← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 212

Sashe 139

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lalla6awa tayi ta haye saman gadon,saitin wurin da Jahad take a kwance,hannu tasa tana É—an bubbugata yayin da take ambaton sunanta a Hankali don kada ta tashi Oummansu,
  "Jahad!jahad!"can cikin bacci jahad tajiyo muryarta,dakyar ta iya buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci,ganin Sehrish yasa ta dan mike daga zaune"lafiya rishi?dama baki yi bacci ba?"
  "Jahad duk ba wannan ba,wata tambayace nakeso nayi maki,A ranar da kuka fita tare da Junaid shan ice cream shin kin kula akwai agogon diamond da ring a hannunshi ko babu"?
  'Meyasa kikayi mun wannan tambayar Sehrish!So kike ki tayarmun da hankalina?Kinsan fa banaso ana tunamun mutuwar Junaid,"tayi maganar hawaye na zuba akan fuskarta
  Arude Sehrish tace"dan Allah ki sassauta muryarki Jahad,bana so kowa yaji,nasan baki so amma dan Allah ki yi hakuri ki amsa mun tambayata,"
  Shiru Jahad ta ɗan yi da alama ta shiga zurfin tunani,kusan minti 5 kafin tace"Kamar naso naga zoben a hannunshi,Amma bazan iya tunawa ba gaskiya"
  "Ko hoto baku ɗauka tare dashi ba"?
  Rai aɗan 6ace Jahad tace"haba Sehrish sai kace wata ƴar jarida,irin waɗannan tambayoyi haka?
  "Nidai ki amsa mun tambayata,"a kule tayi maganar,
  Ganin ranta ya 6aci yasa Jahad cewa"Am Sorry,munyi hoto da junaid,hada ma videos muka ɗauka,Amma wayar bata a hannuna,Tana a wurin Ya Omar....."tunkan takai ƙarshen maganar Sehrish ta fuce daga cikin ɗakin a fujajen.
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋

𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠

*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*

Abun ya É—aurewa Jahad kai,irin wannan tambayoyi haka,Anya ba aljanu bane suka shige ta ba,

Babu kowa a babban falon,ko tsoro bata ji haka ta nufi Upstairs,gudu gudu sauri sauri take tattaka staircases ɗin,kaitsaye ta wuce bedroom ɗin Marshal Omar,sallama tayi jin anyi shiru ba'a amsa mata ba,Yasa ta fada cikin falon nashi,babu kowa a falon,da sauri ta nufi bedroom ɗinshi,a bakin kopar ta tsaya tare da Leƙawa cikin ɗakin nashi,A kwance ta same shi yana ta bacci,Ajiyar zuciya ta sauke,Cikin sanɗa ta shiga cikin ɗakin nashi,saɗaf saɗaf ta nufi side drawer dinshi dake a righ hand na gadon,Zuƙunnawa tayi agaban drawer chest din,Ta sanya hannu tana bubbuɗesu a hankali,tare da bincikawa ko zata ga wayar jahad,babu ita aciki,a hasale ta miƙe ta nufi wardrobe din kayan shi,gaba daya duk ta hargitsa kayan amma bata ga wayar ba,tsayawa tayi a tsanake ta shirya mashi kayanshi yadda suke,Bayan ta kammala jiki asanyaye ta nufi hanyar fita daga ɗakin dakatawa ta yi da yin tafiyar,Waiwayowa tayi tana kallon cikon ɗakin,tunani take yi kamar akwai wurin da bata duba ba,can ta tuna da Drawer ɗin dake ɗauke da mirror,da sauri ta juya izuwa gaban mirror ɗin,Janyo gida na farko tayi lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya,ganin Wayar Jahad ajiye aciki,

Saukowa downstairs tayi,a main palour É—in ta zauna saman Sofa tare da kunna wayar don akashe take,Allah yaso babu password a wayar,

Direct ta shiga Gallery ɗin wayar,videos ta gani tare da hotunan dasu Jahad sukayi tare da juna,A hanzarce ta shiga kunna videos ɗin ta ƙura ido tana kallonsu,
  Cikin motar Junaid shi da Jahad suka ɗauki video ɗin da take kallo,da hannu ɗaya yake ɗaukarsu video,yayin da dayan hannu ya rungumo jahad ajikinshi yana dariya,yana fadin"With My Juliet,My wife to be in sha Allah"
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu rass!rass!a zabure ta miƙe tsaye tana kallon yatsun hannun Junaid dake sanye da diamond ring ɗinsa,ya Aza hannu saman sumar kan jahad Sosai Zoben ya fito mai ɗauke da harafin *J* sai ƙyalli yake yi

Abun yayi matukar É—aure mata kai,a rude tace"Kai!junaid ya fita da zoben shi aranar!Ya akai zoben kuma ya koma É—akin Aunty azmee?Taya akai hakan ta faru?Ta yaya zoben shi ya koma É—akin Aunty azmee..?" tuni zufa ta wanke mata fuskarta,Still bata kawo komai aranta ba,

Jiki na rawa ta nufi bedroom É—insu,asaman side drawer ta É—auki wayarta da ta ajiye,kafin ta ajiye wayar Jahad asaman drawer É—in,

Gaban mirror ta koma ta zauna saman kujera,Layin Aunty Azeema ta kira,Cikin sa'a wayar ta soma Ringing,'natsuwa tayi tana jiran ta amsa kiran nata,jikinta sae kerma yakeyi,Allah Allah take yi acikin ranta ta samu Aunty azeema ta É—aga kiran,
Almost 15 missed Calls hajiya Azeema bata ɗaga kiran ba,A ƙarshe dole ta haƙura da kiran nata,ba don taso ba,saboda akwai wani muhimman abu da take so ta tambayeta kuma a wurinta ne kaɗai zata iya samun amsoshin tambayoyin da take dasu,

Ajiye wayar tayi gaban mirror ɗin,Kafin ta miƙe tsaye tare da kai idanuwanta ta kalli wall clock ƙarfe 2 na dare,

Dafe kanta tayi saboda matsanancin ciwon kan da ya farmata lokaci guda,a sakamakon tunanin da take ta yi,Zuciyarta tayi nauyi sosai,ga kokwanton da take yi,ga fargabar da take ji,Abubuwa dak sun tarar mata,

Don bala'e a zaune ta kwana,batare da ta runtsa ba,sai wuraren sallar asuba bacci ya É—auketa can cikin kunnanta taji ana ambaton Sunanta sehrish sehrish,a firgice ta farka,idanuwanta a zare,

Oummansu ta gani atsaye tana kallonta"Sehrish A zaune kika kwana?meyasa baki tafi É—akin Auntyn taku ba"?
Muryarta da alamun bacci bai isheta ba tace"Oumma,bansan bacci ya É—auke ni ba,"
   "Ki tashi kiyi sallah,Anata kira"ta ƙarasa maganar tare da wuce wa cikin toilet,

Miƙewa tayi dakyar take iya ɗaga ƙafarta saboda baccin da take ji,zuwa ta fara yi ta hau saman gadonsu ta tayar dasu Hosana suka farka tukunna ta sauko,bayan kowa yayi al'wala,Abu ta shimfiɗa masu Sallaya suka kabbara Sallah,a tsanake suke yin sallar,Bayan sun kammala sallar ne sun zauna kowa ya ɗaga hannunshi suna addu'a,Sehrish ta ɗan yi gyaran murya tare da cewa"Oumma,Jahad Hosana,dan Allah ku tayani da addu'a,Akan abunda nake yi,"

"Kada ki damu indai addu'a ce kin samu rishi,"acewar Oummansu,hosana tace"A nawa"?
  Harara Sehrish ta wurga mata batare da ta tanka mata ba,

Suna cikin yin addu'ar nan,Wayar Sehrish dake ajiye gaban mirror ta soma ruri,A zabure ta miƙe tare da nufar wayarta,
   "Kira kuma tunda Asuba?Wanene ke kiranki"?tsayawa tayi cak jin abunda oummansu tace,juyawa ta ɗan yi tare da kallonta,ɗan murmushi ta sakar mata"ummm dama Ina tunani ko Aunty Azeema ce ke kira ne"
  "Okey,ki amsa kiran"da sauri Sehrish ta ƙarasa gaban dressing mirror ta dauki wayar tare da duba screen ɗin,Wani irin farin ciki ne ya lullu6eta ganin kiran Aunty Azeema,

Juyawa ta É—an yi kamar mara gaskiya ta saci kallon Oummansu dake zaune saman darduma,Hosana harta fara hammar bacci sai cewa takeyi"Wai Oumma addu'ar bata isa haka ba?Dan allah mu koma mu kwanta,murmushi abu tayi tare da kallonta,
"kije ki kwanta mana,Wani ya ruƙe maki ƙafafunki,ibadarma baki iya yi da abinci ne duk mun yawanshi sai kin tada shi....."jahad ce tayi maganar tana harararta,
  Ganin hankalinsu ya koma kan Hosana yasa ta lalla6a ta fuce daga cikin ɗakin,Gudu gudu sauri sauri take tafiya,kaitsaye ta nufi hanyar nan da zata sadaka da wajen gidan,fitowa tayi ta nufi garden don batason kowa yaji ta,

A gefen wata bishiya ta tsaya,tare da duba Screen É—in wayar missed call har 3 Aunty azeema tayi mata,Danna mata kira Sehrish tayi cikin sa'a Auny Azeema ta É—aga kiran,

A hanzarce Sehrish ta kara wayar a kunnanta,tun kafin tayi magana Aunty Azeema tace"Sehrish lafiya kuwa?kin tashi hankalina,kawai ina farkawa yin sallar asuba sai naga missed calls É—inki"

Muryar ta har shaƙewa takeyi saboda tsabar saurin tayi magana"Aunty azeema,babu abunda ke faruwa,lafiya lou nake,Dan Allah wasu tambayoyi ne nakeso nayi maki,Wani Assignment ne aka bamu a school,"

"Okey,Allah yasa nasani"
"Aunty azeema,Malamar da ta bamu assignment ɗin tana buƙatar muyi bincike akan wani accident daya faru ne,Sai mu sanar da ita amsar da muka samo,"

Natsuwa hajiya Azeema tayi tana sauraronta,
  "Saurayi ne da budurwa,suka shirya zuwa shan ice cream,to akan hanyar zuwansu,sai suka dakata agefen titi,ita budurwar ta tsallaka titin zata siya musu ice cream,ta bar saurayinta acikin motar,kwatsam sai ga wata truck ƙatuwa tabi ta kan motarsu,nan take kuma sai wuta ta kama ci da motar,kafin ƴan kwana kwana su ƙaraso wurin,Wutar taci ta cinye,ba'a samu komai ba daga sassan jikin saurayin,

Katseta Aunty azeema tayi"ita malamar taku me takeso ku gano mata ne,"

"Bari na kai maki ƙarshen labarin,shi saurayin ya zama toka,sai ƙarahunan motar aka samu,to abun mamaki kawai sai kuma ga Zobenshi na Diamond an tsince shi a hannun wani dattijo,zoben bai yi komai ba,sai ƙyalli yake yi kamar sabo,to shine take son kowa yayi nazarin labarin ya fada mata abunda yake hasashe"

Abun mamaki tana kai ƙarshen labarin sai taji Aunty azeema na dariya,bubbuga ƙafa Sehrish tayi kamar tana agabanta"Wayyo Allah mommy azeema,meyasa kike dariya,dan Allah ki taimaka ki bani amsar tambayata,"

Tsagaitawa tayi da yin dariyar,sannan tace"Abun mamaki abun Al'ajabi,kawai sai aka tsinci zoben diamond ɗin saurayin a hannun wani,bayan shi mamallakin Zoben ya ƙone ƙurmus,Gaskiya Sehrish ta baku Assignment me wuya,Amma fa ni abunda nake tunani,in har babban Diamond ne kamar irin wanda na ta6a siya ma Junaid,nasan kin ta6a ganinshi a hannunshi mai harafin J,"

  Muryarta har kerma takeyi wurin amsa mata"eh naganshi ahannunshi"
"Yawwa,so kin ga kalar wannan Diamond ɗin,In har wuta ta ta6a shi baiyin komai,Sai dai akwai wani abunda yake yi idan wutar ta haura mintuna tana ci ajikinshi,Stone ɗin jikinshi zaiyi duhu sosai,kuma ba hakan yana nufin ya mutu bane,Lafiyarshi ƙalau Amma fa wannan duhun da dutsen jikinshi yayi,A nigeria basu da chemical ɗin da zasu gogeshi,Sae dai anan dubai Companyn da nake siyayyar Diamonds ɗin a wurinsu ne kaɗai zasu iya goge wannan baƙin ya dawo yana ƙyalli"

"Amma Aunty Azeema me kike tunani game da Zoben da aka tsinta hannun wani dattijon?Wanda kuma ba'a gabanshi hatsarin ya faru ba,kuma shi saurayin da zoben ya shiga cikin motar Har ya haɗu da hatsarin"ta ƙarasa maganar tana jiran amsarta,don a ƙagare take,
Chapter 139 · 0% Book details