Sashe 181
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saukowa yayi daga saman kujerar,Ya zuƙunna saman guiwowinshi agabanta,
Cikin sanyin murya ya soma magana"dan Allah ammi kiyi haƙuri,banaso nayi silar da hawayenki zasu fita,hakan zai ƙara jefa rayuwata cikin matsala,na tuba bazan ƙara ba,Komai kikeso wlh shi zanyi,yaya hossein...."ya ambaci sunanshi tare da mayar da idanuwanshi kanshi"Kayi haƙuri da abunda nace yayana nakaina,nasan kalamaina sun 6ata maka rai,zuciyata ce sam batayi mun daɗi,Nafi kowa sanin yadda kakeson Jini na..."duk yabi ya ruɗe,
   "Ka tashi ka koma ka zauna,inason magana daku,"miƙewa yayi jiki na rawa ya koma saman kujerar ya zauna,gwanin ban tausayi ammi ke kallonsu,
 "Kada ku bari son ya'ya yayi silar da zaku raba kanku,bana fatan hakan ya faru,Ban goyi bayan abunda Rafayet Ya aikata ma ƴar wurinka ba,Kuma ban goyi bayan kowannanku ba,dakai dashi,duk abunda ya faru Laifinku ne,Tunda ku kuka haɗa aurennasu,Sannan kuma kuka soma ƙoƙarin tursasa mashi akan ya sake ta,wanda silar hakan ne yasa shi Rafayet ɗin yayi mata aika aikar da yayi,maimakon daya nuna yana son Ya tafi da ita ku ƙyaleshi yayi rayuwarshi da matarshi,amma sai kuka matsa lamba akan ya saketa bacin kuma kunfi kowa sanin halinshi,Wannan shine kuskuren da kuka aikata......"
 Shiru ta ɗanyi tana kallon kowannansu,gaba ɗaya sun natsu suna sauraronta,cigaba da magana tayi"Abusufyan amadadin Rafayet ina mai baka haƙuri,tabbas ya cutar da ƴar wurinka,Abunda yayi sam bai kyauta ba bai sa hankali ba,Amma inaso ka sani,Duk yayi wannan ne saboda tsananin son da yake yi mata,Yana gudun ku rabashi da ita ne shiyasa ya yanke shawara ya aiwatar da hakan,A tunanin shi in yayi mata hakan ba zaku iya raba shi da ita ba,Sai dai kash ya tabka babban kuskure,Ya kusanceta a lokacin da yake cikin fushi,shi kanshi yanzu nasan yayi danasanin abunda ya aikata mata fiye da tunaninku,kuma duk yacce kuka kaiga jin ɗacin abunda ya aikata mata wlh baku kaishi ba,Yafi ku jin raɗaɗin abunda yayi mata acikin zuciyarshi,da ace da son ranshi yayi mata wlh bazai gudu da ita ba,Anan zai bar maku ita,Ya tafi yabar kasar,Ya zakuyi dashi?tayi tambayar tana kallonsu,duk jikinsu yayi sanyi,
 "Duk inda yake yanzu nasan cewa yana tare da ita,Kuma zai gyara 6arnar da yayi ne,Sannan inaso ku kwantar da hankalinku,in sha Allah zasu bayyana ne,kuma kudaina tunanin cewa ko ta rasa ranta ne,tana araye bi'iznillah,kuma zata ji sauƙi ta dawo kamar yadda take ada"sosai ammi tayi masu nasiha,duk ta kashe masu jikinsu,
 A ƙarshe tace"idan har Allah yasa Rafayet ya dawo da yarinyar nan,zan zaunar dasu agaban kowa zan tambayi ra'ayinsu,idan har duka suka amince zasu rayu da junansu,To bana so wani daga cikin ku ya ƙara tada maganar saki,Idan kuma har ita jikar tawa ta nuna cewa batason shi,Zanyi adalci atsakaninsu in raba auransu,'
Ajiyar zuciya kowannansu ya sauke,Abusufyan yace"In sha Allah,nima bazan ƙara tursasa mashi akan ya sake ta ba,"
Abba kuma yace"Duk hukuncin da kika yanke masu dai dai ne,mungode sosai da irin nasihar da kikayi mana,kuma in sha Allah,ba zaki ƙara jin kanmu ba,"
 "Allah yayi maku Albarka,Allah ya ƙara hada kan zuri'armu,"
Atare suka amsa mata da Ameen,
"Amma ammi,bansan ya zanyi da zainab ba"acewar Abusufyan
 "Kada ka damu,idan ta tambayeka akan Yarinyar,ka sanar da ita komai game da auran yarinyar,amma bance ka faɗa mata ainihin abunda ya faru ba game da abunda rafayet ya aikata mata,Idan kace mata Mijinta ya tafi da ita,Bazata damu ba,"
 Jinjina kai yayi"shikenan nagode sosai,Zan sanar da ita hakan,
   "Yanzu yakamata mu mayar da hankali wurin neman inda ya tafi da ita,",'
 "Zamuyi kokarin yin hakan,Yanzu haka Omar tun safe suke gararin nemansu acikin garin nan,Amma har yanzu shiru bamu ji daga gare shi ba,"Abba ne yayi magar,
 "Allah ya taimaka,zasu bayyana ne nasan zai dawo da ita ne"daga haka ta basu iznin tafiya,Miƙewa sukayi atare har sun kusa fita daga ɗakin,Ammi ta kuma kiran Abusufyan Dakatawa yayi tare da juyowa ya dawo wurinta,
 Dafa kafadarshi tayi"game da abunda ka yiwa yayanka,Ya tsaya mashi arai,yaji zafin abun har hawaye saida ya zubar akanka,sam banji daÉ—i ba daka buge mashi hannunshi don yana Æ™oÆ™arin dakatar dakai,kafi kowa sanin yadda Hossein ke tsananin sonka,yafi kowa son ganin farin cikinka,Bai kamata kayi silar shigarshi cikin damuwa ba,Idan kukayi hakuri komai mai wucewa ne,Wata rana sai dai muji ana É—aura auren jikokinku,".Â
 Murmushi Abusufyan yayi,cike da jin kunya ya sunnar dakanshi ƙasa,
 'Koda yake naji ƙishin ƙishin wurin azeema cewa kanaso ka maida auranku da Zainab,dagaske ne'?
 Hannu yasa tare da shafa ƙeyarshi,
Murmushi ammi tasaki"Allah yasa ina da rabon sake ganin wasu Ƴa'ƴan na Abusufyan,"ƙasa kasa ya amsa mata da Amin,
 Hannu tasa ta ɗan bugi kafaɗarshi"rasa kunya,wayace maka ana amsawa,da ace yayanka ne,Cikin zuciyarshi zai amsa mun,"dariya sosai Abusufyan yayi,
  ɗaure fuska ammi tayi"Nama tuna fushi nake dakai,Ni banji daɗin maganar da kayi ba,nacewa wai nafison Yayanka akanka,kasan irin yadda nake jinka acikin zuciyata"?tayi tambayar tana kallonshi,duk tana yin wannan ne don ta faranta mashi ranshi,ko hankalinshi ya kwanta yadaina sanya damuwa aranshi,
 "Kiyi hakuri mommyna,bazan ƙara ba,nima nace ne kawai,ba don ina nufin haka ba,bana jin daɗin zuciyata ne shiyasa harna furta hakan batare dana tauna maganarba,"
 Shafa sumar kanshi tayi"Allah yayi maka albarka,dan Allah ka sanyaya zuciyarka,Allah ya baka hakuri da juriyar cinye wannan jarabawar,'
 "Ameen ameen Ammina,"rungumeta yayi sosai ajikinshi,Yaji daɗin kalamanta,Daga bisani yayi mata sallama Ya futo daga ɗakin,
Yana kokarin shiga bedroom É—inshi,Muryar Abu ta katse mashi hanzarinshi,
 "Abban Jahad,"har sai da gabanshi ya fadi,A sukwane ya juyo yana kallonta,
 Jikinta na sanye da hijabi dogo,
Murmushin yaƙe yayi mata tare da cewa"Na'am Oummu Sehrish,"
 Murmushi itama ta sakar mashi,
Matsawa tayi kusa dashi"shiru har yanzu,Yayan sehrish bai dawo da ita ba ko"?tayi tambayar fuskarta É—auke da matsananciyar damuwa,
 "Waya faɗa maki haka"
"Jahad ce ta sanar dani É—azu,To naji shiru har yanzu basu dawo ba,duk nashiga damuwa,Gashi tabar wayarta agida,inason nasan a wani hali take ciki,"
 Bai bata amsa ba,sai da ya fara buɗe dakin ya nuna mata hanya"Mu shiga daga ciki,inason magana dake,"
Shiga ciki abu tayi yabi bayanta,Gefen gadonshi ya nuna mata"ki zauna,"
 Girgiza kai tayi"a'a,muyi maganar daga tsaye,inaso in koma ɗakine,
 "Ki kwantar da hankalinki,Ƴarki ko ince ƴarmu tana cikin ƙoshin Lafiya,Tana atare da yayanta kamar yadda Jahad ta sanar dake,
 Aruɗe abu tace"Dare fa yayi sosai,duk inda suka je ya isa ace yanzu sunyi tunanin dawowa gida,"
 "Shiyasa nace ki zauna muyi magana,akwai abunda nakeso in sanar dake,"jin haka yasa abu ta samu wuri ta zauna,tana kallonshi,daga can gefenta ya zauna suna fuskantar juna,
 "Nayi maki laifi bansanar dake ba,"
Cike da mamaki tace"Laifi kuma,na me kenan,"?
Daƙyar ya daure yace"naso na sanar dake amma halin da muka shiga a kwanakin baya yasa ban samu lokaci munyi magana dake ba",
Kasa kunne abu tayi tana sauraronshi,har ta ƙosa ya gaya mata,
 "Ina sauraronka,Ka sanar dani kawai,"
 "Sehrish tana da aure,"
Gabanta ne ya faÉ—i rass,A ruÉ—e ta maimaita abunda yace"Sehrish tana da aure?tun yaushe"?
 "Ina tunanin ya wuce wata hutu da yin aurenta,Ita da babban yayansu,Nasan kin gane shi,"
Abun yayi matuƙar bata mamaki,sai lokacin ta tuna da ranar nan da sehrish tayi jinya har ta kwana ɗakinshi,abun ya tsaya mata aranta ashe mijinta ne shi,zurfin tunani ta shiga,Abusufyan kuwa zuba mata ido yayi yana kallonta cike da fargabar amsar da zata bashi,
 Can yaga ta ɗan saki murmushin gefen fuska,
 "Ashe ina da suruki bansani ba,shine ba'a sanar dani bako"?tayi maganar tana harararshi,
 Ba ƙaramin daɗi abusufyan yaji ba,duk da halin da yake ciki,
 "am sorry,nasan nayi laifi amma yanzu na goge laifina tunda na sanar dake komai,"
"Hakane,naji dadi sosai,saboda na yaba da kyawun halinshi,Yana girmamani sosai"
 Kallonta kawai Abusufyan yake yi,acikin ranshi yace"da ace kinsan meya aikata ma ƴarki,da yanzu ba wannan zancen ake yi ba"a fili kuma yace"Ae abun alfahari ne shi,Mutumin kirki,yana da kyakkyawar zuciya,"
 "Yanzu kenan shiya tafi da ita,amma baka faɗamun inda suka je ba,kuma yaushe zasu dawo,"ba don yaso ba,Ya shiga shirga mata ƙarya,
 "Sun tafi kaduna ne,wani aiki ne yakai shi,Shine ya tafi da ita,Amma bai sanar dani lokacin da zasu dawo ba,"
 Jinjina kai Abu tayi"Allah ya dawo dasu lafiya,Har hankalina ya kwanta yanzu,Dama Hosana ta addabeni da tambayar ina Rishi ɗinsu take ne,Kaga yanzu na samu amsar da zan fada mata idan ta ƙara tambayata,"ta ƙarasa maganar tare da mikewa tsaye,
 Tashi yayi shima"mu je na rakaki ɗakin,Inaso na gansu,"
 "Kunya nake jifa,idan wani yaganmu atare fa?Kuma yanzu nasan sunyi bacci ma,"
 "Koda sunyi bacci nidai inason ganinsu,"duk yadda taso ta hanashi bin ta sai da yabita,Lokacin da suka shiga ɗakin A kwance ya samu jahad da hosana suna ta sharar bacci,tamkar ya fashe da kuka haka yaji,Saboda tunawa da halin da ƴar uwarsu take ciki,Yasan tana cikin mawuyacin hali,da ace sunsan halin da take ciki da baza suyi wannan baccin ba,Allah sarki,
Ya jima aÉ—akin yana kallonsu,Kafin yayi ma abu sallama Ya koma É—akinshi,
Aranar kowa yayi bacci banda waÉ—annan mutanan,Abba,Abusufyan,Omar,Da duk wanda Yaji abunda ya faru da Sehrish,Baccinsu ragagge ne,sun shiga damuwa sosai,
*Boss Bature*
Tun da sanyin safiyar,Wayar Mommy dake ajiye saman side drawer ta soma Ringing,can cikin bacci ta dinga jin ringing ɗin wayar,daƙyar ta iya buɗe idanuwanta saboda baccin da ke fusgarta,Mikewa tayi daga zaune,batasamu Abba acikin ɗakin ba tun da suka fita sallar asuba shida Junaid bai kaiga dawowa ba,
Hannu takai tare da É—aukar wayar,ta duba sunan mai kiran nata,Dr Harriet ce,É—aya daga cikin aminnanta wanda ke zaune a Nigeria,tayi mamakin ganin kiranta a irin wannan lokacin,don sun jima basu yi waya ba,