← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 212

Sashe 187

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daya gaji da zamanne ya kwantar da kanshi gefen saman gadon,har bacci yayi awon gaba dashi,Lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar asuba,Wayar abusufyan dake ajiye saman side drawer ta soma ringing,da ƙarfi kiran ya shigo,har cikin kunnanshi yajiyo sautin,A hankali ya ɗan buɗe idanuwanshi masu ɗauke da bacci don bai ishe shi ba,daga kwancen da yake ya wurga idanuwanshi kan Agogon bangon ɗakin,Lokacin sallar asuba yayi,dama sai da ya kawo hakan aranshi,don kuwa bamai kiranshi a wannan lokacin in ba abba ba,domin ya tashe shi sallar asuba,sam bai lura da mutun a gefenshi ba,daƙyar ya samu ya miƙe yana yin hamma,tare da yin miƙa,kafin ya sauke hannunshi ne karaf idanuwanshi suka sauka akan Sgr dake kwance yana ta sharar bacci,Gabanshi ba ƙaramin faɗuwa yayi ba,don baiyi tsammanin ganin mutun adakinsa ba,kuma farat ɗaya bai waye shi ba,don har sai daya ɗan raza,Cike da mamaki yake binshi da kallo,Abun yayi mugu mugun ɗaure mashi kai.
"Rafayet"!ya ambaci sunanshi da ƙarfi,hannu yasa ya ɗan bubbugi kafadarshi,nan fa ya fara sambatu yana faɗin"Am sorry uncle,ka yafe mun,bazan ƙara ba,Nasan nayi kuskure amma ba'a son raina ba uncle i ave realized my mistake,a shirye nake dana kar6i koma wani irin hukuncine daga gare ka........"duk cikin bacci Sgr yake wannan sambatun batare daya sani ba,hada hawaye akan fuskarshi,tsananin tausayinshi ne ya kama abusufyan,ya lura da irin ramar da yayi,sam babu natsuwa atattare dashi,dama sai da ammi ta sanar dasu cewa duk irin raɗaɗin da zasuji na abunda ya aikata,Basu kaishi ba,don saiya fi su jin jiki,tuni idanuwan abusufyan sun cicciko tab da kwalla,

Slowly yakai hannunshi saman sumar kanshi,bai ta6a tunanin Sgr zai iya sauke girman kanshi ba,Yazo neman yafiya a wurinshi,sai gashi da kanshi ya bashi mamaki,Allah kadai yasan tun lokacin dayazo É—akin yana jiranshi ya farka,

Bubbuga kafaɗarshi yayi tare da ambaton sunanshi"Rafayet!Rafayet"!a firgice Sgr ya farka,yana faman zare blue eyes ɗinshi,Koda su kayi ido biyu da Uncle abusufyan da sauri ya sunnar da kanshi ƙansa,cike da jin kunyarshi,
"Tun yaushe kazo ne"?
Cikin sanyin murya yace"Tun wuraren ƙarfe sha biyu da rabi,nazo na same ka kana bacci,".
"Meyasa baka tashe ni ba"?
"Saboda Banaso na takura maka ne,"daƙyar yake magana,saboda nauyinshi da yake ji,
Yaƙi yarda su hada ido,Baisan yaushe Sgr ya fara jin kunya ba,Tabbas Ya fara ganin Canji atare dashi,'
"Kanason magana dani ne"?yayi tambayar yana kallon fuskarshi,.
É—aga mashi kai yayi alamar eh
"Okey,Ina sauraronka,"yayi maganar tare da matsowa Ya sauko da ƙafafunshi kasa,Kafin Ya mayar da hankalinshi kan Sgr,
"Uncle,"ya ambaci sunanshi,tare da saukowa daga saman gadon,Ya tsugunna agabanshi,abun mamaki abun al'ajabi,Kamar a mafarki haka abusufyan ke kallon lamarin,Yau Sgr ya sauke girman kan nan nashi,Ya zuƙunna agabanshi,Lallai yau babba rana ce agareshi,

Ruƙo hannunshi yayi acikin nashi,Calmly Ya soma magana"Pls uncle,Kaina bisa wuya na,ka yafe mun,Nasan nayi hurting dinka sosai,wlh na gane kuskurena.........'tun da ya fara magana,bai bari sun haɗa ido da abusufyan ba,shi kuwa ya kafe shi da ido yana kallonshi,
"Ka yanke mun duk wani hukunci daya dace dani wlh i will accept it,amma dan Allah uncle,kada ku rabani da ita,bazan iya jure rashinta ba,atare dani,na saba da ita sosai......'tunkan yakai karshen maganar,Abusufyan ya katse mashi hanzarinshi dacewa"Zaka tafi da ita a matsayin mai aiki ko kuwa"?
Da sauri yace"A'a,Zan tafi da ita,A matsayin matata,in har kun amince mun,"

Murmushin gefen fuska abusufyan ya ɗan saki,batare daya bari Sgr ya gani ba,ci gaba da magana abusufyan yayi"Naji daɗi daka gane kuskurenka,Dama ni can ban ruƙe ka araina ba kawai banji daɗin abunda ka aikata mata ba,Amma bbu komai,komai ya wuce Allah ma muna yi mashi laifi ya yafe mana balle mu ƴan adam,Don haka na yafe maka rafayet,Allah ya yafe mana gaba ɗaya,Sannan bazan ƙara shiga tsakaninka da matarka ba,Yanzu ya rage tsakaninku da Ammi ne,tace zata yi adalci atsakaninku idan har ku duka kun amince da junanku toh,idan kuma har ɗaya daga cikinku ya musa,to zata raba aurenku ne,"
Cikin sanyin murya yace"bansan da wasu kalmomin zanyi amfani wurin gode maka ba uncle......"
"Kada ka samu damuwa,komai ya wuce,Allah ya baku zaman lafiya kaida matarka......."daga haka Abusufyan ya zarce dayi mashi nasiha,duk ya kashe mashi jikinshi,fuskarshi ɗauke da murmushin nasara ya futo daga ɗakin Abusufyan ya nufi bedroom ɗin abbansu,knocking ɗin ƙopar yayi,
"Wanene"?Muryar abbansu ce,
"Ni ne abba,"
BuÉ—e kopar abba yayi jikinshi sanye da jallabiya da alama shirin zuwa masallaci yayi,
Tunkafin yayi magana abba ya ruga shi cewa"kaje wurin abusufyan É—in"?
"Eh,daga can nake,"nan ya kwashe duk abunda suka tattauna a tsakaninsu ya sanar dashi,farin ciki ne ya lullu6e abba,har baisa lokacin daya rungumo Sgr ajikinshi ba,
"Allah yayi maka albarka My son,"
"Ameen abbana,"
"Nima na yafe maka,"
Har cikin ranshi ba ƙaramin sanyi yaji ba,
Bayan ya raba jikinshi daga nashi,Ya ruƙo hannunshi zuwa cikin ɗakin"mu shiga daga ciki,in bakayi alwala ba,kayi sai mu tafi masallaci,'
Ba ƙaramin daɗi sgr yaji ba,Mommynsu na kwance tana bacci lullu6e da bargo,toilet ɗin ɗakin ya shiga,Abba ya tsaya a tsaye yana jiran fitowarshi,After some minutes Ya fito,
Suna hada ido da babansu Ya sakar mashi murmushi,mayar mashi da martanin murmushi yayi tare da cewa"inaso zan canza kayan jikina"
Shikenan,Zan jiraka a palour,Daga nan ka tashi su Omar,su fito mu tafi masallaci,"
Amsa mashi yayi da toh,kafin ya futo daga dakin,Jiki na rawa ya haura upstairs bai nufi ko'ina ba sai bedroom É—in Omar,tunkafin ya shiga ya soma kwala mashi kira,
"Omar,Omar,"a firgice Omar ya farka,tare da miƙewa zaune yana tambayarshi lafiya,fadawa saman gadon Sgr yayi tare da rungumeshi ajikinshi,Yana dariya,
Tun da yaga haka,Ya gane cewa Sun yafe mashi
"Omar ka tayani murna,Uncle da abba sun yafe mun,kuma yace bazai ƙara shiga tsakanina da reesh ba,Ya amince na tafi da ita,"
Omar yayi farin ciki sosai,Amma kuma akwai sauran rina akaba,idan su sun amince mashi,Itafa Yarinyar!!!

Shafa bayanshi Omar yayi"Am so happy rafayet,ashe da rabon asha shagalin bikina tare dana ka,Kafin mu wuce U.s,tare da matayenmu,Alhamdulillah My dream will come true,

Zuciyar kowannansu a wanke take da tsantsar farin ciki mara misaltuwa,
"Amma wani hanzari ba gudu ba,jiya kaje wurin Sehrish kuwa?naji kayi magana akan maganinta"?
"Bansamu naje ba,amma idan muka dawo daga masallaci,Zan je na duba Lafiyarta,"
"Hakan ma yayi,bari na je nayi alwala sai mu wuce masallaci"acewar Omar,yakai ƙarshen maganar tare da saukowa daga saman gadon,Toilet ya shiga Sgr kuma Ya wuce part ɗinsa,don ya canza Kayan jikinshi,

Batare da 6ata lokaci ba suka hallara gaba dayansu matasan gidan a babban falon gida,atare suka wuce masallaci,

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 8 na safe a lokacin Su oumma sun hallara a kitchen suna shirya breakfast ɗin gidan tare dasu Mommy,da hajiya azeema,

A wannan lokacin ne Sgr ya shirya tsaf cikin fararen suit,wankan ya hau dashi sosai,fitowa yayi daga part dinsa Ya nufi corridor din dakinsu Sehrish,a baƙin ƙopar ɗakin ya tsaya,tare da sanya hannunshi yayi knocking din ƙopar ɗakin,
Daga ciki yaji ance"Wai wanene"shiru bai tanka ba,Ya sake kwankwasa kopar,Da ƙarfi yaji a bude ƙopar,a ruɗe ta sanya hannu abakinta,ido ya raina fata,sam batayi tsamanin Baban yayansu bane,
"Yaya rafayet,ashe kaine,wlh nayi tunanin wanine daban"abun ma dariya yaso ya bashi,
"Rishi kake nema"?tunkafin ya bata amsa taci gaba da cewa"In ma oumma kake nema,tana a kitchen,Jahad kuma ta tafi wurin aunty hafsaf,Ni kaɗaice nake jinyar sehrish,baiwar Allah wlh saita baka tausayi,duk ta rame,duk taji ciwo abakinta,abinci ma daƙyar take iya ci ......'
Surutunne ya ishe shi"its Okey,Zan wuce,"matsa mashi hanya tayi ya nufi cikin É—akin,
"Tayi breakfast"?yayi tambayar yayin da idanuwanshi ke akan sehrish dake kwance magashiyyan tana bacci,
"Inafa,bataci komai ba tun jiya da daddy yabata farfesu tasha,tare da ɗan tea bata ƙara cin komai ba,koda daddare sai da oumma ta bata abinci ta amayar dashi duka......'
Surutun Hosana ba ƙaramin mamaki yake bashi ba,Amsa kaɗan yake buƙata amma sai zuba takeyi mashi kamar radiyon da bata da saiti ,lallai Omar zaiyi fama,
"Its okey,Kije ki amso mata breakfast É—inta yanzu ina jiranki "
"Toh,"ta amsa tare da fucewa daga cikin dakin

Xama yayi daga gefen gadon ,ya zuba mata waɗannan sexy eyes ɗin nashi yana kallonta,tsananin tausayinta ne ya kamashi, hannu yasa ya zame bargon data lullu6e half body dinta dashi,Still blue gown ɗin nan ce ajikinta,bata canza kayan jikinta ba,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,har baiso ya ƙyafta idanuwanshi daga kan fuskarta, hannu yakai saman side drawer inda ya ajiye ledar allurorin nata tare da magungunanta,shaf shaf Ya ɗura ruwan allurar acikin syringe,so yake ya tayar da ita daga baccin amma ya kasa,Saboda baison Ya katse mata shi,don ya lura da yadda take yinshi cikin kwanciyar hankali,

Ajiye injection ɗin yayi sama drawer din,slowly yakai hannu yana ƙoƙarin shafa wuyanta,Hosana ta banko ƙopar ɗakin hannunta ɗauke da tray,A firgice Sehrish ta farka,Tana kokarin mikewa zaune,duk ta rikice,har yanzu bata daina jin fargababa,
"Reesh are u okey,"?jin muryarshi yasa ta mayar da eye balls ɗinta akanshi,koda suka haɗa ido lokaci guda Ta ɗaure fuskarta tamau babu annuri ko misƙala zarratin,janye idanuwanta tayi daga kan fuskarshi,hankalinshi ya ɗan tashi da ganin irin kallon da tayi mashi mai cike da tsantsar tsana,kuma wani abu daya ɗaure mashi kai lokacin da suka haɗa ido,Sai yaga tana gyara wuyan rigarta,saboda ƙirjinta daya fito sosai,kamar taga wani wanda ba muharraminta ba,Tashin sense,
Chapter 187 · 0% Book details