanunta, wanda suke sheƙin hawayen dake nuni da zazzafan son da takeyi mishi.
Kauda kwayar idanunshi yayi, da sauri.
Jannart kuwa hannun Sitti ta kamo ganin zata jawo tray.
A hankali Sheykh Khalillullah wanda yake ƙanin Sitti ya gyara zama cikin sakin fuska da murmushi ya kalli jikan nasu, nitse yace.
"Laaba'as". Dib-dib haka ƙirjin Sheykh Jabeer Habeebullah ya fara bada sauti, fahimtar kakanun nashi zasu ɗaura zabin kan, fahimtar lafazin Haroon.
Shi kuwa Haroon, wani irin murmushi jin daÉ—i yayi.
Shi kuwa dottijon nan, ido ya zubawa Æ´aÆ´anshi da jikokin Æ´aÆ´an nashi, da wasu jikokinshi. Kallonsu yake yana nazartansu.
Chapter 29 · 0% Book details