← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 183

Sashe 63

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

By
*GARKUWAR FULANI*Ta É—an buga table É—in, tare da cewa.
"Malam ka tashi kaje ka taimakawa yan uwanka musulmai! in kuma baka da lfy ne ka nemi bokaye irinka su duba lfyarka".
Zuwa yanzu gaba É—aya jikinshi tsuma yakeyi ta ciki. Kanshi ne yakeji yana jujjuya mishi sabida yadda ta konkotsa glass table É—in da kanshi ke kife a kai. Ga kuma sautin muryarta da yake jinshi har tsakiyar kanshi.
Da sauri ya É—ago kanshi tare da ware matsakaita kyawawan idanunshi na zaiba.
Cikin sauri Haroon ya matsoshi ganin idanunshi sun cika tab da ƙwalla sai sheƙi sukeyi alamun suna iya zubda ƙollan a ko wanne lokacin.
Cikin harÉ—ewar murya ta larabci yacewa Haroon.
"Please ka fitar da ita a nan, ta matsa kaina zata fasa min dodon kunne".

Ita kuwa Shatu cikin tarin mamaki da al'ajabi ta zaro manyan idanunta tare da cewa.
"Laaah!". Sai kuma ta fara É—an ja da baya tare da cewa.
"Afwan baka da lfy ne!?." Wani irin fitinenne murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"Eh baya jin daÉ—i ne, É—an fita zamu kira wasu bokayen suzo su dubashi".
Cikin sauri tace.
"Subahanallahi bokaye kuma?".
Kai ya gyaÉ—a mata tare da cewa.
"Yesss ba haka kikace ba, ya nemi bokaye Æ´an uwanshi su dubashi".
Kanta ta É—an dafe tare da cewa.
"No kada ka munana min zato, ina nufin likita bokan turai ka gane ko?".
Da sauri taja da baya ganin Jabeer ya miƙa tsaye da ƙarfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer tsayuwanta kusa dashi barazana ce ga zuciyarshi tabbas zata iya faso ƙirjinshi ta fito.
Ganin yadda ya haÉ—e fuska ya nuna mata hanyar fitane, yasa ta juya ta fita.

Shi kuwa Jabeer komawa yayi ya zauna tare da sauƙe wasu tagwayen ajiyan zuciya a jere a jere.
A hankali yake jin bugun zuciyarshin na É—an dai-dai-ta kamar dai yadda yaji kafin ta shigo.

Sai kuma ya fara jin zuciyarshi na tsinkewa ras-ras kamar dai tana tsoron kada wani abu yayi nesa da itane.
"Ya ilahi ya mujibadda'awati ya hayyu ya ƙayyum".
Sune kalaman da Jabeer yaketa maimatawa a saman lips É—inshi.

Haroon kuwa wani irin kallo yakeyi ma Jabeer mai cike da nazari.

Jalal ma kallonshin yake cike da tarin mamaki duk da sun san baya son akeyin mgn da ƙarfi a kanshi, to amman idonshi bai taɓa ciko da hawaye ba, sai yau.

Ita kuwa Shatu, ido ta zubawa Rafi'a da ta tsareta da ido, cikin yin ƙasa da murya tace.
"Rafi'a dama, wannan shugaban tuzuran ƙasar nan, yana aiki anan asibitin gwamnatin jihar nema?".
Kamo hannunta Rafi'a tayi tajata sukayi gaba.
Haroon kuwa dariya yayi sabida, duk da rage muryarta da tayi sunji abinda tace, sabida wurin da suke É—in yanada amsa kuwar amo.

Cikin yin ƙasa da murya sosai Rafi'a tace.
"Garkuwa ki nitsufa ki rufa mana asiri, kin ko san waye wannan?!".
Shiru sukayi dukansu lokacin da suka juyo wata kekyawar mata tana bawa wasu ƴan mata Nurses a ƙalla sun kai goma lbri.
Ido Rafi'a da Shatu suka zubama wannan matar cewa.
"Shi wannan Dr Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoÉ—a, ba kamar sauran mutane bane, shi mutunne da Allah yayi masa wasu baiwa da nasabobi masu tarin yawa".
Wata Æ´ar kekyawar cikinsu ne ta É—an lumshe ido tare da cewa.
"Allah ya sani Aunty ina sonshi, ina son wa'azin shi, muryarshi kawai in naji yana zuba larabci sai inji bani da sauran damuwa a duniya, sai dai shi kuma yana nan kamar dutse!".
Da sauri Matar nan tace.
"Ai bazai yiwuba, wlh bazai taɓa kulakiba, duk nacinki da korkosarki, shiyasa wasu ke raɗe-raɗin shi waliyi ne!".
Numfashin ta sauƙe tare da ci gaba da cewa.
"Duk matsayinki, kyanki, mulki, sarauta, gata, ilimi!. ko da meye kike taƙama dashi a duniya ya fiki abin".
Kusan a tare suka haÉ—a baki wurin cewa.
"Kawai dan shi jikan sarkine sai yafi mu komi?".
Kanta ta jinjina tare da gyara zaman ta cikin sanyi tace.
"Ba haka bane. Bari kuji kaÉ—an daga cikin nasabarsa.
Kunga forko dai shi mutum ne wanda ubangijin yayi mishi baiwar ilimin addini dana zamani.
Yana É—aya daga cikin manyan malam da Afirka gaba É—aya take ji dashi.
Sabida a ƙiyasin malamai babu yaro matashi mai jini a jiki da tarin ilimin addini kamarshi.
Tun yanada shekaru takwas a duniya ya haddaci al'ƙur'ani mai girma.
Sannan ya fara karatun littafai shine matashin da yakeda haddar hadisai zunzurutunsu a kanshi sama da dubu ashirin.
Kunji wannan darajeta da tasa ko manyan mutane suke girmama shi.
Sannan shi jinin Masarautar JoÉ—a ne ta wurin mahaifinshi.
Ta wurin mahaifiyarshi kuwa shi jinin sarki Jalaluddin ne, masarautar sarkin Musulmai.
Kana ta wurin kakarshi data haifi mamanshi. Asalin balarabiyar saudiya ce, wacce zuriyarta ne limamen Harami.
Kunga nasaba kan nasaba kenan.
In kyau ne na halitta, babu irin kyan da bai ganiba,
In kuwa kuɗine, ku leka ƙasan gidan saman nan zakuga ayarin motocin da sukayi mishi rakiya, to ko kakan nashi Lamiɗo motar da yake hawa bata kai ta Jabeer ba.
Uwa uba shi mutun ne da ya ƙoshi da sunna, baya son bidi'a.
Shi mutun ne wanda ya samu kekyawan zato a wurin mutanen duniya ake mishi shaidar salihi, mumini, mai tausayi."
Da sauri suka ƙatseta da cewa.
"To Aunty meya hanashi yin aure har yanzu?".
Cikin maida numfashi tace.
"Allahu alamu, sai dai ance kamar shi bana miji bane!".
Cikin sauri wata tace.
"Kai mgnar. Duniya dan Allah kiji zancen ƴan shashi faɗi. Bita da ƙulli har an samo sharrin da aka liƙa mishi bawan Allah."
Rafi'a kuwa kai ta jinjinawa Shatu alamun kinji ko, ita kuwa Shatu zuru tayi kamar makahon daya tsinka garaya".
Cikin sauri wacce tace tana sonshin tace.
"Wlh ni dai ko shi bana miji bane zan iya zama dashi a hakan in da zai yarda muyi aure".
A hankali Shatu ta gyara riƙon da tayiwa wayarta tana ɗaukar su video.

A hankali matar nan ta nisa tare da cewa.
"Uhum Nafeesat kenan ai kuwa da wuya ya aureki duk abinda zakiyi.
Sabida kin ga Dr sugzana yar India ce ƙabilar buramin bautar wuta takeyi.
Tace tana sonshin, tace in dai zai aureta zata musulunta, amman yaƙi".
Da sauri É—aya dake cinsu tace.
"Sabida me yaƙi duk da tayinta na shiga addinin Allah?".
Cikin sanyi matar tace.
"Yayi bayani kuma manyan malamai sun gamsu da hujjarsa, inda yace, tace dole sai in zai aureta zata musulunta, kenan badon Allah zata musulunta ba sai dan sonshi.
Ta kuma ce in sunyi aure duk yaransu rabasu zasuyi rabi suyi addininshi rabi suyi addininta bi ma'ana wasu suyi bautar wuta wa iyazubillah.
Yace wannan dalilin yasa bazai aureta ba, kuma shi baya sonta, ya kuma gargaÉ—i mata su dena cewa suna sonshi.
Dan shi yanzu al'majiri ne sai ya girma zaiyi aure".
Dariya sukayi baki É—ayansu.
Jin hakane yasa Rafi'a yana Shatu suka ci gaba da tafi.

Su kuma waÉ—ancan sukaci gaba da hirarsu.

Tafiya kaÉ—an sukayi suka samu wasu yan mata da samari suna hira É—aya daga cikinsu na cewa
"Ni tsarin Sheykh Jabeer yana masifar burgeni a rayuwata.
Shifa tunda yake a duniya babu wani mahaluƙin da zaice yaga koda singalalin hannunshi ne a waje.
Mutum ne da Allah yayi mishi sutura, yake kuma suturce kanshi."
Cikin dariya wani yace.
"Kai nima yana burgeni sai dai tsarinshi na wai mata su dena yafa gyale, su rinƙa yin shigar zurmuƙa-zurmuƙan hija baine bai minba, to mu matasa taya zamuyi ta kallonsu munajin daɗi.
Ni wlh wani lokacin a kallonma nake biyan buƙatar damuwata sai dai inje inyi wonka".
Cikin tashin hankali É—aya daga cikinsu yace.
"Ouzubilla, ka nemi gafar Allah wlh zina kakeyi".
Cikin zaro ido yace.
"Kai malam dakata ni banyi zinaba".
Cikin sanyi babban nasu yace.
"Wlh kayi sabida ita zina ai kashi-kashi ce akwai ta ido akwai ta kunne haka kuma akwai ta zahiriya, fisabilillahi ka kalli yar mutane na tafiya har kaji ka biya buƙatar ka?".
Kai ya gyaÉ—a musu cikin sanyin jiki.
Nan sukayi ta mishi nasi daya kame idanunshi

Da sauri suka wuce su.
Ita kuwa Rafi'a cikin murmushi tace.
"To bari in baki amsar tambayar ki.
Yana zuwa nan asibitin sau É—aya cikin ko wanne sati. In yazo kuma ranan duk wanda ya duba magani kyautane, in kuma aikine kyautane.
Kinga Hospital É—in school É—inmu shi kuma a wata yake zuwa sau É—aya,
Nanam da kyar ya yarda, yanada asibitinshi mai zaman kanshi can yafi maida hankali".
Ajiyan zuciya Shatu tayi tare da cewa.
"Uhum can yake tara kuɗin bayin Allah ya ƙwamushewa dai".
Kai Rafi'a ta jujjuya tare da cewa.
"No ba haka bane, duk abinda zan ce miki bazaki gamsuba in sha Allah sai Next month in ciwon mararki ya tashi, zan kaiki can zakiga zahiri.
Amman dai daga sunan asibitin zaki iya fahimtar manufarsa".
Kallonta ta É—anyi tare da cewa.
"Menene sunan asibitin?".
Ƙara saurin tafiyarsu sukayi tare da cewa.
"Ballitai Hospital". Kanta ta gyaɗa alamun gamsuwa da sunan asibitin kana taja hannun Rafi'a suka tafi can maraba da baƙi.

Abin mamaki suna isa suka samu.
Kusan rabin DOCTOR'S din asibitin duk suna wurin.
Duk DOCTOR'S É—in da Shatu tayiwa mgna sunzo nan sunata basu taimakon gaggawa.
Kana ga Nurses tako Ina, sunata tura marasa lfyan ana basu gadaje.
Cikin abinda bai gaza awa É—aya da rabi ba.
Komai yayi dai-dai hatta waÉ—anda za'ayiwa aikin anyi musu.

Bisa umarnin Lamiɗo kana ya rinƙa bin gadajensu yana ajiye musu kuɗi dubu biyar-biyar.

Sosai wannan abun yayi masifar yiwa Shatu daÉ—i, tana kallon dattijon tamkar wani nata,
Godiya sosai sukayi musu da zasu tafi, suna fita nan sukayi kiciɓis da Jabeer da yanzu ya fito ɗakin tiyata.
Chapter 63 · 0% Book details