← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 212

Sashe 27

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuraren ƙarfe 2 na dare junaid ya farka sakamakon zungurar shi dayaji anyi da sanda,a firgice ya tashi zaune yana faman zazzare manyan idanunshi masu ɗauke da bacci,ƙasa ƙasa yaji ana ambatar sunanshi Junaid!junaid!aikuwa a tsorace ya sanya hannunshi tare da toshe kunnanshi ya fasa uwar ƙara,kai tsaye sautin ƙarar daya saki ta daki dodon kunnan Alexandra,a firgice ta farka,ganin junaid da tayi a zaune jikinsa sai kerma yake yi hakan yasa ta miƙe tare da janyoshi jikinta tana faɗin"junaid!romeo ɗina what's wrong with u?baka lafiya ne,"duk tabi ta tsorata da halin da yake ciki,
..Muryarshi na kerma yace"Mommy,wani abu zai faru dani,dan Allah ki taimaka mun,banso in mutu yanzu,"
  Jin wannan maganar ta junaid ba ƙaramin tayar mata da hankali tayi ba,kankame shi ta ƙarayi muryarta na rawa tace"Junaid,kadaina faɗin haka banason ji,babu abunda zai faru dakai indai kana tare dani,nasan cewa mafarki kayi,pls calm down ur mind,mu koma mu kwanta,
  ɗagowa yayi daga jikinta,cikin shessheƙar kuka yace"Mommy dan Allah,ki tashi muyi sallah,sai kiyimun addu'a,"
a ruÉ—e tace"Salla kuma junaid,am not a muslim bana sallah,zan daiyi maka addu'a,"
   "A'a mommy nidai ki tashi muyi sallah,kiyimun addu'a,"Ashagwa6e yayi maganar,
  "Junaid ka fahimce ni,bakasan cewa niba musulma bace!ko daddynku bai ta6a faɗa maka bane,Ni bana sallah,I don't even know how to do it,"
  Jin haka yasa junaid sake fashewa da wani sabon kukan mai sautin gaske yana cewa"Mommy ki tashi muyi sallah,ki tashi mommy!wlh idan baki tashi munyi sallah kinmun addu'a ba mutuwa zanyi,"
  Tashin hankali,gaba daya junaid yabi ya rikice mata ya hanata sakat,duk yadda taso ta fahimtar dashi akan cewa ita ba musulma bace,bata sallah amma abun ya faskara,junaid ya kurmance mata,
  Babu arziƙi ta amince zatayi sallar,tasata gaba yayi ta shiga toilet ta dauro alwala,ko alwalar bata wani iyaba,ruwa kawai ta watsa a fuskarta,ta wanko hannayenta da kafafuwanta tafito,shi ma ya shiga cikin toilet ɗin,wucewa tayi wurin wurin closet ɗinsu,ta buɗe kayan Abbansu ne a jere sai kayan sawar ta,wanda tazo dasu,gaba daya babu hijabin da zata sanya,dakyar ta samu wani mayafin doguwar rigarta mai ɗan tsayi,ta ɗauko shi tare da sanyashi ajikinta,sae yayi mata tamkar hijabi,
  tsayawa tayi tana jiran junaid ya fito suyi sallar,lamarin nashi ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,ƙiri ƙiri junaid yasata za tayi sallah,ya rufe idonshi ya nuna tamkar baisan cewa ita ba musulma bace,aranta tace"Anya junaid bai samu ta6in hankali ba?in ba haka ma meyasa zai yi forcing ɗina akan inyi salla bayan yasan cewa ni ba musulma bace,Omg!ni bansan ma ya akeyin sallar ba,ko time ɗin baya dana ta6a musulunta ba don Allah nayi ba,ko sallah banyi a lokacin,"
tana cikin zancen zucin nata sai ga junaid ya fito daga cikin toilet yana faman yarfa hannunshi,ruwan alwalar da yayi yana ɗiɗɗigowa ƙasa,
   Carpet ɗin salla ya dauko masu na abbansu sannan ya dawo ya shimfiɗa masu shi,
  Juyawa yayi tare da kallon Mommyn tasu wanda tayi sototo tana binshi da kallo,
  "Ni zan shiga gaba saiki tsaya abaya,"
   Dawowa bayanshi tayi ta tsaya,shi kuma ya tsaya agaba,tare da daidaita natsuwarshi,ya kabbara sallar,anatse suka shiga yin sallar atare,tunda suka kai raka'a dayan farko,bacci ya kwashe Alexandra,junaid bai sani ba yaci gaba da yin sallarshi,sai da yayi kusan raka'a takwas sannan ya sallame,
  cikin bacci taji an ambaci sunanta da ƙarfi"Mommy"!!a firgice ta farka tare da buɗe idanunta tana kallonshi,muryarta adisashe irin ta mai bacci tace"junaid har mun kammala sallar,"zum6ura mata baki yayi rai a6ace yace"nadai kammala sallar mommy,kin barni ni kaɗae,kina ta bacci,"
  cikin lallashi tace"kayi haƙuri romeo ɗina,saida na faɗa maka cewa banyin sallah,nifa ban iya ba,nadai samu nayi ɗaya,dakyar itama na samu nayi ta,don bacci nake ji,"
  "Shikenan kiyimun addu'a yanxu,sai muje mu kwanta"
  Yadda yayi maganar ba ƙaramin tausayi ya bata ba,nan take taji kamar bata kyauta mashi ba,jiki asanyaye ta sanya hannunta tare da ruƙo hannunshi,ta shiga karanta mashi addu'oin,cikin harshen Faransanci,bai damu da yaren da takeyi mashi addu'ar ba,saboda yasan cewa Allah yana ji da kowani irin yare aka roƙesa,"
  Ta jima tanayi mashi addu'a tana tottofa masa asaman sumar kanshi,kafin daga bisani suka koma saman gadon suka kwanta,ba ƙaramin kwanciyar hankali junaid ya samu ba,tunda ta tofa mashi addu'ar nan take yaji wani sanyi aranshi,tamkar an bashi ƙwarin guiwa,kuma tunda ya kwanta bacci ya ɗaukeshi bai ƙara jin an zungure shi ba,

DARE YAYI GARI YA WAYE,

Tun bayan Kammala Sallar asuba,Azmee da Saude,Suka fara ɗaura girke girken da zasuyi anan cikin gida,Uban aiki ne a gabansu,saboda Abinci ne kala kala zasuyi,na kasashe daban daban,saukin su ma Naman da za'a yanka basu zasuyi aikinshi ba,An riga da an bada aikin naman already,sai dai kawai in an kammala akawo masu shi Hada snacks sukayi order wanda za'a ci,akwai kuma Naman da Azmee zatayi masu farfesu dashi,da kuma tsiren nama,don ta kware a wannan 6angaren,Sunyi nisa acikin aikin sai ga Hajiya azeema ta shigo,bayan sun gaisa da junansu,itama tace tazo ayi aikin da ita,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,nan suka haɗu su uku,suka tasar ma girkin nan,Cikin ƙanƙanin Lokaci,Wani irin daddaɗan ƙamshi ya gauraye ko'ina na kitchen ɗin,

Hatta main palour ɗin kamshi ya karaɗe cikinsa,gwaggon katsina dake kwance,saman gado,tun bayan sallar asuba ya ɗauketa,tana cikin bacci ta dinga jin ƙamshin abinci nashiga Hancinta,ba arziƙi ta farka tana faɗin"wannan wani irin ƙamshi ne mai tashin mutun daga bacci"?tana maganar tana shinshinar kamshin,saukowa tayi daga saman gadon,jikinta sanye da kayan baccin nan nata na gado,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin nata tana tunkarar inda kamshin ke fitowa,

Kamar daga sama suka ji muryar gwaggo tana cewa"Ikon Allah,ƙamshi ya tashe ni daga bacci,ya kawo ni cikin kitchen,don inci daɗi,"
  Murmushi suka saki gaba ɗayansu,kafin suka shiga gaishe da ita,
  ƙarasawa tayi cikin kitchen ɗin suna haɗa ido da saude ta watsa mata harara tare da cewa"ya akai kuka bar wannan tana girki?bafa ta iya girki ba,Rannan ta zuba mana Gishirin lalle amatsayin gishiri cikin farfesun nama,gaba ɗaya girkin nan bai ciyu ba,ƙarshe saboda tsoran kar asirinta ya tonu inyi mata faɗa,ta dauki farfesun ba tare da sanin kowa ba taje ta zuba ma karnukan layinmu,kunsan kare da nama nan fa suka lashe farfesun nan tasss suka cinyi shi,aikuwa cikinsu ya kumbura sumtum,sukayi mussai,gaba ɗaya suka mace aka zubdo su,mai karnukan nan yace bazai yarda ba,sai yayi shari'a da Saude,ranar saude har gudawa saida tayi don jin za'a kaita ƙara kotu,yarinya tabi ta burkice mana,daƙyar Harrisu ya biya diyarsu,daba don haka ba,da tuni saude an jima da yanke mata hukuncin kisa....'
  Tunkan gwaggo takai karshen Labarin da take basu gaba ɗaya suka fashe da dariya,banda saude wadda ta tur6une fuska,rai a6ace tace"Kai gwaggo,"
  gwaggo tace"ƙarya nayi?ko ba haka akayi ba,ki faɗi tsakaninki da Allah in ba ayi hakan ba,ranar fa har gudawa kikayi,kika dinga kuka kina cewa gwaggo ki maishe ni rugarmu,saboda kawai na kashe karnuka shine za'a kai ƙarata kotu,wlh ko shanun baffa na kashe ba za'ayi mani wannan hukuncin ba,sai ku ƴan gayu da kuka ɗauki ran kare da mahimmanci karen da ko hisabi baza'ayi dashi ba,"
  Sake fashewa da dariya sukayi,yadda gwaggo take kwaikwayon muryar Saude,ba ƙaramin dariya ta basu ba,saboda hausar irin ta fulanin da basu kware bace,"
fuskar saude tamkar zatayi kuka,batasan meyasa gwaggo keyi mata haka ba,duk in suka shiga cikin mutane saita kunyata ta,wannan labarin da take bayarwa ya jima da faruwa,tun lokacin da Dr harris ya ɗaukota daga rugarsu ya kawota gidansu,lokacin batasan komai ba,ita arayuwarta ba abunda ta bama mahimmanci inba Kiwon shanu ba shi kadae tafi sani,gwaggo kuma bata koyar da ita komai ba,kwana uku da zuwanta gidan ne,ta shiga kitchen ta ɗaura masu girki,tana cikin girkin ta fara neman gishiri zata zuba acikin,gafa gishirin acikin farar roba an zubashi,amma saboda ta saba ganin gishiri kulle acikin leda yasa tayi zaton koba gishiri bane,hakan yasa ta fito ta wuce ɗakin gwaggo don ta sanar da ita cewa babu gishiri a gidan,tana shiga ɗakin gwaggon katsina,ta same ta tana bacci,harta juya zata fita shine taga wasu kullun kaya da aka kawoma gwaggo acikin leda,nan fa ta shiga laluban kayan,ta zaƙulo ledar gishirin lalle ta fuce dashi,duk a tunaninta gishiri ne,dayake kanta a toshe yake,kwata kwata bata lura da lallen dake acikin ledar ba,ita dae kawai gishirin lallan ta ɗauko,taje ta zuba masu acikin girkin,ba don Allah yasa gwaggo ta tashi tana neman gishirin lallanta ba,har saude taji,daba ƙaramin illa zata yi masu ba,karshe dai abun kan karnukan layinsu ya ƙare,tun daga wannan lokacin ne harris ya sanyata a makaranta,da kuma makarantar koyon girki,har ta samu ta kammala secondary,daga nan ne akasamu kanta ya waye,
  "Gwaggo me kikeso a zuba maki ne?nasan yunwa ce ta koro ku,"azmee ce tayi maganar,
  Gwaggo tace"komi ma da kuka girka,a zuba mun in ɗanɗana inji yaya ɗanɗanon girkin naku yake,don tunda kuka sanya saude acikin girkin nan naku nasan cewa dole a samu matsalar rashin gishiri kodae ta zuqa shi,ko kuma yayi kaɗan,"
murguɗa mata baki saude tayi tare da juyawa ta shige cikin store,tana faɗin"nashiga uku da wannan matar,a haka Haris yakeso in zama surukarta,bansan ya zan ƙare da ita ba,lafiya lou nake yin girkina acan gida,har santi takeyi amma yanzu tazo sai sharri takeyi mun agaban mutane,Zamu koma gida ne,nasan me zanyi mata,ae mun saba dama,"
  Saude bata fito daga cikin store ɗin ba,sai da taji fitar gwaggo daga kitchen din,bayan sun zuzzuba mata abincin da suka girka,komai sai da tasa suka zuba mata,a ƙaton tray ta fuce dashi tana cewa"idan na cinye wannan zan dawo a ƙara mun,"
  dawowa tayi cikinsu suka cigaba da aiki,azeema tace"sai kin dinga haƙuri da ita,bayin kanta bane,ku tayata da addu'a,Allah ya yaye mata wannan haukan da aka ɗaura mata,"
  Saude tace"insha Allah,zamu cigaba da tayata da addu'a,ae yaya harris ya sanar dani komai,na tausaya mata sosai,Allah dai ya tonu asirin waɗanda ke shirya masu wannan maƙarƙashiyar,Allah ya kawo ƙarshensu,"
  Azmee tace"ae bazasu kai labari ba,a sannu asannu zasu gane kurensu,"
  Suna aiki suna tattaunawa game da irin rayuwar da su sehrish sukayi a baya,
Chapter 27 · 0% Book details