Sashe 9
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
aikuwa,junaid na ƙarasawa kopar dakin,a hankali ya sanya hannunshi tare da tura ƙopar dama a buɗe take,zura ƙafarshi ya fara yi kafin ya ƙarasa shiga bedroom ɗin,koda baby junaid ya shiga ciki bai kai idanunshi kansu ba,sae da ya fara rufe ƙopar ɗakin sannan ya juyo fuskarshi a washe,Karaf idanunshi suka sauka akan abusufyan dake rungume da hosana suna bacci,gabanshi ne ya faɗi rass cike da mamaki yace"Kai uncle tare da rishi ɗina,kwance saman gado suna bacci,Anya kuwa bansamu matsalar idanu ba......'
 "Junaid!" Jin an ambaci sunanshi yasa shi juyawa a firgice yaci karo da Sehrish dake zaune gaban mirror tana shafa powder a fuskarta,sae faman sakar mashi murmushi take yi,waro ido waje junaid yayi a tsananin tsorace ya mayar da idanunshi kan hosana dake rungume da abusufyan ya kalleta ya sake juyowa ya kalli wadda ke zaune agaban mirror,
 Muryarshi na rawa yace"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Nashiga ukuna!wai meyake damuna ne!meyake shirin faruwa dani ne!kodai nafara gamo da aljanu ne......'bai kai ƙarshen maganar tashi ba yaji an buɗe ƙopar toilet ɗin dakin,da sauri ya wurga idanunshi wurin,
 Jahad ce ta fito,jikinta sanye da bathrobe,alamar wanka tayi,
 Tashin hankalin da ba'a sa mashi date,
 Hankali amatuƙar tashe junaid ya dinga kallonsu ɗaya bayan daya,idan ya kalli jahad sai ya kalli sehrish dake zaune gaban mirror,sae ya kuma juya ya kalli Hosana dake manne da uncle ɗinsu,
Tunkarar shi jahad tayi fuskarta É—auke da murmushi,sehrish kuma na cewa"Junaid nice fa,baka gane ni ba,"
 Ae ina,a gigice junaid ya fasa wata uwar ƙara wadda tayi sanadiyar tashin Abusufyan da hosana daga dogon baccin daya ɗaukesu,
Da gudun gaske junaid ya damƙi handle din ƙopar ɗakin tamkar zai balle ta,buɗewa yayi tare da watsa wa da gudu har yanayin tuntube,tun kan ya fito daga corridor din dakin,Abbansu da mommynsu dasu twins suka nufo wurin saboda jin sautin razananniyar ƙarar da junaid ya saki,
 A sukwane ya faɗo wurinsu,hankalin Abbansu ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin yadda junaid ke gudu duk tsigar jikinshi ta tashi,
 Daƙyar suka samu suka damƙoshi saboda ƙokarin guduwa yake yi daga cikin gidan,
Hatta Marshal Omar da Sgr sai da suka jiyo ƙarar junaid,duk wani mai bacci acikin gidan sai da ya farka,ɗaya bayan ɗaya suka shiga fitowa suna tambayar ko lafiya,
 Jikinshi sae kerma yake yi duk yabi ya firgice,tambayarshi suka shiga yi ko lafiya,
 Muryarshi na kerma yace"Abba rishi uku acikin ɗakinta,Abba na mutu wlh aljanune ke bibiyata......'yana faɗin hakan ya sume ajikin Abban nasu,
 Tunda sukaji haka ransu ya basu Cewar yaje ɗakin Sehrish ne,Abbansu baiso hakan ba,dama yasan shi firgitacce ne,yaso ace tun farko saida ya fara yi mashi bayani anatse sannan yaje ɗakin nasu,
 Ayaan kuwa tun lokacin da yaji junaid ya fasa ƙara,ya ƙumshe dariya abakinsa,saboda yasan tsiyar daya tsula mashi,zaiyi wuya junaid ya yarda cewar Sehrish ƴan uku ne,ba kasafai yake fahimtar irin waɗannan abubuwan ba,sai an zaunar dashi cikin lalama anyi mashi bayani dalla dalla,sannan ake samu ya yadda,
"Junaid ne ko"?abusufyan ne yayi tambayar,yayin da yake daga zaune saman gadon,
 Sehrish tace"Shine daddy,ya ruɗe ne saboda ya ganmu mu uku,ya tsorata sosai naso na fahimtar dashi amma sai naga ya watsa aguje,'jin haka yasa abusufyan yin hanzarin saukowa daga saman gadon ya fuce daga ɗakin,
 Jikin jahad ba ƙaramin sanyi yayi ba,ganin halin da junaid ya shiga saboda ya gansu su uku,tsoronta kar wani abu ya same shi,ganin yadda ya watsa waje aguje,
  "Inaso naje naga halin da yake ciki,bansan meyasa ya firgita ba har haka,"sehrish ce tayi maganar a yayin da take miƙewa daga saman stool,jikinta na sanye da farar riga da dogon wando fari,kanta kuma na sanye da hula fara ta roba,buɗe ƙopar dakin tayi ta fuce tare da nufar inda suke,
Komawa jahad tayi ta zauna saman kujerar gaban mirror,hannu tasa tare da É—aukar man shafawar sehrish ta buÉ—e shi tana lakuto shi a hannunta tana shafa ma jikinta,
"Jahad wai meya faru ne?naji sautin ƙara a kunne na," hosana ce tayi maganar,tana zaune tsakiyar gadon sae faman hamma takeyi saboda yunwar da take ji,
"Ƙanin Ya Omar ne,junaid ya shigo ɗakin nan,ina tunanin ya tsorata ne da ganinmu shiyasa ya firgita,saboda yaga fuskokinmu iri ɗaya dana sehrish,"
sauko da ƙafafunta tayi ƙasa tana cewa"bari naje naga meke faruwa a wajen,"
Da sauri jahad tace"Kada ki fita hosana!sehrish ta fita muddin ya ƙara yin arba dake zai zauce ne,ki bari sehrish tadawo sai muji daga bakinta,idan an fahimtar dashi ya fahimta,sai mu fita atare,
Hosana tace"amma fa Yunwa nake ji sosai aciki na,'
"Bari daddy ya dawo zanyi mashi magana,nasan zai sa ashirya mana breakfast É—inmu,'acewar jahad,
Murmushi hosana tayi tare da cewa"jahad bakiji irin farin cikin da nayi ba jiyan nan!,wlh inason Daddynmu sosai,tun lokacin da gwaggon katsina tace mu Æ´a'Æ´an abusufyan É—inta ne,ta kuma kirashi awaya tabamu mu gaisa dashi,tun daga lokacin nake jinshi araina,na dinga addu'ar Allah yasa ya zama mahaifinmun duk da alokacin nasan wanene mahaifin namu......'
"Nikaina hosana a lokacin,da muka fara waya dashi sai da naji jikina yayi sanyi,naji wani irin yanayi atattare dani ashe dae dagaske mahaifin namu ne,gaskiya munyi dacen uba,yana da kirki sosai duk da ban zauna dashi na wani lokaci ba,amma tun daga kan Fuskarshi zakasan cewar mutumin kirki ne,ashe lokacin da muna yara har zuwa ya ta6ayi ya ɗauke mu yakaimu gidansu yayi mana wanka sannan yayi mana kitson kalaba,bawan Allah,Allah kaɗai yasan yadda yaji acikin zuciyarshi lokacin da wannan baƙin mugun ya rabashi damu,'
Hosana ta ƙara da cewa"Mummuna kawai,fuskarshi kamar ɗuwawu saboda rashin kyau,har naqosa naga yadda Ya omar ɗina zai karairaya ƙasusuwan jikinshi,"ta ƙarasa maganar tana yin nuni da hannayenta,yadda takeso Omar yayi ma Ya sayyadi,
Ta cikin mirror jahad ke kallonta tana dariya tace"ae ba ƴa'ƴa Omar kaɗae ba,baki lura da yadda wannan mai blue eyes ɗin nan yayi ba,wani fari kyakkyawa mai ƙirar nan,har ni sai da na tsorata dashi ganin yadda ya zabura yabar wurin yana huci......'
Hosana tace"ae nagane shi,Ni wlh tsoran idanunshi nake ji, kaman aljani,wai shima yanzu É—an uwanmu ne ko?duk Æ´an gidansu ya Omar ne ko?
"Yayanmu zaki ce,ae yanzu duk wanda kika gani acikin gidan nan,to yayan mu ne,jiya baki lura da wani matashi acikinsu ba wani fari,mai mutunci wanda yazo ya kira mu,lokacin da alAbbansu ke neman mu"?
Murmushi hosana tayi alamar tagane shi tace"daga gani zaiyi sauƙin kai sosai,kuma da alama ba ƙaramin farin ciki yake damu ba,mun gode ma Allah jahad daya haɗamu da dangin mu,'