← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 212

Sashe 158

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sgr baisamu shiga ba,saboda a halin da yake ciki a yanzu bazai iya duba Abbansu ba,yana cikin matsananciyar damuwa saboda yasan dalilin ciwon Abban nasu,dama yace su fara ƙirgen kwanakin mutuwarshi,in har basu dawo mashi da yaronshi ba,

A saman waiting seat suka zazzauna suna jiran tsammani,Omar da Sgr suna a tsaye,Kowa ka kalli fuskarshi gwanin ban tausayi,
  "I can't forgive my self,idan har Daddy ya mutu silar 6oye mashi mutuwar Junaid da mu kayi,"Ya ƙarasa maganar yayin da idanuwanshi suka cicciko tab da hawaye,
  Ruƙo hannunshi Omar yayi"bakai kaɗai ba Rafayet,nima bazan yafewa kaina ba,in har muka rasa shi,wlh i ave regretted already,Da mun sani tunfarko mun sanar dashi gaskiya kawae tunda dama gudun hakan yasa muka 6oye mashi,"gaba ɗaya duk sun sha jinin jikinsu,

"Dan Allah kukan ya isa haka,twins,fawan da irfan,in na sake jin shessheƙar kukan wani acikinku wlh zaku koma gida ne,"kanal yousouf ne keyi masu faɗa,. 
  "Sai kace ba musulmai ba!maimakon ku tayashi da addu'a amma kun dage sai kuka kukeyi,"ya ƙarasa maganar tare da jan guntun tsoki,idanuwanshi cike tab da kwalla,
  Abu kuwa sai faman lallashin Mommy takeyi,ganin yadda take ta shar6ar kuka,
  Abusufyan ne yace"don Allah Aunty kidaina,kina ƙara tayar masu da hankalinsu,keda yakamata ace kina lallashinsu,"hannu tasa tana share hawayen fuskarta,juriyarce bazata iya ba,ita kaɗai tasan yarda take ji acikin zuciyarta,

Fitowa Doctor emran yayi daga cikin É—akin da aka kwantar da Abbansu,Aikuwa da sauri suka tunkareshi,kowa yana tambayar ya jikin nashi,
  "Ku kwantar da hankalinku,Yana samun sauƙi,Addu'ar ku kawai yake buƙata,"yakai ƙarshen maganar tare da aza idanuwanshi kansu Sgr da Marshal"ina son ganinku a office,"
  Tunda suka ji haka sai jikinsu ya ƙara yin lakwas,gaba Dr emran Yayi suka bi bayanshi,har izuwa Office ɗinshi,Wuri ya samu ya zauna,kafin suma suka zauna suna fuskantarshi,
  A tsanake ya soma yi masu bayani"nasan kunsan meke damun mahaifinku,damuwa ce akan rashin Junaid,Yanzu haka dana baro ɗakin,Sambatu yake yi yana ambaton sunan shi,"dakatawa ya ɗan yi da bayani yana kallonsu,jikinsu sai tsuma Yake yi,
  "Jinin shi ne ya hau sosae,Ga kuma Ciwon zuciya dake barazanar kamashi..."
  Tunkan emran yakai ƙarshen maganar,Omar ya dafe kai jikinshi na kerma,jikinsu Ya gama mutuwa,
  "Yanzu ya zamuyi kenan?menene solution"?Sgr ne yayi tambayar,
  "Akwai matsala fa,saboda ya ƙwallafa ranshi akan son yaron,Idan har ba ganinshi Yayi ba,tofa sai dai abishi da addu'a,"
  "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"miƙewa Sgr yayi da sauri ya fice daga Office ɗin,gaba ɗaya sun rasa inda zasu tsoma ransu suji daɗi,

Miƙewa Sehrish tayi daga zuƙunnan da take abakin ƙopar palourn,Hannu ta zura acikin aljihun rigarta,ta curo wayarta don ta kira Jahad taji Ya jikin Abban nasu,
  Tana kunna wayar,ta shiga Call log anan ta samu missed calls da baƙuwar number,har kusan sau 10 aka kira,Batasan number ɗin wanene ba,Har jaraba kiran Layin tayi wayar nata ringing ba'a ɗaga ba,
  Bayan kiran ya katse ne,ta lura da message ɗin da aka turo mata,Da sauri ta buɗe saƙon ta soma karanta shi kamar haka,
__Sehrish na kira layinki baki ɗaga ba,Amrish ce inason magana dake game da ɗan uwan nan naki,dan Allah idan kinga saƙon nan ki kira ni_
  Abun ya ɗaure mata kai,tunani ta shiga yi wani ɗan uwanta ne Amrish ke magana akai,sake kiran Layin tayi wayar ta dinga ringing amma ba'a ɗaga ba,
  Katse kiran tayi,tana ƙoƙarin juyawa ta koma cikin gidan kira ya shigo layinta da baƙuwar number,da sauri ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta,tunkafin tayi sallama muryar Amrish ta katse mata hanzarinta,
  "Sehrish kina ina ne!ina ta kiran Layin wayarki amma baki ɗaga ba,magana ce akan Junaid na tura maki Address ta message,kibar komai kikeyi kizo ki same mu"tana kai ƙarshen maganar ta katse kiran,
  Wani irin faɗuwar gaba Sehrish taji,Abun ya matukar ɗaure mata kai,musamman data ambaci sunan Junaid,
 
Hannunta na kerma ta shiga duba message É—in da aka turo mata,kwatancen inda zata same su ne,

Tarasa ya zatayi,ita dai ba mota gareta ba,gashi babu wanda ya rage acikin gidan balle ya kaita,kama hanya tayi ta miƙi titin da zai sadaka da babban gate ɗin gidan,Sae faman zumbula sauri take yi,Sai da tasha wahalar zuwa babban gate ɗin,Sojojin dake tsaron gidan suka hanata fita,kamar ta fashe da kuka,

A dole ta shiga kiran layin matasan gidan,Duk wanda ta kira bai É—agawa,har Abusufyan ta kira shima bai É—aga kiran ba,
 
Sai da ƙyar ta samu Hosana ta ɗaga kiranta,da sauri ta kara wayar a kunnanta,
  "Hosana Ya jikin Abban"?
  "Nima bansani ba,Sun shiga dashi ciki,"
  "Dan Allah idan akwai wani kusa ki bashi wayar,"
  "To"ta amsa mata,jim kaɗan taji muryar Kanal yousouf,
  Sai da ta fara tambayarshi jikin Abban nasu,Ya sanar da ita cewa da sauki,tukunna tace"Gani nan zan fito gida an hanani,dan Allah ka taimaka kasa su barni na fita,nima asibitin zanzo,"
"Ki basu wayar,"Cire wayar tayi daga kunnanta ta miƙa ma ɗaya daga cikin sojojin,ya kar6a su kayi magana dashi sannan ya miƙa mata wayar,"Zaki iya tafiya,amma yace kada abarki ki fita ke kaɗai,don haka wani daga cikinmu zai ɗaukeki a mota ku fita,"
  Ba ƙaramin daɗi taji ba,dama ƙarfin hali ne kawai,ko kuɗin abun hawa bata dashi,

Anan ta tsaya,wani sergeant ya É—auko mota ta buÉ—e ta shiga ciki ya tashi motar,saida suka hau saman titi sannan yace"Madam ina zuwa"?
  Karanto mashi Address ɗin wurin tayi kamar yadda Amrish ta rubuto mata a saƙon,

Wani private hospital ne suka shiga,sojan ya fito ya buɗe mata ƙopa ta fito daga ciki,a bakin ƙopar shiga ciki ta samu Amrish a tsaye hannunta ruƙe da waya,wani irin farin ciki ne ya lullu6e Sehrish da gudun gaske ta nufeta,rungume juna sukayi nan take Amrish ta fashe da kuka,
  Ɗago da ita Sehrish tayi tana tambayarta lafiya,
  "Amrish dama kina nan?layinki kona kira bana samu,meya sameki ne?me kike yi a asibitin nan ne"?
  Cikin shessheƙar kuka Amrish tace"mu shiga daga ciki ki gane ma idanuwanki,"
  Ta ƙarasa maganar tare da janyo hannun Sehrish suka shiga asibitin,A A&E aka kwantar dashi,a bakin ƙopar ɗakin Sukayi kici6us da Ya Mu'allim malamin da take ta nema,
  Cike da mamaki ta ambaci sunanshi"Ya mu'allim,"fuskarshi da alamun damuwa atare da ita,Ya amsa mata"Na'am,kina ta nemana ko"?
Jinjina mashi kai tayi alamar eh
  "Naga saƙon da kika turomin,idan muka samu natsuwa zamuyi magana,Yanzu dai ga ɗan uwanki can kije ki duba jikinshi,"
  Gabanta ne ya faɗi rasss!,kawar da idanuwanta tayi daga kallon fuskar Ya mu'allim ta mayar da idanuwanta kan ƙopar ɗakin,mutun ta hango kwance an sanya mashi oxygen a hancinshi,yayin da hannunshi ke sanye da robar ƙarin jini,zuciyarta na harbawa a haka ta nufi cikin ɗakin,lokacin data ƙarasa gaban gadon tayi arba da fuskar Junaid,Sai ta yanke jiki ta faɗi a sume.......

Shigowa Cikin ɗakin Ya mu'allim yayi tare da Amrish,ruwan dake ajiye saman drawer din dake gefen gadon Ya ɗauka,Ya cire murfin ya tarfa ruwan a tafin hannunshi Ya watsa mata akan fuskarta,Nan take ta farfaɗo tana faman Sauke ajiyar zuciya,Yayin da take ambaton Sunan Junaid abakinta,Miƙawa tayi agaban gadon ta zube saman guiwowinta,kamar a mafarki haka take ganin Junaid,bazata Iya jurewa ba,fashewa tayi da matsanancin kuka yayin da take kallonshi,Dama sai da ranta ya bata cewa Junaid bai mutu ba,Yana araye,Ashe dagaske ne,tasha kuka ta gode ma Allah,Cikin shessheƙar kuka ta soma magana tana kallon Ya mu'alim da amrish dake a tsaye,
"Taya akai junaid daya mutu ya dawo?a ina kuka same shi,A iya saninmu junaid yayi hatsarin mota Ya ƙone ƙurmus"
  Jin wannan maganar yasa Ya mu'allim da Amrish suka kalli Junaid,har suna haɗa baki wurin cewa"Junaid Yayi hatsarin mota'?
  Jinjina kai Sehrish tayi"Babbar motace tabi takan Motarsu,Wuta ta kamaci,ba'a samu komai daga sassan jikinshi ba,wannan Shi ne abunda muka sani a game dashi....."tana kuka ta Zayyana masu Komai daya faru har 6oye mutuwar junaid dasu Marshal Su kayi,Da kuma Halin da abbansu ke ciki na rashinsa,. 
  Amrish tasha kuka hada majina,Shi kanshi Ya mu'allim jurewa kawai yake yi,rashin imanin Yayi yawa
  "In sha Allah komai Yazo ƙarshe,duk wanda keda sa hannu a wurin cutar da family ɗinku,Zai gane kuskurenshi,don wannan karan da shirina nazo,"Babu wasa a fuskarshi yayi maganar,
  "Dan Allah ku faɗamun ya akai kuka samu junaid"?tayi maganar yayin da take share hawayen fuskarta,
  Anan Amrish ta kwashe dukkan abunda Ya faru daga farko har ƙarshe

Miƙewa Sehrish tayi tana kuka,Ta rungume amrish tana Yi mata godiya,bawan Allah ashe shine Yake tura mana saƙo da layinki,muka kasa gane wanene,da yake ni ina da numberki,Shiyasa saƙon Ya bayyana da sunanki,nayi tunanin ko kin yada wayarki ne,Ashe junaid ne ya ɗauketa,Bawan Allah,wlh da ace zan iya mayar da ciwonshi jikina da nayi hakan,junaid bai ta6a shan wahala rayuwarba,Sae wannan karan da ƙaddara ta rutsa shi....."
  "Mu gode ma Allah junaid yana raye,duk yarda suka so su cutar dashi,basu ci nasara akanshi ba,domin kuwa junaid kainuwa ne dashen Allah,badai mutun ba,lokacin da muka kawo shi asibitin nan,jinin jikinshi Yayi ƙanƙanta,cikin sa'a likita ya gwada jinina,kuma aka dace yayi dai dai da nashi,gashi nan ana ƙara mashi,Amma yana bukatar jini sosai,"

*ƙarin Bayani*

Abunda ya faru lokacin da Sehrish ta tura saƙonnin nan cike da saran Ya mu'allim zai gani,malaman da ta tura ma saƙon daga ciki akwai numbar Ya mu'alim,Yaga Saƙonta saƙonta sai kuma Aka kirashi a waya ana sanar dashi cewa ɗalibarsa na nemanshi,Sauran malaman data tura ma sakone suka sanar dashi,An turo masu saƙo ana nemanshi,Wannan dalilin ne yasa Ya mu'alimm Ya shirya zuwa gidan,tun lokacin baya ya ta6a zuwa gidan security guards ɗin gidan suka hanashi wuce wa,baisamu shiga ba a wannan lokacin,Sai yau daya samu saƙonnin nemanshi da sehrish keyi,Shi ne ya yanke shawarar Ya fara zuwa gidansu Amrish don tayi mashi jagora zuwa gidansu sehrish ɗin su tafi atare,Da yake ya ta6a zuwa gidansu Amrish lokacin da tayi jinya,kuma cikin sa'a ya zo adaidai lokacin da suke buƙatar taimako,Kunji yarda akai Allah ya hadasu dashi Har ya ɗauke su,
Chapter 158 · 0% Book details