Sashe 48
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suna tsaye a ƙopar ɗakin Ammi,sae ga Junaid,yana hangosu ya shiga sakin murmushin nan nashi,jiki na rawa ya nufi wurinsu,Gaisar da Abusufyan ya fara yi"Gm Uncle,"cike da zolaya Abusufyan yace"a haka zan baka auren ƴa ta?kana gaisar dani daga tsaye sai kace wani tsaranka ba wani respect"?jin haka yasa junaid saurin duƙawa ƙasa,sannan yace"Ina kwana Uncle"?
Dariya su kayi gaba ɗayansu,ganin yadda ya zuƙunna,
 "Lafiya lou in law ɗina,ko kaifa,miƙe tsaye toh tunda ka ƙaraso sae mu shiga ciki atare,"mikewa yayi fuskarshi a washe,duk a tunanin Abusufyan junaid wasa yake yi masa yawan zancen zai bashi auren ɗaya daga cikinsu,baisan dagaske shi kamu yake yi ba
da sallama a bakunansu suka shiga cikin ɗakin,koda ammi taji muryoyinsu,da sauri ta kashe tabar da take zuƙa,ta sanya ta acikin Ashtray dake ajiye ƙasa,da ƙafarta ta tura shi ƙarƙashin gado,duk akan idon Abusufyan abun yaso ya bashi dariya,lallai Ammi ta kimtsu tunda har ta fara jin kunyar jikokinta su ganta tana zuqar sigari,
  A saman carpet,kowannansu ya zauna tare da lankwashe ƙafa,Abusufyan ne ya fara gaisar da ita"Ina kwana Ammi,kun tashi lafiya?Ya gajiyar tafiya"?
"Lafiya lou Alhamdulillah,"ta amsa mashi,Sannan su Jahad suka haɗa baki wurin miƙa gaisuwarsu,da murmushi a fuskarta ta shiga amsa masu ɗaya bayan ɗaya,a ƙarshe ta tsayar da idanunta kan Hosana tace"Kin tashi lafiya"?
 Murmushi hosana ta saki tana faman noƙe kai tace"lafiya lou,"
     Janye idonta tayi daga kan hosana ta mayar dashi kan junaid tace"Sarkin Murmushi,Angona nakaina naga kayi kyau sosai ka kuma ƙara haske,faɗamun menene sirrin"?
 "Kishiya zanyi maki ne"yayi maganar yana murmura mata ido,ɗan waro ido waje tayi tare da cewa"Wacece ita"?
 ɗagowa yayi yana kallonsu,Sehrish har sai da ya gano jahad sannan ya nuna ta da hannu yace"Gatanan,"
 Ammi tace"Kin shirya yin kishi dani ko"?
 Girgiza kai jahad ta shiga yi alamar a'a,
 "To kaji bazata iya kishi dani ba,sai ka haƙura da auren gaba ɗaya,don ni bazan zauna da kishiya ba,"
 "A'a wlh Ammi sai dai ki haƙura dani in aurota,"
Yadda yayi maganar ba ƙaramin dariya ya basu ba,don har saida suka dara,
Ammi tace"wato Ni zaka juya ma baya ko?saboda ka samu zankaɗeɗiyar budurwa sabuwa gal cikin leda,Ni kuma nayi maka tsufa,"gyaɗa kai tayi tare da cewa"bakomai na haƙura,"
 Murmushi suka saki gaba ɗayansu,mayar da idonta tayi kan Abusufyan"Yanzu ya ake ciki game da zancen Mahaifiyar yaran nan"?
 Jin an sako zancen abu yasa shi gyara zama,sannan yace"Muna nan muna shirya waɗanda zasu je kano domin binciko gidan da suka zauna acikinsa,saboda muna sa ran zamu samu wasu muhimman bayanai a wurin makwabtansu,"
 Jinjina kai Ammi tayi"hakan yayi kyau,banason a tsaya 6ata lokaci nafi son ayi komai tun da wuri don ba'a san halin da take ciki ba,"
 "In sha Allah zamuyi hakan,daga nan suka miƙe tare da yi mata sallama suka wuce ɗakin Modibbo,ba ƙaramin daɗi yaji ba daya gansu,sun jima a wurinshi,kafin daga bisani suka wuce ɗakin gwaggon katsina,sun sha barkwanci a wurinta,daƙyar suka samu tabarsu suka fito,ɗakin hajiya azeema suka wuce,sun jima a wurinta suna shan fira,ɗaya bayan ɗaya haka suka dinga bin ɗakunansu kafin daga bisani,Lokacin yin breakfast yayi suka hallara gaba ɗayansu a dining,kowa saida yazo banda Sgr,saboda yasa ma ranshi cewar za'a kawo mashi ne har part ɗinsa,Azmee ce takai mashi,saboda Sehrish ta sanar da ita cewar,bazata samu damar kai mashi ba,tana so tabi Umarnin mahaifinta ne,
Lokacin da Azmee ta shiga part ɗinsa,yana daga kishingiɗe saman Sofa mai mazaunin mutun ukku,jikinshi na sanye da jallabiya,shigowa ciki tayi gabanta na faɗuwa don tasan cewa dole ya tuhumeta akan me ya hana sehrish zuwa,lalla6awa tayi ta ajiye masa tray ɗin a asaman table,gudun karya tuhumeta yasa tayi saurin ja da baya zata gudu tabar ɗakin,har takai baƙin ƙopar ɗakin tajiyo muryarshi yana fadin"ke zo nan,"dakatawa tayi da tafiyar hannunta dafe da saitin zuciyarta,jiki asanyaye ta dawo ta tsaya agabanshi,kwata kwata idanunshi na a lumshe,wayarshi na ajiye asaman wide chest ɗinsa,
 dakyar ta iya cewa gani yalla6ai,
"Bana ce kar na sake ganinki a part É—ina ba da sunan aiki?ko bata faÉ—a maki bane"?
 Shiru azmee tayi,tana faman zazzare ido,ranta ne ya bata cewar kawai ta sanar dashi gaskiyar zance,
Don haka tace"Sehrish ta sanar dani cewar bazata ƙara aiki a part ɗin ka ba...."tunkan ta ƙarasa maganar ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu,nan take azmee tasha jinin jikinta,
 "Ita da bakin ta,ta faɗi hakan"?
Muryarta na kerma tace"Eh,
 Ya kuma cewa"ta faɗa maki dalilin yin hakan"?
"Eh,tace tana son bin Umarnin mahaifinta ne,"
  ɗan ciza gefen la66ansa yayi tare da cewa"its Okey,just leave........" da sauri azmee ta juya tare da kama hanya ta fuce daga part ɗin nasa,
Wuraren ƙarfe goma sha biyu modibbo ya shirya tafiya,Kanal yousouf ne tare dasu Irfan suka kai shi har Airpot ya hau jirgi,
Yinin Ranar Aunty babba na ƙumshe a cikin ɗakin Hayaam,tsoro ya hanata fitowa waje,da yunwa ta addabe ta Hayaam ce ta ɗebo mata abinci ta kawo mata a ɗakin,hosana kuwa kar take dasu,don taci alwashin sai ta tona masu asiri wurin daddynsu,da kuma Ya omar,
Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,jin Cewa sgr bai nemeta ba,duk da ta damu akan son ganinshi,jurewa kawai takeyi,
A ranar Talal Da captain najeeb suka ƙaraso,murna a wurin ƴan uwansu kamar zasu haɗiye su don farin ciki,musamman junaid daya kasance rival ɗinsa ne ya dawo wato Talal,da yake shima autane a ɗakinsu Omar,
After 1 day
*Boss Bature*
Around 2:00 pm,
Zaune take a hakimce saman 2 seater,jikinta na sanye da turkish dress Riga da wando,a launin fata fara ce amma hasken nata hada na bleaching tayi 6au sosai,babbar mace ce a ƙalla zata kai shekara 35,gaba ɗaya idanunta na akan plasma tv din da take kallo aciki,yayin da hannunta ke ɗauke da cup na coffee,lokaci bayan lokaci take kur6asa,ta aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,wuyan kafarta na sanye da ziririyar sarƙa,sai faman karkaɗa kafar takeyi,Tana da manyan idanu dara dara,ga dogon hanci wanda ke manne da nose ring,kai kana ganinta zaka san cewar cikakkiyar ƴar bariki ce,
Jin ringing din wayarta dake ajiye asaman hannun kujerar da take ne yasa ta Ajiye cup din hannunta asaman madaidaicin table din dake a kusa da ita,sannan tasa hannu ta dauki wayar,hidden number ce aka kirata da ita,picking call É—in tayi ta kanga wayar a kunnanta,cikin harshen fulatanci take magana,
Tana cikin yin wayar taga inuwar mutun tsaye akanta,É—agowa tayi a hankali don taga wanene,sauke ajiyar zuciya tayi ganin Amrish ce,jikinta na sanye da uniform,ta goya school bag dinta a abayanta,dawowarta kenan daga school,fuskarta a É—aure kwata kwata babu annuri acikinta,
Rejecting call É—in tayi tare da ajiye wayar asaman sofa din,sannan ta mayar da hankalinta sosai akan Amrish,
 "Welcome back my daughter,Am really glad to see u,"
 Tayi maganar tana buɗe mata hannunwanta don tazo ta rungume ta,rai a6ace tace"Mommy na tsani ganinki wlh,banason ki,saboda baki da halin kirki,so kike ki kashe mun rayuwata da hannunki,"tana maganar hawaye na gangarowa akan fuskarta,
 Maimakon ta nuna damuwarta akan hakan sai ma ɗan ta6e la66anta tare da cewa"Kamar yadda baki so na,Nima haka bana son ki,donni a tsarin rayuwata ban shirya haihuwa ba saboda bana son ƴa'ƴa don su takura ne,na samu cikinki batare dana shirya ba,babu yadda banyi ba don na zubar da cikin,amma ya liƙe ya nace sai ya zauna a mahaifata,a ƙarshe nayi deciding zuwa ƙasar waje a markaɗe mun shi,mahaifinki ya hana hakan,nayi takaici a wannan lokacin kamar nayi suicide,"
 Hankalin Amrish ba ƙaramin tashi yayi ba,jin abunda mahaifiyarta ke faɗi da bakinta,tuni wasu zafafan hawaye suka shiga wankowa a saman fuskarta,cikin shessheƙar kuka tace"ki faɗamun!Su wanene iyaye na!don ina da tabbacin cewar bake kika haife ni ba,"
 Fashewa da dariya matar tayi yayin da take karkaɗa kafafunta,
Jin tayi banza da ita yasa ta daka mata tsawa tare da cewa"Mommy ki faÉ—amun su wanene iyaye na?In ba haka ba zan je na kashe kaina!"
Yunkurawa mommyn tayi tare da mikewa tsaye ta daddage ta kifa ma Amrish mari tare da cewa"Sai me idan kin kashe kanki!?wa kikayi ma asara!shashasha kawai,"
Fashewa da kuka Amrish tayi yayin da zuciyarta ke tafarfasa tace"Mommy yau ke da kanki kika mare ni"?
Dogon tsoki taja tare da cewa"Har kashe ki ma zan iyayi,Saboda kinyi mun tsawa,ko iyayena da suka haife ni basu ta6a gigin daka mun tsawa ba,balle ke Æ´ar dana haifa,idiot"
Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta ɗauki wayarta,sannan tabar falon tana fadin"kafin gobe in samu gawarki dan Allah,"tayi maganar cikin halin ko in kula,
Da gudu Amrish ta watsa,izuwa bedroom dinta dake a upstairs,datse ƙopar ɗakin tayi,bayan tayi wurgi da school bag dinta,ta shiga neman igiyar da zata shaƙe kanta don ta mutu,ganin bata samu ba yasa ta buɗe kopar ɗakin,ta fita,bada jimawa ba sai gata ta dawo cikin ɗakin hannunta dauke da insect powder,buɗe murfin tayi da sauri sauri ta daga robar tare da zazzagawa acikin bakinta,