← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 183

Sashe 129

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Konciya tayi tana nazartan takun Yan Sheykh sai dai duk nisan da zurfin tunaninta kafin taje wuri a tunani ko bincike tuni ya wuce ta.
Abu É—aya ta fahimta, yana bin diddigi akan abubuwa da dama shi mutumum ne bauÉ—aÉ—de mai algibata tako ina ka buga zaka sameshi.

A ranar bata ganshi ba.
Hakama washe gari.

Sai da asuba Ummi ta tasheta akan ta kai mishi.
Abun yin sahur sabida gobe za'a tashi da azumin arfa.

A tsaye ta sameshi a falo da waya a hannunshi.

Bisa alamu da Aunty Hafsat yake mgn.
Gabanshi ta ratsa ta ajiye mishi tray'n a kan stoll dake gabashin.

Ba tare da ya kalletaba ya kamo hannunta ya riƙe lokacin da zata juya ta fita.

Sai kuma yaci gaba da wayar.
"Aunty Hafsat wai har bikin ya isone?".
A can É—aya gefen murmushi tayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa Sheykh saura wata ɗaya da kwanaki ne zulhajji na ƙarewa da kwana biyar na sabuwar wata za'a fara bikin".

A hankali yace.
"To kuma shine zakuzo tun bayan salla da mako É—aya, yanzu ita Ramatu da wa zata bar mijinta ta taho wata kusan biyu".
Hannunta dake cikin nashin hannun ya ɗan ƙara matsewa.
Tare da janta jikinshi.
sai kuma ya É—an gyara tsayuwarshi tare da cewa.
"A a Aunty Hafsat ku bari in bikin saura mako É—aya ko biyu sai kuzo".

Da sauri tace.
"Sai dai biyun".

Uhum yace. Ita kuwa cewa tayi ina.
"Ya ÆŠiyata Aysha kuma yar uwata aborso a rayuwarmu".
Murmushi yayi a hankali tare da lumshe idonsa yanaji wasu zafafan hawaye na tashin hankali na tsastsafo mishi yace.
"Gata".
Yana faɗin haka ya liƙa mata wayar a kunnenta.

Da sauri ta É—ago ta kalleshi.
Tsareta da ido yayi. Jin muryar Aunty Hafsat ne yasata É—an murmushi tare da cewa.
"Aunty Barka da asuba".
Cikin tarin so tace.
"Barka dai Aysha yasu. Jalal da Jamil ya kewan Hibba".

Cikin murmushi tace. "Suna lfy Aunty ina kewar Hibba kam sosai ma".

"Kada ki damu mun kusan haÉ—uwa ai muma zamu zo ai. Ya Jazlaan yana lfy ko".
Cikin jin daÉ—i tace.
"Allah ya kawoku lfy Aunty".

Amin Amin tace.
Kana tace.
"Ya Jazlaan yana lfy ba wata damuwar ko".
ÆŠago kanta tayi ta kalleshi,
Kwaɓe mata fuska yayi tare da mata alamun bata amsa.
Cikin sanyi tace.
"Uhum Alhamdulillah".

"Masha Allah. To sai anjima ko kada in hanaku yin sahur".

ÆŠaga nan sukayi sallama.

Shi kuwa a hankali ya zauna tare da zaunar da ita gefe.
Kana yace.
"Kinyi niyar yin azumin arfanne?".
Kai ta gyaÉ—a mishi alamar eh.
Kauda kanshi yayi tare da cewa.
"To kin nemi izinine?".

Tura baki tai tare da cewa.
"Izinin wa?".
Kanshi ya gyaÉ—a tare da cewa.
"Ok haka kikace ko baki san izinin wanda zaki nema bama kenan ko?."
A hankali ta É—an kalleshi sai kuma tace.
"Kayi haƙuri. Ina son yin azumin, ka amince inyi?.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Uhuumm ai da kinyi ba neman izinin sai da yamma in karyashi".
A hankali tace.
"Ka karya min shi kuma É—ura zakayi min ne?".
Kanshi ya kauda tare da cewa.
"Aikin wani ladan zanyi dai in Kauda naki da nawan, Ni na samu lada biyu na niyan azumin da ladan raya Sunnah".
Shiru tayi tana jin yadda yake murza yatsarshi ma nuniya cikin tafin hannunta.
Ganin lokacin sahur na tafiya ne yace.
"To tashi kije kiyi sahur".
Miƙewa tayi ta fita.

Shi kuwa sahur É—in ya fara.

To Alhamdulillah Azumin Arfa dai yayi zafi sosai kowa ka gani kamar yayi azumi goma.

Kuma yaune LamiÉ—o ya ware raguna aka bada duk cikin masarautar JoÉ—a ahilinshi da bayinshi da hadimai kowa da ragonsa.

Sheykh Jabeer kuwa shima yasa su Jalal sunje sun raba a cikin gari sadaka.

Da yamma suna zaune Aunty Juwairiyya ta shigo gefen Ummi ta zauna.
Ita kuwa Aysha tana kwance bisa kujera kamar sumemmiya. Azaban ƙishirwa da yunwa ne suka dabaibaye kuzarinta.

Cikin sanyi Aunty Juwairiyya tace.
"Aunty Aysha sannu fa, Azumin da daÉ—i kam yau".
A gyatsine ta kalli Aunty Juwairiyya, sabida zuwa yanzu zarginta da takeyi yamafi na baya.

Ummi ce ta É—an kauda zancen da cewa.
"Ya shirye-shiryen aiyu kam salla".

Murmushi ta É—anyi tare da cewa.
"Alhamdulillah Ummi wannan karon ai aiyukan zasu zo mana da sauƙin.
Dan nan za'a kawo ragunan Jamil da Jalal Amarya ta gyara musu."

Ni inji dana Ya Jafar da nawa dana Hajia Mama".

Cikin murmushin Ummi tace.
"A a kada ki mana wayo kinada masu tayaki aiki ga Ladi da Lami duk zasu tayaki."

"Ummi kuma ga Saratu ga Larai gaki ga Aunty Aysha".
Cewar Aunty Juwairiyya.

"Duk da haka aikin da yawafa anan ga na Sheykh ga na Mamey ga ganawa gana Aysha kana ga na Jalal Jamil. Kuma suma su Saratu sunada aikin nasu."

A hankali Aysha ta miƙe zaune tare da cewa.
"Ummi aiki ai ba abin tsoro bane, ba damuwa".

Tana faÉ—in haka ta juya ta nufi É—akinta.
Tazo gab da bakin ƙofar shiga falonta kenan taga wani irin duhu ya rufe mata ido sai jiri da sauri ta zauna.

Sheykh kuwa da yayi al'walan la'asar zai fitone ya É—an zuba mata ido tare da cewa.
"A azumi É—ayan ne kike neman faÉ—uwa zaki sune min ko".
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Azumin fa da zafi Sheykh".

Kanshi ya É—an juyo tare da cewa.
"Kaiya Ummi ragwanci dai".
Murmushi sukayi ya wuce ya fita.
Ita kuma da ido tabi bayanshi ƙeyarshi ta liƙawa wani mayataccen kallo.
Kana ta miƙa tsaye ta nufi ɗakinta.

Ummi kuwa cikin gyara zama tace.
"Gsky Juwairiyya aikin nasu Jamil ayishi a sashinki.
Kinfa San na Sheykh ma biyu ne".
Dariya Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Kai Ummi to shi Sheykh ba a ana tashi sallan idi a wurin ake yanka nashiba, tunda shine liman baza'ayi layya ba sai yayi.
Yanayi kuma a wurin ake rabashi sadaka.
Daga nan kowa ya dawo gida yayi nashi".

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Eh to ai akwai wanda LamiÉ—o ke bashi kuma za'a kawoshi nan".

Miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
"To shike nan Ummi a bar na Jamil tunda shi zaima je ya tayamu aikin ku ku gyara na Jalal".

"To shike nan". tace kana suka tafi salla.

Bayan sun idarne suka fito suka fara aikin buÉ—a baki.

Bayan sunsha ruwa sun hutane.
Suka shiga kitchen kimtsa kayan aikin da aka lodo musu sukayi.
Kana suka É—an haÉ—a aikin da zai iya faruwa a lokacin.

Washe gari aka tashi ranar Sallan layya.
Yara da manya mata da maza al'ummar Annabi na duniya baki É—aya anata shiryawa zuwa idi.

Babu wanda ya tsaya karyawa sabida duk suna azumi.
Wanda sai bayan an sauƙo idi anyi yanka mai layya yayi buɗa baki da hantar dabbarsa.

Sauri-sauri yake kimtsawa cikin wata kekyawar al'kyabbar mai taushi baƙa sai farar jallabiya da yasa a ciki.
Hiraminshi ya kimtsa kana ya fisa turare.

Sannan ya fito da sauri ganin lokacin nata gaba towa.

A falo ya samu Ya Jafar. Tare suka fito babban falon.
Nan suka samu su Ya Hashim, Jalal, Jamil, Imarn, Affan, Sulaiman. Da sai sauransu.

Nan suka rakaya suka nufi masallacin Masarautar JoÉ—a inda nan yake limancin Sallah idi.

Masallacin da ƙaton filin harabar masallacin duk ya cika yayi maƙil tako ina al'ummar Annabi ne keta shigowa.
Cikin shiga mai kyau ta al'farma da tsabtar addini.

Ita kuwa Aysha a hankali take kimtsawa sabida ciwon da mararta keyi.
cikin sanyi ta buÉ—e wodurob É—inta.

Wani tattausan Boyel mai taushi da sheƙi mai ɗan karen kwai ta zaro, dinkin zani da rigace borno sitayel mai masifar kyau.
Kalarshi Sky blue an watsa mishi aiki da zare Pink color mai sheƙi.

Bayan tasa bra and pant wani tattausan ondawuya dan guntu iya guiwa tasa, kana tasa.
ÆŠaura zanin ta dai-dai-ta shi.
Rigar ta zura a jikinta tayi mata cib-cib gwanin burgewa ƙirjinta ya zauna daɓas.

Ninke É—an kwalin tayi tare, murza asetta ta É—an karkatashi kaÉ—an jelan gashinta da bata kitseshi ba, ta barshi kwance a bayanta.
Turare mai masifar ƙamshi ta fesa.

Sannan tasa wani sarka da yan kunne masu kyau.

Gyale pink color ta yafa.

A hankali ta fito falo.
kiciɓis sukayi da Ummi tana cewa.
"Aysha mu tafi ko".
A hankali tace.
"Ummi kuje kawai. Bazan jeba".

ÆŠan jim Ummi tayi sai kuma ta juya kawai ta tafi.

Ita kuwa Aysha kitchen ta nufa.

"Special Arish". tace a hankali kana ta.
Ɗebo dankali da sauran kayan da zata buƙata

SPECIAL ARISH
1.dankalin turawa
2.nama, kwai, tumatur
3.kabeji, bama , maggi
4.tafarnuwa ,man gyada.
Da farko dankalinki ta fara ferewa ba tare da daddatsashiba ta wanke saita-ta tafasashi da ruwa da gishiri kadan.
Sai ta kada kwai da albasa d curry da Maggi Tafarnuwa.
Daga nan saita dinga tsoma dankalin tana soyawa.
Sai ta kuma tafasa nama da maggi da gishiri da curry da tafarnuwa da al'basa har yayi laushi saida ruwan ya kusa tsotsewa saita kara wata al'basa da timatur suka nuna saita kwashe.

Ta yanyanka kabeji kanana sannan ta dafa kwai ta yanyan kasa da. Dan girma sannan ta zuba Maggi da bama ta gaura yeshi .
Sai ta samu Foodflaks ta zuba Irish a gefe sannan hadin namanki ta shina ta sashi a wani kulan shi kuma haÉ—in kabejinki ta sashi a wani kulan shima

Kasan cewar da yawa ta É—an yi shi.
Tana gamawa taje ta jerashi a kan Dinning area.
Sannan tazo ta kimtsa wurin.

Tuni kuma an idar da salla.

Affan dake kusa da Sheykh ne ya É—an matso tare da cewa.
"Hamma Jabeer gacan ragon an kawo mutane nata son tafiya gida suna jiran kayi yankan."
Da sauri yajuya tare da cewa.
"To muje".

Bayan yayi yankanne ya juya ya tafi.
Yasan na cikin gidanma duk shi ake jira.

Affan kuwa a gefen wurin ya tsaya saida aka gama fiɗan dogarin dake raba naman ya yanko hantan yasa a leda ya miƙawa Affan.
Daga nan Affan ya juya ya tafi cikin gida shi kuma yayi ta rabawa mutanen wurin naman.

Yayinda duk sauran mutane gari kuwa aketa tafiya.

A can mayankansu na cikin Masarautar JoÉ—a nan Sheykh ya nufa shida LamiÉ—o da sauran manyan masarautar baki É—ayansu.
Chapter 129 · 0% Book details