← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 212

Sashe 52

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wannan surutan da Abbansu ke yi kaf a kunnan sgr,wanda ke zaune saman front chair na dressing mirror ɗinshi,ya kifa kanshi asaman Dressing mirror,gaba ɗaya sumar kanshi ta rufe mashi side by side na fuskarshi,zuciyarshi ba ƙaramin tafarfasa take mashi ba,ranshi yayi mugun 6aci wai har shi zai bada Command aƙi bin umarninsa?bakowa yafi ji ma haushi ba fa ce Uncle ɗin nasu,don me zaiyi iko da Sehrish?saboda kawai ya haifeta?wani irin huci ne ke fita akanshi tabbas sai ya nemi matsayin dake asama dana mahaifinta ba don komai ba sai don yayi iko da ita,akan idon mahaifinta kuma,
  Yana cikin yin wannan zancen zucin yaji Muryar Abbansu kamar ta wanda yasha giya,saurarawa yayi yana sauraron waƙar da Abbansu ke rera masa daga waje,tun yana yaro idan aka 6ata mashi rai,ya fusata da gudu yake shiga bedroom ɗinsa ya rufe ƙopa,idan abbansu naso ya sauko daga fushin da yake yi sai yazo ƙopar ɗakinshi yana kwankwasawa yana raira masa waƙa,cikin ƙankanin lokaci yake saukowa daga wannan fushin,
  Jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba,ɗan ɗagowa yayi da kanshi ya wurga eyes ɗinshi kan agogon bangon dake a manne ƙarfe kusan ɗaya na dare,Abbansu na waje yaƙi tafiya,kuma in har bai buɗe mashi ƙopar nan ba,to anan wurin zai kwana,saboda ya ta6a yi mashi haka,miƙewa yayi jikin shi babu ƙwari ya ƙarasa tare da jan ƙopar ya buɗe mashi,jin an buɗe ƙopar yasa Abbansu miƙewa jiki na rawa,suna haɗa ido da sgr,yasa hannunshi a idanunshi yana yi mashi kukan ƙarya wai ya barshi a waje,sanyi ya bugeshi,hakan da yayi ba ƙaramin dariya yaso ya ba Sgr ba,
    Juyawa Sgr yayi tare da shigewa cikin bedroom ɗin,abban yabi bayanshi,a gefen gadon suka zauna suna fuskantar juna,
  "Yanzu faɗamun,me yake damunka"?
Shiru ya ɗanyi tamkar bazai tanka masa ba,daƙyar ya iya buɗe bakinshi yace"Abba,Uncle ya gama dani!har ni zan ba yarinyar can Umarni,ya hanata,don kawai yana taƙamar cewar shi mahaifinta ne"?yana magana muryarshi na shaƙewa saboda tsabar 6acin rai,
"Rafayet!ni bansan me zance maka ba,ka san dai inason farin cikinka,duk wani abu da kake so ni mai iya yi maka shi ne,amma banda wannan!zan iya iko da Abusufyan amma bazan iya iko da Æ´arsa ba,shi mahaifinta ne dole tabi Umarninsa tayi mashi biyayya,bijire mashi zai iya sa ta fuskanci matsala arayuwarta....."
Bai ƙarasa maganar ba Sgr yace"That means ba wanda ya isa yayi iko da ita sai shi kawai?kenan Ni bani da wani matsayi a wurinta?bamu isa mu sata abu ba tayi kenan?
Jinjina kai abbansu yayi tare da cewa"Hakane!maganar gaskiya babu wanda ya isa yayi iko da ita a halin yanzu bayan mahaifiyarta sai kuma shi"
"Abba babu wani sama dasu wanda zai iya iko da ita fiye da mahaifanta"?yayi maganar ranshi a É—an 6ace yana kallon Abban nasu,
Gyara zama abbansu yayi,fuskar nan tashi É—auke da wani 6oyayyen murmushi yace"duk duniyar nan bayansu mutun É—aya ne!wanda zai iya yin iko da ita,fiye da iyayenta!'
"Wanene shi"?ya tambaya Yana jiran jin amsar da Abban nasu zai bashi,
"MIJINTA,shine wanda zai iya yin iko da ita fiye da iyayenta!Mahaifinta zai iya kiranta tazo gida mijinta ya hana,kuma dole ta hanu,ko tana so ko bataso,"
Hannu Sgr yasa tare da dafe gefen kanshi,yana faman sauke ajiyar zuciya,muryarshi ƙasa kasa yace"Abba!babu wata hanyar sai wannan"?
Jinjina kai Abbansu yayi tare da cewa"that's the Only solution,"!
Ya ƙarasa maganar yana kallon fuskar SGR,Acikin zuciyarshi kuwa Allah Allah yake akan ya amince zai auretan,Shikenan burinshi zai cika ganin cewa Rafayet yayi aure,
"She's too young for me,Ni bazan iya auren yarinyar da ko Secondry school bata kammala ba,wannan abun kunya ne agare ni,da matsayi na in aureta?da wani ido duniya zata kalleni"?
Zuru Abbansu yayi yana sauraronshi,wato Sgr har yanzu yana nan da wannan ji da kan nashi,
Hannu Abbansu yasa tare da dafa shoulder É—inshi sannan yace"Rafayet!nima ban goyi bayan hakan ba!idan har ka aureta girmanka zai faÉ—i ne!Amma ga wata shawara"?
É—an É—agowa yayi da idanunshi masu É—auke da bacci ya kalli abban nasu"Wane shawara ne wannan"?muryarshi a akasalance yayi maganar,
Abba yace"Me zai hana kuyi auren yarjejeniya atsakaninka da ita yarinyar"?
"Kamarya kenan"?
Ƙayataccen murmushi Abbansu ya saki yana kallonshi kafin ya ɗaura da cewar"Wata nawa ya rage maku ku koma U.S"?
"Remain 3 Months,"ya bashi amsa,
Abba yace"Yawwa,before 3 months É—in nan su cika,me zai hana ka aureta,a matsayin Contract marriage,don tayi maka aiki kawai na tsawon wata uku,kamar yadda kake so da zarar time É—in ya cika,kawai saika bata divorce letter É—inta,Amma ya kake gani"?
Shiru Sgr ya É—an yi yana nazarin maganar Abban nasu,kafin yace"Abba bacci nake ji,i will think about it before tomorrow,"
"Ba damuwa,kafin gobe dae yakamata kayi tunanin abunda ya dace,zan jira jin amsarka da safe," ya ƙarasa maganar tare da juyawa ya fuce daga ɗakin nashi,
Blanket ɗinsa yaja ya lullu6e jikinshi har zuwa neck ɗinsa,maganar Abbansu ce ke tayi mashi yawo acikin kanshi,ga bacci yana ji amma yaƙi ɗaukarsa,sae faman juyi yake yi asaman gadon,tabbas in ya aureta zaici galaba akan Uncle ɗinsu Abusufyan,yana so ya dinga commanding ɗinta akan idon mahaifinta kuma ba yadda zaiyi dashi,na biyu kuma Yana so yarinyar taci gaba da aiki a ƙarkashin ikonshi,har zuwa lokacin da zai koma U.S!!idan har yana so hakan ya faru kenan dole sai ya aureta!?OMG!

"That could not be possible for me as a Surgeon General to marry a young girl who has not even finished her secondary school,"ya furta hakan tare da jan blanket dinsa ya rufe fuskarshi daƙyar bacci 6arawo yayi awon gaba dashi,

*Boss Bature*

Saukowa down abba yayi fuskar nan tashi É—auke da murmushi,anan ya samu abusufyan tsaye yana jiranshi,yana ganin ya tunkare shi,
  "Ina sehrish ɗin take ne"?
Abusufyan yace"Tun ɗazu ta wuce ɗakinsu,Nima kai nake jira muyi sallama kafin inje in kwanta,Amma ya kuka ƙare da rafayet ɗin?ina fata dai ya sauko daga fushin nan nashi"?
Fuskar abba ɗauke da murmushi yace"daƙyar na shawo kanshi,yanzu haka ma ya kwanta,sae kayi haƙuri da surukin naka,"
  Dariya abusufyan yayi kafin yace"ae ni bansan ya zamu ƙare da rafayet ba,lamarin ya fara bani tsoro,ƙoƙarin buguna fa yake yi ne?ahaka zan zama surukinsa?yana yi mun kallon tsaransa?Lokacin dana shiga ɗakin nasa samun shi nayi fa ya damƙi gashin kanta ya ɗaga ta sama kamar wata ƴar babyn Roba,yarinya sae kuka take tana bashi haƙuri amma ko ajikinshi,"
   Abba yace"Ae rafayet sae addu'a,amma abun nashi ƙara gaba yake yi,yana ji Da ƙarfin nan nasa,bakowa zai iya jure zama dashi ba," suna tafiya suna fira har suka zo ƙofar ɗakin Abba,anan su kayi sallama da abusufyan ya wuce nashi ɗakin,
   Fuskarshi a washe ya shiga ɗakin kamar ance ya ɗaga idanunshi karaf suka sauka akan Junaid dake baje saman gadon yana bacci,ga Mommynsa agefe,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,daga fitarsa har ya shigo ɗakinshi,Anya kuwa junaid shi kaɗai ne?yaro kamar mai iska,har leƙa ɗakinshi yayi ya same shi kwance yana sharar bacci shi da Talal,amma yanzu daga dawowarshi ya same shi a ɗakinshi,
  Cike da takaici ya shiga cikin ɗakin,gefen gadon ya zauna tare dasa hannu ya bubbugga ƙafarɗarshi""Junaid!junaid"! Da ƙarfi yake ambaton sunan nashi,yatsina fuska junaid ya shiga yi yana faɗin"Wai wanene ke son takuramin"!
  Yayi maganar yana ɗan ware idanunshi masu ɗauke da bacci,
  Harara abbansu yaa jefa mashi tare da cewa"Ubanka ne,buɗe idonka ka gani mara matunci" koda yaji muryar. abbansu sae ya ƙara tamke fuska,yana faman murguɗa masa baki,Abba yace "Eyyyeh!ni kake murguɗa ma baki," zumbura masa baki yayi,hada sa hannu ya toshe kunnuwansa don karma yaji muryar abban nasu,
 
"Nasan maganinka yaro"yayi maganar tare da kai hannunshi saman side drawer ya É—auko bottle water É—in dake ajiye a sama,buÉ—e murfin robar ya shiga yi yana faÉ—in"Zaka tashi ko saina watsa maka ruwan nan,"
  Wuri wuri yayi masa da ido,yana jira yaga in dagaske abban nasu ruwan zai watsa mashi,
  Jin yayi banza dashi yasa shi ɗebo ruwan a murfin robar,ya watsa masa shi da sanyinsa asaman fuskarshi,aikuwa a gigice ya tashi zaune jikin shi na kerma,hankalin abbansu ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yadda ya tsorata daga watsa mashi ruwa a fuska,abu kamar wasa sai ga junaid yana kuka hawaye jaga jaga a fuskarshi,
  Tsawa abbansu ya ɗan daka mashi tare da cewa"Yi mun shiri rigimamme kawai,"
  Wannan maganar da abbansu yayi ba ƙaramin ƙona mashi rai tayi ba,saukowa yayi daga saman gadon yana shassheƙar kuka yace""kuma Allah tunda ka kore ni,ɗakinsu sehrish zanje na kwana,"yayi maganar tare da bubbuga ƙafarshi ya fuce,
  Sakin baki abbansu yayi yana kallonshi har ya fuce daga ɗakin,girgiza kai kawai yayi tare da gyara kwanciyarshi,

Junaid kuwa bayan fitarshi daga ɗakin Abbansu,bedroom ɗinsu sehrish ya wuce kai tsaye,cikin sa'a ya samu ƙopar ɗakin a buɗe,hannu yasa ya tura door din,sannan ya shige ciki,

Sun cika gadon su uku abunsu,sae faman sharar bacci sukeyi banda mutun ɗaya wadda ta rufe idanunta tamkar maiyin bacci, gaba daya hosana ta yaye masu bargon da suka lullu6e dashi,dama ita bata iya kwanciyar bacci ba,zaiyi wuya ta kwanta batare da ta faɗo ƙasa ba,dalilin dayasa suke sanyata tsakiya kenan saboda gudun karta faɗo,sehrish na kwance a left hand,hosana tana a middle ɗinsu,yayin da jahad ke a right hand,saitin inda yake tsaye,hannu yasa tare da kashe masu hasken ɗakin da sehrish ta bari a kunne,lalla6awa yayi ya haye saman gadon,gefen jahad ya kwanta, tare da ja masu bargon ya lullu6esu duka,cikin ƙankanin lokaci bacci ya ɗaukeshi,tabbas Sehrish taji lokacin da aka kashe masu hasken ɗakinsu,amma batayi tunanin ta buɗe idanunta ba don taga wanene,saboda halin da ta shiga,Zuciyarta ba tayi mata daɗi ga hawaye sae faman shararowa suke yi daga cikin idanunta,babban abunda ke damunta shine wani hali sgr yake ciki?Yayi bacci ko idonshi biyu?bataso abunda ya faru ba,sai dae ba yadda ta iya dole tabi umarnin mahaifinta da wannan zancen zucin bacci ya sace ta,
tashin hankali,Junaid fa ya shige acikinsu sae faman sharar baccinsa yake,sun manne ma juna shi da jahad,duk a tunaninta sehrish ce,hada ƙara rungumoshi ajikinta,
Chapter 52 · 0% Book details