← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 212

Sashe 23

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun bayan da Hayaam ta tura ma Aunty babba hotonsu hosana,bata samu damar duba hoton nasu ba,ko whatsapp ɗinta bata shiga ba,wayarma tana ajiye cikin bedroom ɗinta,Shirye shiryen zuwa walima kawai sukeyi,atare da hafsat suka fita saloon daga nan za'ayi masu ƙunshi,bayan nan kuma zasu biya Shopping mall,saboda siyayyar da tace zatayi ma Ƴa'ƴan uncle ɗinsu,basu suka dawo gidan ba sai wuraren karfe shida na yamma agajiye suka dawo,kowa ya wuce bedroom ɗinshi,Aunty babba na shiga ɗakinta,kai tsaye ta faɗa saman gadonta ta shiga sharar bacci,Hafsa kuwa saida ta fara yin wanka,ta canza kayan jikinta izuwa riga da skirt marasa nauyi,sannan ta fito falo ta kwashe shopping bags ɗin da suka bari a falo,takaisu ɗakinta,tana cikin dudduba kayan wayarta dake ajiye gaban mirror ta shiga ringing,hannu takai tare da ɗaukar wayar tana kallon screen ɗinta,ganin Sunan Aunty Hayaam ya bayyana akan secreen ɗin wayar,yasa ta ɗaga kiran tare da karawa a kunnanta,
  "Assalamu Alaikum aunty hayaam,'
Ko amsa mata sallamar batayi ba tace"Hafsat ina Aunty laila take ne?tun da sassafe na tura mata hoton bata duba ba,har nagaji da jira,"
  Hafsat tace"yanzu muka dawo daga kasuwa agajiye,tana a bedroom ɗinta ina jin bacci ne ya dauketa,ko inyi mata magana ne"?
  Hayaam tace"A'a,kawai idan ta tashi ki sanar da ita cewa na tura mata hoton ƴa'ƴan abusufyan ɗin,ta duba ta whatsapp ɗinta,"
  Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hafsat,muryarta na rawa tace"hoton ƴa'ƴan Abusufyan dinmu!zan sanar mata kuwa,"
  Rejecting call ɗin tayi,da gudu ta fito daga bedroom ɗinta,kai tsaye ta haye upstairs ɗakin aunty babba,tura kopar ɗakin tayi tare da shigewa ciki,a kwance ta samu aunty babba saman gadonta sai sharar bacci takeyi,ga wayarta ajiye agefenta,
  Cikin sanɗa takai hannu tare da ɗaukar wayar,ta danna power ɗinta ta kawo haske,ganin akwai password yasa ta ɗan bubbuga kafarta tana cewa"Kai mommy,yanzu dole sae kin tashi sannan zan samu damar ganin hoton babies ɗinmu!gaskiya ni a ƙagare nake,"
  Tana cikin maganar,ta tuna da finger print ɗin dake akwai ajikin wayar,nan take zuciyarta ta bata shawarar cewar me zai hana,ta lalla6a ta hau saman gadon,ta dangwalo yatsan aunty babba,kota samu wayar ta buɗe,Good idea,ta furta hakan tare da lalla6awa ta hau saman gadon,cikin sanɗa ta ƙarasa inda aunty babbar take,hannunta ta ruƙo tare da sanya yatsan hannunta a wurin,ya rubuta mata wrong,haka ta dinga bin yatsun hannun aunty babba tana jarabawa,har sai da taci nasarar buɗe wayar,saukowa tayi daga saman gadon,ta tsaya atsaye,hannunta har kerma sukeyi wurin daddana wayar,tsoranta kar Aunty babba tafarka saboda tasan halin Mommyn nata,ta tsani wani ya ɗaukar mata wayarta,kamar mara gaskiya,
   Tana shiga whatsapp ɗinta,sai ga wani security ɗin,rai a6ace tace"Mommy kamar mara gaskiya,duk tabi waya ta garƙame da security,"
  Allah yaso shima finger print ne,komawa tayi tare da dangwalo yatsan aunty babba,whatsapp ɗin ya buɗe,
  Kaitsaye ta shiga chat ɗinsu da Hayaam,anan taga hoton da Hayaam ta tura mata,bai buɗe ba hoton saboda data a kashe take,cikin sauri hafsat ta kunna data ɗin,nan take yashiga loading yana ƙoƙarin budewa,a hankali hoton ya soma bayyana,ƙura ido hafsat tayi tana jiran hoton ya kammala buɗewa,
  Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu ji kake Daram!!Dararam!!tamkar ana buga ganga,Waro ido waje hafsat tayi agigice a matukar razane,tamkar wadda taga Zombie,hankali a matuƙar tashe tace"Kai!!!"
  Hannunta har kerma yakeyi wurin yin zooming ɗin hoton nasu ta matso dashi kusa don tagani dakyau,gaba ɗaya tagama kiɗima,wata irin zufa ce  ta soma tsattsafo mata agefen fuskarta,daƙyar take iya haɗiye yawun bakinta saboda maƙoshinta daya bushe ƙamas,juyawa tayi ta kalli Aunty baba dake ta faman mutsu-mutsu alamar zata farka daga baccin da takeyi,aikuwa cikin sauri tayi deleting ɗin hoton gaba daya,sannan ta rufe wayar,tayi wurgi da ita asaman gadon,jikinta na kerma ta fuce daga dakin,gudu gudu sauri sauri haka take tattaka stairs ɗin ƙiris ya rage ma tayi tuntu6e saboda yadda jikinta ke rawa kafkaf kamar wadda sanyi ya kama,
  Bedroom ɗinta ta koma,tana shiga ta aza hannu akai tana faɗin"Tashin hankali!In har dagaske ne abunda idanuna suka gane mun acikin hoton nan kenan hakan na nufin cewa HOSANA DA JAHAD Suna araye kuma suna a gidansu daddy!taya hakan ya faru?Kenan Ya Omar shine ya ɗaukesu?Ina wannan tsohon mutumin da mommy tasa ya kwashe su da nufin ya zubar dasu?Taya akai hosana da jahad suka kasance ƴa'ƴan uncle ɗinmu!?wacece ita ɗayar yarinyar mai kama dasu sak!dama su ƴan uku ne?Tabɗijancan,akwai matsala,
  Komawa tayi gefen gadonta ta zauna tare da kifa hannunta asaman fuskarta,hosana da jahad suna raye,suna gidan abban mu,wayyo Allah na,ina farin ciki sosai,duk da ina tsoran abunda zai biyo baya,Ashe jinina ne su!shiyasa akace rashin sani yafi dare duhu,mun cutar dasu sosai,mun zalunce su bayin Allah,mutuwa ce kawai batazo ta daukesu ba acikin gidan nan amma sunsha wahala,sun ƙuntata,tabbas Mommy mun shiga uku,idan Abba yaji,daga ni harke ba wanda zai tsira,kwara ni hukuncina mai sauƙi ne tunda na nuna masu soyayya daga baya amma ita mommy itace silar fitar dasu daga gidan nan don azubar dasu,Wayyo Allah na!,
  Yatsun hannunta sae faman kerma sukeyi,jiki na rawa ta ɗauki wayarta tare da lalubar numbar junaid ta danna mashi kira,
  A lokacin junaid yana tare dasu Uncle abusufyan,dama sai daya fara kiranshi a waya ya tambayi address ɗin inda suke ya bashi,har an kammala yi masu saloon tuntuni,anyi masu ƙunshin jan lalle a hannuwansu,daga can suka wuce shoprite siyayya,bayan sun kammala siyayyar,suka biya gidan Uncle ɗin nasu wuraren 6,saboda su kwaso wasu daga cikin kayansu Jahad da hosana wanda zasuyi kwalliyar walima dasu,
  A bayan motar junaid aka sanya trolley ɗin kayan nasu,sannan Sehrish da hosana suka shige motar abusufyan,jahad kuma ta shiga motar junaid,atare motocinsu suka fita daga cikin gidan,
  Tunda jahad ta shiga motarshi,ya ɗaure fuskarshi,dama tun wurin siyayyar yake ta shan mur yana murtuke mata fuska,amma hakan bai hana tayi masa magana ba,duk in ta ɗauko abu sai ta gwada mashi ta tambayeshi zaiyi mata kyau,daƙyar yake amsa mata da eh,ko a'a,sai dae kawai tayi murmushi ta girgiza kai,
    Kiran Hafsat na shigowa a wayarshi,yace"ki ɗauki wayar,ki amsa wayar sai ki sanyata a handsfree,"
   hannu jahad tasa tare da ciro wayar daga aljihun gaban rigarshi,picking call ɗin tayi bayan ta sanyata handsfree sannan tayi Mata sallama,
   Muryar hafsat ce ta karaɗe kunnansu"Junaid!kana ina ne"? Gaban jahad ne ya faɗi rass saboda jin muryar hafsat,duk da bata tabbatar da cewar ita bace,amma muryar tayi mata kama da ta sister hafsat,
  "Ina akan hanyar komawa gida ne yanzu hakan,"
   Hafsat tace"junaid dan Allah so nake in tambayeka,waɗannan yaran ƴa'ƴan uncle abusufyan Ƴan uku ne"?
  "Of course they are triplet,"ya bata amsa a yayin da yake ƙoƙarin juya sitiyarin motar,ya karya kwana,
  Hafsat tace"Ya sunan su"!
Juyowa yayi ya É—an kalli jahad da idanunta ke akan shi,kafin ya mayar da idanunshi kan driving din da yakeyi,a jere ya ambaci sunayensu"Hosana Sehrish Jahad"!hafsat na jin haka,a gigice ta kashe wayar,
  "kiran ya katse,"Jahad ta faɗi tana ƙare ma wayar kallo,
  "May be network ne,idan na koma gidan zan kirata,"
   "In mayar maka da wayar"?
  "A'a ki ruƙe a wurinki,idan mun isa gida zan kar6a,"
  ta amsa mashi da toh,
Gallery É—inshi ta shiga tana kallon kyawawan hotunanshi da yayi,tare da videos,yawanci duk na ban dariya ne,wasu yana a kwance,wasu ya zullo harshe waje,wasu hotunan ya kashe idanunshi,
  Dariya ta dinga yi a yayin da take kallon videos ɗinshi na tiktok,duk yana sauraron sautin dariyarta,wani lokacin har satar kallon fuskarta yakeyi,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,musamman inta tuntsire da dariya,wani sa'in hada kifa kanta saman laps dinta saboda tsabar dariya,murmushi kawai yayi tare da mayar da hankalinshi akan driving ɗin da yake yi,a haka har suka ƙarasa gida,

Bayan hafsat ta katse kiran,ta Kifa kanta asaman pillow ɗinta,tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka,dama ance dana sani ƙeya ce,

Farkawa Aunty babba tayi da wata irin matsiyaciyar yunwa,sae faman hamma takeyi,tashi tayi daga zaune tare da kai hannu ta É—auki wayarta tana cewa"Ko hayam ta tura mun da hoton?bari na duba na gani,Allah yasa dai bata manta ba,"
  shiga cikin whatsapp ɗinta tayi tare da duba chat ɗinsu da hayaam,rai a6ace taja dogon tsoki tare da cewa"Wai dama bata turamun hoton ba!harfa ƙara nanata mata nayi akan ta tura mun hoton amma bata turo ba," ta ƙarasa maganar tare da yin wurgi da wayar saman gadon,
  Saukowa tayi daga saman gadon,fita tayi daga cikin bedroom din ta sauko ƙasa,kai tsaye ta nufi kitchen,
  Batare da 6ata lokaci ba,ta shiga harhaɗa kayan da zatayi amfani dasu,bayan ta ɗaura girkin,ta ɗebo snacks a plate ta haɗo da coke mai sanyi ta dawo falo,ta zauna,tana ci tana kallo a plasma hankalinta kwance,
Chapter 23 · 0% Book details