← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 183

Sashe 113

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana katse kiranshi da Sheykh yaji wani kiran ya shiga wayarshi.
Amsa kiran yayi tare da kara wayar a kunne.
Sauya murya ba'ana yayi tare da cewa.
"Ina mgn da Malam Liman ko baban Aysha mai ciwon hannu".
Da mamaki Bappa yace.
"Waye ne?".
Ciki kaurara muryarshi yace.
"Sarkin bakan nufe ne, bincike nane ya nuna min ciwon hannun yarka tana can masarautar JoÉ—a.
An kawo wani sarkin baka yana mata mgni sai dai mugune magautansu yakewa aiki.
In har zaku biyani ni Shanu hamsin zan je kuma zan mata aiki a take zataji sauƙin".
Cikin sanyi Bappa yace.
"To yanzu kai ina kake".
A nitse yace.
"Ni yanzu haka ina bakin iyakar ƙasar Nufe da Nigeria ne.
Yau zuwa gobe zan shiga ƙasar".
A hankali cikin sanyi Bappa yace.
"To ba matsala, nima jibi zan shigo.
Mu haÉ—u a can in dai kayi mata mgnin ta warke a take zan biyaka da abunda kace".
Cikin jin daÉ—i yace.
"To sai mun haÉ—u."

Katse wayar yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah Shatuna zata samu lfy. Zan kuma samu shanu hamsin. Sannan zanji lbrinta, zaka kuma isarmin da manufata.
Kunga na jefi tsuntsu biyar da dutse É—aya."

Jinjina mishi sukayi kana ya shiryawa Burun komai nagnin ya nuna mishi yadda zaiyi da yadda zai isar mishi da saƙonshi wurin Aysha.

Bappa kuwa Murmushi yayi dan ya gane Muryar Ba'ana.
Dama ya sani bazai rabu dasu haka a sauƙaƙeba yasani yanzu duk motsin Aysha yana tafin hannunshi.
Abinda yasa ya yarda su haÉ—u kuma yasan ba shi da kanshi zai jeba.
Sai dai ya wakilta wani.
Ya kuma sani tabbas yanada makarin ciwon taɓen sihiri wato ƙetare.
Yakuma san bazai cutar da Aysha ba yasan tabbas taimaka mata zaiyi dan baya son abinda zai cutar da ita.

A haka shima ya kira ArÉ—o Bani suka tattauna kana ya fara shirin tahowa.
Ko Ummey bai gaya mata abinda ke faruwa ba.

A can jihar Tsinako kuwa sha ɗaya dai-dai jirginsu Umaymah ya tashi ya nufi jihar Ɓadamaya.

A cikin Rugar Bani kuwa. Tun shekaran jiya su Junaidu suka dawo gida.
Alhamdulillah duk sun worke kuma har gida aka dawo dasu.

Sosai ArÉ—o Bani da sauran dattawan sukayi mamakin jin Sheykh ne ya kaisu sibitinshi ya kuma kula dasu har suka samu lfy.
Kana yayi musu komai ya dawo dasu lfy.
Alhamdulillah kuma yanzu Rugar Bani basu da matsalar komai.
dan ya rigada Allah yasa tsoron fulanin a zuƙatan Ɓacamawan.
Yanzu kowa harkar shi yake ba kare bin damo.

Suyi kiwonsu lfyta shanayensu nata habaƙa.
Yanzu kuma sun maida hankali kan shuke-shuke amfanin gonakin su.
Sabida shigowar damuna.

A cikin masarautar JoÉ—a kuwa.
Sheykh yana gama mgna da Bappa ya shiga bathroom.

Cike da mamaki ya É—an sunkuyo ya kalli boxes dake jikinsa,
wanda dashi zaiyi wonka.
hannunshi yasa ya damƙi bnnarshi da tun jiya da safe data harba ta miƙe ta tsaya ta rinƙa kumbura da cika da miƙewa tayi tsawo.
Har yau har yanzu harbawa takeyi babu ƙaƙƙautawa yadda zuciyarshi ke harbawa haka itama.
Kuma tana tsaye gam tamkar zata faso boxes É—in ta fito woje.
Shiyasa yake jin tsikar jikinshi yana zubawa.
A hankali ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, wanka yayi kana, ya fito ya kimtsa ya shirya jikinsa cikin manyan kayan.

A falon kuwa LamiÉ—o da Galadima da Sarkin bakan.
Ne suka shigo bayan. Sallama yayi musu jagora.

A bisa kujera Lamiɗo da suka zauna sarkin baka kuma a ƙasa.
Hakama Ummi da Hibba.
Jalal da Jamil kuwa tun É—azu suka fita, suka tafi Side É—in Mama.
A can suka samu Ya Affan.

Cikin girmamawa Ummi ta É—an rusunar da kanta tare da cewa.
"Barka da isowa LamiÉ—o shugaba mai adalci".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Barka dai Jakadiya mai gsky,
ya jikin É—iyar taki, ina take".
Cikin ƙara rusunar da kai tace.
"To jiki dai da asuba da sauƙi amman kwana mukayi babu bacci.
To rana na fitowa kuma ciwo ya harzuƙa ya zarta na baya".
A hankali LamiÉ—o da Galadima sukace
"Subahanallahi".
Sarkin baka kuwa.
sunkuyar da kanshi yayi tare da sakin murmushin mugunta,
kana ya gyara riƙon da yayiwa wayarshi yadda, waɗanda suka sashi aikin zasuji bayanin komai da kunnensu.
da kiransu da ya haÉ—a.
A can kuwa magautan dariyar jin daÉ—in lbrin.
Sukayi.

A hankali ya kalli Ummi yace.
"Sauƙi a hankali yake samuwa, zai nayi yana lafawa har yazo ya bari gaba ɗaya".
Kai ta gyaÉ—a alamun gamsuwa.

A hankali ta miƙe bayan Lamiɗo yace mata.
"Jeki kira min ita tazo".
To tace kana ta nufi shashin Sheykh.

Shi kuwa Sheykh yana cikin fesa turare kenan.
Ya juyo ya kalli Aysha da ta tashi zaune da sauri tasa hannu a kanta tana yarfa É—aya tare da cewa.
"Wash! Wash! Wayyoooooooo Allah na!'.
A hankali ya ajiye kwalban turaren kana yazo gaban gadon.
Tare da cewa.
"Sauƙo". Cikin rawan jiki ta sauƙo tana yarfa hannunta.
Cikin haÉ—e fuska yace.
"In zakiyi kuka fice min a É—aki".
Cikin rauni tace.
"Yah Sheykh zafi! zafi!! zafin nakeji yana dawowa".
Da sauri ya juyo ya kalli ƙofar ɗakin jin ana bugawa.
Jiyo muryar Ummi ne yasa ya juya ya nufi ƙofar.
Yana buÉ—ewa tace.
"Sheykh, LamiÉ—o ne yazo yana son ganin hannun nata".
Kanshi ya É—an gyaÉ—a kana yace.
"Fito kije, Ummi a kawo mata É—an kwali ta É—aure wannan dogon gashin da kitseshi ma aikine shiyasa ko yaushe kai a tsefe ai kuwa al'janu kam sayi ta shiga lodi-lodi".
Da sauri Ummi ta miƙo mishi ɗan kwalin doguwar rigarta dake hannunta tun sanda ta wurgar dashi.
Kanshi ya juya tare da cewa.
"Fito".
Cikin zubda hawaye ta fito.
Gaban Ummi ta tsaya tana cewa.
"Wayyo Ummey na".
Cikin tausaya mata Ummi tace.
"Sannu ko". Ta ƙarishe mgnar tana yafa mata ɗan gyalen.
Kana ta kama hannunta na hagu suka nufi falon.

Shi kuwa Sheykh hiraminshi yasa ya dai-dai-ta komai.
Sai dai abin da ya sashi jin kunyan kanshi da kanshi ganin.
Har yanzu bnnarshi a tsaye ƙiƙam duk da danneta da yayi da boxes.
shi da kanshi in ya sunkuyo yana ganin tudunta kaÉ—an danma manyan kayane a jikinsa.
matseta yayi kana ya buÉ—e al'kyabbar da kyau, sannan ya fito ya nufi falon yanajin yadda take harbawa duk da kai tsaye bawai sha'awa yakeji ko makamancin hakaba.

Wayarshi ce kaÉ—ai a hannunshi ya fito.

A falon ya samesu tana zaune gaban LamiÉ—o da Galadima.
Gefensu ya zauna.
Sarkin bakan dake gabanta yana kwaɓa mgnine ya kalla tare da cewa.
"A bar wannan mgin haka, kada a sake shafawa".

Cike da mamaki Sarkin bakan ya É—ago ya kalleshi tare da cewa.
"Sabida me?".
Idonshi na kan wayarshi yace.
"Nace kada a shafa ko". LamiÉ—o ne ya juyo ya kalleshi tare da cewa.
"Za'a shafa".
Shi kuwa Sarkin baka ido ya zura musu.
Shi kuwa Sheykh miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
"Shike nan!".
Ya ƙarishe mgnar da kallon hannun Aysha mai ciwon.
Kana ya juya ya kalli Ummi tare da cewa.
"Bari in É—auko Umaymah ta iso".
Da sauri Hibba ta miƙa tare da bin bayanshi tana cewa.
"Hamma Jabeer inzo muje".
Kai ya gyaÉ—a mata, kana suka fita.
Ummi na ce musu.
"Allah ya kiyaye hanya".
Amin Amin sukace sannan suka fice.

Ita kuwa Aysha zuwa yanzu ta fara gigicewa.
Sai mutsu-mutsu takeyi, tare da shishita.
Galadima ne ya kalli Sarkin baka yace.
"Kayi aikinka!".
To yace kana ya fuskanceta da kyau yace.
"Kawo hannunki".
Jiki na rawa ta miƙa mishi hannun tana mai lumshe idonta hawaye na zubowa.
"Sannu ko Mamana". LamiÉ—o ya faÉ—a cikin tausayawa sabida sunan mahaifiyarshi Aysha.

Ummi ma sannu ta mata.

Shi kuwa Sarkin bakan da yawa ya daƙumo maganin ya labta a kan hannun.
Sannan ya fara shafawa.

Wani irin zillo tayi tare da sunkuyar da kanta ta kifeshi kan hannun kujerar da LamiÉ—o ke kai.

Gaba É—aya jikinta karkarwa yakeyi tamkar mazari.
A haka ya gama shafe magungunan sannan ya bata wani yace sai dare ta shanye shi.

Ummi ce ta amsa tare da yi mishi godiya.
Kana LamiÉ—o da Galadima sukayi mata sannu da jiki suka tafi.

Suna fita, ta miƙe da sauri ta nufi falon ta.
Da sauri Ummi ma tabi bayanta tana cewa.
"Lafiya kuwa."
Babu mgna tana shiga kan gado ta faɗa ta kife kanta a filo murya na rawa alamun sanyin zazzaɓi tace.
"Ummi rufeni rufeni sanyi zai kasheni a kashe min AC."
Da sauri ta ajiye maganin kana ta rufeta da jibgegen blanket É—in sannan ta juya ta kashe AC'n.

Ta dawo gefenta ta tsaya.
Cikin al'hini take cewa.
"Sannu! Sannu ko Aysha".
Ina babu mgna sai karkarwa takeyi tamkar zata faɗo ƙasa.

Haka yasa hankalin Ummi tashi.

Shigowar Aunty Juwairiyya ce da ta kawo musu abincin rana.
Dana tarban Umaymah ne.

Cikin mamaki tace.
"Ummi ko dai in kira. Sheykh yazo muje asibitine gafa yadda take rawan sanyi".

Ummi kam tama rasa bakin mgn, shiru kawai tayi tana riƙe da haɓa.

Suna cikin hakane Hajia Mama ta iso.
Cikin tashin hankali tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ummin Jabeer ya za'ayi da wannan yariyar ne? Mu tafi asibiti fa, da sauri ta juya ta fita zata kirawo Affan.

Tana fita da miti bakwai. Su Umaymah suka shigo.
Kai tsaye suka wuce har cikin É—akin jiyo mgnar su Ummi a can.

Shi kuwa Sheykh, asibitin Valli ya wuce.

Umaymah na shiga ta isa bakin gadon.
Zama tayi a gefe tare dasa hannu ta buÉ—e borgon.
Ganin yadda taketa karkarwa ne, yasa Umaymah É—agota ta É—aura kanta bisa cinyarta.
Tana cewa.
"Innalillahi wannan wane irin sabon al'amari ne mai firgitarwa".
Da sauri tace.
"Hibba kiyi gudu ki kirawo min Jazlaan kada ya fita."
Da sauri Hibba ta juya ta nufi waje.

Ita kuwa Ummi da Aunty Juwairiyya ko sannu da zuwa Allah bai basu ikon yiwa Umaymah ba sabida ruÉ—ani.

Wani irin numfarfashi ta fara fiddawa a jere-a jere sai ga jikinta ya fara lafawa da rawan da yakeyi.
Wani irin zufa ya fara tsastsafo mata duk ta inda hudar gashi yake a jikinta.

Cikin sanyi suka fara sauƙe ajiyan zuciya.
Suna cewa.
"Alhamdulillah".

Gyara mata konciya Umaymah tayi ganin tayi bacci.
BuÉ—e mata borgon tayi kana ta kalli Juwairiyya tare da cewa.
"Kunna AC".
To tace kana ta kunna.
Chapter 113 · 0% Book details