← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 212

Sashe 195

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan Omar ya fito a hanzarce ya nufi ɗakin Azmee,A lokacin Sehrish tana ƙumshe cikin bargo,tajiyo bugun ƙopar ɗakin,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,duk a tunaninta Sgr ne ya dawo,gabanta sai faɗuwa yake yi,ƙin buɗe ƙopar tayi Har sai da Omar ya ɗaga Murya tare da cewa"Sister Omar ne,Zo ki buɗe mun ƙopa,"
  Cire blanket ɗin tayi cike da fargaba ta ƙarasa gaban door din tasa hannu ta buɗe mashi,tunda take bata ta6a ganin Omar cikin 6acin rai irin na yau ba,jikinshi har wani jijjiga yake yi,sam babu annuri akan fuskarshi,
  Muryarta na kerma ta ambaci sunanshi"yay...ya Omar,"
  Shiga cikin ɗakin yayi bayan ya sanya hannu ya garƙame kopar,
  A fusace Ya damƙi kafaɗunta tare da jijjigata yace"Ke!Ashe baki da hankali bansani ba?Anya kuwa kinsan ciwon kanki?kin bani kunya kin kuma bani mamaki,Ki rasa abun wulakantawa Sai Sgr?tsaran wasanki ne?dan Kin samu Allah ya mallaka maki shi shine har kike kokarin banzatar dashi?Idan saboda laifin da yayi maki ne baya baki hakuri ba!shine bazaki hakura ba!........"fashewa tayi da wani irin matsanancin kuka,

   "Don me zaki ce wai jikinki yake so?ke kinsan adadin matan dake bibiyar rayuwarshi don kawai su samu shiga awurinshi koda da sunan lalatane bada aureba,Sai ke don Allah ya jarabceshi da Sonki,ni shaidane Akan Sgr,wlh da ace baisonki bazai ta6a sha'awar ta6a jikinki ba,don yana sonki ne yasa har yake yi maki hakan,shi baturen mutun ne shiyasa yake nuna maki so ta hakan........"dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana mayar da numfashi,zufa duk ta wanke mashi fuskarshi,Sehrish kuwa sai faman shessheƙar kuka take yi,

Sassauto da Muryarshi yayi kafin yaci gaba da cewa"Yanzu hankalinki ya kwanta,kin kaishi ƙarshe,Gobe zai koma U.s,duk don saboda abunda kikayi mashi,Kuma inaso ki sani da zarar ya ɗaga ƙafarshi yabar ƙasar nan,Akwai mata dayawa dake jiranshi,daga Cikinsu akwai Eva his Uncle's Daughter,dawowarshi kawai take jira don a ɗaura masu aure...tun suna yara take sonshi,ba abunda bata mallaka ba da duk wani ɗa Namiji zai buƙata a wurin ƴa mace..,......"
  Tunda ya soma maganar tafiyar Sgr U.s da kuma Maganar Eva,hankalin Sehrish yayi mugun tashi,duk tabi ta ruɗe ta susuce,
   "Sgr baya kula mace don bashi da ra'ayin yin aure,kuma shi ba ɗan iska bane bai ta6a kusantar zina ba balle har ya aikata ta,baisan menene so ba,baisan kuma ya akeyin shi ba,Amma wannan karon Akanki Yasan menene So,ya kuma san daɗin mace,Kinga kuwa da zarar yabar ƙasar nan Ya koma can,zai amince da Auranta ne,kodan ya nema ma kanshi mafita,ke kuma zakiyi dana sani ne,domin kuwa duk macen data samu miji kamar Sgr tayi watsi dashi wlh sai tayi danasani na har Abada,"

Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan tamkar ranta zai fita,Sam ta kasa buÉ—e baki tayi magana,

"Ya Sauke duk wani girman kai nashi,Ya ajiye matsayinshi duk don saboda ke ɗinnan,Don Ya samu soyayyarki,da kanshi ya nemi da in koya mashi soyayya saboda yana son ya faranta maki,Yana kuma son ki gane cewa ba jikinki yake so ba,Zuciyarki yake so,kuma kinyi kuskure da iliminki da hankalinka,kika bari Mijinki yake kwana da baƙin cikinki acikin zuciyarshi!?"

Rass taji gabanta Ya faɗi,girgiza kai Omar yayi,tare da juyawa rai a6ace ya nufi hanyar fita daga ɗakin har ya ruke handle ɗin ƙopar ya kuma juyowa ya kalleta,
  "Ina ƙara tunasar dake,Gobe da Safe zai tafi,shawara ta rage taki,wlh don kina ƴar uwata ne yasa na zauna ina yi maki wannan gargaɗin,Saboda ina sonki dashi,Kuma kema kina sonshi,wannan damarkice ta ƙarshe kiyi tunani kafin nan da safe,nabarki lafiya,"

Yana kai ƙarshen Maganarshi,Ya buɗe kopar ya fuce waje,

Tashin hankali,Wani irin zazza6ine Ya lullu6eta,hawaye ta ko'ina saman fuskarta,wani irin tuƙuƙin baƙin ciki take ji acan ƙasan zuciyarta,sunan Eva ya tsaya mata aranta,saboda ta ta6a jin sunyi magana akanta a lokacin baya shi da Omar,har yake cewa in ma akwai Macen da ya dace ta mallake shi,to itace,

  A hankali ta soma ambaton"Innalillahi wa'inna ilahirraji'un,"

Maganganun Oummansu ta shiga tariyowa acikin kanta,daƙyar ta iya lalla6awa ta haye saman gadon ta kwanta,sosai tashiga raira kuka kamar jinjira jikinta sai kerma yake yi,Wani irin kishine ya rufeta,cikin shesshekar kuka take faɗin"Ya Rafayet zai tafi U.s ya barni,zai je ya aureta,"nutsar da fuskarta tayi jikin pillow tana ta raira kuka,

A daren Ranar Mutun biyu basu runtsa ba,WaÉ—anda zuciyoyinsu ke cikin halin ha'ula'e,kamar yadda Sgr ya kwana kwance saman gadonshi cikin mawuyacin hali,Haka itama Sehrish ta kwana da tunanin abu biyu,kalaman Oummansu da kuma kalaman Marshal Omar sun tsaya mata aranta,shi kanshi Omar É—in bai samu isasshen bacci ba,saboda damuwar daya shiga duk akan ÆŠan Uwanshi,

Wuraren Sallar Asuba Sehrish tana a kwance kamar matacciya,jikinta duk ya saki,ga zazza6in da take fama dashi tare da matsanancin ciwon kai,daƙyar ta samu ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet,agaban Sink ta tsaya tana kallon kanta cikin Mirror,fuskarta tayi jaga jaga da hawaye hada majina,jan bakin data shafa duk ya 6ata fuskar,duk ta harmutsa gashin kanta,tasha kuka sosai,lips ɗinta duk sun kumbura,hancinta yayi jawur dashi saboda matsar daya sha,tajima acikin Toilet ɗin kafin ta samu tayi alwala,

Lalla6awa tayi ta fito daga toilet ɗin ta tunkari wardrobe ɗin kayanta,hijab ta ɗauko tare da darduma ta shimfiɗata,daƙyar ta samu ta tattara natsuwarta kafin ta kabbara sallah,bayan ta kammala Sallar ta zauna tare da ɗaga hannuwanta,tana Addu'a hawaye na shararowa akan face ɗinta,jikinta duk yayi sanyi,A saman dardumar bacci ya ɗauketa,

Baccin bai kaiga yin nisa ba aka soma kwankwasa ƙopar ɗakin,kwan kwan,can cikin bacci take jin bugun ƙopar,firgigit ta farka,zufa sharkaf akan fuskarta tamkar an watsa mata ruwa,bakomai bane ya fado mata aranta ba fa ce Maganar Omar na cewa Yau Sgr zai koma U.s,A hargitse ta miƙe tare da nufar ƙopar tasa hannu ta bude,Amrish ce a tsaye jikinta sanye da hijabi,ganin Sehrish cikin damuwa yasa tace"Meya faru ne?baki da lafiya ne?a ruɗe tayi tambayar,

Sehrish bata tsaya jin amsarta ba,duk hankalinta ya tashi,ta gefen Amrish tabi da gudun gaske ta nufi babban falon gidan,babu kowa duk basu tashi daga bacci ba,Upstairs ta haye har tana tuntu6e wurin taka matattakalar,Idanuwanta sun makance tana tsoran ta rasashi,a fujajen ta faÉ—a part É—insa,shigarta falon keda wuya,Sai ga Sgr Ya turo trolley a hannunshi,Ya kammala shirin shi tsaf zai tafi Airport,Jikinshi nasanye cikin jeans da T-shirt,fuskarshi sam babu annuri akanta,ga hannunshi daya jima rauni,

Cikin sanyin Murya ta ambaci sunanshi"Ya Rafayet,"ɗagowa yayi da idanuwanshi akan fuskarta,ita kanta ta tsorata da ganin launin idanuwanshi,Sun yi jawur dasu gwanin ban tsoro,tsantsar 6acin raine acikinsu,bai amsa kiran sunanshi da tayi ba,tamkar ma baisan da zuwanta ba,janyo trolley ɗinshi yayi kaitsaye ya nufi hanyar fita daga falon inda take a tsaye,tayi tunanin zai kula ta,amma ko kallo bata ishe shi ba,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,tuni hawaye sun wanke fuskarta,Yana ƙoƙarin bi ta gefenta ya wuce,a hanzarce tayi saurin sanya hannu ta ruko damtsen hannunshi,
  Muryarta na kerma tace"Ya Rafayet,idan ka tafi ni kuma fa?ya kakeso nayi da rayuwata"?

Runtse idanuwanshi yayi"ki sakarmun hannuna,tunkafin ranki ya 6aci,"A kausashe yayi maganar,

"Na yarda kayi mun duk wani hukunci da ya dace dani Saboda bani da hankali,amma dan Allah kada ka tafi ka barni,"
  Tana kai ƙarshen maganar,ta faɗa saman faffaɗan kirjinshi ta rungumeshi sosai tare da fashewa da matsanancin kuka,har cikin zuciyarshi yake jin kukan nata,
   "Ya rafayet am sorry,bazan ƙara ba,"cikin shessheƙar kuka tayi maganar,lokaci guda kuma ta ɗauke ɗuff,a hankali ya buɗe idanuwanshi tare da sauke su akanta,tayi tighting ɗinshi sosai,kamar ance za'a ƙwace mata shi,
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ya shiga saukewa,wani irin sanyine ya ratsa zuciyarshi,sakin trolley ɗin hannunshi yayi tare da ruƙota,ya ɗago da kanta daga jikinshi,da alama ta sume,fuskar nan tayi jaga jaga da hawaye,ta jigata sosai,jikinta yayi zafi sosai,tsantsar sonta da ƙaunarta ne acikin zuciyarshi,kamar ya haɗiyeta cikin cikinshi haka yake ji,
  Gaba ɗaya ya sa6eta saman kafaɗarshi,ya juya da ita zuwa bedroom dinshi,a saman katafaren gadonshi ya sauketa,ya gyara mata kwanciyarta,ya kasance tana fuskantar ceilling,hijabin jikinta ya cire mata,ganin yadda take zufa,a gefe ya ajiye hijabin,ya sauko daga saman gadon ya fita palour,within minute ya dawo hannunshi ɗauke da bottle water mai sanyi,gefen gadon ya zauna bayan ya buɗe murfin ya tarfa ruwan a hannunshi ya yayyafa mata shi asaman fuskarta,nan take taja dogon numfashi haɗi da sauke ajiyar zuciya ajere,tunkafin ta buɗe idanuwanta,ta soma sambatu"ya rafayet kada ka tafi ka barni,bazan iya rayuwa batare dakai ba,'
Chapter 195 · 0% Book details