← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 183

Sashe 146

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani ƙaton kaskone a gabansu.
Cikin muryar da babu daÉ—in amo boka Dumba ya cewa Ba'ana.
"Leƙa ka gani, gacan ajiyarka tana kwance tana bacci lfy lau babu wani mahluƙin namiji da zai iya taɓa koda farcenta ne bai mutuba, bare har ya shafeta ko ya kai ga taɓa wani sashin sirri na jikinta bare a kai ga ya kusanceta".
Tuni Ba'ana ya leƙa kanshi yana ƙarewa fuskar Aysha kallo, cikin jan dogon numfashi yace.
"Boka Dumba to shi wannan haskenfa da yake kwance kusa da ita menene shi kuma wane haskene ya zagaye É—akin da fuskarta?".
Cikin yin cacuɓe-cacuɓenshi yace.
"Wannan haskene dake wanzu da izinin ubangiji haskene dake kare wanda ke kusa da ita sam bamu da tsumi ko dabarar ganin komai a kanshi, sabida shi mutum ne da bakinshi baya bushewa da ambaton Allah kana baya rabuwa da al'wala a jikinshi.
Ita kanta in dai tana kusa dashi ainun jikinta ya taɓa nashi to bazamu ga komai a kanta ba, batun kusanta ne dai tabbas babu mahaluƙin da zai kusanceta ya rayu, domin madadin ɗanɗanon ni'imomin da ko wacce mace take dashi, in namiji ya sadu da ita, to ita dafin kuna da macijiya ne ni'imarta zata shigeshi a sashi mai tsada a jikinshi kan gari ya waye zai mace ya bar duniya".
Wata iriyar muguwar dariya suka kece da ita kamar zasu fasa kogon da suke ciki, boka Dumba ne yaci gaba da cewa.
"Kai dai ka gama aiyu kan ka hankalinka kwance, shi wannan da yayi sanadin faɗinka gasar Shaɗi har yasa kabar ƙasarku, tuni munsa ajalinshi a jikin matar da yakega matarsa ce, kaga koda baka tare da Shatu zata tayaka yaƙi ba tare da ta sani bama".
Cikin jin daɗi da baƙar mugunta Ba'ana yace.
"Dole ma ya mutu, sai dai babarsa ta haifi wani hegen bafullatani mai jajayen kunnuwa".

Daga nan sukaci gaba da hirarsu da tanadin hana fulanin ƙasar Nigeria da Cameroon zaman lfy.

A nan Ɓadamaya kuwa, cikin Masarautar Joɗa, a wannan lokaci na tsakiyar dare.
Suka fito cikin masarautar suka nufi gidan boka Tsitaka, garin yayi duhu yayi dim sai azabar zafi da ake tsulawa zafi irin na tsakiyar damuna irin wanda in an kwana biyu ba'ayi ruwan samaba, bisa alamu hadari ke diddigowa daga ƙasa shiyasa garin yayi dim babu alamun iska.

Suna shiga Boka Tsitaka ya kwashe da dariya tare da cewa.
"Lbri mara daÉ—in gashi can konce da matarsa bisa gado É—aya, sai dai kun san É—an naku ba'a iya ganin sirrinshi, ko matar tashi bana gani sai wani haske daya rufesu.
Kuma yana gab da ɗirkawa ƴar fulani ciki hegen yaro dan yanada ƙoyayen haihuwa da ƙenƙesa".
Cikin tashin hankali É—ayan yace.
"Kusantar mata harda haihuwa, anya kuwa bazan sa a dandatse min wannan yaron ba, shin wai shi wanne irin mutum ne da baya jin sihiri da tuggu da makirci".
ÆŠayan ne yace.
"Ai kuwa koda ya haihu yarane dai bazasu rayuba".
Dariyar mugunta Boka Tsitaka yayi tare da cewa.
"Ku dai kun iya kawo aiki kun kuma iya faÉ—in mugunta sai dai tabbas akwai wani wanda yake gefenku, da yake aikata musu fiye da shirinku, kullum in kun tuna yimasa wani abun kafinma kuyi abun zakuga fiye da hakan ya faru tun shekarun baya.
To bare kuma yanzu an sake samun wani taƙadirin ma yasa mishi ido".
Dariyar jin daÉ—i sukayi kana sukaci gaba da muhawarar mugunta.

Washe gari azahar Gimbiya Aminatu ce zaune gefen LamiÉ—o da ya kira Sheykh suna gaisawa, tare da cewa.
"Muhammadu Akwai babban uzurin dake buƙatar ka dawo gobe".
Gyara zamanshi yayi tare da kallon Aysha dake gefenshi ita da Hibba da Jalal da sune suka kawo musu abinci a hotel É—in da suke. Maida kanshi yayi ya jingina da kujera kana ya lumshe idonshi tare da cewa.
"Eh dama gobe zamu taho, amman sai dare jirginmu zai tashi.
Su Ya Hisham da Affan kuwa sunce sammako zasuyi wai tafiyar mota zasuyi".
Cikin sauƙe numfashin Lamiɗo yace.
"To Allah ya kaimu ya kuma dawo daku lfy, itafa Juwairiyya sai yaushe zata dawo".
Kanshi ya É—an mirgina kana yace.
"Zan dai taho da Ya Jafar da Jalal, in bata gama uzurorinta ba, sai ta koma masarautar Jadda ta dawo daga baya."
Cikin gamsuwa da hakan LamiÉ—o yace.
"To hakan yayi Allah ya kawoku lfy".
Amin Amin yace kana ya katse kiran.

Jalal ne da Hibba suka miƙa tare da cewa.
"Mu zamu tafi."
Bai kulasu ba, Jalal ne ya É—an matsoshi tare da cewa.
"Umaymah tace ka kai mata ÆŠiyarta taga ya ta kwana da jikin".
Kai ya gyaÉ—a alamar to.
kana Hibba ta kalleta tare da cewa.
"Aunty Aysha sai kin dawo, Allah ya ƙara sauƙin".
Amin tace tana gyara zamanta tare da jawo Æ´ar jakar kayan da Hibba ta kawo mata. Wai na anko É—in fansan idon da za'ayi.

Su kuma nan suka fita.

Suna fita, ya miƙe ya rufe ƙofar, kana ya dawo ya hau kan gado ya kwanta.
Da ido ta bishi tare da cewa.
"Yah Sheykh gado kuma to yaushe zamu tafi ko inbi su Hibba kawai ne?".
Lumshe idonshi yayi alamun bacci zaiyi, a hankali tace.
"Dole ne kullum sai kayi baccin tsakanin azahar da la'asar É—in nan". Kanshi ya gyaÉ—a mata alamar eh.
kana ya juya mata baya.

Dole itama É—in ta hau ta kwanta, tana konciya ya jawota jikinshi nan take sukayi bacci.

Ƙarfe uku da minti arba'in da biyar ya farka, da sauri ya zareta daga jikinshi kana ya shiga bathroom, wonka yayi fes kana yayi al'wala ya fito.
zaune ya sameta bakin gado.
"Tashi kiyi wonka mu tafi tunda ke bakya cikin masuyin salla".
Cikin sanyi tace.
"Ah ina cikin masuyin salla mana".
Kai ya gyaÉ—a yana zura tattausan al'kyabbar shi. Yace.
"Eh amman ni dai tun jiya banga kinyi salla ba".
Cikin rashin fahimtar wayon da yake mata tace.
"In Sha Allah gobe dai da safe ai zan fara".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To tashi kiyi wonka kafin inyi sallan".
To tace kana ta miƙe ta shiga Bathroom da ƴar jakar kayanta.
Shi kuwa ya kabbarta sallan la'asar.

A cikin bathroom É—in ta canza kayanta bayan ta kimtsa jikinta.
Kana ta ninke wanda ta cire ta saka a ciki ta feshe jikinta da turarenta mai sanyin ƙamshi, sannan ta fito.

Zaune ta sameshi bisa sallayar yasa System É—inshi a gaba ya maida hankalinshi kab kanta. Bisa alamun wani abu mai tarin mahimmanci yakeyi.
Dan gaba É—aya yatsun hannunshi aiki sukeyi sai kwayar idanunshi da yake jujjuyawa kan screen É—in na'ura. Yanayi kuma yana motsa lips É—inshi alamun still kuma tasbihi yakeyi bincikar number da ake tura masa text a rufe yakeyi yadda zai samu ya buÉ—e layin yabi diddiginshi.
A hankali ta kalleshi da kyau, kana ta kalli kayanshi da ya cire É—auka tayi ta ninninkesu ninkewa mai kyau, tasa a Æ´ar jakar ta zuge zip ta rufe.
Sannan ta koma gefenshi can ta zauna bayanshi.
Cikin sanyi tace.
"Ni dai banga wayata ba".
Bai kulata ba, domin aikin da yakeyi ya tunzura mishi nitsuwa.
Cikin sanyi tace.
"Ayyah to dan Allah. Sammin wayarka in yi kira".
Tura mata wayarshi dake gefenshi yayi sabida ya samu ta rabu dashi dan tana raba mishi hankali".
ÆŠaukar wayar tayi sai kuma taga akwai security code a jiki.
Matsoshi tayi da mamaki dan tasan akwai woyoyin shi biyu data taɓa riƙewa basa da security, jujjuya yar wayar tayi ganin yar micilace kuma harda liƙa mata matakan tsaro, taɓe baki tayi tare da cewa.
"Me code É—in buÉ—e shi".
"Mamey". Yace mata ba tare da ya kalleta ba.
jujjuya yar mitsitsiyar wayar tayi a tafin hannunta, contacts ta danna da nufin ta ɗan duba ko da number sai ta samu nanma a garƙame yake.
Ikon Allah tace a hankali kana ta danna. Phone na ma kirib yake, cike da mamaki tace.
"Wayarfa tako ina ansa mata kan tsaro".
Da sauri ya juyo ya kalli wayar da ke hannunta. Hannunshi yasa ya amshi wayar da sauri tare da zurata a al'jihunsa kana ya yasa kan yatsunshi ya ɗan bugi goshinsa tare da kwaɓe fuska kana ya kalleta cike da alamun damuwa yace.
"Kai Alhamdulillah, Allah na gode maka daka jarabceni da wannan fitinenneyar yarinya Aish mata, kinzo kin tasani gaba da surutu, kuma kina gani aiki nakeyi, ko so kike na ki rikitamin tunani ne".
Kanta ta langoɓar tare da kwaɓe fuska tace.
"A a, Ni kawai wayata zan kira".
Cikin zubawa lips É—inta ido yace.
"Ba kin barta a motaba".
Da sauri tace.
"Laah hakafa ni na manta ma".
Kanshi ya gyaÉ—a kana ya gyara zamanshi ya fuskanci System É—in nasa.
Gefenshi ta É—an kalla tare da cewa.
"Yah Sheykh!".
Shiru bai amsa ba yaci gaba da aikinshi.
a hankali ta kuma cewa.
"Yah Sheykh!!".
Bai amsaba bai kalleta ba.
A karo na huÉ—u ta kuma kiranshi.
"Yah Sheykhhhh". Ta ƙarashe kiran murya can ƙasa da alamun bacci ya fara kamata, a hankali ya ɗan juyo kwayar idanunshi ya kalli inda take.
Cikin lumshe ido tace.
"Mu tafi mana, za'ayi fansan ido da bamu jeba".
Kanshi ya gyaÉ—a alamun to, daga nan ya meda kai yaci gaba da aiki.

A can gida kuwa, tuni anyi fansan idon amarya da ango gaba É—aya an gama komi da komai.

Har an fara shirya farfajiyar Side É—in Umaymah wanda anan za'ayi shagalin mother's day É—in.
An gyara wurin an kimtsa an shirya komai yadda ya kamata.

Ƙarfe biyar dai-dai duk an gama shirya amarya cikin shiga ta al'farma, hakama ango Haroon ɗan ayi.
Aunty Rahma kuwa tasa mabusan masarauta da makaÉ—a yan kakaki da tambura da al'gaita duk sun shiryawa shagalin tunda abu na jinin sarauta ai dole a gwada iyawar.
Chapter 146 · 0% Book details