← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 208 OF 212

Sashe 208

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin tsami jikinta yayi mata,tamkar an jibga mata kayan wanki,cikin shessheƙar kuka take ambaton sunanshi"My Romeo,"har cikin kunnanshi yake jin kiran sunan domin kuwa yana a rungume da ita,yunƙurawa yayi tare da miƙewa zaune yasa hannuwanshi ya ɗauro Jahad saman laps ɗinshi,
  "Am really sorry......."
Girgiza mashi kai tayi"Jikina babu daÉ—i,ko'ina zafi,ka taimaka mun,"sam baisan me zaiyi mata ba,
  "Inason shiga toilet,ƙafafuna basu iya ɗaukata,"tana magana hawaye na wanke fuskarta,tsananin tausayinta ne ya kamashi,yayi tunanin zata rufeshi da faɗa,kota bijiremashi amma sae yaga akasin hakan roƙonshi ma takeyi akan ya taimaka mata,ganin tana kuka yasa shima ya fashe mata da kuka"Bansan ya zanyi ba jahad,bari na kira Abba in faɗa mashi"dayake shi ya koya mashi komai,
  A rikice ta dakatar dashi"Ni bance ka kira kowa ba,ka ɗaukeni ka kai ni toilet,Ni nasan me zanyi,"shi kanshi jikinshi ba ƙarfi wani irin zazza6ine ya rufeshi,saukowa yayi daga saman gadon,da ƙarfinshi na ƙarshe ya kinkimi Jahad yana faɗin"Ash!wash"yana tafiya yana tangal tangal zai faɗi a haka har ya shige toilet da ita,da taimakonshi ta gasa jikinta sosai da ruwan ɗumi,tallabota yayi suka fito daga toilet ɗin ya ɗaura mata towel,wuri ta samu saman front chair na mirror ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya,jikinta sae kerma yakeyi kamar wadda sanyi ya kama
Naɗe bedsheet din yayi ya ɗaukeshi,Ya dauko masu wani sabo ya shimfiɗashi,Kayan sanyi ya ɗauko mata farare na saƙa,Ya taimaka mata ta sanyasu ajikinta,sannan ya kamo hannunta ya taimaka mata ta kwanta saman gadon,Hada jan bargo ya lullu6e mata jikinta,
  Zuƙunnowa yayi saitin fuskarta"My Juliet am sorry,"yayi maganar tare da kama kunnuwanshi,idanuwanta cike tab da kwalla ta ɗago tana kallonshi,maimakon taji haushinshi,saima tsananin son shi da ƙaunarshi da ta ji,lumshe idanuwanta tayi a hankali kafin ta furta"kaje ka tsarkake jikinka,"amsa mata yayi da toh,ya miƙe a hanzarce ya nufi toilet,har ya kusa shiga ta kuma cewa"Kasan me zakayi"?
  "Eh Abba ya koya mun,"cizon le6enta tayi tare da cewa"Ya kyauta,"ƙarasa shiga kewayen yayi,tare da jan ƙopa ya rufe,

Baccine ya É—auketa mai daÉ—in gaske,sama sama taji motsinshi a É—akin,Shirin zuwa masallaci ya yi,jallabiya ya sanya ajikinshi,sai da ya fara zuwa saman gadon ya manna mata kiss asaman fuskarta tukunna ya fuce daga É—akin,

Lokacin da ya sauko downstairs haɗuwa sukayi da Sgr yana saukowa a gaggauce Shima jallabiyarce a jikinshi,da sauri Junaid ya ƙarasa ya rungumeshi,shafa sumar kanshi yayi"how are u my boy,hope u slept well,"
  "Am fine,Nayi missing dinka,Jiya bamu haɗu ba,"
   "Naji jikinka da zafi?Lafiyarka kuwa,"yayi maganar hannunshi akan wuyan junaid,"
  ɗagowa yayi daga jikinshi"Lafiyata Lou,". 
"Anya,idan muka dawo zan dubaka,"
  Ya ruƙo hannunshi suka nufi part ɗin Omar,a ƙopar palourn suka tsaya,Ya zura hannu aljihun jallabiyarshi Ya ɗauko wayarshi,Layin Omar ya kira,Tayi ringing har ta gaji ta katse,sake kira yayi almost 3 times amma ba'ayi picking ba,Ga time ɗin salla na shirin ƙure masu,shiga palourn suka yi atare da Junaid,A ƙopar shiga bedroom ɗin suka tsaya,bubbuga ƙopar yayi ba'a buɗe ba,duk hankalinsu ya tashi,Text message ne ya shigo wayar Sgr,duba saƙon yayi
  Bayan ya kammala karantawa Ya kalli Junaid,
   "Ka jiramu a main palour,"Amsa mashi yayi da toh kafin ya fuce,knocking ya kuma yi"Omar zo ka buɗe man ƙopa,"baijima da yin maganar ba Omar ya buɗe mashi ƙopar,daga shi sai short ajikinshi duk yabi ya ruɗe kusan irin haukan da Sgr yayi,bai 6oye mashi komai ba game da abunda ya faru,
Layin Dr É—insu ta cikin gida ya kira,dama saboda Su Jahad suka ajiyeta koda ace basu kusa in wani bai lafiya zata iya duba lafiyarshi tunda suna da Medical room acikin gidan,"
  shaf shaf Omar ya shiga toilet ya tsarkake jikinshi ya sanya Jallabiya,itama Hosana ya gyara mata jikinta,ya sanya mata rigarta,jim kaɗan Dr Jonet ta ƙaraso,already tazo da duk wani abu da zatayi amfani dashi wurin treatment ɗinta,daƙyar Sgr ya shawo kan Omar suka fito,sun bar Dr aciki tana dubata,Lokacin da suka sauko palour Junaid suka samu ya gyara kwanciyarshi saman 3 seater sai bacci yake yi,amma da alama baccin nashi baiyi nisa ba,tada shi yayi suka fito waje,Acikin motocinsu suka shiga,kafin suka nufi masallaci,

 [3/19, 9:44 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*

*💃LAIFIN DAƊI ƘAREWA💃*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Zazzafar haja daga Minjibir ventures,Ina masu buƙatar siyan kayan sallah Kada ku bari a baku Lafiya,Ga kaya na kece raini Na shiga tsara,Koda kudinka sai da rabonka,Kadan daga cikin abubuwan da muke siyarwa akwai Lace
Veils
Atamfa
Shoes
Bags

Address
Hotoro ladanai kan titin ring road
Chat 09126570345
Call 09136122503 saikun Zo💃💃💃💃

Tun bayan sallar Asuba sehrish ta koma bacci,ringing ɗin wayarta ya tayar da ita,lalubo wayar tayi ta duba me kiran nata,Murmushi tasaki ganin Sunan Oummansu Ya bayyana,Picking tayi ta kara wayar a kunnanta"Oumma ina kwana,kun tashi Lafiya,"ta yunƙura ta miƙe daga zaune,
On the other hand Oumma tace"Lafiyalou rishina,ina fata kuna cikin ƙoshin Lafiya,"
  "Alhamdulillah yanzu ma na tashi daga bacci,"_
"An samu hutu ko?Ae naga hotonanku,kunyi kyau sosai hutu ya zauna maku,"
Murmushi sehrish tasaki"Ina Daddy Oumma,nayi missing É—inku sosai"
  "Ya shiga toilet,nima nayi kewarku sosai,"
  "Yaushe zaku zo?
"Kinji ki da wata magana,daliline kawai zai kawo munan kinsan me nake nufi,"
  Murmushi sehrish tasaki"Allah ya kawo dalilin nan Oumma,i will keep praying har sai dalilin nan yazo,"
  tana jiyo dariyar Oummansu"ina Jahad ina Hosana,duk nayi trying Layinsu ba'a ɗaga ba,"
   "Ae yanzu basu isa su farka daga bacci ba,nima ringing ɗin wayarki ne ya tashe ni,kuma naji daɗi sosai,"
  "Ina surukin nawa yake"?
"Baidawo ba,tunda suka tafi sallar Asuba,Amma nasan suna akan hanya,"
  "Ki gashe mun dashi"
"Zaiji insha Allah,"
Shiru suka É—an yi kafin Oumma ta kuma cewa"Bansani ba,kowani ya faÉ—a maki,"
  A ƙagare tace"Mekenan Oumma?Banyi waya da kowa ba,babu wanda ya faɗamun"
   "To Albishirinki".
"Goro,"ta faÉ—i tana murmushi,
  "Surukarki ta musulunta"waro ido waje Sehrish tayi,tsabar farin ciki yasa ta duro daga saman gadon ta daka tsalle bakinta yaƙi rufuwa"wayyo Allah Oumma,Mommy ta musulunta"?
  Dariya abu tayi"Bayan tafiyarku,ta kar6i addinin musulunci,Nima a wurin Daddynku naji,Yanzu tace batason kowa ya dinga kiranta da Alexandra,Sunanta FATIMA,"wani irin farin cikine Ya lullu6e sehrish,
  "Amma na tayata Murna,baki ji irin farin cikin da nake ciki ba,"
  "Albishir ɗin bai ƙare ba,Akwai saura,"
  A ƙagare sehrish tace"Ina sauraranki Oumma,"
  "Ina wannan yayan naku"?aɗan ruɗe sehrish tace"Wanne daga ciki"?
   "Ɗan wurin Azmee"A ruɗe Sehrish tace"Ya haroon?Ya dawo?an ganshi?bari na maida Video Call,nan take ta canza kiran zuwa Video,A gaban window ta tsaya ta ɗaga wayar suna kallon juna,kwance Oummansu take asaman gadon dakinta na Gidan Abusufyan wanda su Jahad suka ta6a yin rayuwa aciki,jikinta sanye da kayan bacci,Hutu ya zauna mata yadda kasan baturiya dama jawur take,ta saki gashin kanta gefe da gefe,
  Sai faman murmushi suke sakarwa Juna,
  "Oumma faɗamun Ya Haroon Ya dawo"?
Jinjina mata kai Oumma tayi"Ya dawo tare da wannan yayan naku,Brigadier general Abuhaisam,Ashe Lokacin da Azmee taba shi kuɗi akan ya gudu yabar ƙasar saboda gudun kada a Yanke mashi hukunci,sun shirya mashi komai na tafiya,Shi kuma yaji bazai iya tafiya ba,Saboda Yana son Ya nemi yafiyarsu Abba,maimakon ya tafi sai ya wuce Jos gidan wani abokinshi ya fara sauka yayi jinya,kafin Bayan wani lokaci yaje gidan shi Abuhaisam din cikin mawuyacin hali,bai 6oye mashi komai ba game da abunda ya faru ya nuna masa yayi nadama,Haisam ya taimakeshi sosai don abunda haroon din bai sani ba shine, lokacin an riga anga Junaid kuma alokacin duk sun san cewa abunda haroon din yake yi ba yin kanshi bane,Shiya kaishi Asibiti yayi jinya sosai,Kafin aka sallamesu,a gidanshi yake kwana,Ko Lokacin da Irfan Ya rasu daya zo gida Baisanar da kowa game da haroon ba,har yazo Shagalin bikinsu Yousouf,duk Haroon Na'a wurinshi,Sai da yaji Labarin Abba na nemanshi,Tukunna Ya nuna yana son dawowa gida,Cikin satin nan suka yi mana zuwan bazata,baki ga yadda ya canza ba,Babu ruwanshi bawan Allah,

Tuni idanuwan Sehrish sun cicciko tab da ƙwalla,
  "Allah sarki Ya haroon,Na tausaya mashi sosai,Aunty azmee zata ji daɗi sosai,idan taji labarin dawowarshi,"
  "Daddynku ya sanar dani cewa Zasu rakashi can prison ɗin don ya gana da ita,"
  "Naji daɗi sosai,Oumma ki gaishe mun dashi,"
  "Aikuwa dai yana ta tambayarku,musamman ke,"
"Allah sarki,idan Allah ya kawo dalilin da zaku zo nan,Dan Allah atattaro kowa da kowa yazo,"
  Fashewa abu tayi da dariya,daga ita har sehrish ɗin kunya suke ji,Dalilin da suke nufi bakomai bane face Ciki,In sun haihu lokacin suna zasu zo America,"
"Kunyi waya Da mommy azeema ne"?girgiza kai sehrish tayi"a'a,tun jiya dai Da rana munyi waya da ita,
Oumma tace"Yau da safe ta Koma Lagos,Mijinta ya dawo,"
Waro ido Sehrish tayi irin mamakin nan"Dama Mommy Azeema tana da aure?"
Dariya abu tayi"Tana da aure mana,Mijinta business man ne,A dubai yake da zama,atare suke kasuwanci dashi,koda muka Je Yi maku siyayyan kayan lefenku,A gidanshi dake acan muka sauka,Mutumin kirkine Kamar ita haka yake,"
Murmushi sehrish tasaki"Allah Sarki,gaskiya zanso na ganshi mu haÉ—u,"

  Sun jima Suna waya har Daddynsu ya fito daga toilet ya kar6i wayar suka gaisa da Sehrish,kafin tayi masu sallama,tana kokarin ajiye wayar gaban mirror,Taji shigowarshi ɗakin,juyawa tayi tana kallonshi,
  "Ya rafayet"ƙarasawa yayi tare da janyota jikinshi yayi hugging ɗinta,bayan ya manna mata kiss a gefen fuskarta holding hands dinta yayi"inaso kije ki duba jikin Hosana,"aruɗe tace"me ya sameta"?
  "Ba wani abu bane,she's not feeling well,inaso ki ɗan lallasheta,"Jinjina mashi kai tayi,a hanzarce ta fuce daga ɗakin,Side bed ya zauna,tare da curo wayarshi ya kira layin Abbansu don su gaisa kamar yadda yasaba,duk safiyar Allah sai ya kira Iyayenshi da Surukanshi a waya ya gaishe dasu,
Chapter 208 · 0% Book details