← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 193 OF 212

Sashe 193

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuraren ƙarfe shida na marece,Ya mu'allim yazo gidan domin duba jikin junaid,tun bayan da yayi parking ɗin motarshi,adai dai lokacin Kanal Yusif da Abba suke ƙoƙarin fitowa daga entry din falon,Suka yi arba dashi,Yana sanye cikin shigar nan tashi ta Larabawa,sai ƙamshi ke tashi daga jikinshi,fuskar kowannansu ɗauke da murmushi,
Mika mashi hannu abba yayi suka gaisa tare da rungume juna,"Nayi farin ciki sosai da zuwanka,Dama junaid ya addabe ni da tambayarka,Har cewa yake yi shi dai ayi mashi kwatancen gidanka Yaje ku gaisa"yayi maganarne bayan sun raba jikinsu,
"Allah sarki,junaid Ya jikin nashi,wlh nima nayi kewarshi sosai,Shiyasa na gaza hakura,"Ya kai ƙarshen maganar,tare da miƙawa Kanal yusif hannu suka gaisa"sannu zuwa,ya gida ya aiki,"
"Alhamdulillah,Yusif Ya mai jiki"!yayi tambayar yana kallonshi,
Yusif yace"mai jiki da sauƙi,Yana nan yanzu ba inda bai zuwa da ƙafafunshi,don da ace yana da mota da ba abunda xai hana ka ganshi ƙopar gidanka,"
Dariya suka saki gaba É—ayansu,Abba yace"bismillah mu shiga daga ciki,"

Atare suka nufi falon Ya mu'allim na a tsakiyarsu,lokacin da suka ƙarasa cikin babban falon,mutun uku suka samu zaune suna fira,Major general osman tare da Adam da Najeeb,miƙewa sukayi ganin abbansu,Gaishe dashi suka yi kafin suka miƙa ma Ya mu'allim hannu ɗaya baya ɗaya ya gaisa dasu,daga bisani kowannasu Ya zauna suka ci gaba da firarsu

Hannu abba yasa cikin aljihun wandon jikinshi ya lulubo wayarshi,Mommy ta dannawa kira,tana fara ringin mommy ta É—aga kiran,
"Kina ina ne"?
"Na shiga wurin azeema ne,"
"Okey,Ya mu'allim ne yazo,muna buƙatar abunsha,"
Amsa mashi tayi da toh"Gani nan zuwa,"daga haka yayi rejecting kiran,tare da mayar da hankalinshi kan Ya mu'allim
"Yakamata ka gayyace mu zuwa gidanka,tunda mun zama É—aya,ko ba haka ba"?yayi tambayar yana kallon su Yusif,
"Hakane daddy,abunda na lura dashi,baya son sakewa acikin gidan nan,kuma kullum zaizo shikaÉ—ai yake zuwa,banda ya'yanshi,"acewar yusif,
Murmushi ya mu'allim ya É—anyi kafin yace"Bani da ya'ya,"
Abba yace"Karfa kace mun baka da aure"?
Dariya yayi batare daya ce komai ba,Osman yace"Haba ya za ace baida aure,Yadda yake malamin nan kyau ace yana da mata huÉ—u cuf,Ya cike sunnah kenan,"
Sunnar dakai ƙasa ya mu'allim yayi yayin da yake wasa da key ɗin motarshi,
Abba yace"Kayi shiru bakace komai ba?
Najeeb yace"duk kunsa yaji kunya,kunsan fa bakowa keso ayi mashi maganar iyali ba,musamman idan ya kasance baidasu,"
Jin wannan maganar yasa Ya mu'allim ya É—an É—ago tare da kallon Captain najeeb da yayi maganar,domin kuwa ya canko dai dai,
"Ae ni tun rana ta farko dana fara ganinshi,raina ya bani cewa,duk irinmu ne,"adam ne yayi maganar,fuskarshi dauke da murmushi,

Abba yace"wai dagaske ne?kaima irinsu ne"?
Daƙyar Ya mu'allim ya iya amsa mashi"hakane abba,"
Tafa hannu abba ya shiga yi yana FaÉ—in"Subhanallahi!An shiga uku!haba Ya mu'alim,Ni duk a tunani na ka cike sunnah,ashe ko É—aya baka ajiye ba,"

Murmushi kawai Ya mu'allim keyi batare daya ce uffan ba,Saboda kunyar abba da yake yi,
"To dai ga junaid É—inka nan,In sha Allahu cikin sati mai zuwa zai angwance,"
Cike da mamaki Ya mu'allim yace"junaid zaiyi aure"?
Jinjina kai abba yayi"ƙwarai kuwa,Ae bashi kaɗai ba,Suna dayawa,kusan dukansu zan aurar a lokaci ɗaya,Ina fata kaima kafin lokacin zaka fiddo da mata inyi maka aure,"
Murmushi kawai ya mu'allim yayi,

Fitowa mommy tayi daga cikin kitchen hannunta É—auke da tray,wanda ta shirya masu abunsha mai sanyi acikin glass cup,hada snacks ta haÉ—o masu,

Adai dai Lokacin hafsat ta nufe wurinta,jikinta na sanye da arab gown white colour ta yafa mayafi akanta,
"Mommy,"da sauri takai idanuwanta kan hafsat data ambaci sunanta,
Fuskarta asake tace"Hafsat,ina zuwa haka"?
"Ba ko'ina,nagaji da zama cikin É—akine,Shine nace bari na fito in É—an zagaye gidan,"
Kafin mommy ta kuma cewa wani abu,hafsat ta nuna tray É—in hannunta"Wannan fa"?
"Abbane yazo da baƙo,wannan malamin dake duba junaid,shine ya buƙaci in shirya masu drinks,"
"Bari nakai masu,"
Ba ƙarami daɗi mommy taji ba,Miƙa mata tray ɗin tayi,ta sanya hannu biyu ta kar6a,kafin ta wuce cikin palourn,Mommy kuma ta juya zuwa ɗakinta,

"Assalamu Alaikum"cikin sanyin murya tayi masu sallamar,gaba É—aya suka É—ago suna kallonta,cikin girmamawa ta shiga gaishe dasu,fuska asake suke amsa mata,
Abba ta fara mika mawa ya É—auki kofin É—aya,
"Ga ya mu'allim nan ki miƙa masa,"juyawa tayi wurin Ya mu'allim ta miƙa mashi cup ɗin,a hankali ya sanya hannunshi ya ɗauki cup ɗin,har zata juya taji yace"kina mace kike shafa turare har haka"?ƙasa ƙasa yayi maganar
Gabanta ne ya faɗi rass,dama sai da ranta ya bata cewar zaiyi wuya in bai tanka mata ba,saboda tasan halin malaman nan,kuskure kaɗan sai sunyiwa mutun wa'azi akanshi,'ƙasa ƙasa da murya tace"Za'a gyara,'bata jira amsar da zai bata ba,tayi saurin yin gaba wurin Su osman ta miƙa masu,

Murmushi abba ya É—an saki bayan ya kur6i lemun yace"Nasan bakasanta ba,Jikata ce,sunanta hafsat,"
Murmushi Ya mu'allim ya É—an saki kafin yace"Masha Allah,"
Abba da É—umi sai cewa yayi"itama bata da aure kamar kai,sai dai bansani ba,ko tana da saurayi,"
A sukwane hafsat ta juyo tana kallon Abba,hankalinshi kwance yake magana,
Ƙumshe dariya kanal yusif yayi ganin yadda hafsat ta gumtse fuska,taji ana ƙoƙarin yin tallatarta,da sauri ta juya tabar wurin,sai da tayi nisa,takaici ya isheta,juyowa ta kuma yi don ta kalli Ya mu'allim,karaf suka haɗa ido dashi,watsa mashi harara tayi,duk don saboda yayi complain akan turarenta,abun ya bashi mamaki,hakan da tayi kuma ba ƙaramin burgeshi tayi ba,har yayi tunanin yin magana da abba akanta,idan sun ke6e,

Bayan ya kammala shan lemun,Abba yayi mashi jagora zuwa bedroom É—in junaid,Lokacin da suka shiga zaune suka same shi,tare da Talal suna kallo acikin laptop É—inshi,

Cike da zolaya ya mu'allim yace"kaida zan sameka kana karatun qur'ani,sai in sameka kana kallon drama?haka mu kayi dakai"?

Saukowa junaid yayi daga saman gadon ya ƙarasa da sauri ya rungumeshi,ba ƙaramin daɗi Ya mu'allim yaji ba,ganin yadda junaid ya samu lafiya sosai,har ƙiba yayi sa6anin da,
Shafa sumar kanshi yayi"Masha Allah,jiki yayi kyau junaid,Naji daÉ—i sosai,Allah ya Albarkanci rayuwarka,"Abban ya amsa mashi da Ameen
ÆŠagowa junaid yayi fuskarshi É—auke da murmushi yace"I really missed u,meyasa bakazo ba,2 days banganka ba,"ya É—anyi maganar shagwa6e
Waro ido abbansu yayi ganin junaid na shagwa6a,
"La haula masalli ila!Junaid me nake gani haka?Dama har yanzu akwai sauran shagwa6ar"?
Dariya ya mu'allim yayi"A jininshi take,shiya sanya har yanzu bata rabu dashi ba,kuma hada ƙarin autane shi,dole yayi shagwa6a,"
Abba yace"amma yaci ace ya daina,Nan fa da wani lokaci zai zama ango,"jin wannan maganar yasa junaid,Jin kunya da sauri ya koma saman gadonsu,Ya janyo pillow ya kifa kanshi asama yana dariya,Talal ma dake a gefenshi dariyar yake yi,

"Yana da kunya sosai,"acewar Ya mu'allim,
Abba yace"hmmmmm abar kaza cikin gashinta dai,kar atona,"

Dariya sosai su kayi,Sun jima a wurin Junaid sai da aka fara kiran Sallar magrib tukunna,suka fuce atare,

*Sehrish*

A hankali ta turo ƙopar toilet ɗin,jikinta sanye cikin bathrobe fara ƙyal,ta ɗaure igiyar rigar,wani irin ƙamshine ke fita daga jikinta,kamar wadda tayi wanka da ruwan turare,lallausar suman kanta tayi mata rumfa a bayanta,mai yawan gaske,jiƙe take lemar ruwa,tun bayan sallar Azhar,ta dawo ɗakin Azmee,gudun kada hajiya azeema taga tabaro shi,

Gaban mirror ta zauna,zugudum bakomai keyi mata yawo aranta ba,face maganganun da oummansu ta faÉ—a mata,sun tsaya mata aranta,
  A hankali ta furta"Ya rafayet sona yake yi,ko jikina yake so?taya za'ae na gane haka?,tana tsoran tayi irin kuskuren da Oummansu tayi,Nayin watsi da damarta,

Hand dryer ta fara É—aukowa,ta jona ajikin socket,busar da gashin kanta tayi,bayan ta kammala ta kashe ta,jikinta ta soma gyarawa,ko'ina ta shafe shi da mai,

Turo ƙopar ɗakin Hajiya azeema tayi da sallama abakinta ta shigo,Sehrish ta amsa mata,fuskarta adan sake ta amsa mata,
  'Ina yini aunty azeema,"
"Lafiya Lou daughter,Ya jikin naki"?
  "Alhamdulillah,ina samun sauƙi sosai,"
   "Naga gashin kanki,Yayi tsayi sosai,ga yawa,yakamata ku shirya in kaiku wurin Saloon dake da ƴan uwanki,amma fa idan kinji sauki,"_
  "Ae nama ji sauƙi,warwarewa kawai zan ƙarasa yi,"
  Hararar wasa Azeema tayi mata"A haka din,kina ɗan gyasa ƙafa shine kinji sauki?
  Dariya sehrish ta ɗanyi"bari nayi maki make up,"acewar hajiya azeema,
  Ba don taso ba,Saboda yanzu bata buƙatar yin kwalliya,tunda wanda take yi dominshi,Rabuwa zasuyi,
   Within mins hajiya azeema tayi mata make up,fuskar ta fito sosai,jan bakin data shafa mata red ne mai ƙyalli ajikinshi,daga sama ta shafa mata lip gloss,fuskar ta lindu da foundation mai kyan gaske,ga eye brows ɗinta natural amma ta ƙara mata da brown eye pencil,
  "Masha Allah my daughter,Allah yayi maki kyau,ki godewa Allah,Son kowa ƙin wanda Ya rasa,"
  Murmushi sehrish ta ɗan saki,
"Bari na ɗauko maki,kayan da zaki sanya,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi wardrobe ɗin kayanta,
  Can ta hango wata Atampa,Golden glitter,Brown Colour,Riga da skirt ne,ɗinkin ya haɗu over,
  Juyawa tayi tare da kallon Sehrish"Har na hangoki acikin wannan,"
  "Sunyi kyau sosai,Amma dare yayi,koda na sanyasu,zan cirene in na tashi kwanciya,"
  "Duk da haka,ki sanyasu,in yaso daga baya kin cire,"
  Gyaɗa kai tayi"shikenan,"ta ambaci hakan tare da mikewa,taje ta kar6i atampar daga hannunta,
"Bari naje,na kawo maki dinner dinki,"tayi maganar tare da nufar hanyar fita daga dakin,Harta ruƙe handle ɗin kopar ta juyo ta kalli sehrish"Munyi magana da Amrish,tace tana so taje gidansu ta kwaso kayanta,bansani ba kota fada maki"
  "Bata faɗamun ba,"
"Okey,in Allah yakaimu,Zuwa gobe zanyiwa wani magana cikin matasan gidan nan,yakaita gidan ta dauko kayanta,"
  "Allah yakaimu Lafiya,"
  "Ameen"ta amsa mata tare da juya ta fuce daga ɗakin,

Shaf shaf ta shiga zura kayan ajikinta,sun zauna mata sosai sunbi dirin jikinta,bata É—aura É—ankwalin ba,don bata iyaba,zama tayi gaban mirror É—in tana jiran dawowar,Hajiya azeema don ta É—aura mata shi,

After some minutes hajiya azeema,ta shigo hannunta dauke da tray mai fadi,Asamanshi food stuff ne,Saman table ta sauke tray É—in,kafin ta nufo Sehrish,
  "Banta6a ganin budurwar da atampa keyi mata kyau ba irinki,yadda kasan donke companyn suka ƙerata,"fashewa sehrish tayi da dariya,don ba ƙaramin nishaɗi ta sanyata ba,

Bayan ta kammala É—aura mata É—an kwalin,style me kyau,tace"Aikina ya qare,ga abincinki can kije ki zauna ki ci,"
  "Nagode sosai,"tana kai karshen maganarta,ta fuce daga dakin,

Murmushi sehrish ta ɗan saki tana kallon kanta ta cikin madubin,miƙewa tayi daga gaban madubin ta dawo gefen gadon ta zauna,sae ƙamshi ke tashi ajikinta,

Tsaf Ya kammala Shiryawa cikin shadda Ash colour,wa'iyazubillah,kyau iya kyau,a tsaye yake gaban mirror yana gyara agogon diamond É—in hannunshi,
Chapter 193 · 0% Book details