← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 212

Sashe 75

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

   Hannu tasa tare da janyo gashin kan nata,ta dawo dashi ta gabanta,tana kwaikwayon yadda sgr yakeyi in ya fito daga wanka,ta daure fuskarta kamar yadda yake tamke fuskarshi,a ƙarshe ta fashe da dariya,
  Tana cikin rahar nan,hosana ta turo ƙopar ɗakin nasu,Ta cikin mirror take hangenta,Hannunta na ruke da system ɗinsu,jikinta na sanye da doguwar riga ta material,
   "Sehrish ga lunch ɗinki can a dining,Aunty azmee ta ce idan kin gama baccin lalacin naki kije ki ci,"
   Ta ƙarasa maganar a yayin da take zama daga gefen gadon nasu,
   Juyowa sehrish tayi tare da kallon hosana tace"daddy ya kira wayarki a switch off,wai ina kike ajiye ta ne"?
  Yatsina fuska hosana tayi kafin tace"Oho,nima bansan inda take ba,nemanta na keyi ruwa ajallo,dan Allah ki tayani nemanta,inaso in kira Ya Omar,nayi nayi da jahad ta kira munshi amma taƙiya,dama kece mai ɗan mutuncin,"
  Harara sehrish ta watsa mata tare da cewa"Sai yau kikasan da haka?bayan kinsaba cewa nafi kowa tsiwa,bayan duk acikinmu ni ce innocent,"
  Marairaice mata fuska hosana tayi,"pls rishi komai ya wuce,dan Allah ki bani aron wayarki yanzu dai in kira Ya omar,2 days banji Voice ɗinshi ba,Ni fushi nakeyi dashi ma,ko ya kira yaji ya nake,amma bai kira ba,"rai a6ace tayi maganar,
   "Kada ki isheni da surutu,don nasanki bakya gajiya,ga wayar nan ki ɗauka,salon ki cinyemun katina,"
   Cike da zumuɗi hosana ta ajiye system ɗin asaman gadon,sannan ta ɗauki wayar da sauri ta fuce daga ɗakin,
   Gaban wardrobe ta koma tare da buɗewa,tana neman kayan da zata sanya,shirt ce ta ɗauko off shoulder Ash colour tare da dogon wandon Jeans,batare da 6ata lokaci ba ta zura kayan ajikinta,bayan ta kammala sanya kayan ta koma gaban mirror, tana shafa powder,sannan ta ɗan shafa lip gloss,murza la66an tayi,tana cikin sharce sumar kanta,Jahad ta turo ƙopar ɗakin,
   Hannunta ruƙe da wayarta,fuskar nan awashe sae faman sakin murmushi take yi,
   Juyowa sehrish tayi tare da kallonta tace"Sai yanzu kika kammala shan Love ɗin?Ni wannan soyayyarta ku tana ɗaure mun kai wlh,ko gajiya bakuyi,yadda kasan Romeo da juliet,kullum kuna a manne da juna,"
  Jahad tace"da alama baƙin ciki kikeyi mun Allah,"
   "In rasa dawa zanyi baƙin ciki sae dake?kin manta wa nake aure?Ni fa matar Surgeon general ce,ke fa?Ni har kunya ma nake ji,ki rasa dawa zakiyi soyayya sae wannan shagwa6a66an..."
  Tunkan takai ƙarshen maganar jahad tace"Auren da yanzu saura 2 month ya mutu!dashi har kike tutiya,"
  Gaban sehrish ne ya faɗi rasss!lokaci guda jikinta yayi wani irin sanyi,yayin da idanunta suka ciko tab da kwalla,
   Ita kanta jahad,bataso ta faɗi hakan ba,ranta ne ya 6aci saboda ta tsani a kushe mata baby Junaid ɗinta,Wannan ne yasa har ta faɗi maganar da tayi,
  "Jahad!ni kike faɗa ma haka"?
Da sauri jahad tace"dan Allah kiyi haƙuri,wlh bansan na faɗi hakan ba,raina ne ya ɗan sosu,"
  "Kinayi mun fatan aurena ya mutu kenan"? Tayi tambayar hankalinta aɗan tashe
  "Dan Allah rishi kidaina faɗin wannan maganar,nace maki ba a son raina na faɗi hakan ba,"tayi maganar tare da ƙarasawa wurin sehrish ɗin,ta ruƙo hannunta,
   "Pls kada ki bari hawayen nan sun fito daga cikin idanunki,kinsan cewa bazan ta6a yi maki fatan aurenki ya mutu ba,kuma wlh ban faɗi hakan ba donna 6ata maki rai ba," fuskar jahad tamkar zatayi kuka saboda tausayin sehrish,
   Tuni hawaye sun shiga wanke mata fuskarta,cikin sanyin murya ta wanda ya karaya tace"kin faɗi gaskiya jahad,bai kamata inyi prouding da aurenshi ba,Ni sam na manta ashe yau saura 2 month babban yaya ya sake ni,ni nama ƙosa ya sake ni in huta,'
   Hannu jahad tasanya tana share mata hawayenta"in sha Allah Babban yaya bazai ta6a sakin ki ba,banayi maku fatan rabuwa da junanku,Nafison ku kasance atare na har abada,Daso samu ne kawai wani abu ya shiga atsakaninku,Ana saura sati daya auren ya mutu,aga kina amai kinga shikenan babu zancen saki,Sae dai a fara tanadin suna,"cike da zolaya jahad tayi maganar,aikuwa nan take sehrish ta fashe da dariya,
  Ganin tafara dariya yasa jahad taci gaba da tsokanarta"gaskiya naƙosa in ganki da ciki,cikin ma na babban yayanmu,Wayyo Allah na bansan wani irin farin ciki zanyi ba aranar,zanso naga babynku,wlh ba ƙaramin kyau zaiyi ba,idan ya biyo kowannanku,"
  Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Najima ina burin wannan ranar,bazan 6oye maki ba jahad,inaso inga nima na haifi ɗan babbyna,Amma nasan ba yanzu ba,"
   "Dont worry ur self,Very soon zaki haifa ma babban yayanmu twins ko triplet,tunda muma triplet ne,nasan acikinmu baza'a rasa wadda zata haifi ƴan biyu ba ko ƴan uku,"Acewar jahad,
  Shiru sehrish ta ɗanyi tana murmushi,duk da tasan abune mai wuya amma taji daɗin maganar nan ta jahad,
   "Inaso naje naci abinci,yunwa nake ji,"
   Ta ƙarasa maganar tare da kama hanyar fita daga ɗakin,Bin bayanta jahad tayi da sauri tare da ruƙo hannunta cikin nata,
   "Mu tafi atare,nima ae banci abincin ba,"
  Dining suka nufa,Wuri suka samu asaman dining chairs ɗin kowa ya zauna,Tray ne mai faɗi azmee ta ajiye masu asaman dining ɗin,Warmers ne guda biyu babba da ƙarama ta miya ajiye asaman shi tare da plate,sae drinks data ɗauko masu,
   Da yake mutanen gidan duk basu nan shiyasa bata girka abinci dayawa ba kamar yadda ta saba,ita kanta ta ɗan samu hutu yanzu,
   "Munyi waya da daddy,"sehrish ce tayi maganar a yayin da take ƙoƙarin buɗe warmer ɗin,
   "Ya faɗa maki ranar da zasu dawo ne"?_
  "A'a bai faɗamun ba,sai dai yayi mun albishir mai daɗi,"
  Cike da zumuɗi jahad tace"Wani albishir kenan"?
   Murmushi ta ɗanyi a lokacin ta kammala buɗe warmer ɗin,wainar shinkafa ce acikinta,
   "Ya sanar dani cewa da zarar sun dawo daga damaturu,A washe garin ranar zasu tafi kano,wurin nemo oumman mu,"
  Maimakon taga farin ciki akan fuskar jahad,sai taga idanunta sun ɗan ciko daa kwalla,

   "Meyasa bakya farin ciki ne"?
"Sehrish farin ciki fa kika ce?Bana Farin ciki,Idan har kika ga nayi farin ciki,toh An samu oummaan mu ne da ranta kuma da lafiyarta,ina fargabar abunda zaibiyo baya,idan suka je nemanta,Kinsan yadda oumman mu take tsananin son mu sosai,Amma lokaci guda aka nemeta aka rasa,tsorona kada ace ya sayyadi ne yayi mata wani abun,dama yasha faɗin cewa zai kashe ta idan har bata daina bin ƙwaƙƙwafin da takeyi mashi ba....."dakatawa jahad tayi da yin maganar,jikinsu duk yayi sanyi,
   "Addu'a yakamata muyi mata akan Allah yasa su samota,Amma nikaina ina fargabar a wani hali zasu same ta,"
    Duk sunsha jinin jikinsu,zuba masu wainar tayi acikin plate,sannan ta buɗe ƙaramar warmer ɗin,Miyar ganye ce,taji ganda lu6u lu6u acikin,Tuni ƙamshinta ya gauraye wurin,
   Daƙyar suke iya cin abincin,kamar waɗanda akayi ma dole suci,

   *HAROON*
Chapter 75 · 0% Book details