← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 179 OF 212

Sashe 179

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fucewa tayi daga cikin É—akin,Ta nufi kitchen,Oumma tasamu tare da Hajiya azeema da Saude suna shirya abincin karin kumallonsu,kamar yadda suka yi jiya,Suna aiki suna fira,tunda tashiga kitchen É—in,idanuwanta na akan Abu dake tsaye agaban Gas cooker tana motsa Farfesun da ta É—aura,
Hajiya azeema ce ta lura da ita"Ina kwana Aunty,kin tashi lafiya,"daƙyar Mommy ta ƙaƙaro murmushin dole,
"Lafiya lou,sassanunku da aiki,Tun É—azu naso na shigo kitchen É—in,na tsaya wurin Junaid ne,"
Juyowa abu tayi suka haÉ—a ido da Mommy,murmushi tasakar mata,cikin girmamawa abu ta gaisar da ita,mayar mata da martanin murmushin tayi tare da amsa mata gaisuwar,Saude ma ta gaishe da ita,
Cike da zolaya,Mommy tace"Amaryar harrisun gwaggo,yau naga hada make up akan fuskarki,Shi kikayi ma kwalliya,"Cike da jin kunya,Saude ta ajiye wuƙar da take yanka kayan lambu da ita,Ta sanya tafin hannunta akan fuskarta,dariya su kayi gaba ɗayansu,
"Kamar wata me kunya,Ae gwaggo ta sanar dani komai,abar kaza cikin gashinta dai kar a fige,"ta ƙarasa maganar da zolaya,
A shagwa6e Saude tace"dan Allah Aunty azeema kidaina yarda da maganar Gwaggo....."bata ƙarasa maganar nan ba,Gwaggon katsina ta faɗo cikin kitchen ɗin,Jikinta sanye da waɗannan kayan baccin nata na gado ƴan ƙasar turƙiya,Duk sunyi squeezing sun cukuikuye,kanta ko kallabi babu duk hurhura,ta ƙwama glass baƙi kato akan fuskarta,
Tsayawa tayi tare da ruƙe qugu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya,kafin tace"Waye ke kiran sunana?Wato ina can ina bacci ana nan ana yi mun munshari,"
Ƙumshe dariya sukayi gaba ɗayansu,dabsauri hajiya Azeema ta nuna Saude"Kin ganta nan itace ke kiranki,"
Uwar harara gwaggo ta watsa ma saude"Munafuki dai baiji daÉ—in rayuwarshi ba,Ae naji abunda tace,Wato adaina yarda da maganata,Ni ga mahaukaciya ko?Wlh saude kiji tsoran Allah,A haka kikeso In bari Harrisu ya aureki?kina yi mun rashin kunya?Allah ya kiyaye,Ae sai dai ki koma rigarku ki samu irinsu jauro ki aura badai harrisuna ba,"tayi maganar tana murguÉ—a mata baki,
"Gwaggo nifa ba haka nake nufi ba,dan Allah kiyi haƙuri idan na 6ata maki rai,
Guntun tsoki taja,kafin ta mayar da idanuwanta kan Abu,Lokaci guda ta soma washe baki"Ina Æ´a'Æ´an Abusufyan É—ina suke?yau har mafarkinsu nayi,"
Murmushi abu tayi"Gwaggo suna nan cikin ƙoshin lafiya,"
"Madallah,bari naje na dubosu,dan Allah ashirya masu lafiyayyen abinci,suci su ƙoshi,"
Hankalin Mommy ne ya tashi,Gudun kada gwaggo taje ta taras babu É—aya daga cikinsu,Da sauri ta dakatar da ita,
"Gwaggo,ki tsaya mana,ga farfesu ya sauka,Yakamata ki É—anÉ—ana girkin Amaryar Abusufyan É—inki,"
A sukwane ta juyo fuskar nan É—auke da murmushi"dagaske abusufyan zaiyi aure"?
"Eh mana,Za'a maida aurenshi da zainabu abu,kinga nan bada jimawa ba zaki samu wasu Æ´a'Æ´an na Abusufyan,"
Wani irin farin cikine ya lullu6e gwaggo,Hada sanya hannu ta dafe saitin zuciyarta,
"Wlh bakiji daɗin da naji ba,Wayyo Allahna,Ranar dana daɗe ina jira gashi zata zo,Zainabu abu zata koma ɗakin Abusufyan,Ga harrisu shima zai angwance,dole inyi rawa," ta ƙarasa maganar tana kwaso shoki da hannuwanta,Gaba ɗaya suka fashe da dariya,

A 6angarensu Hayaam,Sun fuskanci matsanancin tashin hankali A gidan malam liman,Duk sun rame sun kode saboda yunwa,Ga tsangwamarsu da akeyi,aikin gidan gaba ɗaya ya dawo kansu,sune wanke wanke,Sune shara hatta dabbobin gidan suke wanke garkensu,duk yawan mutanan gidan Suke girka masu abinci,a ƙalla yana da ƴa'ƴa kusan talatin,Ga matanshi huɗu,Sun tsanesu sun addabi rayuwarsu,Wata rana kwatsam sai ga mahaifinsu Ya dawo Abie,Ya zama cikakken mutun,Yanzu babu asirin mammy ajikinshi,tun lokacin da Amal ta bashi waɗannan kuɗin ta gudu wurin Amani,Shima Ya gudu zuwa kano wurin wani Abokinshi,Acan ya fara ta6a kasuwanci,Labarin mutuwar mammy ne ya riskeshi acan ta hanyar wani ɗan uwanshi da suka haɗu dashi a nan kano ya sanar dashi komai daya faru ya kuma bashi shawarar ya dawo ya rungumi ƴa'ƴanshi,tunvkafin ya rasasu,

Wannan dalilin ne yasa Abie yayi tattaki zuwa Maiduguri,Lokacin da yayi arba dasu Abra,Hankalinshi ya tashi sosai,A ranar ya kwashe su zuwa gidansu,sunyi kuka sosai sun nemi yafiyarshi,Yace masu komai ya wuce tunda sun shiryu,sati ɗaya suka yi a gida,Ya tattara su gaba ɗaya ya tafi dasu kano,Saboda zama maiduguri bazaiyiwu ba,mutane sun addabi rayuwarsu,Ko ƙopar gida ba damar su leƙa sai ahau zaginsu ana nunasu da yatsa,

Gidan haya ya fara kama masu,Sai kuma ga Kuɗi Amani ta turo masu ta account ɗin hayaam kusan miliyan ɗaya da rabi,dama yana da wasu kuɗi hannunshi na gidansu daya saida kafin su baro,kuɗi suka cika 3 million Ya sama masu gida irin na masu rufin asiri,Ya siya masu,Ba ƙaramin daɗi suka ji ba,Yanzu basu da sauran damuwa,rayuwarsu ta canza sosai,Har makarantar islamiyya abie ya sanyasu,wannan kenan,

*Very Soon Littafi zai ƙare sai dai kawai kuji nace Alhamdulillah,Ga azumi yana zuwa Allah yasa muna da rabon ganin watan ramadan👌Ga duk mai buƙatar littafin Abban sojoji yayi mun magana kai tsaye ta layina,Amma fa whatsapp kawai banda kira,08103884440*

 
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

_Double page ne,Saboda jiya da bana jin daɗi bansamu nayi ba,that's why na hada maku pages biyu💋_

Lokacin da Abusufyan ya fita a fusace ya shiga motarshi yayi mata key da gudun gaske ya fusgeta,shi kanshi baisan ina zai dosa ba,A ƙarshe gefen bishiya yayi parking ɗin motar Ya kifa kanshi jikin steering,tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,Bai ta6a tunanin Sgr zaiyi mashi haka ba,duk irin yadda yake treating ɗinsu,tun suna yara yake hawa jirgi daga Turkey zuwa U.s don kawai ya gansu,saboda ƙaunar da yake yi masu shi da Omar Amma sai gashi yau Sgr Yayi mashi abunda bazai ta6a mantawa ba,Tsananin damuwa ne akan fuskarshi,zuciyarshi sai tafarfasa take yi,Zufa tuni ta wanke mashi fuskarshi,cikin shessheƙar kuka Ya furta"Why Rafayet!why!ban ta6a tunanin haka kake ba"lumshe idanuwanshi yayi,Anan Ya yini gefen bishiyar,

Duk ta damu saboda rashin ganin Sehrish ga wayarta dake ajiye saman side drawer tun safe,tun tana zarya acikin bedroom ɗin harta fara tunanin Zuwa nemanta,hijab ta zura ajikinta ta buɗe ƙopar ɗakin ta fito,miƙar hanya tayi tana tafiya,Adai dai ƙopar bedroom ɗinsu ta tsaya,Hannu tasa tayi knocking ɗin ƙopar,

Jahad ce ta buɗe mata ƙopar,jikinta na sanye da pakistan wando Burgujeje pink da Riga fara mai dogon hannu,daga ƙasan rigar anyi mata adon stones,Ta yafa mayafin a ƙafada,Yayin da ta saki sumar kanta,

Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Amrish"ta ƙarasa maganar tare da yin hugging ɗinta,Suka rungume juna,bayan sun kammala gaisawa Amrish ta soma tambayarta
  "dama ina neman Sehrish ne,tun asuba dana farka banganta ba,bansani ba ko tazo wurinku ne,ko ta fita daga gidan,"
  Gaban jahad ne ya ɗan faɗi don ita kanta duk yinin ranar bata sanya Sehrish a idanuwanta ba,
  "Gaskiya bansan inda taje ba,nima duk yau banganta ba,Amma abunda za'ayi bari na bincika cikin gidan may be ko tana wurin Aunty azeema ne,"
  Juyawa Amrish tayi,da sauri jahad ta ce"Ki shiga mana,Ga Hosana can tana kallon drama,".
  Murmushi ta ɗan saki tare da gyaɗa kai tace"okey,"Matsa mata hanya Jahad tayi ita kuma ta shige ɗakin,A kwance ta samu Hosana ta baje saman gadon,Ga laptop agabanta ta ƙura ido tana kallo,wuri ta samu daga gefe ta zauna,
  "Hosana,ya kike,"
Juyowa hosana tayi fuskar nan a yamutse tace"Lahiya,"ta mayar da idanuwanta kan laptop din,zama sosai Amrish tayi suka cigaba da yin kallon atare,

Tana ƙoƙarin fitowa daga Toilet,tajiyo Muryar Mommy tana sallama,Ƙarasa fitowa Hajiya Azeema tayi jikinta sanye da bubu ta atampa ,fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa mata"Wa'alaikum salam,Aunty ki shigo daga ciki mana,"
  turo ƙopar mommy tayi jikinta na sanye da jallabiya fara,babu mayafi akanta,sam babu kwanciyar hankali atattare da ita,ganin fuskarta a hargitse yasa Hajiya azeema tace"Aunty Lafiya naga kamar akwai damuwa a fuskarki,"
  Mommy tace"Ina fa lafiya,Rafayet yayi aika aika,yabarmu da zullumi,"tayi maganar yayin da take zama daga gefen gadon nata,
  "Me Rafayet yayi"?
"Hmmmm,É—azu Abban Junaid ke sanar dani,Nasan kinsan da auren sirrin da su kayi mashi ko"?
  jinjina kai hajiya azeema tayi"Eh,nasani,"
  "Oh ashe kema kinsani,Ni aka mayar shashasha,babu wanda ya sanar dani,"
  Murmushi hajiya azeema ta ɗan yi"Naso in sanar dake Aunty,Kawai ina fargabar yadda zaki ɗauki abunne,"
  Ta6e baki Alex ta ɗan yi,
"Amma meya faru ne"?
Nan Mommy ta kwashe duk abunda Abba ya sanar da ita,tun daga farko har ƙarshe ta sanar da ita,..
Hannu Hajiya Azeema ta É—aura akai,Hankalinta amatukar tashe take ambaton"Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un!Nashiga uku!"duk tabi ta ruÉ—e,
Cike da takaici Mommy taci gaba dacewa"Wlh tun safe ake ta faman nemanshi ba'a ganshi ba,Ni yanzu babban tashin hankalina shine a wani hali yarinyar take ciki!Ina Rafayet ya kaita!Tana raye kota mutu"?.
Tuni idanuwan hajiya azeema sun cicciko tab da kwalla,bakinta ya mutu,Jikinta yayi sanyi,
  "Amma rafayet bai kyauta mana ba Allah,duk da nasan yayi ne saboda son da yake yi mata,Yaji tsoran su rabashi da ita ne amma....."tunkan takai ƙarshen maganarta,Mommy ta katse mata hanzarinta"aini banso Suka tursasa mashi akan ya saketa ba,Wannan shine kuskuren da suka aikata,Babu wanda baisan halin Rafayet ba acikinsu,tunda ya nuna yana son ya tafi da ita,to tabbas Yana sonta ne,Ni nasan wanene rafayet,Wlh da ace baison yarinyar nan,ko kallo bata ishe shi,balle har ya aureta,Amma tunda yayi accepting aurenta as a contract wlh yana sonta ne,So bana wasa ba,that's the reason why yaƙi sakinta,Shima kuma da laifinshi,komai sai yace zai nuna ƙarfi,Ai akwai abunda ƙarfi ko dukiya basa iya siyawa mutun,duk da ana siyan soyayya da kuɗi,Amma bakowace zuciya bace zaka iya mallakarta cikin sauƙi ba,kuma hada ƙarin shi bai ta6a soyayyaba,balle yasan yarda zai baiyanata,"

Jinjina kai Hajiya Azeema tayi"Allah sarki Sehrish,wlh na tausaya mata baiwar Allah,banji daɗin abunda ya faru ba,Yanzu ya zamuyi?wlh duk na ƙagu da insan a wani hali take,Ga Abusufyan ma,Naji kince Ya fita ba'a san inda yake ba,"ta ƙarasa maganar tana kallon Mommy,Duk sun shiga damuwa,
  "Tun ɗazu suka fita nemansu,Amma har yanzu shiru babu wani labari,yanzu sai dai muyi ta jiran tsammani"acewar Mommy,
Chapter 179 · 0% Book details