← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 212

Sashe 101

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jikinshi sae kerma yake yi,Duk da ya ɗan ji sauƙin Zafin saboda fiffitar da take yi mashi tana kore mashi saurayen,ko gajiya bata yi baiwar Allah,Haka ta hana idonta bacci,ta zauna tana kula dashi,sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi,har lokacin yana manne da ita,
   A hankali bacci yayi awon gaba dashi,kamar wani jinjiri,gyangyaɗi ta fara yi,tana fiffitar bacci na fisgarta,idanuwan nan sunyi jawur dasu,taƙi bari bacci ya ɗauketa,saboda gudun halin da Sgr zai shiga,idan ta daina yi mashi fifitar,
   Tafin hannunta ta sanya asaman fine face dinsa,ta shafa gefen fuskarshi har izuwa saman pink lips ɗinshi,kafin ta mayar da hannun saman dogon wuyanshi,fatar wurin tayi haske sosai mai matukar jan hankali,la66anta takai asaman cheek ɗinsa ta manna mashi kiss,ɗagowa tayi tare da aza tsinin hancinta cikin sumar kanshi,daddaɗan ƙamshin dake fitowa daga wurin ta dinga shaƙa,tana faman lumshe idanuwanta,da hannu ɗaya take yi mashi fiffitar,

  Tana cikin wannan yanayin,ta galabaita sosai saboda baccin da take ji,Ƴan nepa suka dawo da wutar,a hankali fankar ta soma jujjuyawa,nan take iska ta karaɗe ko'ina na bedroom ɗin,wani irin farin ciki ne ya ratsa zuciyarta,
   "Allah na gode maka,da suka dawo da wutar nan,nayi farin ciki sosai,"
   Lokaci guda Mosquitoes ɗin nan kowa ya kama gabanshi,saboda wutar mai ƙarfi ce,iska duk ta kaɗa shaggun,
  A hankali ta lalla6a ta janye Sgr daga jikinta,ya koma saman mattress ɗin,ta dauki wayanshi ta kashe fitilar ta daura ta saman bedside drawer,gefenshi ta kwanta,tare da jan bargo ta lullu6e jikinta,banda nashi saboda ta lura dashi baisan Zafi ko misƙala zarratin,

*Boss Bature*

Wuraren Sallar asuba,Abusufyan ya farka,Saukkowa yayi daga saman Sofa ɗin,yana faman murza wuyanshi,Wurin yayi mashi zafi saboda kujerar tayi mashi karanta,ya takure kansa sosai,Ƙopar ɗakinsu yaje tare da sanya hannu yana ɗan kwankwasa ƙopar,
   Sehrish ce ta farka,saukowa tayi daga saman gadon,sai da ta fara kunna hasken ɗakin,sannan taje ta buɗe ɗakin,
  "Daddy,"ta ambaci sunanshi,
"Na'am,Daughter,"
"Wlh jiya munji jiki daddy,dama haka Yaya Rafayet ke da jin Zafi? Ga sauraye suka takura masa,jiya daga ni harshi bamu samu isasshen bacci ba,"muryarta tamkar zata yi kuka tayi maganar,
"Ae dama saida nace mashi,Yaje hotel amma yaƙiya,banji daɗi ba gaskiya,duk ban shirya ma zama gidan ba,dana sani tun kafin muzo,nasa an gyara shi,An sanya generator da A.C an kuma yi mashi feshin maganin sauro,Amma ban yi tunanin hakan ba,Wllh koni jiya naji jiki,"
  Ya ƙarasa maganar tare da cewa"Yanzu ya yake?Yana lafiya kuwa,"?yayi tambayar yana jiran amsarta,
  "Ya samu bacci,da suka dawo da wutar,bansani ba ko yana lafiya ko kuwa,Still dai bacci yake yi bai farka ba,"
  Jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa"je ki taso munshi,Yazo mu tafi masallaci,Lokacin salla yayi,"
  "Toh daddy"tayi maganar tare da juyawa ta shige cikin ɗakin,

Yadda tabarshi haka ta same shi,kwance yana bacci,
  Zama tayi daga gefen gadon,sannan ta ambaci sunanshi"Ya Rafayet"!shiru bai motsa ba,sake kiran nashi tayi"Babban yaya ka tashi,time ɗin sallah yayi,"_
  Ganin yaƙi motsawa yasa takai hannunta saman damtsen hannunshi,ta ɗan bubbugashi,dogon numfashi yaja a hankali ya soma ƙoƙarin buɗe idanuwanshi,
  Biji biji ya fara ganinta,kafin idanuwan nashi suka washe,
  "Ankira sallah,Daddy yana jiranka a palour,"
  daƙyar ya iya furta mata Okey,miƙewa yayi daga zaune,yakai hannu ya ɗauki shirt ɗinshi,Ya zurata ajikinshi,Hada ido su kayi da ita,da sauri ta kawar da idonta gefe guda,miƙewa tayi daga tsaye,ta bashi wuri don ya wuce,
  Saukowa yayi daga saman gadon,Ya kama hanyar fita daga ɗakin,
  "Adawo lafiya,"
"Okey,"yasa kai ya fuce,

Bayan fitarshi,toilet ta shiga,ta É—auro alwala,bayan ta fito ta É—auko darduma ta shimfiÉ—a,a natse ta kabbara Sallah,tana gama yin sallar ta É—ebe hijabin ta ninke dardumar ta turasu cikin wadrobe,
  Wani irin bacci take ji acikin idanuwanta,saboda jiya bata samu isasshen bacci ba,Cire doguwar rigar jikinta tayi tare da sagala ta saman Murfin wardrobe ɗin,
  Toilet ta wuce,Saboda jikinta duk babu daɗi,After some minutes ta fito jikinta sanye da Brazier,tare da Short,farare,ba ƙaramin kyau su kayi mata ba,dama dasu ta shiga wankan,
   Tunda ta fito kuma,baccin ya ya ci gaba da addabarta don ba karamin dadin jikinta taji ba,bata samu ta sanya kaya ajikinta ba,Saman gadon ta haye taja bargo cikin ƙankanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita,bata ƙara sanin inda hayyacinta yake ba,

*Marshal Omar*

Yayi nisa a cikin baccin shi,yajiyo muryar Hosana tana raira mashi waƙa,
    _Wataran wata rana_
   _za'a kaika gidana_
    _matsayin mijina_
    _kaine madara na_
_na matsu!na matsu na matsu inga wannan rana_
Cike da jan faɗa take yin wakar hada matsawa saitin kunnanshi,Rai a matuƙar 6ace ya farka,tare da wurga mata uwar harara,tana zaune saman gadon tayi zaman cin tuwo,
  A faɗace yace"Hosana!bana hanaki shigomin bedroom ɗina ba?Meyasa baki jin maganata ne"
  Hura mashi hanci tayi tare da murguɗa baki tace"Haramun ne idan nashigo ɗakin ɗan uwana,?to idan ma haramun ne,Sai ka aure ni kowa ma ya huta,"
Hannu yasa tare da dafe kanshi,yana faÉ—in"Allahumma ajirni fi masibati,wa'aklif ni khairan minha,"
  A ƙule tace"Ya Omar,Ni ce masifar"?
  Banza yayi da ita bai tanka mata ba,
  Jin yayi shiru yana kallonta,yasa tace"haushina kake ji ko?to ka kashe ni mana kowa ya huta,"
  Yunƙurawa yayi tare da miƙewa daga zaune,yace"Meyasa kike mun haka ne?kin takurawa rayuwata Hosana,A haka kikeso na"?
  Turo baki tayi tana ɗan satar kallonshi,
  "Baki son farin cikina,kullum burinki ki addabi rayuwata kib hanani sakat,Zunubin me na akaita maki ne,"
   Ashagwa6e tace"Bakomai,"
  "Kinfi so ki ga hawaye na ko,"
Girgiza mashi kai tayi alamar,A'a,
Hannu yasa ya rufe fuskarshi yana raira mata kukan ƙarya,
  Nan fa hankalinta ya tashi,tabi ta ruɗe,
  "Ya Omar bazan ƙara zuwa ba,dan Allah kadaina kukan,yanzu zan tafi na barka,"jiki na rawa ta sauka daga saman gadon tana ja da baya baya tana faɗin"ka gani ko?tafiya zanyi,bazan ƙara dawowa ba,dan Allah ka daina kukan toh,"
  Ƙasa ƙasa ya dinga dariya batare da taji shi ba,har sai da ta fuce daga ɗakin sannan ya zame hannunshi aranshi yace"fitinanna,Allah yasa Daddy ya dawo cikin week ɗinnan zansa a ɗaura mana aure,At first night,zan koya maki hankali,duk wani hauka da kike ji asaman kanki saina sauke maki shi,"
  Yana maganar yana dariya,a yayin da yake saukowa daga saman gadon,jallabiya ce ajikinshi,toilet ya wuce,

Wuraren karfe 8,Sehrish ta farka da wata irin matsananciyar Yunwa,a gaggauce ta miƙe,ta ɗauko jallabiya ta zura a jikinta,kitchen ta wuce,batare da 6ata lokaci ba,ta ɗaura girki,bazata iya jure dafa abu mai wuyar dafuwa ba,Shiyasa ta ɗaura Indomie shaf shaf ta kammala dafuwarta,A cikin plate ta kwasota ta fito daga cikin kitchen ɗin,ta zauna a palour tana ci,sai lokacin ta shiga tunanin ko'ina su Uncle suka tafi?daga fita sallar Asuba har yanzu basu dawo gidan ba,yanke shawarar kiransu tayi idan ta kammala cin taliyar,asaman table tabar plate din da sauran taliyar,ta koma kitchen ta haɗo kakkauran Tea wanda yaji madara da bournvita,dawowa tayi falon ta zauna tana kur6arshi a hankali,
Chapter 101 · 0% Book details