← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 212

Sashe 64

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

sunanta"Jahad!Jahad!"koda jahad ta buɗe idanunta tayi tozali da fuskar Daddynsu saita fashe da matsanancin kuka tana cewa"daddy kaga abunda hosana tayi mana?kawai daga magana ta hau bugunmu ni da Sehrish,duk tabi ta gartsa mana ciwo a fatar jikinmu....'tana magana hawaye na zuba a idanunta,  Runtse ido Abusufyan yayi tare da buɗesu a hankali,abun ba ƙaramin ta6a mashi zuciya yayi ba,  Hannu Omar yasa tare da kar6ar Robar ruwan dake hannun Kanal yousouf ya taka izuwa inda Sgr ke a zuƙunne ya miƙa mashi ita,Kar6a Sgr yayi tare da kur6ar ruwan abakinshi,ya fesar dashi akan fuskar Sehrish,a firgice ta farka gami da mikewa zaune tana faman zazzare idanunta,one by one tabi su da kallo,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin Sgr,ga kuma su hajiya azeema tsaye duk akanta,tafin hannuwanta tasa tare da rufe fuskarta,tana kuka,   "Wani ya ɗauko min FA box a medical room"Sgr ne ya ambaci hakan,da sauri irfan ya fuce daga ɗakin don zuwa ɗauko akwatin,ruƙo hannun Sehrish Hajiya azeema tayi tare da zaunar da ita gefen gadon,"sannu kinji,yi shiru ki daina kuka,"cikin lallashi takeyi mata maganar,     Hawa saman gadon nasu Hafsat tayi,tare da kai hannunta ta ɗago da hosana ajikinta,sae faman kerma jikinta yakeyi,ciwonta ya motsa,da alama an rabu da shan magani,duk a tunanin su abun yayi sauƙi,ashe da sauranta,tabbas hosana tana buƙatar ganin likitan mahaukata,  A faɗace Omar ya daka masu tsawa gaba dayansu yace"wai duk menene yajawo hakan!ba zaku buɗe baki kuyi ma mutane bayani ba!"   Cikin shessheƙar kuka Sehrish tace"Hosana ce,tunda sanyin safiya tafarka,tana raira mana waƙar takusa aure ƙara faɗa breaker,kuma hada kiɗa take raira waƙar duk ta takura kunnuwanmu,har muka farka daga bacci,Don munyi mata faɗa shine ta naɗe hannun rigarta ta hau mu da bugu da cizo kamar ta samu jakuna....'  Cike da mamaki kowa ke kallon sehrish dake kora masu bayani,Ishaq yace"Wai yanzu duk don saboda wannan ku ka kusa illata junanku?gaskiya akwai gagarumar matsala babba ma kuwa,'   Abbas yace"dama da wuya kaga ƴan biyu ko ƴan uku suna zaman lafiya a tsakaninsu,zakaga suna tsananin son junansu,amma ta wani 6angaren basu jituwa,don akwai labarin dana ta6a ji shigen irin wannan daga kokowa suka kashe kawunansu,"  Jin wannan maganar ta Abbas ya ƙara daga masu hankali,Abba yace"in sha Allah,ba zamu bari hakan ta faru ba!tunda abun har yakai ga faɗa da jima juna ciwo,dole a raba masu wurin kwana,shine kawai mafita,"  "Abunda nake ƙokarin cewa kenan"acewar hajiya azeema,  Ammi dai abun yafi ƙarfinta daga ita har Alexandra da hajiya Saratu suna atsaye sun zuba ma sarautar Allah ido,Lamarin yaran yayi matukar daure masu kai,   Dawowa cikin ɗakin nasu Irfan yayi hannunshi ɗauke da First aid box ɗin,ya ƙaraso tare da miƙa ma Sgr akwatin,hannu yasa ya kar6e shi tare da ajiye shi a ƙasa,   Sannan ya zauna,daga gefen gadon,suna fuskantar juna shi da sehrish,wadda ke ta faman shessheƙar kuka,wani irin kallo daya jefa mata,tuni ta nemi kukan da takeyi ta rasa,   "Close ur eyes,"da sauri ta rufe idanunta kamar yarda ya umarta,tana ji yasa mata audiga a wurin ciwon yana goge mata jinin,a sannu ya shiga yi mata dressing din ciwon da taji,bayan ya kammala da ita,Abusufyan ya ruƙo hannun jahad,ya dawo da ita gefen Sgr ya zaunar da ita,cikin lokaci ƙankani Sgr ya kammala yi mata dressing ɗin itama,   "Ita kuma hosana ya zamuyi da ita?kodai asibiti zamu kai ta?Acewar Abusufyan,  Omar yace"Rafayet zai iya duba mana ita anan gida ma"   "Omar am not a psychiatric doctor,though i've experience about their work,zan iya duba ta,Amma a ƙa'ida,psychiatric doctor ya kamata yayi checking ɗinta,bazan shiga aikin da banawa ba,"kaji turawa,ƴan bin ƙa'ida,  Jinjina kai Omar yayi fuskarshi ɗauke da murmushi,ya juya tare da kallon Dr harris dake tsaye ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi yace"Bismillah,"yayi maganar yayin da yake yi mashi nuni da hosana wadda ke kwance ajikin hafsat,idanunta sun birkice sae farar kwayar idon kawai,yatsunta kuwa sae faman kerma sukeyi,hada na kafafunta,  Kallonta kawai Dr harris yayi batare daya ta6a jikinta ba,ya faɗi sunan allurar da take buƙata ayi mata,  Da sauri Omar ya ciro wayarshi tare daddana wasu numbobi,ya kira Dr Emran na asibitin Sgr,kiran na shiga emran ya ɗauka,don haka Omar ya miƙa ma Dr harris wayar don suyi magana,  Bayan sun kammala wayar,ya dago tare da kallon Marshal yace"Ya sanar dani cewa within 15 mins zaizo tare da allurar da kuma medicine ɗinta," Omar yace"Okey,Allah ya kawo shi lafiya,
Chapter 64 · 0% Book details