Sashe 123
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Har tsawon wani lokaci,kuke so na baku ku dawo mun dasu junaid"?Acewar Abba,
 Shiru sukayi gabansu na faɗuwa,Omar ne yayi ƙoƙarin cewa"1 week"a hanzarce Sgr yace"Omar that's impossible,ka manta yarda mu kayi dasu ne?Sunyi mana alƙawarin cewa in dae aka yi masu yadda suke so zasu sakosu,Amma ba a tare ba,saboda suna ganin za'a gano su adau mataki, akwai yiyuwar su fara sauko junaid shi kaɗai acikin satin nan ko kuma su fara sakin Jahad,Ni ina ga kamar one month yayi,Kafin lokacin in sha Allah mun dawo dasu duka acikin gidan,
 Girgiza kai Abbansu ya ɗan yi tare da cewa"Har one month!su junaid basa atare damu?idan suka cutar dasu fa?
 "Abba sunyi mana alƙawarin cewa in har zamu biyasu yadda suke so,bazasu cutar mana dasu ba,"
 "Nawa suka buƙata"yayi tambayar yana kallon faces ɗinsu,
"har yanzu dai su muke jira,sunce zasu kira su sanar damu,sannan sunce mu kwantar da hankalinmu,Bazasu ta6a cutar dasu ba,Zasu basu kyakkyawar kulawa,kuɗi kawai suke buƙata ba wani abu ba,"Omar ne ya kora mashi jawabin
 Cike da takaici Abba yace"just because of money,suka ɗauke mun ƴa'ƴana?Ae da sun sani sun nemi tallafi a wurinmu konawa ne zamu basu basai sun ɗauke mun su ba,"
  Miƙewa yayi sam babu kuzari ajikinshi,tafiya ya soma yi dakyar yake iya ɗaga ƙafarshi,har sai da yabar wurin Sofas ɗin,Sannan ya dakata da yin tafiyar,ya waiwayo tare da kallonsu,gaba ɗaya idanuwansu na akanshi,
 Magana ya soma yi masu babu wasa a fuskarshi"Omar!"
 "Na'am Abba"ya amsa mashi,
"Rafayet"shima ya amsa mashi"Na'am Daddy,"
  "Na yarda daku sosai,abu biyu nake tsammani daga wurinku,Na fako ku dawo mun dasu junaid,Cikin ƙoshin lafiya,Na biyu kuma ku kawo mun waɗannan gur6atattun mutanen da sukayi garkuwa dasu,Wallahi thumma tallahi idan har ku kasa yi mun waɗannan abubuwan dana lissafa maku,inaso ku sani Za ku rasa ni ne,NA HAR ABADA,daga yau zuwa 30 ga watan da zamu shiga,a kowace rana zan fara sa ran dawowarsu acikin gidan nan!kuma daga ranar ku fara ƙirgen ranakun da su kayi mun saura acikin duniyar nan
 *Tashin hankali!*
Mikewa Mommynsu tayi tare da kallonsu gwanin ban tausayi tace"Na yarda daku sosai,ku taimaki rayuwar mahaifinku,Zamu taya ku da Addu'a Har Allah yasa kuyi nasara akan kidnappers ɗin nan,"tana kai ƙarshen maganarta,tabi bayan abbansu,
 "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"wannan shi ne abunda ke fitowa daga bakunansu,basu ta6a ganin tashin hankali irin na wannan ranar ba,A tsaye kowannansu ya kwana,har sun fara regretting ɗin ƙaryar da suka shirya ma Abbansu,
Acikin waɗannan kwanakin,Komai ya hargitse masu,safe da marece dare da rana,kullum cikin Zullumi suke,Suna cikin tashin hankali,Duk sunbi sun firgice,kallo guda zaka yi masu ga gane cewar basa a hayyacinsu,Don gaba ɗayansu daga Omar ɗin har Sgr babu wanda baiyi rama ba ajikinsu,gidan ya zama tamkar maƙabarta,Babu wani sauran farin ciki daya rage masu,Saboda rashin junaid babu mai samun isasshen bacci acikinsu,Abinci ma har Azmee ta fara gajiya da girka masu saboda Asarar shi da akeyi,Yadda ta ajiye haka take zuwa ta same shi,duk rana ta Allah sai Abbansu ya tunasar dasu Adadin kwanakin daya rage masu na ƙwato su junaid a wurin kidnappers,yayin da suke cikin wannan tashin hankalin,Abusufyan na can suma ba kwanciyar hankali wanda hakan ya ɗauke hankalinshi gaba daya batare da ya fahimci halin da gidan suke ciki ba,Ciwon abu ya tashi gadan gadan,Kullum da daddare sai ta dinga kuka tana buge buge tana faɗin sunan sayyadi,hakan ba ƙaramin ruɗani ya sanyasu ba,har Sehrish ta fara zargin cewa,kodai yafara yi mata gizau ne?Anya ba wani abu ke faruwa ba?duk yadda taso Oummansu ta sanar da ita abunda take gani,Hakan ya faskara saboda bata da hankalin da zata iya fayyace mata komai,a ƙarshe dole sehrish ta koma ɗakinta da kwana,duk in haukan nata ya motsa da zarar ta fara raira mata karatun Alƙur'ani sai ta samu natsuwa,a haka suke samu tayi bacci,
A 6angaren Su Hayaam kuwa,ba ƙaramin daɗi suka ji ba,lokacin da Abra ta dawo abuja,Batare da tasha wahala ba,bayan An sallami Hayaam daga Asibiti gidan Amani suka koma,Zasu zauna na ɗan wani lokaci kafin su wuce Maiduguri,duk wannan budurin da sukeyi basu son abunda ke faruwa acan gidansu na maiduguri ba,Sun manta da mahaifiyarsu da suka baro kwance ba lafiya rai hannun Allah,
A 6angaren Aunty babba kuwa ba ƙaramin jiki taji ba,tun bayan da mai motar nan ya hankaɗe ta a Enugu,daƙyar aka samu wani bawan Allah ya ɗauketa a motarshi suka kaita asibiti,Taci baƙar wuya kamar bazata rayu ba,tsawon sati tana kwance a gadon asibiti batasan inda kanta yake ba,Komai ya ƙare mata ƙarƙaf,mutumin daya kawota asibitin tun da ya biya kuɗin da za'a yi mata aiki a ƙafarta da ta samu matsala,bai ƙara tako kafarshi yazo ba,Ga ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa,ta ɗuri ruwa,tayi suntum da ita,daga baya ta ru6e sai uban wari dake fitowa daga jikin ƙafar,Likitoci sunyi iya kar bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sunyi mata magani,amma abun ya ci tura,da suka gaji gashi babu wani danginta a kusa,kuma babu kuɗin da zasu cigaba da kula da ita,A ƙarshe Suka sallame ta daga asibitin,Tashin hankali!ko ya rayuwar Laila zata kasance"?
Â
Yau Two Weeks kenan da mutuwar Junaid,Wanda ya kasance Wata biyu cuf da sati ɗaya da yin auren Sehrish Abusufyan da Rafayet salahuddeen,duk da muna sa ran kwanakin auren nasu zai ƙara tsayi saboda Sgr ya ɗaga tafiyarshi ta komawa U.s,Zuwa Next One Month,dalilin ɗaga tafiyar tashi saboda Investigation ɗin da sukeyi na ƙoƙarin gano waɗanda suka kashe Junaid,Ga kuma Abbansu daya zuba masu ido yana jiran su dawo mashi da ƴa'ƴanshi,bawan Allah ko bacci bai samu,duk ya rame ya fige,bai samun bacci da daddare saboda sallar daren da yake yi, haka zai zauna saman darduma yayi ta yi masu addu'a,Allah ya dawo mashi da ƴa'ƴanshi,ita kanta Mommynsu junaid tana cikin mawuyacin hali,cos ta fara zargin cewa ba Kidnapping ɗinsu akayi ba,there's something behind da suka 6oye masu,har sun fara fidda rai da dawowarsu,A ranar Litinin sai ga JAHAD ta dawo gidan da ƙafafunta,Murna a wurinsu kamar su haɗiyeta,duk da sun shiga damuwa ganin yadda ta rame ta fige,duk ta fita hayyacinta,ƙashin wuyanta duk ya firfito kamar zai fasa fatar wuyanta,Taji jiki sosai,Idanuwanta duk sun kumbura,duk yadda suka so jahad ta buɗe baki ta faɗa masu ina junaid yake,taƙi magana bakinta a rufe yake,sai dai kawai ta dinga binsu da ido,bakomai ya hanata yin magana ba,fa ce kukan dake cinta,muddin ta buɗe bakinta to zata fashe masu da kuka ne,kuma ta ɗaukarwa Su ya Omar alƙawarin bazata tona masu asiri ba nace wa junaid ya mutu,har sai lokacin da suka shirya sanar dasu,tunda ta dawo gidan nan,Ta zama salihar ƙarfi da yaji,magana saita zama dole sannan take yinta,ko ɗakinsu batasan fitowa daga ciki,tun hosana na lalla6ata don ta faɗa mata abunda ke damunta,saboda kullum sai ta farka ta sameta tsakar dare tana sallah hawaye na gangarowa akan fuskarta,Har tagaji da tambayarta ta ƙyaleta,
Kullum ne in zata kwanta da daddare sai ta ɗaukko wannan zanen fuskar junaid da tayi a cikin drawing book ɗinta,ta tasa shi gaba tayi ta kallo,Wani lokacin ta fashe da kuka wani lokacin kuma tayi murmushi,bakomai yafi tsaya mata araiba,kamar rana ta farko da ta fara haɗuwa dashi face to face,Yayi tsammanin Sehrish ce,ya ruƙo hannunta ya turata cikin motarshi,ya tasa ta gaba da wannan kyakkyawan murmushin nashi,jahad tayi kuka tamkar ranta zai fita,har ya bi jikinta,in har bata zubda kwallaba ita kanta bata jin daɗin jikinta,wani sa'in idan raɗaɗin yayi mata yawa ƙur'ani take ɗauka ta zauna tayi ta karantawa har ta samu sauƙi acikin zuciyarta,Sau dayawa Omar yakan kirata a garden su zauna yayi ta lallashinta,yana yi mata nasiha,hakan yasa ta fara samun sauƙin raɗaɗin da zuciyarta keyi mata,har ta fara sakewa da kowa acikin gidan,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,Yanzu saura dawowar Junaid suke jira shima Masu garkuwar su sako shi,😥rashin sani yafi dare duhu
*Boss Bature*
Kano State,