← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 212

Sashe 3

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cike da mamaki azmee tace"taya akai hakan ya faru?dama abusufyan ya ta6a aure ne kenan?
   Ataƙaice azeema ta bata labarin yadda abusufyan ya auri abu batare da saninsu ba,har suka samu ƙaruwar ƴan uku,'
  Wani irin farin cikine ya lullu6e azmee saboda tsabar farin ciki bakinta yaƙi rufuwa,
   "Jahad!dagaske ne abunda kunne na ke jiyo mun"?sehrish ce tayi maganar tana kallon jahad da tsananin mamaki,
  Murmushi jahad tayi ta jinjina mata kai alamar eh,ta ƙara da cewar"jiya duk baki a hayyacinki,abun farin cikin nan ya faru,Mun jima muna wahalar rayuwa ashe muna da dangi mai girma irin wannan bamu sani ba,cikin ikon Allah kuma sai gashi Allah ya haɗa mu dasu ta hanyar da bamuyi tsammani ba,ina tunanin addu'ar da muka jima munayi ne Allah ya kar6a mana,Ashe oumman mu sai da ta fara auren uncle ɗin su abusufyan sannan ta auri wannan fasiƙin mutumin sayyadi,da cikinmu ta shiga gidan shi........'
  Aruɗe sehrish tace"taya hakan zai yiwu?
  Hajiya azeema ce ta katse ta da cewar tabbas zancenta gaskiya ne sehrish!ku ƴa'ƴan ƙaninmu ne Abusufyan,sai da ya fara auren mahaifiyarku sannan Mugun mutumin nan daya ƙuntata rayuwarku ya aureta.......'gaba ɗaya hajiya azeema ta kwashe labarin rayuwar mahaifiyarsu agidan gwaggon katsina da kuma haɗuwarsu da abusufyan har izuwa rabuwar aurensu ta auri sayyadi ta sanar ma Sehrish,'
  tun kan takai ƙarshen labarin nata,Sehrish tayi sujjada,tana shessheƙar kuka,saboda tsabar farin ciki,Ashe ita ɗiyar uncle ɗinsu ce abusufyan?hakan na nufin su Babban yaya ƴan uwanta ne na jini!haba no wonder ae shaƙuwar dake tsakaninta da junaid tayi yawa,kai kana ganin abun zakasan cewar akwai alaƙa ta jini ajikinsu,ta damu da mutanen gidan sosai,ashe danginta ne su ɗin,
  Jikin azmee ba ƙaramin sanyi yayi ba bayan hajiya azeema ta sanar mata irin zaluncin da sayyadi yayi ma su Sehrish,har idanunta sai da suka cicciko da kwalla saboda tausayinsu da taji,ta jima tana tsinar sayyadi acikin zuciyarta,
Muryarta tamkar zatayi kuka tace"dama ina ta son mu samu lokaci Sehrish ta bani tarihinta wllh,ashe haka suka sha ukubar rayuwa bayin Allah,kai koma wanene wannan mugun mutumin ya cika babban azzalumi,saboda tsabar zalunci ya raba yara da mahaifinsu ya kuma ƙuntata rayuwarsu,duniya ina zaki damu.......'azmee na cikin magana,Abusufyan ya turo ƙopar ɗakin bakinshi ɗauke da sallama,gaba ɗaya hankalin su sehrish ya dawo kanshi,shi ma kuma yana ɗago idanunshi suka sauka akan ƴan ukun nashi,kwata kwata ma bai lura da hajiya azeema da kuma azmee dake a ɗakin ba,Su sehrish kawai yake kallo cike da so da ƙauna,ko kyaftawa baiyi,kamar ya haɗiye su haka yake ji,kamar yadda yake jinsu haka suma suke jinsu,sae ƙare mashi kallo suke yi kamar su watsa a guje su rungumo shi haka suka dinga ji,ta wani 6angaren kuwa abun ba ƙaramin yawo yake yi masu akai ba,Wai nan mahaifinsu ne halak malak,ubansu wanda yayi silar zuwansu duniwa,dama suna da uba da dangi a duniya?tambayoyi iri iri suke shiga yiwa kansu,
  Ganin sun zubama juna ido tsakanin Abusufyan da kuma su sehrish dake zaune saman darduma suna kallon shi,hakan yasa hajiya azeema tayi masu gyaran murya hankalinsu ya dawo kanta sannan tace"Zaman me kuke yi ne?baku ga mahaifin naku bane?ba zaku zo ku rungume shi ba,kuji ɗumin mahaifinku a jikinku?
  jin wannan maganar ta hajiya azeema yasa su miƙewa gaba dayansu jiki na rawa suka ƙarasa wurin shi,
Tunkan su ƙaraso ya buɗe masu hannayenshi alamar su shiga ciki,haɗasu yayi dukansu ya rungume su sosai ajikinshi kamar zai maidasu cikin cikinshi,hawaye ne suka shiga gangarowa a idanuwanshi da kuma idanuwansu sehrish,bai ta6a tunanin zaiga wannan ranar ba,yau gashi ga ƴa'ƴanshi sun dawo wurinshi,tabbas Allah ne ya kar6i addu'ar daya jima yana yi,atare suka ɗago idonsu cike tab da hawaye suka haɗa baki wurin cewa"Abba,"
Har cikin zuciyarshi yaji wani irin sanyi ya ratsa shi,muryarshi akasalance yace"Ku sake maimaitawa banji ba,"
"Abba,"suka maimaita mashi kamar yadda ya umarta,
"Wlh kunyarku nake ji!duk wani abu daya faru arayuwarku ni ne sila,Na cuci rayuwarku,Naji na tsani kaina ƴa'ƴana suna a wani hali na rayuwa amma nagaza taimakonsu,zan iya zuƙunnawa saman guiwaowina agabanku domin in nemi gafararku.....,'tunkan ya ƙara maganar gaba ɗaya ya tafi zai zuƙunna saman guiwowins,cikin sauri suka rurruƙe shi suna cewa"Abba dan Allah kada kayi mana haka bamu so,ka daina ɗaura laifin akanka,dama Allah ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan,dan Allah kada ka zuƙunna agabanmu,mu fa ƴa'ƴanka ne,
Ganin dagaske kneel down zaiyi agabansu yasa suka riga shi zube wa saman guiwowinsu,tsayawa daga tsaye yayi yana kallonsu,Azmee da hajiya azeema duk suna kallon abunda ke faruwa,ba ƙaramin tausayi suka basu ba,
  "Abusufyan"! Hajiya azeema ce ta ambaci sunanshi,amsawa yayi yayin da ya mayar da idanunshi akanta,
  Anatse ta soma magana"yanzu ba lokacin baƙin ciki bane ko lokacin tuna baya,Lokacin farin ciki ne wannan,dariya yakamata in dinga gani a fuskar kowannanku ba hawaye ba,ko ba haka ba azmee?tayi tambayar tare da mayar da idanunta kan azmee,
Murmushi azmee tayi kafin tace"Wannan haka yake,Abusufyan ina tayaka Murna sosai,nayi farin ciki mara misaltuwa,naji daÉ—i da sehrish ta kasance Æ´arka ce,ko ince suka kasance Æ´a'Æ´anka ne,lamarin ubangiji da girma yake,babu wanda ya ta6a tsammanin haka,naji ma ina ganin kamannin fuskarka a fuskar sehrish ashe Æ´ar kace.....'magana take hawayen farin ciki na gangarowa daga fuskarta,
   Murmushi kawai abusufyan ke saki,a lokacin harsu Sehrish sun miƙe tsaye suna tsaye akusa dashi,hosana ta rurruƙe hanunshi kamar wani zai kwace mata shi,
Hajiya azeema ce tace"Azmee yakamata mu basu wuri su gana da juna,don na lura da yadda Uban ƴan ukun nan ke zumuɗi akan ƴa'ƴanshi,"cike da zolaya ta ƙarasa maganar tare da miƙewa taja hannun azmee suka fuce suna dariya,
  Ajiyar zuciya ya sauke tare da mayar da idanunshi kansu jahad yace"kun samu bacci kuwa jiya?ya tambayesu ne saboda fuskokinsu daya gani duk a yamutse,musamman idanunsu sun ƙanƙance,
HaÉ—a baki sukayi wurin cewa"Eh,"
  Hosana tace"abba,dagaske kaine Abban mu ko?
  "Ga zahiri kin gani,"yayi maganar yana yi mata nuni da fuskarshi,murmushi suka saki gaba ɗayansu,
  Sun jima atsaye tare dashi suna magana jefi jefi saboda basu saba da juna ba,duk jin abun suke wani iri haka,kamar mafarki ne suke yi ba gaske ba,
   "Ku koma ku kwanta,kuyi bacci ku huta,idan har akwai inda keyi maku ciwo ku sanar mun zansa aduba ku yanzun nan....'wannan maganar tashi ba ƙaramin sanyaya masu jiki tayi ba,
  "Abba,lafiyarmu qalau,babu abunda ke damun mu,'suka faɗi hakan atare,
GyaÉ—a kanshi yayi tare da kama hanya zai juya da nufi yabar É—akin nasu,
Cikin sauri jahad ta ruƙo hannunshi tare da cewa"Abba,dan Alla kada ka tafi kabarmu,muna buƙatarka a kusa damu,muna so mu kasance tare da mahaifinmu,'
Sehrish ta kar6e da cewa"hakane Abba,ka dawo mu zauna atare dakai,muna buƙatar kyakkyawar kulawa daga wurinka,'
tana kai ƙarshen maganar hosana tace"Abba pls,ko don saboda Ni,"
Wani irin murmushin farin ciki abusufyan ya saki yana kallonta,batare da 6ata lokaci ba,suka wuce saman gadon nasu,a tsakiya suka sanya abusufyan,yayin da suka kwanta gefe da gefenshi,sosai ya rungume hosana ajikinshi,duk in ya tuna labarin yada ta samu ta6in hankalinta nan take sai yaji idonshi sun ciko da kwalla,
"Idan Allah ya kaimu gobe,da kaina zan gyara maku gashin kanku inyi maku kalaba guda biyu,kamar yadda na ta6ayi maku Lokacin da kuna yara,nasan ba zaku iya tunawa ba,'

Jikinsu ne yayi wani irin sanyi, wani irin yanayi suka shiga gaba É—ayansu,

 
 
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

_Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna ɗaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_

*Nagode sosai da addu'o'inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃*

*nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅

Bismillah
Chapter 3 · 0% Book details