← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 183

Sashe 69

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna tafiya, Umaymah ta koma É—akin da Aysha take, nan ta samu Ummi na zaune da ita. Nan ta zauna ta suka É—an yi hira ganin alamun gajiya da bacci a tattare da itane yasa, sukayi mata saida safe suka fita suka tafi.

Ratsawa sukayi wurin Gimbiya Aminatu suka mata saida safe kana suka fita suka tafi.

Cikin tsananin jin daÉ—i suke tafiya, har suka iso bakin.
Mashigar sashinsa, cikin nitsuwa sukaci gaba da tafiya.
Shiru ba motsin komai suna gab da isa bakin ƙofar, suka tsaya cikin zaro ido, suka kalli Laminu da Gimbiya Saudatu, cikin haɗe fuska da zafi Umaymah tace.
"Aoozubikalimatillahi taaa'ammati minshirin makalaƙa!."
Cikin tsantsar tsanarta Gimbiya Saudatu tace.
"A kanki hegu masu jajayen kunnuwa".
Tana faÉ—in haka taja hannun Laminu suka fita.
Su kuwa Umaymah da sauri sukayi ciki.

A falo suka tsaya. Ba kowa a falon haka yasa tayi sauri ta nufi arear'n Side É—in Jabeer, a falo ta samu Haroon konce bisa kujera.
Yana ganinta ya tashi zaune.
Cikin gimtse dariyarshi murya a hankali yace.
"Yau duk kayan ahlin masarautar JoÉ—a sai an yagesu baki É—ayansu."
Ya ƙarishe mgnar yana nuna mata ƙofar ɗakinshi.

A hankali ta kutsa kai cikin É—akin tare da yin sallama.
Can ta hangoshi kan gadon yana konce rigingine, idonshi a lumshe,
a hankali takeyin taku tana nufo inda yake.
tare da mgnar zuci.
"Wato harda sharrin Haroon zayiwa É—an Umaymah".
A hankali ta zauna bisa bedside drower'n. Idonta ta sauƙe bisa goshinsa, cikin mamaki ta juyo ta fuskanceshi da kyau ganin yadda Goshinsa ke....!

By
*GARKUWAR FULANI*Wata iriyar zuface ke tsastsafo mishi bisa goshinsa,
Kamar an watsa mishi ruwa.
Ya kamo lip ɗin shi na ƙasa yana taunewa.
Hannunshi dake cikin blanket ta zubawa ido.
Dan son gano abinda yakeyi,
shiru tayi sawon 5 minute kana, a hankali ta É—aura tafin hannunta kan goshinta,
tare goge mishi zufar, daketa tsastsafowa duk da sanyin A/C dake ratsa É—akin.
Idonshi ya saisaita lumshe su da yayi, ya sani Umaymah ce.
sabida babu mai shigar masa É—aki kai tsaye sai ita.
Babu kuma mai taɓa mishi goshi haka sai ita.
Cikin kula tace. "Jazlaan!".
A hankali ya gama buɗe idanunshi da sukayi jazir alamun tarin ƙuna da yakeji a ransa.
A hankali tace.
"Jazlaan!." Ta kuma kiranshi a karo na biyu.
A hankali ya motsa lips É—in shi alamun zai amsa mata.
Amman Ina zafin da zuciyarshi keyi ya danne harshensa hafimtar hakane yasata, nuna damuwarta a hankali tace.
"Kaci abinci?". Ƙarya ba ɗabi'arsa bace ba kuma halittarsa bace, duk ɗacin gsky zai faɗeta, bare a kan kashi.
Kanshi ya girgiza alamun baiciba.
Cikin sanyi tace.
"To Muje kaci koda abu mara nauyi ne!."
Da ƙarfin ya fizgo mgnar.
"Bazan ci ba".
Ta sani yadda yayi mgnar, ta kubce masane, dan in ransa a ɓace yake baya mgna, ɓacin ran mai limini kenan babu faɗe-faɗe bare hargowa ko buge-buge.
Sanin ko ya zatayi bazai cin bane, kamar yadda ya faÉ—a mata yasa,
ta miƙe a hankali kanshi ta shafa tare da cewa.
"Saida safe".
Kai kawai ya iya gyaÉ—a mata,
Haka ta fara tafiya, tana kallon yadda yake motsa hannunshi cikin blanket tabbacin. Wani abun yake yagewa.

Yadda ta bar Haroon haka ta sameshi saida safe tayi mishi kana ta wuce ta tafi.

A can Rugar Bani kuwa. Kamar yadda Ba'ana ya ɗaukarwa kanshi al'ƙawari haka ya bar ƙasar ya nufi ƙasar Cameroon Kai tsaye Yahunde ya nufa, cikin rugagen Fulani, yana tafiyarne da ɗan sauran tsafi da sihirin dake jikinsa.

A haka ya nausa cikin ƙasar Cameroon da yake jihar Ɓadamaya tana bakin bodar ƙasar ne.

Fulanin Rugar Bani kuwa, a daren wannan ranar sukayi gangamin ramuwa, suka faɗawa ƙauyukan kafuran ƙabilun ɓacamawa dake cikin Shikan da kewayenta.
Allah ya basu nasarar yaƙan kafuran nan.
Har suka samu damar ƙona ƙauyem Bonon wanda shine zuciyar ƙabilar ɓachama, kamar yadda Abuja take zuciyar Nigeria.
Cikin daren suka ƙona ƙauye dama dodon tsafinsu Bonon da suka ɗauka a matsayin Ubangiji su sun ƙonashi sun ɓadda shi a doron duniya sai dai tarihinsa.

Wannan labarin shine labarin.
Da gidajen rediyo dana tv da jaridu sukayi.
Breakfast dashi yayinda akayita kuzuzuta cewar Fulani sun zama ƴan ta'adda sun farma garuwa da yaƙi.
Uhummm wannan shine halin da Fulani ke rayuwa a ciki. A zalimcesu, kaji cib duniya babu mai yin mgn su kai ƙorafinsu a koresu. Gwamnatin kasar data jiha suyi kamar basujiba. In fulanin sun rama na lokaci ɗaya sai asa musu sunan ƴan ta'adda ko yan tada zaune tsaye, har ana ikirarin korarmu.😭😭😭

Hankalin ƙabilun Ɓacamawa dake cikin Shikan duk suka ari ta kare.
Hausawa da Fulani kuwa kowa ya koma, cikin gidansa.
Domin Allah ne yabi kadunsu.

Sarkin Shikan da kanshi yayi masifar girgiza da yawan da Fulani sukayi cikin garinshi da kewaye.
Gashi an ƙone dodon tsafinsu nasu kuma babu abinda ya samu fulanin.
Hakane yasa shi kanshi ya arce, sai abu ya lafa ya dawo.

Su kuwa Fulani bayan sun gama.
Suka tsaya suka bawa yaransu da tsoffinsu mafaka, domin su basu kashe yara da tsoffi da mataba.
Anyi an gama, kafin hukuma tazo, ta ƙara sai saita Komai.

A cikin masarautar JoÉ—a kuwa. Washe gari da safe.
Lbrin ya rinski Sarki Nuruddeen, shine ya bada umarnin kada a kama bafulatani ko É—aya.

Aysha ce zaune gaban Umaymah Aunty Juwairiyya na gefenta ita da Hibba, cikin kula Umaymah tace.
"Yauwa Aysha kinga wannan ki É—auke ta matsayin yayarki ita É—in yar babban Yayanmu ne wanda na nuna miki jiya.
Mijinta kuma ya'yan Jabeer ne, Side É—inta na kusa da naku.
In kinga duk wani abun da baki fahimta ba ki tambayeta, in kin gaji da zaman kaÉ—aici zaki iya shiga wurinta, da wurin Mamanku, da kuma nan wurin Gimbiya Aminatu".
A hankali ta É—an kalli Aunty Juwairiyya, tare da cewa.
"Ina kwana Aunty". Cikin jin daÉ—i Aunty Juwairiyya tace.
"Lfy lau ya baƙunta". A hankali tace.
"Alhamdulillah!".Hibba ce ta É—an tsuke baki cikin sanyi tace.
"Shike nan ai, an gabatar mata da kowa sai ni aka ware".
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"To Aysha ga Hibba wutar Umaymah, duk family itace auta a jikokin Sitti na nan ƙasar".
Murmushi ta É—an yi sabida ganin yadda Hibba tayi sai Junainah ta faÉ—o mata a rai.
Ita kuwa Hibba motsata tayi tare da cewa.
"My happiness".
Cikin murmushi Aysha ta nuna kanta, alamun "Nice my happiness?".
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Yes haka Umaymah tace wai kece farin cikin ahlimu da izinin ubangiji".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta.
Haka nan taji tana jin sonsu a ranta, Especially Umaymah da Hibba.
Aunty Juwairiyya kuwa da Ummi breakfast Suka gabatar mata, kana suka fita.
Umaymah da kantane ta haÉ—a mata tea mai kauri ita da Hibba kana ta zuba musu abincin da Aunty Juwairiyya ta kawo musu tare da cewa.
"Bismillah kuci abinci".
tana faɗin haka ta miƙa ta fita,
Ita kuwa Hibba da tsauri ta gyara zamanta tare da ɗaukan Fork ta matso gaban plate ɗin da aka zuba mata soyyyan dankali da kwai, hannun tasa ta soki guda biyu tare da ɗagowa zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya tare da zubawa Aysha ido ganin ta riƙe mata hannunta.
Cikin sanyi da É—an sakin jiki da Hibba ta girgiza mata kai tare da cewa.
"Kada kici wannan abincin".
Cikin juya ido Hibba tace.
"Meyasa!?".
Kai ta jujjuya mata kana ta gyara zamanta, tare da ɗan kallon ƙofar shigowa ta gefen idonta.
Wani kekyawan Foodflaks da aka kawo daga sashin Gimbiya Saudatu ta jawo tare da cewa.
"Ki É—iba a nan kici". Cikin mamaki.
Hibba tace.
"Aunty Aysha, ai Bama cin abincin gidan Gimbiya Saudatu, kuma naga Hadimanta ne suka kawoshi".
Cikin rashin gane manufar zancen Hibba tace.
"Meyasa bakwa ci?".
Juyawa Hibba tayi ta kalli bayanta kana ta juyo ta kalleta da kyau kana a hankali tace.
"Bata son Hamma Jabeer dama duk Æ´an uwanshi, cewa take zata kasheshi in ta samu dama, shiyasa Umaymah take hanamu cin abinci ta".
Wani irin nannauyan ajiyan zuciya ta sauƙe tare da kallon Hibba cikin cushewar tunani ta kalli jerin kulolin da a ƙalla sun kusa takwas a gabansu.
Cikin sanyi tace.
"BuÉ—e su mu gani".
Jin hakane yasa Hibba buÉ—e su É—aya bayan É—aya.
ita kuwa ido take zubawa duk kular da Hibba ta buÉ—e.
Kular ƙarshe wacce ke ɗauke da Chicken Ball's mai zafi sai turiri yakeyi da ƙamshi.
ta nunawa Hibba tare da cewa.
"Kici wannan".
Murmushi Hibba tayi kana tace.
"Yauwa shinema na Gimbiya Aminatu kuma ta iya girki tsohuwar hakana hadimanta, a plate ta zu musu. Kana suka faraci suna É—an korawa da ruwan tea mai zafi da kauri.
Sunaci Hibba nata janta da hira duk da ita Aysha zuciyarta a cushe yake.

Bayan sun gamane, Hadiman Gimbiya Aminatu suka shigo suka tattare komai suka gyara wurin bisa umarni Jakadiya.

Ganin Aysha ta É—an saki jiki da Hibba ne yasa, Umaymah ta wuce Side É—insa ita da Umminshi.

A falo suka samu Jafar, Jalal, Jamil, Haroon. Suna bisa kujerun Dinning area, Aunty Juwairiyya tana zuzzuba musu abincin.
Chapter 69 · 0% Book details