← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 212

Sashe 130

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sunyi parking ɗin motocin,Abusufyan ya fito daga cikin motar,hosana na ganinshi ta ƙwala mashi kira"Daddy"!wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,da gudun gaske ta nufe shi tare da faɗawa jikinshi ta ƙankameshi sosai,tana dariya,
"Hosana,"ya Ambaci sunanta tare da É—ago da ita daga jikinshi yana kallonta,fuskarshi É—auke da murmushi,
ÆŠaure fuskarta ta É—an yi ashagwa6e tace"Munyi fushi daddy,Sai yau zaku dawo"?
Yana ƙokarin buɗe baki ya bata amsa,karaf idanuwanshi suka sauka akan Jahad wadda ta fito daga cikin falon tana tunkaro su,
Gabanshi ne ya faɗi rass!Ganin yadda kamanninta suka sauya tamkar ba ita ba,ta rame sosai ,tafiyar kanta ma daƙyar take yinta,
Ƙarasawa tayi gabansu ta tsaya batare da tace komai ba,idanuwanta na kallon ƙasa,
"Jahad!kinyi rashin lafiya ne"?É—aga mashi kai tayi alamar eh,
"Zazza6i nayi sosae amma naji sauƙi yanzu,"
Hannu yasa tare da janyota ya rungumeta ajikinshi,Kasa jurewa tayi aikuwa ta fashe mashi da kuka sosai,
Hankalinshi ya ƙara tashi,
"Jahad kukan menene"?
Cikin shessheƙar kuka tace"bakomai Daddy,nayi kewarka sosai,"
hannu yasa yana É—an bubbuga bayanta yace"Am Sorry Daughter,pls ki daina kuka kada kisa nima na fara zubar da hawayen nawa,"
Dakyar ta tsagaita da yin kuka ta É—ago da kanta daga jikinshi tace"Daddy,ina rishi take?ina kuma Oumman mu?Hosana ta sanar dani cewa an ganta,"
Murmushi ya saki tare da sanya hannunshi ya É—an kwankwasa glass É—in motar,
BuÉ—e murfin motar Abu tayi tare da fitowa daga cikin Motar,Zuba mata ido su kayi suna kallonta kamar yadda itama take kallonsu,
Atare suka haÉ—a baki wurin ambaton sunanta"Oumma!"
Murmushi ta ɗan sakar masu,tare da buɗe masu hannunwanta don su zo ta rungumesu,Matsawa suka yi tare da faɗawa saman jikinta,ta haɗasu duka ta rungume sosai,fashewa sukayi da matsanancin kuka kamar ransu zai fita,musamman jahad da take cikin wani hali na buƙatar kulawarsu,
Itama abun kukan takeyi sosai,babu mai lallashin wani acikinsu,Fitowa Sehrish tayi daga cikin motar ta other side ɗin,jikinta a sanyaye ta zagayo ta wurin da suke,bayansu jahad ta fada ta rungumesu,abu ta haɗa da ita duka ta ƙanƙame abunta,

Tuni hawaye sun wanke fuskar Abusufyan,Yau burinshi Ya cika na ganin ya haÉ—a kan family É—inshi,wannan rana ce da bazai ta6a mantawa ba arayuwarshi,,

Suna cikin wannan yanayin sai ga Abbansu junaid tare da Alexandra sun fito daga cikin gidan,tsayawa su kayi suna kallonsu fuskar kowannansu É—auke da murmushi,
"Bismilla,Ku ƙaraso daga ciki mana,"Abba ne yayi maganar tare da yi masu nuni da hannunshi,
Kallonsu Abu yayi tare da yi masu gyaran murya yace"Koke koken sun isa haka,mu shiga daga ciki mana,"
Raba jikinsu sukayi dana Oummansu,ta ruƙo hannun jahad da hosana acikin nata,Abusufyan kuma ya ruko hannun Sehrish wurinsu Abba dake atsaye,
tunkan su ƙaraso Abba yace" masha Allah,Yau family ɗin Abusufyan ya haɗu wuri guda,Ga Uwar Ga uban Ga kuma ƴa'ƴansu,"ya ƙarasa maganar yana dariya,
Alex tace "U'r Highly welcome, Abusufyan's Family,Am glad to see guys "ta yi maganar tare da ƙarasawa ta rungumo Abu ajikinta,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,

Sun jima a waje suna gaisawa kafin daga bisani suka koma babban falon gidan,Kowa dake acikin gidan sai da ya hallara A falon,Abusufyan ya shiga gabatar ma abu kowa,Sun yi farin ciki sosai,duk da tashin hankalin da suke ciki hakan bai hanasu yin Murnar dawowar Uncle É—insu ba tare da Oummansu rishi,Abusufyan ya lura da yanayin fuskokinsu,abun ya É—aure mashi kai,mutanen gidan duk sun rame sunyi duhu,bashi kaÉ—ai ba hatta Sehrish ta ankara da canzawar da mutanen gidan su kayi,Sai faman wurga ido takeyi taga ko junaid zai fito amma shiru babu shi,Ranta ne ya bata cewar ko sun fita tare dasu Babban yaya ne tunda bata gansu ba acikin gidan,

Basu tashi sanin halin da Family ɗin suke ciki ba,Sai da suka huce gajiyarsu,tukunna Abba ya sanar da Abusufyan shima ɗin don ya matsa mashi ne akan son ganin junaid,Hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin anyi garkuwa dasu Junaid,baima son lokacin da ya rufe Abba da faɗa ba saboda ƙin sanar dashi da sukayi,Don me zasu 6oye mashi abunda ke faruwa acikin gidan,abun ya ƙona mashi rai,Har cikin ranshi baiji daɗin hakan ba,har ƙwalla saida ya zubar,

Yinin ranar Abu na tare da Æ´an ukunta a bedroom É—insu,Sun sha firar yaushe rabo,har bacci ya É—aukesu atare saman gadon,basu suka farka ba sai wuraren Sallar Magriba,

Bayan kowannansu yayo alwala Jahad ta shimfiÉ—a masu darduma suka jera atare da Oummansu,a tsanake sukayi sallar har suka kammala,basu tashi daga saman dardumar ba,É—aga hannayensu suka yi sama suka shiga karanto addu'o'a abakunansu suna masu kara mika godiyar su ga Allah(S.W.A),

Allah Allah Sehrish take yi su kammala Sallar taja jahad gefe saboda ta tambayeta ina junaid yake sannan kuma ta bata Labarin Artabun da suka yi tsakaninsu da ya sayyadi,ita ma jahad ɗin a ƙagare take dasu ke6e ita da Sehrish,Don ta bata labarin mutuwar junaid,kota samu ta rage raɗaɗin dake acikin zuciyarta,bazata iya 6oyema Sehrish ba,duk da An gargaɗeta akan karta fadama kowa,

Basu suka samu lokacin kebewa da junansu ba,Sai bayan sallar Isha'e,kowa ya hallara a dining area,Suna cin abincin darensu,

Su biyu suka rage acikin bedroom É—insu,Zaune daga gefen gadonsu,kowa yayi tsit,na wani lokaci kafin Sehrish tace"Jahad,tun É—azu nakeso na tambayeki game da canzawar dana ga mutanen gidan nan sunyi,kowa ya rame yayi duhu,musamman ke kamar kin yi ciwo,"
Cikin sanyin murya Jahad tace"Labari ne mara daÉ—in ji Sehrish,Zan faÉ—a maki amma ina gudun na jefa ki cikin tashin hankali,"
"Kada ki damu jahad,ki faÉ—amun koma menene,in sha Allah zan jure bazan tashi hankali na ba,"
"Shikenan zan faɗa maki Amma kafin nan inaso ki yi mun alƙawarin cewa bazaki faɗa ma kowa ba"
..Sehrish tace"I promised you jahad,babu wanda zaiji abunda muka tattauna dake,"
Shiru jahad ta É—an yi yayin da take yin wasa da yatsun hannunta,
"Ina sauraronki jahad,"ta faɗi hakan ne don a ƙagare take da ta ji abunda jahad zata sanar da ita,
"Sehrish!munyi babban rashi,wanda ya raunata zukatanmu,"
..tunkan ta ƙarasa maganar sehrish taji gabanta ya faɗi rasss,
AruÉ—e tace"Jahad kada ki ce mun junaid ya mutu......!"
Hawaye ne suka fara saukowa daga cikin idanun Jahad,bata 6oye mata komai ba game da mutuwar Junaid,Abun mamaki sai taga Sehrish na Zabga murmushi kamar wata zautacciya,
Bata karaya ba,cigaba da magana tayi"Babu wanda yasan ainihin abunda ya faru,daga ni sai su ya Omar sai kuma Jami'an Æ´an sandan da suke je wurin da kuma Sojojin dasu ya Omar suka je dasu,"
Dakatawa tayi da yin maganar tare da kallon Sehrish,wadda ke ta sakin murmushi,
Fashewa da kuka Jahad tayi tare da cewa"Sehrish meyasa kike yin murmushi?na faɗa maki ne don in rage raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata,wlh da kinsan halin da muka shiga ni dasu Ya Omar da baki yi mana dariya ba,"tana kai ƙarshen maganar ta ƙara sautin kukan nata,
Sai lokacin Sehrish ta tsagaita da yin dariyar,Sannan ta soma magana"Haba Jahad,taya zaki ce mun Junaid ya mutu farat ɗaya in yarda?bazan ƙaryata ki ba,mutuwa na akan kowa babu wanda yafi ƙarfinta,Amma ni dai ban yarda cewa junaid ya mutu ba,tunda banga gawarshi ba,"tuni hawaye sun cicciko acikin idanuwanta,
Cikin Shesshekar kuka jahad tace"Taya za'ae kiga gawarshi!nace maki ko ƙashi ba'a samu ba daga sassan jikinshi,Saboda ya ruga da ya ƙone ƙurmus ya zama toka,"
"Jahad ni ban yarda ba,Allah Junaid É—inmu bai mutu ba,ki daina wahalar da kanki wurin faÉ—a mun,"
Rai a6ace Jahad tace"Wlh dole ki yarda Sehrish!meyasa zakiyi mun haka!Maimakon ki tayani jimamin rashin shi amma shine kike ƙara jefa ni cikin damuwa,"
Girgiza kai sehrish ta shiga yi tana faÉ—in'wlh bazan yarda ba,"tashin hankaline yasa Sehrish ta burkice mata,
"Ko kin ƙi ko kin so dole ki yarda Sehrish,Junaid has gone forever,"
Miƙewa Sehrish tayi jiki ba ƙwari ta nufi toilet,Shigewa ciki tayi tare da jan ƙopar ta rufe,
Zuƙunnawa tayi ajikin ƙopar,sai lokacin ta fashe da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,
"Allah sarki Junaid,Allah ya jiƙanka,bazan ta6a mantawa da halarcin da kayi mun ba,

 

  

  
  
 
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Zuƙunnawa tayi ajikin ƙopar,sai lokacin ta fashe da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,

"Allah sarki Junaid,Allah ya jiƙanka,bazan ta6a mantawa da halarcin da kayi mun ba,Allah yasa ƙarshen wahalarka kenan"
Chapter 130 · 0% Book details