← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 212

Sashe 161

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har saman wuyanshi Junaid yakai hannunshi zuwa saman ƙirjinshi,har lokacin bai daina ambaton sunanshi ba,ga la66anshi sae kerma  su ke yi,
  Murmushi kawai suke saki suna kallonshi,
"Gaskiya tunda nake banta6a ganin ƙauna tsakanin mahaifi da ɗansa ba,irinta mahaifinku da wannan ƙanin naku,"Dr emran ne yayi maganar,da mamaki akan fuskarshi,
  Sai lokacin Alex ta samu damar yin magana
  "Nikaina da nake mahaifiyarshi bana tunanin yanayi mun irin son da yake yiwa mahaifinshi,Koda yake dole yaso mahaifinshi akaina,shaƙuwarsu ta wuce tunaninmu,"
  Suna cikin yin maganar,Abbansu ya fara ƙoƙarin buɗe idanuwanshi,Wani irin nauyin bacci ne ya hanashi tun ɗazu ya farka,amma yana jin muryar Junaid acikin kanshi,sake ambaton sunanshi Junaid yayi da wata irin kasalalliyar murya,
  "Abba,"tunkafin Ya buɗe idanuwanshi ya soma kiran sunanshi"Junaid"gaba ɗaya suka matso kewaye da gadon suna murmushi,Yayin da idanuwansu ke akan Abbansu,
  Ruƙo hannun Junaid yayi acikin nashi,sosai har cikin ranshi Yaji dagaske Shi ɗinne,kokawa ya shiga yi da baccin dake ƙoƙarin hanashi buɗe idanuwanshi,
  Daƙyar ya ɗaure ya ware idanuwanshi,a wani slow ya wurga eye balls ɗinshi kan Junaid dake kwance agefenshi,Tunda ya ɗaura eyes ɗinshi akan fuskar Junaid ko ƙyaftawa baiyi kamar an dasa mashi aya,wani irin farin ciki ne ya lullu6eshi lokaci guda hawaye suka shiga wanke mashi fuskarshi,Muryarshi na kerma Ya ambaci sunanshi"Junaid!dagaske kaine a kusa dani,Junaid ɗina ne atare dani"?
  "Yaya hossein dagaske ne abunda kake gani,ga Junaid ɗinka nan,an dawo maka dashi"Abusufyan ne yayi maganar,
  Lumshe idanuwanshi yayi tare da sake buɗesu a hankali yana cigaba da kallon fuskarshi,Lokacin daya ankara da Jini da ake ƙara mashi aruɗe yace"Me ya same shi?Sun cutar mun dashi ko?duk sun canza mun Junaid ɗina kamar bashi ba,"
  "Abba,ka kwantar da hankalinka,Junaid yana samun sauƙi,"Omar ne yayi maganar cikin sigar lallashi,
   "Alhamdulillah Ya Allah daka dawo da farin cikana"ya ƙarasa maganar tare da dago da hannunshi zuwa cikin sumar kanshi,
  "Allah Ya baka lafiya Junaid ɗina,ka yafe mun duk laifina ne halin daka shiga,Bazan ƙara yin kuskuren da zan rasaka a kusa dani ba"yana magana hawaye naci gaba da sauka akan fuskarshi,

Jikinsu duk yayi sanyi,tsananin tausayinsu ne ya kamasu,

Wuraren ƙarfe 10 na dare,Abusufyan ya kwashe su Sehrish zuwa gida,Su biyar ya ɗauko hada Amrish da Oummansu,Ba don sun so ba ya ɗaukosu,lokacin da ya ƙaraso cikin gidan bayan yayi parking ɗin motar,Buɗe motar Oummansu sehrish tayi tare da fitowa waje,Bayan Abusufyan Ya fito ya zagaya ya buɗema su Sehrish,saukowa tayi daga cikin motar,Amrish ma ta sauko bayan ita sai Jahad,duk suka fito banda Hosana,ruƙo hannunta Yayi tare da ambaton sunanta,Daƙyar ta iya buɗe idanuwanta,
  "Ki fito ku wuce gida,Sae ki kwanta ki ƙarasa baccin naki,"A yamutse ta fito daga cikin motar,ruƙe hannunta Sehrish tayi ganin tana tangal tangal zata faɗi ƙasa,
  Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da kallonsu yace"Ku wuce ciki mana,Ni zan koma ne,zuwa gobe zamu dawo gida sai acigaba da jinyar tasu a gida,"
  Gyaɗa kai abu tayi tare da cewa"shikenan,Allah ya basu Allah,Amma Mommy fa?zata dawo itama"?
  "Sai zuwa gobe zamu dawo tare da ita,"ya ƙarasa maganar tare da kallon Jahad,
  "Banga kina farin ciki ba,ko bakiyi murna da ganin Masoyin naki bane"? Zuba mashi ido kawai tayi batare da tace komai ba,itafa har yanzu bata yarda Junaid bane,zaiyi wuya ta yarda inba an sanar da ita Yarda akai Ya tsira daga cikin motar nan ba,
  Sehrish na ƙoƙarin buɗe baki tayi mata magana,muryar AZMEE ta katsesu,
  "Sannunku da dawowa,"gaba ɗaya suka kai idanuwansu kanta,
  Jikinta na sanye da dogon hijabi,fuskarta da alamun damuwa,
  Ɗaure fuska Abu tayi,sam ta tsani ganin Azmee arayuwarta,
  Ƙarasowa tayi gaban motar da suke a tsaye,
  "Abusufyan Ya mai jikin?ɗazu naso na biyoku asibitin amma bansamu hali ba,Da yake tunda safe ina kwance ba lafiya,"tunda ta soma magana,Amrish ta ƙura mata ido tana yi mata kallon sani,kamar yarda amrish ke kallonta,itama haka take kallon Amrish ɗin,
  "Jikinshi da sauƙi,zuwa gobe zamu dawo gida,Ya jikin naki?naji kince bakya lafiya,"
  "Alhamdulillah,Naji sauƙi,Idan zaka koma asibitin akwai dinner dana kammala Yanzu,bari na shirya maka kayan abinci saika kai masu,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta wuce ciki,
  Abu ji take kamar ta hana Abusufyan ya kar6i abincin nan don bata yarda da ita ba,tsoranta kada ta sanya masu guba aciki,"
   Ganin sunƙi shiga gidan Yasa Abusufyan yi masu magana"Tsayuwar me kuke yi ne?ku wuce ciki mana,wanda zaiyi wanka yayi wanka,ku kwanta ku huta,"
   Sallama su kayi mashi,kafin suka nufi cikin gidan,Sehrish sae faman waiwayon Abusufyan take yi har sai da ya lura da kallon da take yi mashi,tsoro take ji Ya tafi ya barsu tare da Aunty Azmee cikin gidan,gashi babu kowa Su kaɗaine mata,
Bayan shigarsu da Æ´an mintuna,Azmee ta fito hannunta É—auke da food basket mai faÉ—i,A bayan boot É—in motar ya shigar dashi,komawa ciki tayi jim kaÉ—an ta dawo da wasu kayan abincin ya lodasu bayan motarshi,Sallama sukayi dashi ta juya ta koma cikin gidan,

*Boss Bature*

Bayan Shigarsu gidan kaitsaye ɗakinsu suka wuce,bayan sun shiga Amrish ta buƙaci shiga toilet don tayi wanka jikinta yayi mata nauyi,bayan ta shiga wankan Sehrish ta ɗauko mata kayan da zata sanya idan ta fito daga wankan,asaman gadonsu ta ajiye mata kayan,
  "Oumma Yunwa nake ji,"Hosana ce tayi maganar tun lokacin da suka shiga dakin ta baje saman gado,Jahad na zaune gefen gadon tayi zugudum,
  Tunanin zuwa kitchen tayi don ta Shirya masu abinci,tana ƙoƙarin ruke handle ɗin ƙopar,Sai ga Azmee ta turo ƙopar ɗakin,
  "Na shirya maku abinci,nasan kuna jin yunwa,"
  Bata jira amsar da abu zata bata ba ta juya ta fuce daga dakin,Saukowa saman gadon hosana tayi jiki na rawa ta kama hanyar fita ɗakin,da sauri Abu ta ruko hannunta"Ina zaki je,"
  "Abinci zanci,"
  "Ba zaki ci shi ba,Ki bari in girka maku,"
  Kamar zata fashe da kuka tace"Nidai ki barni inje inci na Aunty Azmee tunda ta gama,"
  "Koma ki zauna,yanzu nima zan kammala girka maku,"
   "Kina tunanin cewa zan cutar daku ne?"Kwatsam taji muryar Azmee,turo ƙopar ɗakin tayi"Don me zaki hanata cin abinci na"?ranta a6ace tayi maganar,
  "Saboda ban yarda dake ba,bazan bari ƴa'ƴana suci abincinki ba,"
  "Hosana,koma ki zauna,"tayi maganar tare da nuna mata cikin dakin,
  Idanuwanta cike tab da kwalla ta juya zata koma,
   Miƙewa Jahad tayi tare da takawa zuwa bakin ƙopar ɗakin,
  "Oumma!Meya haɗaki da Aunty Azmee"?
  "Jahad babu komai,kawai banason Hosana taci abincinta ne,"
  "Amma meyasa oumma?kullum ita ke girka mana abinci muna ci,sai yau kuma Oumma"?tayi tambayar da damuwa akan fuskarta,
  Sehrish dae tana cikin ɗakin tana sauraronsu,
  "Bansan laifin da nayi ma Oummanku ba da har ta hanaku cin abinci na,Babu komai,Nidai ga abinci can wanda yaga dama yaje yaci,"takai ƙarshen maganar tare da juyawa tabar ɗakin,

  Guntun tsoki abu taja,kafin ta fuce daga ɗakin ta nufi kitchen,Don ta girka masu abincin da zasu ci,

Komawa Jahad tayi jiki asanyaye ta samu wuri gefen gadon ta zauna,yayin da zuciyarta ke ci gaba da tariyo mata fuskar Junaid,
  Hosana sae faman shessheƙar kuka take yi saboda an hanata cin abinci ga yunwa tana ji,

Fitowa Amrish tayi daga cikin toilet jikinta É—aure da towel,
"Idan kin kammala shafa mai,ga kayanan na ɗauko maki,wanda zaki sanya"ta ƙarasa maganar tana nuna mata,kayan da ta ajiye mata saman gadon,
  Murmushi ta ɗan saki tare da cewa"Nagode sosai,"sai lokacin ta lura dasu Jahad,tun suna asibiti take taso tayi mata maganarsu amma tashin hankali ya hanata,Tayi mamakin kamaninsu koda yake wannan ya wuce kama,
  "Ƴan uwana ne su naga kina kallonsu,ƴan ukune mu,Ga Jahad can wadda ke zaune gefen gadon,Wannan mai kukan banzan kuma Sunanta Hosana,Sha takwas sha tara ce,ina fata kin gane,"ta ƙarasa maganar tana dariya,Wurgo mata harara Hosana tayi ba don tana jin yunwa ba da ba abunda zai hana takai mata bugu,

Murmushi Jahad tayi tare da cewa"kiyi haƙuri,tun a asibiti naso mu gaisa,bansamu dama ba saboda halin da muka shiga,Amma yanzu inayi maki barka da zuwa,"ta ƙarasa maganar tare da ƙokarin yin murmushin dole,
  "Nagode sosai da irin karramawar da kukayi mun,"hankalinta ya ƙara kwanciya,gaban dressing mirror ta zauna,ta dauki man shafawarsu ta soma shafama jikinta,bayan ta kammala,Sehrish ta miƙa mata Kayan baccin da ta dauko mata,hannu biyu tasa ta kar6a tana yi mata godiya,

Juya baya Sehrish tayi don tasamu damar sanya kayan,Ganin hosana na kallonta yasa Sehrish wurga mata harara tace"Lafiya kike kallonta?baki ga tana sanya kaya bane,"
MurguÉ—a baki Hosana tayi'Yo me zan kalla,Tana mace ina mace,Dama Namiji ne"
  Gaba ɗaya suka fashe da dariya,hatta Amrish ɗin,ba ƙaramin nishaɗi ta basu ba,
  Shaf shaf amrish ta zura kayan ajikinta ba ƙaramin kyau su kayi mata ba,white colour ne,
  "Nasan kina jin yunwa,Kiɗan ƙara haƙuri,ga Oummanmu can tana girka mana abinci,bari naje na tayata ma,"kama hanyar fita ɗakin tayi da sauri,
  Gefen gadonsu Amrish ta zauna,
"Yaushe zaki tafi gidanku"?
Baki asake Jahad ke kallon Hosana,
Shiru Amrish tayi bata tanka mata ba,saboda bata da amsar da zata bata,
"Nan zaki kwana ne"?ta kuma tambayarta,
  Rai a6ace Jahad tace"Ba'a sani ba dan uban mutun,Ina ruwanki da ita?ko saman kanki zata kwana ne?sai shegen ɗumi kamar aku,"
  Tsuke baki hosana tayi"nidai ba ubana ba,daga tambaya sai cibi ya zama ƙari?ƙari kuma ya zama ƙwababa"
Cike da takaici Jahad ta kalli Amrish"Am sorry pls,Wlh bata da hankali,Sai addu'a,Kuma hada ƙarin tana jin yunwa shiyasa take ta soki burutsun nan,"
Murmushi amrish ta É—an saki tare da cewa"Bakomai,na fahimce ta,"
Chapter 161 · 0% Book details