← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 183

Sashe 152

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kar-kar haka jikinshi ke rawa da tsuma tamkar mazari, yana mai jiyo amon sautin muryar Aeech cikin kunnuwansu.

Ita kuwa Aysha a hankali tasa tafin hannunta ta tallabe gefe da gefen fuskarshi ta karkatoshi gareta, cikin sanyi da tattausan lafazi tace.
"Mai hankali keyin mgn ya dami mutane ba, majanuniya irinta ba. Bata da ma dafa, ita fa bushiyace mai baya kamar allurai, Please kada idonka ya sauƙa a kanta".
Ta ƙare mgnar tana jan hannun sa na dama tana ja ta nufi Side ɗinsa.
Cike da mamaki Ummi, Affan, Jalal, Jamil, Hadiman Gimbiya Saudatu suka bisu da ido ganin ya bita a baya, tuni ta sarrafa fushinsa.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu har yanzu lalube takeyi wanda yasa Affan da Jamil murmusawa dan sai tafi kyau da makanta.

Ita kuwa Aysha Kai tsaye har bedroom nashi ta wuce riƙe da hannunshi suna shiga ta faɗa jikinshi.
Wani irin rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi tare da ruggumeta tsam a j...!

Littafin GARKUWA na kuÉ—ine Special Group 1k Normal group 300 zaku turo ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276.
Bana son VTU in kinyima ni ba ruwana. In ya kama dole ma baki da damar tura kuÉ—in ta Account É—ina to katin mtn zaki saya ki copy numbers É—in ki turo min ta whatsapp 09097853276.

Gareku *Murmushi group* ngd da halaccin ku, zumuncin kenan.

By
*GARKUWAR FULANI*
A jikinshi, ya matseta da ƙarfi, sabida tsananin fushin da yake ciki da tafasar da zuciyarsa keyi, ji yakeyi tamkar ya matseta ya medata cikin jikinshi kanta ya danni zuciyarsa ko zaiji sassaucin.
Ƙuna da ƙuncin da kalaman da Gimbiya Saudatu ke jifarshi dashi da mahaifiyasa dasu.
Haƙiƙa ita kaɗaice mutun da ta samu nasarar gano abinda ke ta'azzara fushinsa har ya kasa control ɗin kanshi ta tunzurashi.

Wani irin wahaltaccen numfashi Aysha ta fesar a hankali sabida jin wani fitinenne rugguma da yayi mata tamkar zai gamesu ya cure jikinsu wuri É—aya.
Gaba É—aya jikinshi rawa da kerma yakeyi tamkar mazari.
Cikin fizgo numfashin ta kwantar da kanta bisa ƙirjinshi dai-dai kan ƙahon zuciyarsa,
Kana tasa hannun ta saƙalo wuyanshi, ta ware yatsunta manya tana yin sama da ƙasa dasu a kan tattausan sajensa
Cikin sanyi tare da muryar kwantar da hankali tace.
"Indai har ikon Allah kan iya yaye duhun dare da hasken rana ya meye gurbindun.
To tabbas yaye baƙin ciki i zuwa farin ciki a zuciyar bawansa al'amarine mai sauƙin gaske.
Abin sani kawai shine su mumanai girman jarrabawa ko ƙalubalen rayuwa baya sasu fidda tsammanin samun rahamar ubangijin taliƙai."
Murza kanta ta kumayi bisa ƙirjinsa sabida tanajin wuya da zafin ruggumar da ya mata cike da fushi.
Cikin sassanyan murya tace.
"A shawarce kayi ƙoƙarin jagorantar zuciyarka, kayi baya da lamuran kowa ka ruggumi naka.
Sabida kana zagaye da Magauta makusanta yau da gobe ita ce zata ganar da kai abubuwa da yawa, ka fuskanci magautanka ka dena dukan dungu."
Mutsu-mutsu ta farayi a jikinshi sabida kalamanta na ratsashi kuma suna sashi zafafa ruggumar da yayi mata. Koda yake hakan baya rasa nasaba da hautsunewar kwanyarsa a kan kalamanta.
Cikin É—an buÉ—a murya taci gaba da cewa.
"Kafin ka yarda da mutane to ka rinƙa morar Kekkyawar ƙwaƙwalwarka mai tarin basira da nazartarsu, ka dena yarda da mutun a bisa fuskarshi ta zahiriya.
Kafin ka buÉ—e musu zuciyarka ba basu kekkyawan mazauni na mutane masu amana.
Da yawan mutane dake da kaifin basira da iya tsara zance, har su sanyaya zuciyar mutun su sa mishi yardarsu a ransa.
Da idan zaka shiga zukatansu zaka samu dafin guban dake zuƙatansu yafi na baƙin kumurci.
Yah Sheykh kada ka damu da sauyin É—an Adam tunda dama shi halittace mai rauni kan rikon amana da halaccin.
Har kullum ka jingina da kanka, duk wanda ya nuna zai zamto tsanine a gareka, koma yake ganin shine tsaninka, nuna mishi tun kafin zuwasa gareka.
A tsaye kake da ƙafafunka.
Ta hakane zai san ƙaucewarsa bata nufin faɗuwarka."
ÆŠan tsagaitawa tayi ta É—ago kanta, ta kalleshi sabida jin yadda tattausan gemunshi ke shafa goshinta.
Lip ɗinshi na ƙasa ya taune tare da girgiza gemun.
Ya kuma rumtse idanunshi sai dai yanzu ya É—an fara sassauta ruggumar da yayi mata.
A hankali taci gaba da cewa.
"Gimbiya Saudatu fa, ba belbela bace, Yah Sheykh ka nazarci kalamai na, ita bushiyace ko ince kunkuru.
Zanfi son ka ɗauki zancenta dana mai taɓun hankali a ma'auni ɗaya.
Ni dai ban san menene tsakaninku ba, sabida bani da damar sanin komai naka, da ace na sani da ni zanji da ita, sai dai batun gsky ka dena yankewa littafi hukunci a bisa bongon bayanshi, ka buÉ—e littafi ka nazarceshi shafi zuwa shafi kafin ka yanke wa littafin hukunci".
A hankali ya buÉ—e idanunshi.
Ya zuba matasu, tabbas yaji wani abu ya É—arsun masa a zuciya, da zai samu yanzu duk suturan jikinta zai kekketashi ko zaiji sassaucin abinda yakeji.
A hankali ya saketa.
Kana ya zauna a bakin gado,
Kanshi ya dafe da hannunsa duka biyu.
Still har yanzu jikinshi kerma yakeyi.

Ita kuwa Aysha juyawa tayi da sauri ta nufi falon, da nufin ta É—auko mishi ruwan sanyi yasha ko zaiji sassaucin abinda yakeji a ransa.

Ba ruwa Fridge É—in nasa.
Hakane yasa kai tsaye ta wuce babban falon.

A can falon kuwa Affan da Jamil, sai dariya sukeyi ganin yadda har yanzu Gimbiya Saudatu taketa lalube a inda ta faÉ—i kasa dirsham.
Tuni fuskarta ta haye ta kumbura tayi sintim.
Hakama bakinta.
A hankali ta fara bude idanunta, sai ta kuma rufesu.
Ummi ce tayi murmushi mai cike da jin daÉ—in marukan da Sheykh ya yayyarfa mata.
Cikin dakiya ta kalli hadiman Gimbiya Saudatu dake gefe suna murmushi suma tace.
"Ku matso kuyi mata jagora".
Da sauri Gimbiya Saudatu ta gyara zamanta tare da buÉ—e jajayen idanun nata, cikin masifewar murya tace.
"Ke tafi daga nan Jakadiya mara galihu".

Da sauri suka juyo suka kalli inda Aysha ke tsaye wacce ta nuna Gimbiya Saudatu hanyar fita tare da cewa.
"Ki ɓace min daga nan, sabida mijina bazai juri jin ihun haukanki ba".
Wani mugun kallo ta watsawa Aysha da jajayen idanunta kana tace.
"To fitsarerriyar ƙauye, mai gaggawar tsiri da cewa miji Baba, waya kasa dake bare ki zari babban kashi".
Jalal ne ya ƙaraso cikin falon, sabida yana son yaga matakin da Aysha zata ɗauka tunda ta iya fesa Hajia Mamansu ma rashin kunya.
Ummi, Jamil, Affan, suma gyara zama sukayi.
Ya Jafar da yanzu ya shigo ma gefen Jalal ya zaune.

Ita kuwa Aysha cikin isa da ƙasaita ta iso gaban Gimbiya Saudatu kujerar dake gabantan ta zauna a kai wacce kujerar zaman Sheykh ne. Kai ta jinjina tare da cewa.
"Ƙauye tushen kowa! Duk wanda bashi da ƙauye to bashi da asali kenan, shin baki san cewa da ƙauye akanyi birni ba.
Shin ke kinma san me ƙalmar ƙauye take nufi kuwa?".
Ƙafarta ɗaya ta ɗaura kan ɗaya, kana taci gaba da cewa.
"Da fari Makka itace babban birni sabida Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cikinta.
Da yayi hijira ya koma madina kuwa sa madina ta zama babban birni mai cike da salama sabida addinin da kanshi ya koma can.
In kin gane me ƙalmar ƙauye take nufi garin da babu addini ba ilimi garinda kafurai suke, shine ƙauye, domin duk inda hasken addini yake da ilimin da masana ilimin to sun zarta ace musu ƙauyawa, domin kalmar ƙauyawa tana nufin jahilai, niko nan da kike ganina gidanmu tushene na tsanƙaya yara da dattawa.
Dan haka janye kalmarki ta fitsarerriyar ƙauye, gorinki bai samu muhalliba."
Tsaki taja tare da cewa.
"Baki san cewa kunne ya girmi kaka ba ko? To inma baki saniba Ni nan Aysha ina sane da labarin ƙuruciyarki da rashin kunyar da fitsarar da kikayi da taraddadin da kika sawa iyayenki na alamun lalacewa, dan haka kece fitsarerriyar. Kana kuma in kin mance in tuna miki ƙauyenmu ya zarta asalin naku ƙauyen girma da daraja ko dai kin mance inane asalin ƙauyenku.
In kin mance in tuna miki, ita kanta masarautar Joɗa kafin a auroki cikinta zata amsa kiran suna ƙauyen da hausawan ke nufi.
Yau da gobe shike sauya komi da kowa.
Ni nan da kike gani da mgnarki data É—aurerre a turu basu da maraba."
Cikin masifa Gimbiya Saudatu tace.
"Sai dai in kece mahaukaciyar".
Dariya tayi tare da cewa.
"A a akan bola nake".
Miƙewa tsaye Gimbiya Saudatu tayi tare da fara gyara al'kyabbar jikinta, tare da cewa.
"Zanyi mgninku zaku gane kurenku".
Taɓe baki Aysha tayi.
Ita kuwa juyawa tayi ta, fice hadimanta na biye da ita a baya.
Dariya sosai Ya Jafar yayi wacce saida ta basu mamaki.

Sheykh kuwa da tun É—azu ya fito bayan yayi al'wala ganin azahar tayi,
Tsayuwa yayi yana jin yadda Aysha keyi da Gimbiya Saudatu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu ganinshi ne yasa ta miƙe maza ta fice.
Miƙewa Aysha tayi da sauri jin muryar sa yana cewa.
"Ku tashi kuje kuyi al'wala lokacin salla yayi".
Juyowa tayi ta zuba mishi ido.
Tabbas daga jin muryarsa da yanayin fuskarsa zai iya nunawa mutun cewa har yanzu a zuciye yake.

Kallonta yayi a fizge kana yaja idonshi yayi gaba su Affan na biye dashi a baya.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Dai-dai kenan yau dai Sheykh ya sawa Gimbiya Saudatu tsoron zuwa nan ta baje kolin rashin kunyar ta."
Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
"Uhummm Ummi an dukan tenki akefa aka bar jaki a É—aure"

Cikin sauri Ummi tace.
"Kamar yaya?".
Kai ta jinjina kana tace.
"Muje muyi salla, Ummi".
To tace tana mai son nazartan kalaman Aysha.

Bayan sunyi salla ne suka fito falon.

Suna zama Sheykh Jabeer ya shigo.
Affan, Jalal, Jamil, Ya Jafar. Na biye dashi a baya.
Su duk Dinning table suka nufa.
Ummi na biye dasu a baya.

Abinci ta fara zuzzuba musu.
Shi kuwa Sheykh tuni ya wuce Side É—insa.
Chapter 152 · 0% Book details