← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 212

Sashe 38

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sam ta manta da hafsat dake kwance a ɗakinta,baiwar Allah tun bayan fitarta daga ɗakin hayaam,ta wuce ɗakin azmee batare da sanin kowa ba azmee ce kaɗae tasan cewa tana a ɗakinta,anan tayi wanka,ta kuma ci abinci ta kwanta,saboda wani irin zazza6i daya saukar mata ajikinta,kwata kwata zuciyarta ba daɗi,tayi danasanin rayuwarta fiye da a ƙirga,idanunta na tsananin son ganin Su Jahad,amma tsoran tunkararsu takeyi,gashi har tsaraba tayi masu don ta basu hmmm,duk in ta tuna irin uƙubar da suka sha a hannunsu,sae ta fashe da matsanancin kuka,tun azmee na rarrashinta har ta gaji ta ƙyaleta,idanunta sun kumbura suntum haka la66anta ma,bakomai take yi ma fargaba ba,fa ce irin hukuncin da Mahaifinta zai yanke mata,don kuwa tasan muddin yaji abunda suka aikata masu jahad,Wlh ba zasu sha ba,su dukan su sae sun fuskanci mummunan hukunci a wurinsa,gaba ɗaya tayi nisa cikin zurfin tunani,taji shigowar azmee cikin ɗakin,buɗe idanunta tayi tana kallon azmee dake shigowa,yanayin yadda taga fuskar azmee ya tabbatar mata da cewar tana cikin damuwa,gefen gadon ta zauna zugudum yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,
  "AUNTY AZMEE" muryar hafsat ce ta dawo da ita cikin hayyacinta,juyawa tayi bayanta tare da kai idanunta kan fuskar hafsat dake kawance,ƙoƙarin 6oye damuwarta tayi kafin tace"har yanzu bakiyi bacci ba?
  Miƙewa hafsat tayi daga zaune,sannan tace"Bazan iyayin bacci ba aunty azmee,inajin tsoron abunda zai biyo baya,nasan cewa daddy bazai ƙyaleni ba,"ta ƙarasa maganar tana faman matse kwallon dake gangarowa akan fuskarta,
    "Kidaina sa damuwa aranki hafsat,a yadda kika bani labarin irin ruƙon da kuka yi masu jahad,da farko atare kuka azabtar da rayuwarsu ke da mahaifiyarki amma kuma daga baya kin nuna masu soyayya,ina mai tabbatar maki da cewar wannan soyayyar da kika nuna masu daga baya itace zata cece ki a hannun mahaifinki...."
  "Taya kike tunanin hakan zai zame mun mafita aunty azmee?bayan ni ce dakaina,na ɗauki su jahad acikin mota ta,na fitar dasu daga cikin gidan,na damƙa su a hannun wannan mugun mutumin wanda mommy tasa ya zubar mata dasu a daji!"tana magana hawaye na zuba a fuskarta,
  "Amma Ae kin sanar dani cewar,Mommynki yaudararki tayi akan cewar gidan marayu zaki kai su ashe zubar dasu take so ayi,"
  "Hakane aunty azmee,amma ae su hosana basu son da haka ba!nasan cewa sun tsaneni yanzu,kallon mayaudariya suke yi mun,kuma ba kowa ne ya jawo mun haka ba,fa ce Mommy,"
   Ta ƙarasa maganar tare da fashewa da wani sabon kukan,
   "Ga shawara"! Cikin shessheƙar kuka Hafsat tace"Ina...sauraronki,koma wata irin shawarace inaso,"
  "Gobe da safe tun kafin Abbanki ko Omar suyi yunƙurin tunkarar Su jahad akan maganar,ke ki fara yin hanzarin zuwa wurinsu ki nemi yafiyarsu sannan kiyi masu bayanin cewar bada saninki ba,wannan mutumin ya ɗauke su ya kaisu daji don ya zubar dasu ba,Mommynki ce ta yaudareki akan cewar gidan marayu zai kai su....."
  "Aunty azmee kina ganin in na faɗa masu hakan zasu yarda dani?hosana fa tana da ta6in hankali,daƙyar zata fahimce ni,"
.."kada ki damu,zasu fahimce ki,ki kwantar da hankalinki kawai,kamar kina acikin jirgi mai ya qare,"murmushi hafsat ta É—an saki,har taji sanyi aranta,fatan ta Allah yasa gobe in taje wurin su Jahad,su fahimce ta,
Sun jima suna tattaunawa atsakaninsu kafin daga bisani,azmee tabar É—akin hafsat kuwa bargo taja ta lullu6e kanta,sannu a hankali bacci ya É—auke ta,
  
Acan falo kuwa bayan komi ya lafa,Ammi tace"Yakamata kowa yaje yayi sallah,ya kwanta ya huta,"amsa mata suka yi da toh,sannan kowannansu ya miƙe tare da nufar Bedrooms ɗinsu,atare Su jahad suka miƙe,saida suka fara yi ma su ammi sallama,ta amsa masu fuskarta asake tare da tunasar dasu akan in zasu kwanta kar su manta suyi addu'a,a ƙarshe dae falon ya rage babu kowa cikinsa,irfan shiya jagoranci Modibbo har zuwa ɗakin da zai zauna kafin gobe,Bayan ya kaishi ɗakin,Azmee ta shirya mashi kayan tea takai masa,kamar yadda ya buƙata,

*Boss Bature*

  🤍❤🤍

A 6angarensu sehrish kuwa,bayan sun koma bedroom ɗinsu,alwala kowannansu yayi sannan su kayi salla atare,bayan sun kammala suka haye saman gadonsu,cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauki Jahad da Hosana,banda sehrish wadda bacci ya ƙaurace ma idanunta,tabbas ɗazu ta tsorata sosai da Ammi ta koresu,abun ya razanar da ita,ta kuma ji matuƙar tausayin Daddynsu,duk in tazo rufe ido,fuskarshi take gani a lokacin daya fashe da kuka yana faɗin cewa sai dai ta tsine mashi amma sai yabi ƴa'ƴan shi,bazai bari rayuwarsu ta wulaƙanta ba,tabbas ba ƙaramin so yake yi masu ba,yana tsananin ƙaunarsu fiye da tunaninsu,lokaci guda abunda ya faru a babban falo ya shiga dawo mata acikin kanta,mikewa tayi daga zaune,ta jingina bayanta a headboard din gadon,yayin da hannayenta ke rungume da pillow,a hankali tashiga tariyo abunda ammi tayi,na bijirema umarnin iyayenta,wanda hakan yasa ita ma ƴa'ƴanta suke bijire mata,Wannan abun ba ƙaramin tsoratar da sehrish yayi ba,saboda tunawa da Umarnin da mahaifinta ya bata na hana ta zuwa sashen sgr da sunan yi mashi aiki,amma taƙi bin umarninsa,hakanan ta dinga jin gabanta na faduwa,runtse idanunta tayi tare da buɗesu a hankali,wasu siraran hawaye ne suka shiga gangaro mata a fuskarta,a hankali la66anta suka soma motsi,ƙasa ƙasa take magana,matsar da kunne na nayi don inji me take cewa,
_Ya Allah ka yafemun!bani da hankali nayi kuskure,saboda kawai son wanda baisan inayi ba,saboda na faranta ma wanda nakeso,naƙi bin umarnin mahaifina,wlh bazan ƙara ba,inajin tsoron nima ƴa'ƴan da zan haifa suƙi bin umarni na,bana fatan hakan ya faru,zan daure nayi mashi biyayya_
  Tafin hannunta tasa ta goge hawayen dake zuba a idanunta,bakomai idanunta ke hango mata ba,fa ce kyakkyawar fuskar SGR,tabbas yau yayi masu abunda ba zasu ta6a mantawa ba arayuwarsu,yana da matuƙar kirki sosai,bakowa ne zai gane hakan ba farat ɗaya,shi na musamman ne,samun mutun mai irin kyakkyawar zuciyarshi a wannan zamanin da muke ciki,zaiyi matuƙar wuya,
  Zuro ƙafafunta tayi ƙasa daga saman gadon,ta miƙe tsaye,jikinta na sanye da riga da wando na bacci,milk colour,takawa tayi izuwa gaban door ɗin dakin,ta buɗe bayan ta fita ta janyo masu ƙopar ta rufe,
  A hankali take tafiya,ga wani irin sanyi dake ɗan ratsa sassan jikinta,amma sam bata jin sanyin,saboda daɗinshi take ji,zura hannayenta tayi acikin aljihun wandon jikinta,kai tsaye ta wuce main palour din,wayaam taga babu kowa kamar yadda tayi tsammani,da alama ma mutanen gidan duk sunyi bacci,hakanan taji tana marmarin tasha Cornflakes acikin wannan daren,juyawa tayi da sauri ta nufi kitchen,within minutes ta fito hannunta ɗauke da Cup,ta cika shi da cornflakes haɗi na musamman tayi mashi,ta zuba uwar madara da bornvita duka ta sanya,ta kuma Tsula sugar,'
  Dawowa tayi falon,ta zauna saman sofa tare da aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,nace sannu ƴar masu gidan,
  Motsa cornflakes ɗin ta shiga yi,da cokalin hannunta sae faman jujjuyashi takeyi aciki,kafin daga bisani ta shiga ɗebowa tana kaiwa abakinta tana sha,tana taunarsa kunnuwanta na motsi saboda daɗin da yayi,bakowa ne ya faɗo mata aranta ba fa ce junaid,abokin shiriritarta,murmushi tayi tare da cewa ɗan uwana rabin raina nasan yanzu haka yana can yana sharar baccinshi,da ace idonshi biyu da atare zamu sha wannan cornflakes din,i really missed u junaid,rashin kwanciyar hankali yasa,mun nisanta da juna,amma insha Allah tunda komai ya dai²ta,yanzu bamu da sauran wata damuwa,zamu dinga fita yawan shaƙatawa atare mu dukkan mu,

Ita kaɗae abunta sai faman sambatu takeyi,kamar wata zautacciya,tana cikin shan cornflakes ɗinnan,ta wutsiyar idonta ta hango mutun a tsaye ƙiƙam,aikuwa hankalinta yayi mugun tashi,kasa juyawa tayi saboda tsoron kar ace dodo ne,tuni jikinta ya fara kerma,dama gata da shegen tsoro,zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi,tunaninta wanene mutumin data hango tsaye a upstairs,tsabar tsoro ya hana ta juyawa ta kalleshi da kyau,wani irin wahalallan yawu ta haɗiye,ajiye cup ɗin dake hannunta tayi,sannan ta lalla6e tare da saukowa daga saman sofa ɗin,ta durƙushe ƙasa tayi sujjada,kamar maiyin sallah,duk don saboda kar dodon ya ganta,a hankali ta shiga rarrafawa a ƙoƙarinta na tabar falon,ta koma ɗakinsu,
  Shikuwa mutumin dake tsaye goye da hannayenshi asaman ƙirjinshi,zuba ma sarautar Allah ido yayi,abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,tsoran yarinyar harya so yayi yawa,ko kallon inda ya ke bata yi ba,ta wutsiyar ido kawai taga inuwarsa amma ta sama ranta cewar wani mugun abunne,sam baiso ta tsorata ba,don bada niyar wannan yazo wurin ba,
  Wani abune ya faɗo mashi aransa,cikin sauri ya koma cikin part ɗinsa,jimmm kaɗan sai gashi ya dawo hannunshi ɗauke da wayarsa,tsayawa yayi tare da saita wurin da take yana ɗaukarta video kasancewar akwai haske sosai a main falo din,
  Ba ƙaramar wahala sehrish tasha ba,da wannan rarrafen ta ƙarasa har wurin da zata shiga corridor ɗin ɗakinsu,gaba ɗaya zufa ta wanke mata fuskarta,tana ƙokarin shiga,wani abu ya faɗo mata aranta,tsayawa tayi tana tunanin kodai ta juya taga wanene shi tunda dae ta iso wurin da zata shiga ɗakinsu,koma menene ai bai isa ya cutar da ita ba,da zarar ta juya taga dodo ne,sae ta watsa da gudu ta shige ɗakinsu,taja ƙopa ta rufe,fakat,
  Jikinta na kerma,amma ahaka ta daure ta ɗan juyo da kanta,takai idanunta saman upstairs din,ae batasan lokacin da taƙarasa juyowa gaba ɗaya ba,ta baza idanunta donta tabbatarma kanta abunda take gani,ƙura ido tayi tana son gano wanene saboda yayi mata nisa,wannan hasken fatar nashi ne ya fara sa ta tunanin kamar sgr ne,ƙara zuba ido tayi anan ta hango wannan doguwar sunar kan tashi,tabbas kuwa shine,ajiyar zuciya ta shiga saukewa a fili tace"Ashe babban yaya ne,nasha wahalar banxa,Allah yasa dai ban zubar da cornflakes ɗina ba,
  ganin tana kallonshi,yasa ya janye phone dinsa,ya kashe camera ɗin ya tura wayar a short pocket dinsa,da hannu yayi mata Alamar taxo,
  Waro ido tayi tare da nuna kanta,don ta tabbatar in ita yake kira,nuna ta ya kuma yi da hannunshi,
  Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba rasss,tsoranta kar ya tuhumeta akan meya hanata zuwa part ɗinsa kai mashi Cofee don yau bata je ba,
Chapter 38 · 0% Book details