← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 212

Sashe 81

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ƙopar bedroom ɗinshi ta tsaya,har lokacin bata daina ambaton La'ila ha illah anta subhanala inni kuntu minazzalimin,acikin zuciyarta ba,saboda tsabar tsoro,zuciyarta tamkar zata fito daga ƙirjinta,saboda bugun da take yi mata,daraam!daraaam,
    A hankali ta ɗan zura kanta tare da leƙawa cikin ɗakin nashi,
  Kwance yake saman gadon,gangar jikin na asaman gadon,yayin da head ɗinsa zuwa wuyanshi suka zuro daga gefen gadon,Sumar kanshi ta zubo har saman floor,
  Gabanta ne ya faɗi rasss!tun daga kan yadda yayi kwanciyar ta gane cewa babu lafiya,gaba ɗaya zufa ta wanke jikinshi tamkar wanda ya watsa ruwa ajikinshi,ta ko'ina zufar ke tsastsafo mashi,gaba ɗaya ga66an jikinshi sun sake,
   Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,batasan ko bacci yake yi ba,ko suma yayi,Allah wa'alamu,
   Zura ƙafarta tayi yayin da gabanta ke ci gaba da faduwa,Shiga cikin bedroom ɗin tayi,har zuwa wurin gadon nashi,Yanayin kwanciyar tashi ma,Zata iya haifar mashi da matsanancin ciwon wuya,saboda yadda ya yi sadda kai,
    Zuba mashi ido tayi tana kallon fuskarshi,daga gani ba ƙaramin jiki yaji ba,
   Tunani ta shiga yi,kodai ta ɗaukko ruwa ta yayyafa mashi,duk da bata da tabbacin cewar ko suman yayi ne,amma ga dukkan alamu ya suma ne......  ,
  Da sauri ta juya ta koma palour,fridge ta nufa da sauri sauri ta buɗe shi ta ɗauko robar ruwa,Sannan ta dawo cikin ɗakin nashi,Tashin hankali,Tsayawa tayi tana tunanin taya ma zata fara yayyafa mashi ruwan batare daya ganta ba?kyau tana watsa mashi ta watsa da gudu kafin ya murmure,
   Jikinta sae kerma yake yi,a haka ta buɗe robar ruwan,ta tarfa ruwan a hannunta,Ja da baya ta ɗan yi,sai da taba da interval sosai a tsakaninsu,daga inda take ta yarfa mashi ruwan akan fuskarshi,yaraf!ya saukar mashi,Aikuwa nan take ya shiga sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya,da gudun gaske sehrish ta 6oye acikin labulen ɗakin nashi,zuciyarta na ɗar ɗar,
  Sannu a hankali ya buɗe blue eyes ɗinshi,yana faman sauke ajiyar zuciya,bin kasan bedroom ɗin nashi yayi da kallo,kafin yayi yunƙurin mayar da kanshi saman Gadon nashi,saman pillow ya aza kanshi,yasa hannu yana murza wuyanshi saboda raɗaɗin da ya ji a wurin,lumshe idanuwanshi yayi tare da sake buɗesu,jikinshi babu ƙwari amma zazza6in ya sauka daga jikinshi,dakyar ya iya miƙewa daga zaune,ya jingina bayanshi a head board ɗin gadon,Yayin da idanuwanshi ke a lumshe,
  Sehrish dake 6oye bayan curtains ɗin ɗakin,tana jin duk wani moving ɗinshi,ta toshe bakinta da hancinta da tafin hannunta,saboda gudun kar ya gane akwai mutun aɗakin nashi,
   Almost 15 mins yana a zaune bai motsa ba,tun da yake a arayuwarshi bai ta6a shiga matsanancin halin daya shiga ba irin na yau,kamar wani mara gata,sae kace ba Surgeon General ba,Yau ya ɗanɗani zafin kadaici,duk a sanadin kalaman da sehrish ta gaya mashi,
   Saukowa yayi daga saman gadon,Ya tsaya atsaye tare da sanya hannu ya tu6e shirt ɗin dake ajikinta,Yayi wurgi da ita saman gadon,Zame belt ɗin wandonshi yayi ya jefar dashi saman rigar,sannan ya zame dogon wandon,Ya rage daga shi sai short light blue,
   yana tafiya cike da rashin ƙwarin jiki,a haka har ya buɗe toilet ya shige ciki,Sehrish na jin motsin buɗe kopar toilet,Jiki na rawa ta lalla6a,saɗaf saɗaf ta fito daga cikin bedroom din,Hannunta riƙe da bottle water din,Saman fridge ta ajiye robar ruwan sannan ta kama hanyar fita daga falon,Har ta kai bakin kopar dakin ta juyo ta kalli kayan Breakfast ɗin da Armstrong ya kawo mashi,nan ta gane cewa bai ci komai ba,
   Fitowa tayi daga part ɗin nashi,ta saukko downstairs da sauri ta nufi ɗakinsu,bayan ta shiga ciki ta ɗauki wayarta,tare da danna ma Aunty azeema kira,nan take ta ɗaga kiran,
  Da sauri ta sanya wayar a kunnanta,tun kafin tayi magana Hajiya azeema tace"Ya ake ciki ne?
  Sehrish tace"Naje part ɗin nashi,na same shi a sume saman gadonshi,gaskiya ba ƙaramin jiki yaji ba,nasamu dae na yayyafa mashi ruwa batare da ya ganni ba,na lalla6a na fito daga ɗakin nasa,naji ya shiga toilet da alama wanka zaiyi,Amma fa naga kayan abincin da aka kawo mashi daga restaurant,Da alama bai ci komai ba,"
  Hajiya azeema tace"Good!,naji daɗi da bai ganki ba,Kuma naji daɗin suman nan da yayi,saboda zai samu sauƙi acikin zuciyarshi,duk da nasan dole ya ƙullace ki a aranshi,"
  Murmushi sehrish ta ɗan yi kafin ta kuma cewa"duk yau baici komai ba,"
"Kada ki damu da wannan,ita yunwa bata da hankali,Ina nan dake wannan abincin da ya bari wanda aka kawo mashi na restaurant,Shi zai nema ina nan dake,yanzu dae ki kwanta kiyi bacci',
  Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,
   "Ki kwanta kiyi bacci,Sae Allah ya kaimu gobe zamuyi magana," sallama sukayi da ita,Sehrish ta kwanta saman gadon tare da ajiye wayarta saman stomach ɗinta,yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling ɗin dakin,

Sgr kuwa,bayan ya fito daga wankan da ya shiga,jallabiya ya zura ajikinshi ash colour,har wani jiri yake gani saboda tsabar yunwar da ya ke ji,ba arziƙi ya dawo palour saman sofa ya zauna,tare da kai hannu ya ɗauki burger ɗin nan,da ya ajiye saman table,Turata yayi cikin bakinsa ya shiga cin ta har yana shaƙewa,a ƙa'ida baya cin abincin da ya sha iska wanda aka bari a buɗe,Amma yau ba kanta,Ci kawai yakeyi,tass ya cinyeta,Miƙewa yayi da sauri ya nufi wurin fridge don ya daukko drink din da zaisha,hannu yakai tare da ɗaukar bottle water ɗin da Sehrish ta bari asaman fridge ɗin,6alle marfin yayi ya kafata a bakinshi yana kwankwadar ruwan,sae da yayi rabin ruwan dake acikinta,sannan ya dakata da shan ruwan da yake yi,Sai lokacin ya ankara da inda ya ɗauki robar ruwan,Shiru ya ɗan yi tare da zubawa robar ruwan dake hannunshi ido yana kallonta,Shi dai yasan bai ajiye ruwa asaman fridge ba,tunani ya shiga yi,Yanayin yarda ya farka duk da akwai zufa ajikinshi,amma tabbas yaji Saukar ruwa akan fuskarshi wannan ya tabbatar mashi da cewar wani ya shigo cikin part ɗinsa,Hannu yasa tare da buɗe fridge ɗin ya saka robar ciki,Sannan ya ɗauki coke mai sanyi,
  Komawa yayi saman sofa din,ya zauna tare da kai hannu ya buɗe daya daga cikin ledojin,take away ya curo ya buɗe shi Chips ne aciki duk yayi sanyi,amma ahaka ya shiga turashi acikin bakinshi yana ci,bai ta6a shiga yanayi irin wannan ba a rayuwarshi,tass ya cinye duk wani abu dake a wurin,bayan ya kammala cin abincin,mikewa yayi ya koma cikin bedroom ɗin shi,ya ɗauko wayarshi,Sannan ya dawo saman sofa ɗin ya kwanta tare da miƙar da ƙafafunshi saman hannun kujerar,
  Zubama screen ɗin wayar ido yayi yana kallonshi batare da ƙyaftawar ido ba,yama rasa wa zai kira yaji sanyi aranshi,numbar Abbansu ya lalubo ya danna mashi call,Ringing din farko Abbansu ya ɗaga kiran nashi muryarshi da alamun bacci yace"My son,Me kake yi har yanzu baka yi bacci ba"?
   batare da ya amsa mashi tambayarshi yace"Daddy,when zaku dawo?gida duk ba daɗi,"
  Tsananin mamakine ya kama Abbansu,Yau Sgr da kanshi yake cewa Gida babu daɗi saboda basu nan,ta wani 6angaren kuma yaji daɗin hakan sosai,
   "Kayi missing ɗinmu ne"?Abba ya tambayeshi,
muryarshi akasalance yace"Yeah,especially you,I missed u so much,"
  Farin ciki ne ya cika Abbansu,kamar ya janyoshi ta cikin wayar ya rungumeshi,
    "Pls Daddy,just come back home,if not zan biyoku damaturun ne,in yaso saimu dawo atare,"
  Sgr na jiyo sautin muryar Abbansu yana tiƙar dariya,
   "Are u laughing at me"?
Tsagaitawa Abbansu yayi da yin dariyar yace"dole nayi dariyar Farin ciki mana,Yau ya kasance rana ta farko daka nuna kayi kewarmu sosai,naji muryarka wani iri tamkar zaka yi kuka,tell me what's wrong with u,wani ya ta6a mun kaine"?
  Sgr yace"bana jin daɗin zuciyata ne,ko zaka sanyani farin ciki?
  Abba yace"yanzun nan kuwa,bari na tuna maka wani abu,lokacin da kana ɗan jinjiri dakai cikin towel,kyakkyawa da kai,Na ƙwallafa rai sosai akan ka, kai kuma ga kyuyar tsiya,ka ƙi jinin baƙin mutun ya ɗauke ka,koni da nake mahaifinka ban isa na ɗauke ka ba,in ba bacci ya ɗaukeka ba,Sae in lalla6a in shiga ɗakinka,In zauna saman gadon in zuba maka ido inta kallonka,araina ina cewa Yanzu wannan mallakina ne,Allah ya bani Halak malak,Haka zan tasaka gaba ina kallonka,da zarar ka farka kuwa,mukayi ido biyu,kamar kaga wani 6arawo haka zaka fasa ihu kana ambaton sunan Mommynka,"
   Lumshe ido Sgr yayi yana sauraron Abbansu,fuskarshi asake tamkar zaiyi murmushi,wata irin natsuwa yaji acikin zuciyarshi,
  "Amma daga baya,saboda irin kulawar da nake baka sae ka gane cewa ni mahaifinka ne,kuma inason ka sosai fiye da kowa,sae gashi da kanka,kake zuwa wurina don in ɗauke ka,mu tafi yawo atare,"
   jikin Sgr ba ƙaramin sanyi yayi ba,kalaman Abbansu sunyi matuƙar ta6a mashi zuciya,
   "Amma ni sai inga kamar baka sona,baka damu dani ba kamar yadda na damu da kai...."
  Tunkan ya ƙarasa maganar Sgr ya katse shi da cewa"Daddy kadaina faɗan hakan bana jin daɗi,duk duniya bani da tamkarka,kaine mahaifina,Jigona kuma ginshiƙi na,Abun alfaharina,madubin dubawana....".
  Wani irin farin cikine ya lullu6e Abbansu,bai ta6a jin irin wannan yabon daga bakin Sgr ba,sai yau har ya fara tunanin anya kuwa cikin hayyacinshi yake gaya mashi waɗannan kalaman?ko kuwa ya ɗan kora wani abune,Gashi ya saki jiki sai surutu yake yi mashi kamar ba wannan miskilin ba..."
  "Pls Rafayet,ka maimaita mun kalaman nan daka faɗamun,inaso nayi recording ɗinsu,"
  fashewa da dariya Sgr yayi,hakan ba ƙaramin ɗaurewa Abbansu kai yayi ba,
  Cike da mamaki yace"Rafayet,dariya kakeyi mun,dan Allah faɗamun kodai kasha kwaya ne yau,"
   "Daddy bansha komai ba,lafiyana ƙalou,kawai ina jin daɗin waya da kaine,ka bari idan ka dawo gida zan sake maimaita maka sai kaji a kunnanka,"
  Cikin raha sukayi wayar gwanin ban sha'awa hira irin ta da da mahaifi suka yi wadanda suke cikin begen juna,a karshe sukayi sallama,sauke ajiyar zuciya yayi tare da aza wayar saman chest ɗinshi,wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi,still kalaman Sehrish nadawo mashi acikin ranshi,waɗannan kalaman dae su suka fi ta6a mashi zuciya,Mara tausayi mara Imani,da kuma danganta shi da ya sayyadi,
Chapter 81 · 0% Book details