Sashe 150
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yana cikin zancen zucin nan,Ya fara Jin numfashin Sehrish dake fita da ƙarfi da ƙarfi,Da sauri Ya koma gefen gadon Ya zauna yana kallonta,A hankali ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci,biji biji ta fara ganinshi,har sai da ta sanya hannunta saman fuskarta tana mutsustsuka idanuwan tukunna ta samu damar ganin shi da kyau,kwata kwata Jikinta babu ƙwari daƙyar ta samu ta miƙe zaune,Ciwo na yini ɗaya amma duk ta rame,idanuwanta duk sun faɗa,lips dinta sun dan kumbura,jikinta sai kerma yake Yi,
"How was ur body"?yayi tambayar Yana kallon Clavicle É—inta,
Shuru bata bashi amsa ba,Sai dai zuba mashi ido da tayi tana kallonshi,Sake maimaita mata yayi"Ya jikin naki,"nan ma shiru bata bashi amsa ba,Cike da mamaki yace"Baki ji ina magana ba"
 Tunawa da ciwon bakinta ne yasa shi yin shiru,don yasan bazata iya magana ba sai a hankali,
 "If u can't talk to me,zaki iya yi mun alama ta yarda zan fahimci abunda ke damunki,"
Lumshe idanuwanta tayi tare da buÉ—esu a hankali
 "Are u hungry"?.
Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a,ba don taso ba,ita kaɗai tasan halin da take ciki,Ga matsiyaciyar yunwa tana ji amma fargabar abunda zata ƙara gani acikin abincinta take ji,
 Moving yayi kusa da ita,tare da sanya tafin hannunshi ya ruƙo kanta,A saman ƙirjinshi ya kwantar da ita,nan take taji natsuwa ta zo mata,hawaye ne suka soma zarya akan fuskarta,taso ace zata iya buɗe baki ta sanar dashi ainihin abunda ke damunta amma ta kasa,harshenta Ya raunata sosai,magana ma wuya take yi mata,
Shafa sumar kanta ya soma yi har izuwa tsakiyar bayanta,sosai ta manne mashi tana shaƙar kamshin jikinshi,
 "I really worried about it,pls Tell me what scared you?meyasa kike firgita"?
 Yayi maganar tare da mayar da hannunshi saitin zuciyarta dake ta bugawa da ƙarfi da ƙarfi,tunda ya aza hannun kuma sai heartbeat ɗin nata ya dai daita,
 Ƙanƙameshi tayi sosai,tana ji aranta kamar bazata rayu ba,tun da ta fara wannan ƴan gane ganen na tashin hankali,
 Waist ɗinta Ya ruƙo tare da Janyeta daga jikinshi,Miƙa hannunshi yayi gaban drawer chest,Ya curo biro tare da jotter,
 Miƙa mata yayi tasa hannu biyu ta kar6a
 "Ki rubutamun duk wani abu dake damunki anan,"
 Hannunta na kerma ta buɗe empty page ta soma rubutu,bayan ta kammala ta miƙa mashi jotter ɗin
 Hannu yasa ya kar6a yana karantawa
_Oumma tasan komai,Ka tambayeta zata faÉ—a maka abunda ke damuna_
Wannan shi ne abunda Sehrish ta rubuta mashi,
É—agowa yayi tare da kallonta suka haÉ—a ido,hannu ya zura cikin front pocket É—insa Ya zaro wayarshi,Nan take ya kira Fawan ya sanar dashi cewa Ya kira Mashi Oummansu,
Miƙewa Yayi ya nufi cikin ɗakin,sai gashi ya dawo sanye da sleeping dress ɗinshi riga da wando Maroon colour,Gefen gadon Ya koma ya zauna yana jiran zuwan Abu,
Kusan 15 mins,Abu tayi sallama a ƙopar ɗakin,
 "Assalamu alaikum,"
"Wa'alaikum salam,"ya amsa mata tare da bata izinin shiga daga ciki,
Tana sanye da hijab ajikinta,Tunkan ta ƙarasa Sgr ya mike tare da janyo mata chair ɗin dake gaban dressing mirror ɗinshi ya ajiye mata ita,Tunda ta shigo ɗakin idonta ke akan Sehrish,Ba ƙaramin daɗi taji ba da sehrish ta farka,da alama jikin nata da sauki duk da akwai sauran ciwo atattare da ita,
 "Ya jikin naki"?tayi tambayar bayan ta zauna,shiru Sehrish bata ce uffan ba,Hakan yasa ta ɗan tashi hankalinta,
 "Kada ki damu,ba zata iya magana a yanzu ba,saboda raunin dake abakinta,
 Ajiyar zuciya abu ta sauke kafin tace"Allah ya baki lafiya,"
"Ameen"ya amsa mata amadadin Sehrish É—in,don ita sai dai ta É—aga kai,
gaisar da ita Sgr yayi cikin girmamawa,ta amsa mashi fuskarta asake,
"Inaso ki faÉ—amun meke damunta ne"?
Buɗe baki abu tayi zata yi magana kenan taji anshaƙe mata maƙoshinta,runtse idanuwanta tayi tana ambaton Sunan Allah acikin Zuciyarta,
"Be calm and answer me pls"Ya faɗi hakan ne don Ya lura tamkar bata a cikin natsuwarta,Sehrish kuwa hankalinta ya tashi ganin Oummansu ta kasa buɗe baki tayi magana,tuni idanuwanta sun cicciko da ƙwalla,
Wasu addu'oi abu ta shiga jerowa acikin bakinta,da ƙarfi da ƙarfi,bata daina ba har sai da Maƙoshinta Ya buɗe,nan take zufa ta wanke mata fuskarta,miƙewa Sgr yayi cikin sauri ya shiga palour,within secs ya dawo hannunshi ɗauke da bottle water,zama yayi tare da cire murfin ya miƙa ma Abu,hannu biyu tasa ta kar6a,kusan rabin ruwan ta shanye,janye robar tayi daga bakinta,har lokacin tana cigaba da karanto addu'o'in neman tsari a wurin ubangiji don ta gane cewa so ake a hanata magana,gashi ita kuma gwana ce wurin yin ibada, da kuma yin azkhar da sauransu,zaiyi wuya sihiri ya kama irinsu wani lokacin sai dai suci wahala,
Lokacin da taji zata iya magana,da sauri ta soma bayyana mashi halin da sehrish ke ciki"tun jiya da ta shiga ɗakin Azmee bata ƙara samun natsuwa ba,ta sanar dani cewa tana ƴan gane gane,wasu abubuwa nayi mata gizau,kamar ɗazu da safe lokacin da muke cin abinci,Sehrish ta dinga sambatu tana faɗin tsutsotsi ne acikin plate ɗinta,har tayi wurgi da plate ɗin ta watsa da gudu ta shiga ɗaki,wannan ne silar data rikice ta shige toilet tana wanke bakinta da Omo da soso,kamar yarda ka gani....."
Dakatawa ta ɗan yi da yin maganar tana faman sauke ajiyar zuciya,Sehrish sai murmushi take yi farin ciki kamar ta miƙe ta rungume Oummansu,
Shiru Sgr yayi yana kallonta yayin da yake nazarin wani abu acikin brain dinshi,bakomai ya faÉ—o mashi arai ba face daren jiya da Sehrish tazo É—akinshi ta tsorata harta yi wurgi da plate É—in hannunta,tana fadin Ya rafayet maciji kunama zasu harbeka,anan ya gane cewa Bayan ta fito daga É—akin Azmee ne ta shigo É—akinshi,
Jinjina kanshi ya É—an yi tare da cewa"Kina Zargin Azmee"?
Da sauri abu ta É—aga mashi kai Alamar eh,
"Meyasa kike zarginta"?
"Saboda na santa,lokacin dana haifi su Sehrish,Itace Ƴar uwar sayyadi wadda tazo yi mun wankan jego,"
Tunkan takai ƙarshen maganar Sgr yace"Kenan ita ƴar uwar shi ce?",
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,murmushin takaici Sgr ya saki,
Yana ƙoƙarin buɗe baki ya kuma tambayarta,Yaji Sehrish ta ruƙo hannunshi,da sauri yakai idonshi wurinta,
Da hannu ta dinga yi mashi Alamar ya miƙo mata jotter dinnan zata yi rubutu,
Hannu yasa ya dauki jotter É—in tare da mika mata,dama biron na hannunta,
Zane yaga tana yi maimakon rubutu bayan ta kammala ta mika mashi jotter É—in,
Hannu yasa ya kar6a tare da kallon abunda ta zana,Zobe ne ta zana,bai gane me take nufi ba,
"Zan iya ganin me ta rubuta?"abu ce tayi tambayar,
Miƙa mata jotter din
Yayi tasa hannu ta kar6a,koda abu taga zanen sai ta tuna da binciken da Sehrish ke yi dangane da Junaid,dayake ta bata labarin mutuwarshi,baiwar Allah tana so tayi mashi maganar Junaid É—in ta kasa,Gashi ita kuma abun ta manta bata sanar dashi ba,
"Kin gane me take nufi"?
Jinjina kai abu tayi kafin ta ɗaura da bayani"Ta sanar dani komai daya faru dangane da mutuwar ƙaninku Junaid!"tunda sgr yaji ta ambaci junaid,hankalinshi gaba ɗaya ya koma kanta,
"Akwai wata rana da ta shiga ɗakin Azmee,zatayi sallah tana ƙoƙarin ɗauko hijabi acikin wardrobe ɗin ita azmeen,Sai ga zoben ƙaninku na Diamond ya faɗo daga cikin wardrobe ɗin,A binciken da sehrish tayi ta gano cewa tare da zoben nan Shi Yaron ya fita aranar da al'amarin ya faru kuma abun mamaki Zoben nan nashi baiyi komai ba!babu alamar wuta taci shi!"
Gaban Sgr ne ya faɗi rasss!ya ware idanuwanshi gaba ɗayansu,Abun ba ƙaramin girgiza shi Yayi ba,jikinshi har kerma yake yi,aruɗe yace"Taya akai Ita reesh ɗin tasan cewa tare da zoben Ya fita aranar'?
"Ta hanyar hotunan da suka É—auka tare da Junaid a wayar Jahad,"
A hanzarce Sgr ya É—auki wayarshi tare da dannawa Fawan kira,tana fara ringing ya É—aga kiran,
"Fawan Am sorry na takura ka ko"?
On ther hand fawan yace"A'a babban Yaya,baka takuramin ba,"
"Idan kana kusa,pls inaso ka kira mun Jahad,ka sanar da ita cewa tazo mun tare da wayarta da kuma wayar Sehrish ina buƙatar ganinsu,"
"Toh babban Yaya"yana kai ƙarshen maganar ya ajiye wayar,zuciyarshi sai faman tafarfasa take yi,ita kanta daurewa kawai takeyi saboda maƙoshinta da ake ƙoƙarin shaƙewa ta dage sai ta faɗi gaskiya,koda kuwa Rai zaiyi halinsa,