← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 212

Sashe 194

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Omar dake zaune gefen gadonshi sai faman sakin murmushi yake yi,yayin da yake kallonshi,
  "Kasan Allah duk macen data mallake ka ba ƙaramar me sa'a bace,cos you're expensive,komai naka Extraordinary ne,wlh mace koda Ilminta koda kyanta koda arzikinta sai da rabonta,"Sai faman zuzutashi Omar yake yi,Shidai baice mashi uffan ba,a hankali yakai hannu tare da ɗaukar turaren nan nashi,Yabi ko'ina na jikinshi ya feshe,
  "just ka bayyana mata irin son da kake yi mata,ka ƙaddara cewa yau zaka fara dating......"
  Slowly ya juya gefe tare da kallon Omar"how can i do that"?
  "Ni zan koya maka,"
Girgiza kai yayi,Omar kasan ban iya soyayya ba,'
  Matsalarka kenan,tunda baka iyaba ka bari in koya mata,natsuwa sgr yayi yana sauraronshi
  "Kece sanyin idaniyata,bana iya runtsawa in bakya a kusa dani....."
  Kwata kwata Sgr baya fahimtar abunda Omar ke koya mashi,
  "Na lura baka fahimtata,Zamuyi amfani da bluetooth,zaka manna shi a kunnanka,Idan kaje wurinta,zan dinga karanto maka,kai kuma kana faɗa mata,haka yayi"?
  Ɗaga mashi kai yayi"yeah,i can try it,
 
[3/19, 2:58 PM] +234 810 388 4440: _💋The father Of Soldiers💋_

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Story
&
Written
by
*_Boss Bature_*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

Dedicated to my beloved sisters. 😍

Proud Of My First Novel💋

_Warning banyarda wani yayi amfani da wani sashe na littafina ba, kada a ta6amin komai na littafina,Sannan kar a kuskura a haɗamun document,Ga mai buƙatar karanta Littafin Abban Sojoji from Book one to 3 yayi mun magana ta whatsapp 08103884440_

Canza ra'ayi yayi"Omar,bana buƙatar using the bluetooth Just komai ya dace ka sanar da ni,"
Murmushi Omar ya ɗan saki don yasan cewa Sgr zai iya,A nan ya shiga kwatanta mashi yadda zai bayyanar da Soyayyarshi,bayan Ya Kammala Sgr yace"thanks,sai nadawo,"yakai ƙarshen maganar tare da juyawa ya nufi hanyar fita ɗakin,Yana jiyo muryar Omar Yana faɗin"Wish u all the best,"

A lokacin Sehrish tana zaune ta tasa abincin da Aunty Azeema ta haɗa mata sai ci take yi,bayan ta kammala ta yagi tissue tana goge bakinta,A dai dai wannan Lokacin taji an turo ƙopar ɗakin,dakatawa tayi tana jiran ganin mai shigowar,Natsuwa tayi tana shaƙar daddaɗan kamshin turaren dake kai ma hancinta ziyara,tunkafin ma Ya shigo ƙamshin jikinshi ya gauraye ɗakin saƙo da lugu,

A hankali ya sako ƙafarshi kafin ya ƙarasa shigowa ciki,Har sai da gabanta ya faɗi rass,Saboda razana da tayi da kyawun da Sgr yayi,Kayan hausawa ba ƙaramin kyau suke yi mashi ba,yadda kasan danshi kamfanin shadda suke ƙerata,cikakkiyar surar jikin nan nashi ta ƙara fito da kyan shaddar,
Tunda ya ɗaura idanuwanshi akanta,gaba ɗaya wankanta ya tafi da imaninshi,natsuwa yayi yana kallonta,from head to toe,Atampar jikinta ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,Ya kasa kawar da idanuwanshi kamar yadda itama take Kallonshi,

Sallama yayi mata cikin sanyin Murya ta amsa mashi,kafin ya ƙarasa shiga ciki,gefen gadon ya zauna dab da ita,tuni kasala ta fara baibaye kowannansu,

Almost 15 mins,tsit kake ji ba wanda yace uffan acikinsu,Ajiyar Zuciya ya É—an sauke kafin Ya soma magana,
  "Ya jikinki?"A hankali tace"da sauki" jinjina kai yayi yana cigaba da kallonta,hakan yasa ta Sunkuyar da kanta tana kallon hannuwanta,

"Reesh,nasan nayi maki laifi wanda yasa kika juyamun baya,But Why can't u forgive me?komai ya wuce mana,Idan har bana ƙaunarki serious bazan kulaki ba,kuma abunda ya faru,duk don saboda ƙaunar da nake yi maki ne,Naji fargabar su rabani dake,I thought yi maki hakan da nayi will be the solution,sai dai nayi mistake na kusantarki a lokacin da nake cikin fushi,wanda duk Iyayenmu ne suka jawo hakan,"ya ɗan dakata da yin maganar Yana mayar da numfashi,jin yayi shiru yasa ta dago,yayin da idanuwansu ke kallon cikin na Juna,
  "Ina neman alfarma a wurinki,For the Last time,ki bani dama,zan gyara kuskure na,Zan canza maki kamar yarda kikeso,"
  Jikinta ya ɗanyi sanyi da jin kalamansa,Amma still tana kokwanto akanshi,gani take kamar Sgr bazai ta6a sonta don Allah ba,sai don ya mayar da ita abun biyan buƙatarshi kamar yadda ya saba yi mata,Zurfin tunani ta shiga,ba zato ba tsammani,taji ya ruko hannuwanta Acikin nashi,sosai ya ruƙe hannun yana shafa lallausar fatar hannun,a hankali ya fara matsawa yana niyyar rumgumeta....
  "Reesh,I've Fallen for you......   "Tunkan yakai ƙarshen Maganar,Rai a matuƙar 6ace Sehrish Ta ƙwace hannunta daga nashi tare da yin wurgi da hannunsa ta dan ja baya,Abunda bai ta6a tsammani ba,Waro idanuwanshi yayi waje yana kallonta,
  A fusace take magana"Wlh ba sona kake yi ba don Allah,Ni nasani don kawai biyan buƙatarka yasa kake so naci gaba da kasancewa dakai,idan har dagaske kana sona,Meyasa tuntuni baka sanar dasu cewa kana sona ka maida ni matarka ba,kuma tun farko kayi accepting aurena don kawai naci gaba da yi maka Aiki,Saboda kafi ƙarfin kayi soyayya dani,bankai matsayin da zan zama Matarka.....     "Kasa ƙarasa Maganar tayi sakamakon gigitacciyar tsawar da Sgr ya daka mata,A firgice ta zazzare idanuwanta tana kallonshi,tuni idanuwanshi sun Canza launi sosai,Ranshi yayi Mugun 6aci,Zuciyarshi ta hasala,har ya ɗaga yatsu biyar cuf zai wanka mata mari,Ta fashe da matsanancin kuka,Ta dinga ja da baya har ta ƙurewa kan gadon,ta runtse idanuwanta sosai,'

Yarfar da hannun gefe yayi,wani irin raɗaɗi yake ji acikin zuciyarshi,tuni idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla,takaicin Duniya ya ishe shi,ƙaramar yarinya kamar wannan ce take gaya mashi Magana,gudun kada ya karya ƙasusuwan jikinta ne Yasa yayi saurin miƙewa da saurin gaske har yana tuntu6e ya fuce daga ɗakin,A makance yake tafiya Allah yaso babu kowa a babban falon,A zafafe ya nufi twin stairs ɗin Ya haye,yana taka staircases ɗin wasu Zafafan hawaye suka wanke mashi fuskarshi masu ɗumin gaske,har wani zazza6i yake ji ajikinshi,Sehrish ta hasala shi sosai,

Yana shiga Bedroom Yasa hannu Ya tu6e rigar jikinshi yayi wurgi da ita ƙasa,A haukace Yakai hannu Ya damƙi bedsheet din gadon Ya yayeshi tare da Jefar dashi gefe guda,Dunƙule hannunshi Yayi da ƙarfin gaske Ya naushi Dressing Mirror ɗinshi,gaba ɗaya madubin ya farfashe ya zube,hatta hannunshi sai da glass din ya faffasashi,jini ya shiga tsastsafowa,raɗaɗin da yake ji a hannunshi bai kai raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi ba,lokacin da Sehrish ke faɗa mashi wannan maganganun,Biji biji ya fara gani acikin idanuwanshi,Jiri ya soma ɗaukarshi,tangal tangal yayi zai faɗi,kaitsaye ya faɗa saman gadonshi,numfashin shi na fita da wani irin huci,ga wani matsanancin ciwon kai daya farmasa,

Wuraren ƙarfe 12 na dare,Omar ya faɗo part ɗinsa,fuskarshi ɗauke da Murmushi,Yazo cike da sa ran sunyi nasara,Tun a palour Yake ƙwala mashi kira"Bro!bro!"shiru ba Amsa,har yayi tunanin ko bai kaiga dawowa bane,Acikin ransa har yana cewa"Yanzu haka yana can manne da ita suna shan Soyayya,"ya ƙarasa zancen zucin yana kokarin juyawa kwatsam Idanuwanshui suka sauka akan Agogon Diamond ɗin Sgr,dake yashe a ƙasan tiles,
  Har sai da gabanshi ya faɗi,don yasan cewa ba ƙaramin abu bane zaisa Sgr ya yarda watch dinsa ba,zuƙunnawa Omar yayi tare dakai hannu ya ɗauki wrist watch ɗin,A fili Ya ambaci Sunanshi Rafayet,Da gudun gaske Omar Ya faɗa bedroom ɗinshi,A kwance ya samu Sgr tamkar baya numfashi,hankalinshi yayi Mugun tashi,A sukwane ya haye saman gadon saitin fuskar Sgr,hannu yasa yana shafa fuskarshi"Rafayet meya faru dakai?Meyasa kayi hakan?duk ka hargitsa ɗakin ka fasa glass,"ɗago da kanshi yayi tare da ɗaurashi saman laps ɗinshi,Omar sarkin tausayi tuni idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla,
  Muryarshi na kerma yace"Dan Allah Rafayet ka fadamun meya faru da kaine?nashiga damuwa sosai pls....."tuni hawayen fuskarshi sun soma sauka saman fuskar Sgr,

Sai lokacin Sgr Ya yunƙura tare da miƙewa daga zaune,yana faman fitar da huci,
  "Omar,Reesh batasona,She hates me completely,i can see dat in her eyes,danasan zata ci mutuncina haka da banje ba,nafi ƙarfin wulaƙancin mace,Saboda Allah ya jarabce ni da son ta shiyasa har take ƙoƙarin gaya mun magana".....Ya ɗan dakata da yin maganar,Omar ya kasa kunne yana sauraronshi,.
  "tana tunanin cewa Jikinta nakeso!Me take dashi?Mata nawa ne suka sha kawomin kansu wanda suka fita komai don kawai nayi lalata dasu,Amma banta6a kula ɗaya daga cikinsu ba,sai ita da Allah ya bata dama?
Jinjina kanshi ya ɗanyi kafin yaci gaba da cewa"As a Surgeon General,I stoop too low don kawai inason cigaba da rayuwa da ita,wata ƴar ƙarama da ita,if not love dat's Crazy me zanyi da ita.........."tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,
  "Itace mutun na farko da ta fara sani zubar da ruwan hawayena,"
  Jikin Omar ba ƙaramin sanyi yayi ba,Hannu Yasa tare da janyoshi jikinshi lallashinshi ya shiga yi,Yana tausarshi,
 
"Omar,dama kadaina Wahalar da kanka,Na yanke shawarar gobe zan tafi U.s,"
  "Dan Allah Rafayet mubi komai a sannu,Ni nasan cewa tana sonka,zata sauko ne,amma tafiya U.s will not be a Solution,"
  "Na riga na yanke shawara Omar,i will distance Myself from her,nasan hakan zai sa nasamu kwanciyar hankali in na daina ganinta,So Zan tafi kawai first thing tomorrow Morning",
  Shiru Omar yayi,don kuwa yasan Sgr bazai canza ra'ayinshi na tafiya ba,
"Shikenan,bazan hanaka tafiya ba,bari na taimaka maka,Hannunka yana bleeding,"
  Girgiza kai yayi"a'a,kabarshi kawai,"yana faɗin hakan ya sauko daga saman gadon Ya nufi toilet ɗinsa Ya shige,

Saukowa Omar yayi daga saman gadon,Ranshi ya 6aci sosai baiji daÉ—in abunda Sehrish ta yiwa Sgr ba,bai ta6a tunanin zata Iya furta mashi waÉ—annan kalaman ba,

Gyara mashi Bedroom É—in ya tsaya yi,Sai da ya kwashe glass É—in daya zube duka ya kawar da komai,kafin Ya sauko Downstairs Ya nufi Medical Room É—insu,P.A box ya É—auko Kafin Ya koma up part É—in Sgr,Ya ajiye mashi asaman gadonshi don yayi dressing É—in hannunshi,
Chapter 194 · 0% Book details