← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 212

Sashe 2

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana cikin tsayuwar ne har aka kira sallar asuba bai ankare ba,sae da Yaji ana mashi knocking ƙopa,muryarshi ashaƙe yace"Wanene,"
"Ni ne"muryar Abban su junaid ce,
Hakan yasa shi cewa"ƙopar abuɗe take yaya ka shigo daga ciki,". 
Tura ƙopar Abba yayi ya shiga ciki yana ganin Abusufyan atsaye yace"dama saida rai na ya bani cewar baka yi bacci ba abusufyan,'
  Yayi maganar tare da ƙarasawa ya dafa kafaɗarshi yana kallon fuskarshi da hawaye suka wanke ta sharkaf,
Cikin sanyin murya yace"duk wanda yace maka kayi haƙuri tamkar ya cuce kane!amma ya zakayi abusufyan?dole haƙurin nan shi zakayi,nasan abun da ciwo,raɗaɗinshi na iya zarce na ƙunar wuta,abusufyan bazan ce kayi laifi ba,amma kasan cewa dole ne dama kaga badai dai ba!kayi aure batare da sanin mahaifiyarka ba,baka sanar mata ba balle tasanya albarka acikin auren naku,kunyi komai a6oye kai da gwaggon katsina,sai gashi yau Allah ya bayyana mana komai,nasan kai kanka kayi mamakin ganin Ƴa'ƴanka su duka ukun a ƙarƙashin kulawar gidan mu,kaɗan daga cikin Ikon Allah kenan!kwata kwata yaran basu san suna da dangi ba,garari kawai sukeyi a wulaƙance cikin gari,mu ma haka bamu son cewa akwai wasu ƴa'ƴa waɗanda suka kasance jinin mu ne su ba,babu wanda yasan haka,amma cikin ikon Allah da yake shi hakimun ne,sai gashi silar aikatau ɗaya ta faɗo hannunmu,yayin da silar ciwon ɗaya daga cikinsu da aka kai asibiti Allah ya ƙaddara haɗuwarsu da Omar yayin da shi kuma yaje wurin ɗan uwanshi Dr haris,lamarin ubangiji girma gare shi!gaba ɗaya Allah ya haɗa yaran a wurinmu ta hanyar da bamu ta6a tsammani ba,kamar yadda kai da gwaggon katsina baku yi tsammanin abunda kuka aikata asirrance zai tonu ba,tunda baku sanar mana ba sae gashi Allah ya sanar damu,su kansu yaran basu yi tsammanin zasu haɗu da dangin ubansu na asali ba,su dama basu da masaniya akan wanine ubansu......'
Dakatawa abba yayi da maganar yana kallon abusufyan dake ta faman shessheƙar kuka muryarshi na kerma ya shiga cewa"Ya Allah ka yafe mun kuskuren dana aikata na auren abu batare da sanin mahaifiyata ba da kuma dangina ba......tun farko nine silar jefa rayuwarsu Cikin halin da suka tsinci kansu,da ace ban 6oye ma kowa ba,duk da ammi bazata barni in auri abu ba amma ina da tabbacin cewar Abbanmu salahuddeen zai aura mun ita inna nasanar mashi,iyakaci dae Ammi zata zangwameta ne daga baya kuma nasan zata fara sonta,wlh ni sam tunanin hakan baizo mani ba a wannan lokacin,idona ya makance,kuma ba laifin gwaggon katsina bane,Son da takeyi mun ne yasa ta aikata hakan don ta faranta mun ganin halin da na shiga a lokacin jin cewar Mommynmu ba zata bari in auri abu ba,gashi na mutu akan sonta
kaicona.......'fashewa yayi da wani sabon kukan,dana sani kenan irin wadda ba'ason yinta,abun yayi ta maka ciwo azuciyarka,shiyasa kullum muke cewa Allah ya tsare mu daga aikata aikin danasani,saboda bai da daÉ—i,É—aci gare shi,
    Ba ƙaramin tausayi yaba Abba ba,tuni shima hawaye suka fara sauka akan fuskarshi,janyo abusufyan yayi ajikinshi sosai ya rungume shi yana lallashinshi,
  A ƙarshe yace"Abusufyan ka manta da duk wani abu daya faru dazun,yanzu lokacin farin cikine,yakamata ka nuna godiyarka ga Allah subhanahu wata ala daya nuna maka wannan ranar da ya haɗaka da triplet ɗinka dukkansu da ransu kuma da lafiyarsu!wlh abusufyan dana ga yaran nan amatsayin ƴa'ƴanka kaɗan ya hana in buga tsalle saboda murna.....'yayi maganar yayin da suka raba jikinsu dana juna,
  tallabo fuskarshi abba yayi cike da zolaya yace"Kasan me?
  Abusufyan ya girgiza mashi kai alamar a'a,
  Abba yace"nifa ɗazu dana ga ka firgita da ganin yarinyar nan nayi tunanin cewa ko ka ƙyasa ne,har ina cewa shikenan lokacin barin gwaurantakar abusufyan yayi aduniya ashe ashe uban ne gaba ɗaya........'
  Ya ƙarasa maganar yana dariya,murmushi abusufyan ya ɗanyi,
  Abba ya kuma cewa"Wai yanzu nan duk aikinka ne waɗannan abusufyan?ashe dae ƙanin nawa bana wasa bane...'
  fashewa da dariya abusufyan yayi tare da sunnar da kanshi ƙasa,
  Hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Abba ba,dama so yake ya sanyashi farin ciki don ya gusar mashi da damuwar da yake ciki,
  dafa kaɗarshi abba ya kuma yi tare da cewa"duk haihuwata ya'ya goma sha takwas akan su jahan ne kawai na samu ƴan biyu,amma kai da yake mai sa'a ne,na ku ba irin namu bane sai gashi ka haifa mana ƴan uku reras!ko Ya ammi zata ji in taga ƴa'ƴan mara jin maganar nan nata abusufyan....nasan zata ce shegen bisa zai aika ae,
  Wannan karan atare suka fashe da dariya,
Daga bisani Abusufyan yace"yaya hussein inaso naga yaran nan sosai,na damu dasu wlh....'
  Wani irin kallon rainin wayau Abba yayi mashi kafin yace"yau naga ikon Allah!ni kake fadama kana son ganin ƴa'ƴanka?Yaran nan fa naka ne halak malak,ae ni nama yi tunanin a wurinsu zaka kwana,saboda suna buƙatarka sosai atare dasu,yanzu basu da burin daya wuce suga mahaifinsu atare dasu,"
  Wani irin daɗi ne ya lullu6e abusufyan yace
  "Zan iya zuwa wurinsu yanzu"?
Abba yace"Ka bari mu dawo daga masallaci inyaso kai tsaye kawai sai ka wuce wurinsu,"
  Fuskar shi ɗauke da farin ciki yace"okey,bari naje nayi alwala,"
  Abba yace"muna jiranka a main palour in ka kammala,ka same mu acan,"
  Yana ƙarasa maganar tashi ya juya tare da nufar ƙopar ɗakin nashi ya fuce tare da tura masa ƙopar,
  Toilet abusufyan ya shiga batare da 6ata lokaci ba,ya ɗauro alwalar,
Lokacin daya fito babban falon anan ya same su kowannansu ka kalla zakaga alamun damuwa a fuskokinsu,wasu ma da alama basuyi bacci ba,musamman Marshal Omar babu alamar yayi bacci adaren jiya,hatta Sgr ma akwai alamun rashin isasshen bacci atattare dashi,taya zaiyi bacci sayyadi na yawo acikin gari,shi fa in ya ƙullaci mutun irin haka har sai yaga bayanshi sannan yake samun kwanciyar hankali,su twins kuwa fuskokinsu sunyi jawur su da fawan,kowa dae da damuwa aranshi,

Bayan sun kammala haÉ—uwa suka wuce masallaci atare,

Tura ƙopar ɗakin nasu azmee tayi don ta tashe su sallar asuba,ba ƙaramin mamaki tayi ba,ganinsu ajere suna sallah,kowaccensu na sanye da dogon hijabi a jikinta hijjaban sehrish ne hosana da jahad suka sanya,abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,dama indae suna tare su ukun,musamman in akace maka akwai jahad atare dasu tofa basa wasa da ibada,duk da itama Sehrish ɗin ba daga baya ba,amma jahad ɗin itace kan gaba,saboda ita ba'a tashinta sallar asuba da zarar anfara kiran sallar asuba duk nisan baccin da tayi zata farka ne da kanta,abun sama rai ne da kuma sabo da yi,da kuma imanin mutun,

*Murmushi kawai azmee ke saki tana kallonsu gwanin ban sha'awa,ƴa'ƴan abusufyan,jikokin Ammi da salahuddeeen,ƴa'ƴan ƙanin Abban sojoji Abusufyan,ƙanne ga Marshal Da Sgr duk su kaɗae,abun farin ciki abun murna!yanzu su sun zama abunso wlh,yayyansu gaba ɗaya sojoji har goma sha takwas,ko sauro ne yayi gigin Cixon fatar jikinsu sae yaji saukar alburushin bindiga asaman goshin shi* 🤣

Azmee na tsaye tana kallonsu taji alamun motsin mutun a bayanta,jin an dafa ta yasa tayi firgit ta ɗan juya,Hajiya azeema ce jikinta sanye da hijabi blue,hannunta ruƙe da carbi,fuskar nan ɗauke da murmushi tace"Nazo ganin ƴa'ƴanmu ne,idan ba damuwa ki bani hanya in wuce ciki,"
  Murmushi azmee tayi tare da matsa mata hanya ta wuce ciki,sai da ta shiga ciki sannan azmee tabi bayanta tana cewa"sallah nazo in tashe su suyi,shi ne na same su ashe har sun tashi ma,abun ba ƙaramin burgeni yayi ba dana gansu ajere su ukun suna sallah,'
  Murmushi hajiya azeema tayi ayayin da take zama daga gefen gadon su tace"Albishirinki,"tayi maganar tana kallon azmee,
  Azmee tace"Goro,"
"Fari ko ja,"cike da zolaya tayi maganar,
  "Fari dae,shi ne ke tare da alkhairi,wannan launin jan alamace ta hatsari,"
Dariya hajiya azeema tayi kafin tace"Tab jiya anyi babu ke!Labari da É—umi É—uminsa!zazzafan gaske....'
  A ƙagare azmee tace"Meya faru"!
A lokacin su jahad sun sallame sallah,suna zaune saman dardumar suna sauraransu,
Nuna su hajiya azeema tayi tare da cewa"Ke wai ashe yaran nan Æ´a'Æ´an abusufyan ne!!!"
  Gaban azmee ne ya faɗi Rasss!saboda yadda maganar ta dirar mata kai tsaye acikin kunnuwanta,
  "Wai dagaske"?tayi tambayar cike da mamaki,
  Hajiya azeema tace"hmmmm ke dae bari,wani iko sai ubangiji,dagaske fa nake,babu wanda baiyi mamakin wannan abun al'ajabin ba,yara dae ƴa'ƴan ƙaninmu ne sufyan,'
  Juyawa azmee tayi tana kallonsu sehrish da sukayi zuru suna kallonsu musamman Sehrish da batasan kan zancen ba,saboda bata a hayyacinta lokacin da akayi maganar,amma lokacin da jahad ke bada labarin rayuwarsu taji komai a kunnanta kuma daga nan ne Sihirin jikinta ya lalace saboda tunaninta daya rinjayi kwalwarta harta tariyo dukkan abunda ya faru arayuwarsu ga kuma addu'ar da Sgr keta yi mata acikin kunne,
Chapter 2 · 0% Book details