← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 183

Sashe 44

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Hashimu ne da ya samu ya dawo gida jikinsa da sauƙine, yayi wani irin kabbara mai ratsa zuciya, cikin sanyi yace.
"Ziyararku tayi haske sabida kun zo mana da mai hasken addini a jiki da zuciyarshi".
Ga mamakinshi sai yaji ÆŠanzagi na cewa.
"GARKUWA ya amsa Sheykh Jabeer Jikan sarki tsatson sarki gaba da baya".
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali yake takunda yasa al'kyabbar sa buÉ—uwa tana bajewa, sabida É—aga hannunshi da yayi yanai musu sallama irin ta addinin Musulunci.
Mafi akasarin mutanen tafukan hannunshin suka zubawa ido, sabida kai da ganin tafin hannunshi kasan ya gauraye da ni'imar ambaton sunan Allah da rike littafi al'ƙur'ani, da kuma jin daɗin.
Shi kuwa Jabeer ƙara sarƙafe carɓin shi yayi cikin yatsun hannunshi, kana, ya fuskanci gefen hagunshi, ya ɗanga musu hannu tare dayi musu sallamar kamar yadda yayiwa yan gefen damanshi.
A haka har suka isa tsakiyar ƙaton filin.
Inda LamiÉ—o da sauran tawagarsa ke zaune.
Bisa fararen kujerun robar da anka jera musu cikin rumfar suka zazzauna.
Bayan sun amsa musu sallamar da sukayi.
Cikin nitsuwa LamiÉ—o ya kallesu tare gyara zamanshi.
Muryar ÆŠanzagi ce ta karaÉ—e wurin da cewa.
"Gyara kimtsi. A saurara dai LamiÉ—o jikan É—an Lami Bubayero jikan LamiÉ—o JoÉ—a zaiyi mgna".
Wani irin harara suka watsawa Danzagin, shi kuwa LamiÉ—o cikin nitsuwar datattaku tace.
"Da farko dai zan fara da baku haƙurin zalumcin da akayi, muku, Allah ya jiƙan wanda suka rigamu gidan gsky."
Da ƙarfi Ɗanzagi yace.
"Amin". Su kuwa dattawan ido kawai suka zuba mishi.
Shi kuwa LamiÉ—o a hankali yaci gaba da cewa.
"Ina mai baku haƙuri da kuma umarnin kada kuce zaku ɗauki mataki domin ramuwa."
Kamar daga sama sukaji Muryar Bakur yana cewa.
"Babu wani sarkin da ya isa ya hanamu É—aukar fansa sai, Ubangijin daya busa mana, numfarfashi".
Da ƙarfi Wani dogarin ya ɗago zabgegiyar bulalarshi ya zabgawa Bukar.
Wanda saida yayi tsalle ya kurma ihu.
Cikin tsauri LamiÉ—o ya É—agawa duka fadawanshi da hadimanshi da dogara shi hannu alamun kada su sake dukan kowa.
Saura su Waziri kuwa duk shiru sukayi,
Jabeer kuwa, a hankali yaci gaba da tasbihin da yakeyi, sabida danne abinda yakeji zuciyarshi nayi.
Shi kuwa LamiÉ—o cikin sanyi ya fara mgna, dan yasan zafin rashin da sukayi ne yasa sukace sai sun rama, a hankali ya kalli fuskokin dattawan da yasan sunje mishi har fadanshi dan neman zaman lfy, cikin kula ya kalli ArÉ—o Bani tare da cewa.
"Arɗo Bani zaku haƙura, hukuma da masarauta ta bi muku kadun cutar damu da akeyi, ko zaku ɗauki makami dan ramawa?".
Cikin tarin kufula da harzuƙa da kuma son cinma wata gagarumar manufar da ya daɗe yana fatan ya samu da sai yau, fuska a haɗe yace.
"Babu wani wanda zan kuma hana É—aukan makami,
Dan kare kanshi da ramuwar kisar gillan da akeyi mana."
Cikin tarin Mamaki da al'ajabi Bappa da sauran dattawan suka buÉ—e baki tare da kallon Ardo Bani, Jabeer ma idon ya buÉ—e cikin sanyi yace.
"Baba Ardo kayi haƙuri, muyi aiki da al'ƙalami, domin al'ƙalami yafi tokobi, ina nan inata shirin samar da tsaro na musamman kan FULANIN ƙasarmu da nake shugabanta."
Cikin nuna tsantsar fushi da son fusata LamiÉ—o ArÉ—o Bani ya dakawa Jabeer tsawa tare da cewa.
"Kada rufe min baki, meka sani akan Fulani? Me ruwanka damu? Damuwarmu ta shafeka ne? Ina kake sanda ake kashe mana mata, yara, jikoki, mu kanmu bamu tsiraba, in munje mun kai kukanmu a koremu tamkar karnuka, sabida duk baku san darajar fulani ba."
Cikin sauri ÆŠanzagi yace.
"Hattara dai Ƙaramin Ardo, wannan sarkine na fulɓe masarautar filɓe ce gaba da bayanta".
Cikin É—aga Muryar Ardo Bani yace.
"Tafi can baƙin bawa, bawan banza bawan wofi mai ka sani kan fulɓe, meka sani banda bauta da fadanci, masarautar da kuke bautawa bata san menene fulɓe ba".
Cikin sauri Waziri ya yunƙura zaiyi mgna, da sauri Lamiɗo ya dakatar dashi, sabida zuwa yanzu zuciyarshi ta fara tafasa, yaya daga kawowa mutane ziyara dan ja-jantawa suke neman tozarta mushi masarauta. Cikin ɓacin rai ya kalli su Bappa daketa kama hannun Arɗo bani daketa fizge-fizge yana kwaza musu baƙar mgna, cikin fushi yace.
"Masarautar JoÉ—a É—ince bata fulani ba?".
A harzuƙe Arɗo Bani yace.
"Tabbas dan data fulanice, da an bamu kariya da tsaro, da an duba kukanmu, a kashemu a hanamu ɗaukar fansa, an kuma kasa bamu tsaro. Nan da mukaje ina shi jikan naka da yake matsayin Garkuwan Fulani, yana can ƙasashen woje, da iya dukiyar da ake bashi tsaro da kariya shi rai ɗaya ta kai a kula da fulanin daji dubu a kuma basu tsaro.
Yau kwana uku da kashe mana mutane sai yau zaku É—ebo manyan riguna kuzo mana da batun wai kada mu rama, sara da suka da yanka mana mutane da akeyi,
Kaida kab zuriyar ka da masarauta ka, babu mutun ɗaya da zai iya jurar koda bulalar *(SHAƊI)* ma bare sara da yanka da suka da wuƙa a hakan kuke ganin kanku Fulani".
Cikin tarin zafin ƙuna da tafasar zuciya Waziri yace.
"To me kuke so muyi muku, tun randa akayi abun munzo bamu sameku ba".
A harzuƙe Bukar yace.
"Ƙarya ne babu wanda yazo".
A hankali Jabeer ya buÉ—e baki da nufin zaiyi mgna sai yaji LamiÉ—o na cewa.
"Uhum jinina kuke cewa ba fulaniba, to ko jaririn da aka haifa yau a jikin masarautar JoÉ—a zai iya jurarar bulalar SHAÆŠI bare manya ko É—an baiwa zai iya bare jinina Æ´aÆ´ana ko jikokina, ko kun manta masarautar JoÉ—a ce tushen ShaÉ—i?".
Cikin son harzuƙa Lamiɗo Arɗo Bani yace.
"A da can baya ba, yanzu kuma da aka san lusarai ake haifa a masarautar inji an haramta shaɗi a masarautar, yau in kun isa fulani ka bada ɗan ka ko jikanka ayi gasar Shaɗi dashi, in ya iya jurewa, to mun yarda mun gamsu ku fulanine ku masarautar Fulani, in kuwa kun kasa fidda goninku to, ku ba masarauta fulɓe bace."
Wani irin karkarwa jikin Lamiɗo ya fara sabida fusata, wai suda masarautarsuce tushen fulɓe a ƙasar, su ake cewa ba fulani ba, har ake kiransu lusarai, Galadima, Waziri, Wambai, Ɗan iya, Ɗan buram, Ɗan Maliki, Sarkin Dawaki.
Gaba É—aya hankalinsu yayi masifar tashi sabida ganin tsananin fushi da tashin hankalin Sarki LamiÉ—o.
Jamil Jalal Haroon kuwa , hankalinsu na kan Jabeer bisa alamun yana cikin wani hali.
Shi kuwa Jabeer bugun da zuciyarshi keyi ne yasa,
Hankalinshi tashi, ƙarfin addu'o'in da yakeyi ne, yashi iya fahimtar abinda suke cewa.
Kamar daga sama kamar cikin mafarki, sukaji murya LamiÉ—o na cewa.
"Ga jikana, Jabeer GARKUWAN FULANI, na badashi a matsayin matashi mai yin gasar ShaÉ—i ku fito da duk gwanin da kukega shine makurar gwayen yankinku. Ayi ShaÉ—i dashi yadda zaku samu gamsuwar yakai matsayin ya kasance GARKUWAN FULANI".
Tunda ya amɓaci sunan Jabeer, Sarkin Fada yayi wani irin murmushi mai cike da jin daɗin alamun burinshi zai cika.
Hakama ArÉ—o bani wani irin asirtaccen murmushi yayi.

Jala, Jamil, Haroon, Hashim, Imran, Galadima, kuwa wani irin zazzaro ido sukayi.
Cikin tsananin kaÉ—uwa da firgicin batun LamiÉ—o suka zuba mishi ido.

Bukar kuwa cikin karaji yace.
"Ba'ana Bukar shi zai kara dashi."
Ya ƙarishe mgnar da fatan Ba'ana ya kashe wanda aka kira da Jabeer tunda jikan Lamiɗo ne.

Jabeer kuwa wani irin kallo yayi kakan nashi, irin kallon nan.
Na lallai kam tsohon nan ka haukace, ka zauce, ai bani bakam ko inuwata bazaku kuma gani a garinkuba bare kuyi wannan gwajin dashi.
Ga mamakinsu kab sai sukaji ArÉ—o Bani na cewa.
"A yau É—inan kuma Yanzun nan, a kuma nan za'ayi gasar ShaÉ—i in har kun isa fulani."
Sosai Lamiɗo yaji hakan bai mishi ba dan a zotonshi za'asa ranane ya koma ya shirya Jabeer kafin ayi gasar, to fahimtar ƙuresu suke neman yi, yasashi gyara zamanshi cikin danne fargabanshi na anya Jabeer zai iya jura yace.
"Na Aminc....!

Yau bisa wani uzuri ban samu yin posting da wuriba, kana kuma ba editing a gurguje na watsoshi, bari in nemo PAGE 16 ko zuwa yan da yamma ne.

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 16

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘

*FREE PAGE SUN ƘARE DAGA WANNAN PAGE 16 DIN IN DAI KIKAGA LITTAFINA GARKUWA BA TARE DA KIM BIYA NA SAKI A GROUP BA TO NA SATANE, DAN ALLAH DA MANZONSA KADA KU FITARMIN DA LITTAFI DAN ALLAH KU BARI IN SAMU KUƊI zuwa makka😂😂😂*

*Littafin GARKUWA na kuɗine dan Allah da Manzonsa kada ki karanta na sata, kada ki watsamin littafi a sata, turo katin MTN na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 ki biya ki karanta cikin aminci ba tare da haƙƙi naba. Ko kuma ki biya 1k domin shiga Special Group wanda cikin sati biyu rak za'a gama Part 1, da izinin ubangiji kana a shiga 2, turo dubunki ɗaya ta wannan asusun 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidan biyanki ta wannan number 09097853276 in baki da halin biyan dubu ɗaya ko baki da ra'ayi kina iya turo ɗarinki uku kacal da ban tsauwalaba sabida halin rayuwa da muke ciki. Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki sai littafina in dai kin san niyarki ki saya ki fitar da shine in kuma. Har kin sayane to dan Allah da Manzonsa gaya min in baki kuɗinki in cireki a group na, dan Allah🙏🏻 nace badon niba*

"Na Amince!". Cikin tarin mamaki Jalal, Jamil, Imran, Haroon, Hashim, da duk sauran tawagar LamiÉ—o suka, zazzaro ido cikin tarin mamaki da al'ajabi, sam basuyi zaton jin haka daga gareshi ba,
Ya Salmanu kuwa wani irin farin cikin mara misaltuwa ne, ya rufewa, domin yana ganin ikon Allah da yake nuna mishi zahirin abinda yake nuna mishi a mafarkansa tsawon kwanakin da yake a gadon asibiti.

Ba'ana kuwa da tun É—azu ya iso, wani irin ihu yayi mai cike da farin ciki, da jin daÉ—in yana ganin zaiyi abinda gaba ko kashe mutanen Rugar Bani sukayi gaba É—aya, masarautar JoÉ—a bazata kulasuba,
Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi sabida azabar muguntarsa dake tasowa.
Chapter 44 · 0% Book details